Showing 18001 words to 21000 words out of 74587 words
ya zauna agabanta yana kallon yanda take share hawayen dasuka kasa daina tsayawa cikeda damuwa yace "why are you crying? I thought today suppose to be the most happiest day of our lives Widad we've come a long way, we are getting married in 7days" shiru yayi yana kallonta ganin takasa daina kukan, ahankali yace "are you missing your Mum?" dago jajayen idanunta tayi ta kalleshi duk duniyan nan banda Aby no one understands her like Ahmad, intai kuka yasan kukan me intai bakin ciki yasan name hakama intai murna, saisa take sonshi, ganin takasa bashi amsa sai kallonshi take wasu hawayen nasake fitowa yasa yadawo ta saitin inda take zaune ya zauna a gefenta tareda lankwashe kafa yay dan shiru sanan ya kalli sararin samaniya yana bin taurarin dake sama da kallo, cikin yar lallausan murya yakira sunanta. "Widad look up 👆" yanda yay maganan yasa ta dago kanta ta kallai ganin sama yake mata pointing yasa ta kalli saman itama yace "kinga wanchan taurarin dayafi kowanne cikinsu haske" shiru tayi tana kallon tauraron dayake nunama ta, yace "let's take your Mum to be that tauraron, trust me your Mum is up there tana kallonki, and believe me inna gayamiki abu daya datafi tsana aduniyan nan shine taga hawaye nafita daga precious eyes dinki, banda hakama ni she will be angry with me" da sauri ta kallai irin kallon tambayan nan, dan juyowa yayi ya kalleta shima yazubamata kyawawa fararen idanunshi yana kallon fuskarta cikin tsantsan begen so yace "I promise Mum tun kafin tarasu akan I will always make u happy, bazan taba barin yarta ta zubar da hawaye ba gashinan yau I couldn't keep my promise sai kuka kike, am a bad person I couldn't keep my word am a bad person" yafadi shima kaman zaiyi kukan yana kallon kwayar idanunta, ahankali ta girgizamai kai tace "you are not a bad person in fact you are the best human I've ever come across in this world" takai hannunta ta share hawayen tass tana kallonshi Kaman yanda shima ke kallonta kaman ya tsaga jikinshi yasata aciki yakeji kawai yahuta, tun yana University yanadan saurayi yake son Widad tun ranan da Abban shi yazo dashi gidan wajen Aby dan Aby da Abban shi na business tare sosai, lokacin Widad kaman 11yrs take tun lokacin yake sonta, kuma yana bala'in alfahari da ita dan yasan bata taba kallon wani namiji ba balle harta tsaya kula wasu samari dudda tanada mugun kyau da farin jini but shi kadai takeso, yazauna yayi zaman jiranta all this while dan alkawarinsu was sai tagama makaranta zai jiranta sanan sai suyi aure amman hakanan yan kwanakin nan yaji bazai iyaba saisa yadami Abba yazo yasami Aby akai maganan saka rana da biki, yau kuma daya ganta hakanan yakeji kaman ma bazai iya jira kwana bakwai dinan ba kaman a daura auren yanzun nan yakeji a ranshi jiyake kaman za'a kwace mai ita. "Ahmad" Widad takirashi ganin kaman yay nisa atunani, dan murmushi yayi yace "Widad" murmushi tayi tace "tunanin me kakeyi?" shiru yayi yana kallonta kaman bazai bata amsaba saikuma yace "tunanin ranan da am gonna make u mine, namiki ciki" "subhanallah" tafadi da sauri tareda tashi tsaye zata gudu dan kunya taji dan tunda suke tsawo shekaru 10 kenan yanzu baitaba mata maganan banza hakaba, karap taji yarike hannunta yatashi tsaye shima turo baki tayi batare data kalleshi ba tace "ka sakeni" batare dayasake taba yazo ta bayanta yace "kinsan in kika haifamin mace sunan Mum dinki zamu saka ko Widad" akunyace tajuyo ta runtse ido ita adole kunya take ta kalleshi tanaso ta fizge hannunta tace "ni naji to kasaken natafi kaga ana jiranmu ko" dan bakinta yake kallo yanda idanunta ke arufe tana mai shagwaba, ahankali yakai bakinshi saitin nata wani abu na pulling dinshi kaman zai mata kiss saikuma kawai ya rungumeta tsan tsam ahankali yace "I love you so much Widad, I love you" "Widad" Sabeeha ta kwalamata kira da aka turo takirasu a mugun tsorace tabude idanunta tareda fizge jikinta daga jikin Ahmad, Ahmad baitaba rungumeta ba sai yau bama tasan ya akayi hakan yafaru ba dan abin yafaru cikin few seconds ne, sakinta Ahmad yayi ya kalli Sabeeha da idanunta kyam akansu yace "baki iya sallama ba" juyawa tayi tareda watsamai harara tace "baka koyamin ba, dayake kana batama Aby y'a ai dole kace haka" ta juya tafice abinta, a mugun tsorace Widad ta juyo ta kallai zatai magana kuma takasa sai kuka tace "mesa ka rungume ni kaga zata fadima Aby ko" yana bala'in son yaga Widad ta rude bala'in bala'in kyau take, ganin murmushi yake yasa tafashe da kuka, ganin yanda take kuka tana bubbuga kafa akasa yasa yace "wlh in bakimin shiruba kamaki zanyi naita kissing inyaso su Aby sazosu ganmu ahaka kinga a daura auren mu ma yau ko dan ansan mun kosa" yay maganan bakodar atattare dashi shiru tayi takasa cigaba da kuka murmushi yayi yazaro handky ya mika mata yace "wipe those tears mutafi" karba tayi ta share tass sanan yakama hannunta yarike suka wuce suka sauka daga rooftop din.
[10/20, 11:42 AM] +234 806 139 0121: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫
✍️ M SHAKUR
9️⃣
_*This novel is 500 Fanmily*❤_
_How to Subscribe to TWO DIFFERENT WORLD_
_zaki turo 500 to account 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to watsapp number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting DUNIYA BIYU MABANBANTA_
_*NIGERIA*_
Abuja
Washegarin ranan biki
Misalin 9 na safe yafito yana sanye da fararen kaya, farin t-shirt sai farin wandon shadda ajikinshi da farin slippers din kafarshi, yana tafiyan nan tashi dai dai yana kallon yanda ma'aikatan gidansu ke aiki ana kara gyara gidan da aka gama biki jiya aciki kaman ba'ayiba, dan gajeren tsaki yaja yawuce ya shiga flat dinsu, babu kowa a falo sai wasu mata guda biyu dake sanye da uniform suna aiki daya na goge Centre table dayan na jera abinci dining, gaidashi duk sukayi amman ko kallonsu ma baiba yawuce yahau stairs dorect dakin dayasan zai sami Mom dinshi yawuce, bude kofan yayi bayan yay knocking akan dadduma yaga Mom hakan yasa yamaida kofar kawai yarufe ya shigo ciki hawa kan gado yayi yay kwanciyarshi tareda lumshe ido kaman mai jin bacci yay shiru kana gani kasan yaje dogon tunani. "Dan Yaro" Mom ta kirashi tana linke hijabin jikinta bayan ta tashi daga kan dadduman, dago kanshi yayi ya kalleta yace "morning Mom" "morning katashi lpy, daman yanzu nake shirin naje naduboka, kaci abinci?" yatsine fuska yayi yana tashi yana zama batare daya amsataba, daukan dadduma tayi ta linkeshi shima sanan ta ijiye ta taho ta zauna gefenshi abakin gadon takai hannunta ta daura akan kunnenshi tashafa tace "Dan Yaro how do you feel? Yau zaka koma gidan amaryan ka" yatsine fuska yayi batare dayace komiba murmushi tayi tace "muje dinning kai breakfast" tai maganan tana tashi tashi yayi shima yabita suka sauka kasa dinning sukayi tahadamai shayi yasha ba laifi dan yau yatashi feeling strong, ta zubamai Irish da source fork yadauka yafaraci duk sukai shiru.
Ahankali take tattakala matattakalan benen, tun kafin ta sauko take kallonsu barinma Waleed, ko tari batayiba takarasa saukowa kamshin turarenta yasa Mom ta dago kanta ta kalleta, tai bala'in kyau tana sanye cikin wata dark brown atampa da milk color na English wax, tai kyau irin hajiyoyin matan nan, washe baki Mom tayi tareda ijiye spoon din datake cin abinci dashi tace "ina kwana Adda kin sauko" gyadamata kai Ammi tayi still looking at the Waleed, ahankali yadan dago kanshi ya kalleta hada ido sukayi saikuma ya dauke kai murya chan ciki yace "good morning Ammi" "morning" ta amsashi atakaice tawuce kan dogon kujera ta zauna tareda daukan remote ta chanza tashan zuwa African magic taga ko anfara series dinan the Johnson's badan komi takeson shirin ba saidan bada dariya da Nigerian series din keyi.
Ajiye fork din Waleed yayi yadau tissue yana goge baki Mom tace "badai harka koshi ba Waleed ai bakaci komiba anan ga peppersoup ga yamballs you haven't touched any" ashagwabe yace "nina koshi, thanks Mom" yay maganan yana tashi daga dinning yamaida kujeran yafito zai fita batare daya kalli Ammi data bishi da kallo ba, har yakai kofa zai bude Ammi ta kirashi. "Waleed" juyowa yayi ahankali ya kalleta suka hada ido saikuma ya dauke kai, tun yana yaro haka yake in yana fushi da Ammi bai iya kallonta saidai kosunhada ido ya dauke kai kawai kuma bazai taba cemata komiba itakuma dazaran yafara mata haka tasan fushi yake da ita, ganin ya tsaya yasa tace "zonan" zuwa yayi ahankali ya tsaya agabanta yana kallon tiles yace "gani Ammi" gefen ta ta nunamai tace "zauna anan" murmushi Mom dake binsu da kallo tasaki tacigaba da breakfast dinta tana girgiza kai ita ya yarta har mamaki take bata, tanason Waleed fa kaman ranta amman rigimanta yafi karfinta.
Binshi da kallo Ammi tayi daga sama har kasa babu alamun wasa tattare da ita fuskarnan ta daureshi tace "were you sick ne jiya?" juyowa yayi ya kalleta baki yabude zaiyi magana tace "karka sake kamin karya, I ask a question, where you sick yesterday? Maiya sameka jiya?" ta tambaye shi kai tsaye, shiru yayi kaman ba zaice komiba saikuma yace "zazzabi ne nai amai once but am fine now nasha magani" ji Ammi tayi ranta inyay dubu yabaci tace "and u don't think it was important to let me know ko, inda bantambayeka bama yanzu da bazaka fadamin ba eh?" shiru yamata baice komiba tsawa tadakamai cikin fushi tace "am talking to you kamin shiru Waleed, why didn't you tell me u were sick?" cikin fushi shima yace "wai Ammi for godsake when will you stop treating me like a child eh? Komine saina fadamiki? Yes I was sick yesterday, and I treated myself and I feel much better" yay maganan tareda tashi cikin fushi yay hanyar kofa, cikin fushi Ammi ta kwalamai kira. "Waleed, Waleed, Son, Son" ko juyowa Waleed baiyiba yabude kofa yafice abinshi, cikin fushi Ammi ta kalli Mom dake dinning tace "kina ganin abinda danki kemin ko?" ture plate Mom tayi tace "maiya miki? Ai gaskiya yafadi kinbi kin matsama yaro, kin hanashi sakewan rayuwa, kwaf kwaf kikebin lamuran yaron nan, ki maidashi ciki kamai kihuta haba, kin haba yaro sakewa, kina mai dashi kaman jariri, ki ciro nono ki dinga bashi mana karewanta" cikin fushi Ammi tace "ni kike gayawa haka?" itama cikin fushi dan dama tadade tana tike da Ammi tace "mene fadi? Ba gaskiya bace, kin kama kin aurar da yaro batare dakin shawarce shiba ko tambayan ra'ayinshi inda wasu yaran ne angayamiki zasu yarda ne, wlh dawasu ne da kinga tijara, ba dole yaro yadinga fushi dakeba" tai maganan tana ijiye tissue tai stairs da fushi, cikeda mamaki dakuma fada Ammi tadaga murya tace "nizaku hadewa kai kujuyawa baya, dani kuke fushi?" tai shiru saikuma tace "but I choose the best girl for him kema ai kinganta, I want jika, am so lonely I need jikoki dazaici sunan mahaifin Waleed, laifi nayi danna zabama Waleed mata shine kuka fushi dani daga ke har shi?" yanda tai maganan araunane yasa Mom taji wani tausayinta tasan yayarta sama da kowa and tasan Waleed is her weak point dazaran yaron nan yafara fushi da ita har ciwo kamata yake nan da nan BP ta zai tashi, dayake shi Waleed din danyan kai har yanzu bai sakeshi ba baitaba lurada shine weak point din mahaifiyar shiba hasalima kullum gani yake mamanshi is harsh dan Ammi is too strick dashi gata batada fara'a ko kadan Mom tafita fara'a nesa bakusa ba, saisa all abokanenshi sunfi sabawa da shakewa da mom kan Ammi. Ahankali Mom tajuyo ta kalleta tace "Adda baki gane abinda nake nufiba nasan kowani hukuncin kika yanke akan Waleed is for the best, but yayan yanzu bahaka suke ganiba, naga Ilham yarinya mai kyau, ga ilimi ga kunya, ko makaho ya ganta yasan kin zabo sanan kin dirzowa danki mata, but the question is does your son see it that way? No" ahankali Mom tace "ki sauke wanan harshness dinan kije ki lallabo yaron nan kinmai aure and he feels bai shiryama aure yanzu ba, just patch things up with him kinfini sanin yanda zaki hakan, Adda solve this problem once and for all please inba hakaba ke zaibama kunya inya fara wulakanta yar mutane" Mom na maganan tajuya tai sama abinta, bin bayanta da kallo Ammi tayi harta bacemata daga gani sanan takoma ahankali tazauna akan kujera tabuga uban tagumi takai kusan minti ashirin ahaka azaune saikuma ta mike kaman wacce aka tsikara tai waje.
Flat din Waleed tayi bude kofa tayi ta shiga da sauri Waleed dake zaune yana kokarin kunna system dinshi yadago kanshi ganin Ammi ne yasa yamike tsaye ahankali, maida kofar Ammi tayi tarufe cikeda bala'in masifa tace "okay Waleed am now the villain in the story ko, dani kake fushi eh? Mena maka?" cikin kulewa irin exactly child and mother's fight dinan Waleed yace "ni nace kinmin wani abune? Akwai abinda kikace nayi dabanyi ba? U arrange marriage for me I didn't say a thing, kince I shouldn't go to office and am right here at home Ammi what else?" yay maganan idanunshi sunyi jajir kana ganinshi kasan yacika fam, yanda taga yanayinshi yasa hankalinta yawani irin mugun tashi, daura hannayenta akirji Ammi tayi cikin mugun mamaki tace "Waleed, Son!" juyawa yayi da sauri muryanshi narawa yace "ni bakimin komiba Ammi, I need a nap" yana maganan yay hanyar dazai sadashi da bedroom dinshi da sauri Ammi tabishi kafin yasa hannu yabude kofan ta fizgoshi tace "Waleed am talking to you" janyoshi tayi with so much love tai cupping face dinshi tana kallon fuskarshi duk yanda takaiga son su hada ido yaki bata daman hakan, cikin wata irin raunanniyan murya hankalinta inyay dubu yatashi ganin da gaske yaronta fushi yake da ita tace "Waleed dani kake fushi ni mahaifiyarka eh?" cikin muryanshi datahau rawa sosai kaman wanda ke shirin fashewa da kuka yace "Ammi nifa bance miki komiba I did exactly as you said please lea.......leav..." yakasa magana sai hawaye masu dumi, ji Ammi tayi kaman ta kurma ihu da sauri ta rungume shi tace "am sorry, am so sorry Waleed u are crying because me, ni mahaifiyar ka ke saka kuka, no no no, banda burin dayawuce insaka farin ciki aduniyan nan, I never knew my actions hurt this deep, Waleed, my Waleed kallen" tai maganan tana dago fuskarshi daga jikinta, fuskarshi harja tayi sabida hawaye, tsabagen rudewa dan kwalin English atampa dake jikinta hakan yasa gashinta dakenan da furfura anmata kitso shiku ya bayyana tadaura akan fuskarshi ta shiga sharemai hawayen tace "is okay, stop crying, stop crying Son, ya isa" bude bedroom dinshi tayi ta shiga tana rike da shi kan sitter gaban gadon ta zauna ta zaunar dashi tareda rike hannunshi kaman zatai kuka tace "Waleed I never meant to hurt you, kome nayi I did it for you dudda nasan my approach might seems wrong but that is me u know, Waleed kalli kaina" takamo jelar gashin kanta ta nunamai tace "Waleed furfura, am not getting younger anymore, tsufa nike kullum the same way yanda mahaifinka yarasu ya barmu haka nima zan rasu watarana" tadanyi shiru dan batason tai breaking down sanan tadanyi murmushi tai cupping face din Waleed din tace "Son you know about my hypersensitive situation, kaike monitoring minishi kana bani magani, masu irin condition dina can die any moment, na zauna nai tunani na kalleka nakuma karance ka Waleed matama basa gabanka sai aikin gidan marayu, and inaso kai aure inaso naga y'ayan ka my grandchildren kafin nima nabar duniyan nan, batun yau ko jiya nake nema maka mataba, nafara nemama matan aure tun kana 25yrs amman banga wacce tamin ba sai akan khadija, Khadija tayi sauka, tagama karatun ta lawyer ce mai zaman kanta, gata yar gidan mutunci, kuma ranan data fara ganinka na fahimci tana sonka so bakadan ba, inhar ban zabamaka irin matar nan ba wa zan baka maka? But I am sorry, na dauka na isa dakai but I guess I am w......" hannunshi yasa yarufe mata baki tareda girgiza mata kai yace "Ammi kin isa dani, I just didn't wanna get married now ne, Ammi am too young, just 28 fa, and ita yarinyar she is 26 da 2yrs fa na girmeta" dan murmushi Ammi tayi ganin ya sauko ta rungumoshi ta hanyar daura kanshi kan shoulder dinta tace "age is just a number Waleed, nasan tsoro kake kan baka wani girmeta sosai ba bazata girmamaka ba, and you being 28 itakuma 26 baya nufin hakan I know yarinyar dana aura maka tanada dattako she will respect you kaman her king son, are we good now kahakura kadena fushin?" gyadamata kai yayi ahankali yace "yes" dago kanshi tayi ta manna mai kiss agoshi tace "thank you, Allah yamaka albarka, yanda ka rufamin asiri baka kunyatani ba kaima Allah bazai taba kunya taka ba duniya walahira, Allah yakareka daga makiyanka, akwai kaya na mussamman dana maka ordersu daga Morocco 🇲🇦"
"Sherwani masu kyau zakayi kaman wani dan India, dama yarona badai kyau ba ballema yasaka sherwani nan, dan murmushi kawai yayi, ahankali ta shafa kanshi tace "nagode kaji, ka rike amana kaji, ka kulada matarka, Uncle dinka ya shiga villa wai yanada meeting da president saisa baka ganshiba kafin anjima by 8 yatafi Airport dan jirgin su 10 zai tashi" gyadamata kai yayi kafin yatashi ahankali kan jikinta da sauri tace "ina zaka?" ahankali yace "waya zan dauko nakira blood" shiru tayi tareda binshi da kallo kaman yautafara ganinshi, wayan yadauko yadawo yay fillo da kafafunta ya kunna wayarshi yay dialing number Arham wayan yaji akashe hakan yasa ya ijiye wayan Ammi dake binshi da kallo tace "ya akayi? Baka sameshi bane?" dan tabe baki yayi yace "wayanshi akashe" gyadakai Ammi