Showing 12001 words to 15000 words out of 74587 words

Chapter 5 - Duniya Biyu Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

12 Dec 2024

463

alamun neman tsokana yace "kai har yanzu bakasan kan dadin abinva trust me this gurl u will enjoy her, kobaka sonta kadinga biyan bukatun ka da ita make ur self a man jor dan har yanzu kai boy ne" dan yatsine fuska Waleed yayi irin na shagwababbun yaran yan gayun nan yace "I can't sleep with a woman I don't have feelings for" cikin takaici Arham yace "kai matsalan ka kenan andai daura muku aure hakkinta na kanka dolen kane wanan wlh, anyway mubar maganan tashi kaje kai salla, ni zanje gidan naje naji mai kawayen Amarya ke bukata kafin gobe mu rakakai daki wayaga su Waleed ango, am even picturing how u will be groaning kaman giw......" jefamai filo Waleed yayi Arham ya arce aguje yay wurin kofa yana dariya sanan yajuyo yace "bye saina dawo" hararan shi yayi yanadan murmushi yace "bye" yatashi yaje yay salla.
[10/20, 11:41 AM] +234 806 139 0121: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫



✍️ M SHAKUR


6️⃣




_*This novel is 500 Fanmily*❤_
_How to Subscribe to TWO DIFFERENT WORLD_
_zaki turo 500 to account 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to watsapp number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting DUNIYA BIYU MABANBANTA_



_MORROCO 🇲🇦_



_please note, any kind of magana dazaku gani at this chapter be it hausa ko english, just know that nan bangaren speak solely Arabic, larabci._
_just relax and chill, banma fara DUNIYA BIYU MABANBANTA ba, more drama, more suspense and more nostalgic moments await you, I said it and I will still say it again no one can ever be like M Shakur, my writeups are blockbuster my readers can testify to that, just surrender😘_




*_MOHAMMED V INTERNATIONAL AIRPORT, MORROCO._*


Karfe shida na safe daidai jirgin British Airways ya sauka a airport din Mohammed VI, sai kataniyar saukowa passinger suke daga cikin jirgin kana ganinsu kasan they're all stressed out sun gaji iya gajiya, saida kusan kowa yagama saukowa daga cikin jirgin sanan ahankali wata yar doguwan matashiya tasawo kanta tawajejen kofan zata fito tana goye da jakar makaranta abayanta tarike igiyoyin gefen jakan gam da hannunta, farace sol yarinyar tana sanye da wata bakar doguwan riga mara kwalliya ko daya ajiki jallabiya, sai gyalen ta datai rolling aka sai abin yay kaman hijabi dudda hakan bai hana bakin suman gaban goshinta bayyana ba sun mugun kwanta sunyi lublub kaman na yar jaririyan da aka haifo yau, tanada manyan idanuwa fararen fat da brown kwaiduwan ido dan ko kadan nata ba bakake bane brown nesu light brown, giran ta full da gashi baki mai shining kaman ta sakamai relaxer, gawani siririn dogon hanci daya ratsa tsakiyan fuskanta ya bala'in karamata kyau, lips dinta pink yirr yan fele fele kananu kaman na yaron da aka haifa yanzu yanzun nan. Sake rike igiyan jakan datake goyedashi tayi gam, ahankali ta lumshe ido iskan garinsu yawani kada mata fuska tasaki murmushi daya lotsar da dimples dinta na both sides, dama da haggu sun lume chan ciki sosai kaman rijiya tai wani irin kyau da ba'a iya misaltawa sanan tabude idanun ahankali kafin tadaga yar kafarta tafara saukowa daga kan matattakalan jirgin tana kallon ko'ina ganin bataga yan gidansu ba daidai da mutum dayaba yasa taji wasu hawaye sun taho mata masu dumi, ahankali takai hannunta kan fuskarta zata share hawayen kaman daga sama taji an kwalamata kira. "Widad! Widad!" wani irin juyawa tayi da saurinta, wata mata tagani ita kadai tadan manyan ta sosai dan akalla zatafi 70 yar tsohuwa ce tana sanye da doguwan riga itama da hijabi daya tsaya mata aciki tana tahowa da dan sandanta a hannu, wani irin tsalle yarinyan tayi hawayen suka karasa zubowa cikeda murna cikin harshen larabci tsohuwan tace "ahlan wa sahlan wa marhababik Widad" cikin wani irin muryan kuka yarinyar da tsohuwar takira da Widad tace "Assalamu Alaykum Amah" holding shoulders nata taohuwan tayi sanan tai kissing left cheek nata sanan tamata ana dama tana murmushi cikin tsantsan farin ciki da tsantsan so takara mata another peck a forehead tace "waallaykumus salam Widad, kaif? (how are you)" juyawa tayi tana kallon ko'ina na filin Airport din kaman mai neman wani abu tace "Alhamdulillah Amah" ganin yanda take kalle kalle yasa tsohuwar tai murmushi sosai batare datace mata komiba tabarta tacigaba da kalle kallenta, tana cikin kalle kallen kaman mai neman wani abu taji anrike mata hannu gam wani irin ajiyan zuciya ta sauke ta tsayar da kanta chak kafin ahankali lebbbenta suka furta "Ab.....Aby" dawani irin sauri ta juyo kaman amafarki, wani magidanci ne tsaye a bayanta yana rikeda hannunta yana sanye da jallabiya fari fat, kafanshi sanye da skos na maza, sai kanshi daure da rawanin larabawa sai farin gilas a idanunshi da daga gani kasan na kara karfin ganin idanune, kana ganinshi kaga tsantsan balaraben morroco kyakkyawa ajin farko, wani irin fashewa da kuka tayi haka Allah yayi ta tanada saurin kuka, very emotional mutum ce ita, sanan duk duniya batada wanda takeso kaman babanta saisa kodaga nesa takanji a jikinta yana kusada ita, fashewa da kuka sosai tayi tace "Abyyyy" anatse magidanci yasakin mata wani kyakkyawan murmushi yakai fararen hannunshi yadaura kan fuskarta ya share hawayen datake tass kafin yarungumeta ahankali yana bubbuga bayanta anatse irin na manya dinan cikin muryanshi na dattawa yace "marhababik, marhababik" sunkai kusan 5min tana jikinshi har lokacin tana sheshekan kuka sanan yadago ta, hannayenshi yasa akan fuskarshi yay cupping face dinta cikin tsantsan so yace "kidayra? (how are you)" ahankali tace "Alhamdulillah Aby" gyadamata kai yayi yace "masha Allah" yanuna mata mutanen dake tareda shi alamun ta gaidasu, ita sai a lokacin nema ta lurada su dazu mahaifinta kawai idanuwanta suka gane mata, yangidansu ne dan gidansu family house ne babban gaske, wata balarabiya dake kusada mahaifinta ta gaida ta hanyar cewa "Assalamu Alaykum Um" sanan ta kalli sauran tacemusu "Assalamu Alaykum" amsata sukayi ko wanne da murmushi kan fuskarshi banda matar dake kusada mahaifinta dako amsata batayiba, cikin harshen larabci mahaifin nata yace "mutafi gida" kasancewan ansan koshi waye agarin saisama aka bari suka shigo har filin jirgin yasa suna zuwa akaimata clearing komi suka shiga wasu manya manyan jeep farare sukai gida, itadai tana cikin na mahaifinta kusada shi sai matar data kirada Amah gefen ta, mahaifinta kuma na gaba da direba, sukabar airport din.





Agaban wani babban tangamemen gida sukai parking, irin gidan nan da aka ginashi na usulin culture larabawa, an zagaye gaban gidan da flowers iri iri daban daban kalolinsu kaman kazo ka kwasa ka gudu, tun kafin tafito daga cikin mota takejin sautin ganga na mandiri ana bugawa ana wake, murmushi tayi ta kalli mahaifinta cikeda so duk lokacin dazata dawo daga school sai Aby yahada mata walima na kayatarwa daban mamaki dan tarbanta kadai, bude kofa tayi tafito sanan tamikama kakanta hannu tafito daga motan Aby yafito yana kallonsu, kowa ya sassauko daga cikin motar akai cikin gidan, babban compound ne da girman tsakar gidan zaiyi girman primary school ana raye raye ana wake ana, ana rawa, ganin Widad din da iyayen ta sun shigo yasa mawakin yataho gabansu da yan amshin shi suna buga mandiri suna rera wake yace "kaifa Anti? Wa kaifa ji'iti? Marbabiki Ya Widad binti Othman Benjalloun" wani irin murmushi tayi ta washe fararen hakoranta tana kallonsu tana kara rike igiyan jakan makarantan ta abubuwa like this nabata peace sosai yanasa tana tunawa da mahaifiyar ta, ahankali mahaifinta ya kalli fuskarta murmushin dayagani kwance kan fuskar yasa yaji hankalin shi ya kwanta sosai, flowers ya karba a hannun daya daga cikin ma'aikatan gidan sanan yazo ta gabanta yabude flower ya sanya mata flower a wuyanta cikin harshen turenci dakeda Arabic intonation yace "wercome bark homer Widad" rungume mahaifinta tayi tana murmushi sosai tama kasa magana, ganin abun nasu bamai karewa bane yasa Amah cikin harshen larabci tace "to mayyar mahaifinta tadawo fa yanzu mun shigesu, saki ubanki muje daki kiyi wanka kizo ki chanza kayan nan kizo kici abinci ki kwanta kiyi bacci" Amah tai maganan tanajan hannunta, binta tayi tajuyo tama mahaifinta waving hannu sukai cikin gida, dan murmushi mahaifinta yayi yajuyo ya kalli matarshi datai kini kini darai cikin harshen larabci yace "kawomin shayi dakina" yay maganan tareda wucewa yashiga wani wakacecen falo irin traditional falon larabawan nan namasu kudin gaske, babu kujeru adakin sai wasu irin filulluka hadaddu set set da ake kishigada akansu gawani wargajejen hadadden carpet daya zagaye ko'ina a falon sai uban laushi kaman da fatar jarirai akayi sai shisha pot asalin pot din na larabawa, dan daidaikun asalin gidan rikakkun balarabe ne zakaje da bazaka ga shisha pot a dakunan su ba.


Othman Benjalloun dattijo ne dakeda shekaru 62 aduniya, bala'in mai kudine agarin morroco, agabaki dayan garin ance bayan Mohammed VI wanda yake number 1 mai kudin garin, Othman shine the second richest person in the whole morroco, yana harkan banking insurance, yanada bankuna yanada kasuwanci da dama, matayenshi uku aduniya, Mahaifiyar Widad itace ta farko wanda a yanzu ta rasu, sai matarshi da biyu wacce Widad takira da Umm, sai ta ukun wacce yasaka sabida cutar da Widad datasoyi Allah ya tona mata asiri, yarshi daya aduniyan nan tal Widad, Allah baitaba bashi haihuwaba sai akanta, itama din harya cire rai dan yaga yay mata uku duk shiru yace halan daga shine sai kwatsam ga mahaifiyar Widad da ciki, yakusan karaman hausa a lokacin daya gane tanada ciki saisa da aka haifamai mace saiya radamata suna WIDAD ma'ana love, yana bala'in son yarinyar so mai zafi, gashi kana ganin yarinyar kaganshi kaman yay kaki, ko office zashi da yarshi da mahaifiyar ta yake zuwa sabida yadinga sata a ido kodayaushe, indan tafiyan fitanshi daga gari ce ta taso saidai yadauki mahaifiyar ta da ita dan bazai iya nisa da itaba saisa itama yarinyar ta taso tana bala'in son mahaifinta, tanada shekaru 18 mahaifiyar ta tarasu daga ciwon kwana daya tal, Widad takusan hauka take mahaifin nata yafita da ita da kyar aka samu taji sauki aka dawo da ita gida tadinga kuka daga karshe taroki mahaifinta tunda tagama sakandire yakaita wata kasar tai University intana gida tunawa da mahaifiyar ta take sosai, da kyar da kyar saima dayaga ta kwanta tana ciwo sanan ya yarda yakaita Egypt yamata komi yasaman mata admission in datake karanta mass communication.








Wani hadadden babban daki suka shiga itada Amah dake upstairs, dakin wakacece ne babba dayasha carpet tako ina mai bala'in kyau dan duk wanda yasan morroco yasansu da sana'ar kera carpet su sayar, gadaje biyune hadaddun gaske masu rumfa da aka zagaye da labulaye farare masu kyau acikin dakin babba da karamin gado, tun bayan mahaifiyarta ta rasu tadawo dakin kakanta da zama kakanta ne kadai takejin dadin zama da ita dan tana sonta kaman ne, jakanta tacire ta ijiye akasa sanan ta taka zuwa gaban wardrobe din dakin dan neman kayan dazata saka, Amah kuma ta ijiye sandarta agefe ta zauna ahankali kan gadonta tanabin bayan Widad din da kallo, shekara daya kacal dabata ganta ba amman saitaga ta chanza mata a ido sosai, dan murmushi tasaki tana tunanin Widad da aka haifa jiyane ta girma haka, batare da Widad tajuyo ta kalleta ba cikin harshen larabci tace "Amahh why are you smiling? Tunanin me kike?" tai maganan tareda juyowa hannunta rikeda wata jan kaftan dayasha ado kaman irin dogayen rigunan India, hararan ta Amah tayi tace "wuce kije kiyi wanka, favourite dinki nasa aka dafa tagine, rice da herbs saikuma flat bread" washe baki tayi ta yarda rigan hannunta kan gado da gudu tai bayi, kyalkyacewa da dariya Amah tayi tadauki sandarta tawuce tafita dan tabbatar da yan aikin sun jera komi a tsakiyan falon barinma wanda tasan yar jikallenta tafiso. Dan aikin datagani awurin yana ijiye plate dake dauke da dry fruits tacema "ina flat breads din danasa ku gasama Widad?" cikeda girmamawa yace "yanzun nan jibril zai karasa baking dinsu yafito dasu" zata sake magana taga Aby na saukowa daga sama shima da hannu tama dan aikin alamu daya wuce yabata wuri, da sauri yawuce bayan ya gaida Aby, saukowa daga benen Aby yayi yazo gabanta mahaifiyar tashi yace "Assalamu Alaykum Amah" "waallaikumus salam" ta amsashi tana zama, ahankali shima ya zauna gefenta yadau inibi daya yajefa abaki yanadan bin wakan da akeyi awaje cikin kwanciyan hankali, ganin yanda yake farin ciki yasa mahaifiyar shi takira sunan shi. "Othman" anatse yajuyo ya kalleta tareda ijiye inibin daya so jefawa cikin baki kan faranti, dan gyara zama Amah tayi da kyau kaman yanda shima ya natsu yana jiran yaji mezatace mai, cikin muryanta na tsofaffi tace "wace shawara ka yanke akan maganan damukai dakai jiya?" fuzar da iska yayi fuskarshi ya dan nuna damuwa yace "I don't know Amah, all I know for sure is bazata koma wanan makarantan babu aure akanta ba, ai nai mata kokari dana iya nabar y'ata wacce ita kadai ce Allah yabani aduniyan nan taje chan wani kasa tana karatu ba, banda hakama Amah bakiga yanda alamomin girma suka bayyana ajikinta sosai ba?" gyadamai kai Amah tayi cikeda gamsuwa da bayaninshi tace "nagani" yace "burin kowani mahaifin ya killace yarshi intana wanan matakin ya aurar da ita, na kashe all meetings danake dashi throughout this week, hutun sati biyu kacal gareta, nariga na sanar da iyayen Ahmad zasuzo anjima da daddare we are having engagement ceremony tonight, nikah zai biyo baya nanda sati in 7days time dudda a al'adance yakamata bayan engagement ceremony da shekara ne ake biki but I can't wait that long" ya karashe maganan ahankali saikuma yasaki dan murmushi mai kama data bakin ciki ya kalli Amah yace "Amah anya zan iya rayuwa kuwa in bana ganin y'ata?" yasakeyin murmushi hawaye na taruwaa idanunshi yace "Amah bantaba fadamiki wanan ba sabida nasan fada zakimin kice nabar yarinya tai concentrating a karatu kaza kaza kaza, kinkosan cewa ban taba kaiwa sati daya cur batare danaje Egypt ba dukko nisan shi?" ware ido Amah tayi cikeda mugun mamakin shi dan tasan dan danta business man ne yana yawan tafiye tafiye but bata taba sanin haka yake zuwa wajen Widad a makarantan ba frequently ba, one thing she knows for sure shine she always wondered ayanda Aby keson Widad kaman zaiyi hauka ya iya hakura hartai shekara a makaranta bai gantaba, maganan shi ne ya yanke mata dogon tunanin dataje yace "kinsan yanzu intai aure bazan iya dinga zuwa haka ina ganota bako" ya share hawayen dayadan zubomai da sauri yay murmushi yace "Amah banson ko kadan Widad ta wahala aduniyan nan, saisa nake aiki nake neman kudi sabida ita, dazaran na aurar da ita I believe lokacin tadawo cikakiyar mace, zanyi handing all over my properties, companies komi da komi nawa, all my assets to her ni zanyi retire na huta, shi will be managing everything, komi da komi dana mallaka nata ne Amah dan banda wani magaji aduniyan nan sai ita, I make sure nabata komi ranan da aka daura aurenta agaban mijinta da kowa, innai haka hankalina zai kwanta dan nasan tanada komi bazata taba wahala ba, yakika gani Amah?" kumatun shi Amah taja cikeda murmushi tace "brilliant thought, kasan I'm always proud of you Othman kai d'a ne nagari mai adalci, ina mai goyamaka baya dari bisa dari akan wanan hukuncin daka yanke, mu munriga munyi rayuwanmu aduniyan nan, munci duniyan mu da tsinke, mutuwa yauko gobe takan iya daukanmu, inhar bamu bama Widad da yanzu tafara girma komi damuka mallaka ba maimuka yi?" dan murmushi tayi tace "nima zinaruka na tunna lokacin aurena da mahaifinka, gabaki daya daman ita nakema ijiyansu ranan aurenta da izinin Allah zan bata, Allah yamaka albarka Othman Allah kuma yasanya ma auren albarka, na yarda da Ahmad sosai, nakuma san yanda yake sonta tun tana yar yarinya" dan dariya Aby yayi yace "kinsan mahaifinshi yacemin daya fadamai maganan engagement din danayi yakusan suma kinji fa yarinta" "ba yarinta bane tsabagen so ne da kauna ta gaskiya" suka kwashe da dariya irin ta manyan nan kafin tai hugging nashi su a dariya atare gwanin ban sha'awa.
[10/20, 11:41 AM] +234 806 139 0121: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫



_*DUNIYA BIYU MABANBANTA*_

✍️ M SHAKUR





7️⃣ & 8️⃣



_*This novel is 500 Fanmily*❤_
_How to Subscribe to TWO DIFFERENT WORLD_
_zaki turo 500 to account 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to watsapp number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting DUNIYA BIYU MABANBANTA, you can also send MTN card 500 idan bakida banki_



FREE PAGE
Fitowa tayi daga wanka daure da blue towel ganin Amah bata daki yasa tawuce tadau doguwan rigan da taciro ta shirya tsaf cikin rigan takarasa gaban dressing mirror taja kujeran ta zauna hannunta tasaka ta warware farin karamin towel din dake kanta gashinta ne yazubo daya saukan mata har waist gashin baki sidik dashi so silky irin gashinsu, wani brush tadauka dake gaban madubin tai brushing gashin dakeda sanstsi gashin nakara tsayi sosai brush kawai yawo yake acikin gashin, murmushi tayi ta kalli kanta dudda babu kwalliya akan fuskarta amman tai shegen kyau ribbon tadauka ta daure gashinta ta dunkule jelan gashin sanan ta mike tai wajen jakanta budewa tayi taciro mac book dinta da wayanta kiran iPhone wajen socket tayi ta makalasu ajikin chaji sanan tafito daga dakin kanta babu dan kwali, karasawa wajen mahaifinta tayi da duk suko juyo suna kallonta jin tafiyan ta murmushi tayi takaraso wajen ta zauna kusada Aby tana dafamai kafa tace "Assalamu Alaykum" "waallaikumu sallam" Aby ya amsata yana ijiye kofin shayin hannunshi akan farintin kofin, ashagwabe tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login