Showing 3001 words to 6000 words out of 74587 words

Chapter 2 - Duniya Biyu Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

12 Dec 2024

461

ma su karasa sukaga har anbude Gate din Abdul da Hasim yagani suka bude suna ihu ango ango ango, samari ne dudda basukai shi girma ba amman suna yanayi dashi saidai yafisu kyau nesa ba kusaba, parking direba yayi sukuma suka shiga maida gate din suna rufewa, saukowa yayi daga motan ya ballamusu harara suka kwashe da dariya, Hasim yace "Ya Waleed muje ka chanza mun karbo maka kayanka kaci gayu wife dinka needs u" baice musu komiba yawuce ya shiga flat din wajen suna biyeda shi, anan falo ya barsu suna hayaniyan su baice musu kalaba yawuce bedroom, kayan jikinshi yacire ya shiga bathroom wanka yayi yafito daure da towel, ayanda yake tafiya zaka gane babu abinda kemai dadi, shafa mai yayi ya shirya cikin wata bugaggiyar shadda mai light ruwan toka ta mugun haska shi sanan yadau turare zai fesa yaji anyi knocking kofar saikuma aka bude aka shigo, wata mata ce fara babba sosai tai kama da matar dazu saidai bata kaita girma ba da manyanta ga dukkan alamu kanwarta ce, ahankali yace "Mom" murmushi tayi ta maida kofar dakin tarufe takaraso gabanshi tana murmushi sosai tana binshi da kallo tace "wow kaga yanda kai kyau kuwa Dan Yaro na, I wish mahaifin ka na raye yaga wanan ranan da Walilin shi zaiyi aure, iyye kawo turaren kaga na fesamaka" karban turaren tayi daga hannunshi tashiga fesamai tana kallon fuskarshi ganin baya kodan murmushi, ajiye turaren tayi sanan takama kafadar shi ta zaunar dashi kan gado sanan tazauna gefenshi ahankali tareda saukar da ajiyan zuciya, hannunta tadaga tadaura ata bayanshi takamo kafadarshi hakan yasa ya kwanta da kanshi kan kafadarta ahankali sukai shiru tanajin yanda yake saukar da ijiyan zuciya sanan tafara magana. "dagani sai Adda umman mu ta haifa, Umma nada cikina Abban mu yarasu, awahale Umma tahaifo ni inada shekara 7 aduniya itama tarasu, wani mutumin anguwan mu, attajiri dake shiri da Abban mu kafin yarasu inji Adda shiya karbemu yacigaba da kulada mu ahaka marigayi mahaifinka daya kasance abokin shi yaga Adda ya aura lokacin inada shekaru 15 ta tafi dani gidan mahaifin ka, da ita da shi suka cigaba da rainona suna tarbiyantar dani nakasance nine first child dinsu, ahannun Adda nataso nai girma, tadauki lokaci mai tsayi kafin ahaifoka, Waleed kakosan dani da mahaifinka ne muka samaka sunan nan, Waleed" tai murmushi sanan tacigaba tace "u are everthing to me Waleed with a plus, nina raineka ita kanta Adda har mamakin irin son danike maka takeyi, saisa zakaci har yau bata taba kirana da Maman Hasim saidai takirani da Maman Waleed, na raineka na kula dakai to the extend ko numfashi ka fitar ina gane ta rashin lafiya ce kota farin ciki, Waleed I know Adda na sama dakowa, and nasan kowace irin hukunci tadauka a rayuwanka is for the best badan ta cutar dakai ba dan zan iya rantse maka kaine farin cikin mahaifiyar ka, kai kadai takesawa a ido taji dadi, u are her entire world, batada miji kaine komi nata, kasaki ranka, today is your day, auren ka akeyi, be happy, for once ka manta da wanan aikin Arham na nan I know yaron kirkin nan will handle everything, ka shirya kaje wajen Ilham kaji medame take bukata kabata bikinku ake, rabon dakeje wajen yarinyar nan zance anfi wata, haba Waleed so kake Adda tai fushi, kasaki ranka, and enjoy yarinyar nada hankali ga kyau, gata graduate, lawyer fa eh, kodan yanda Adda keson auren kaima saikaso, bakasan Adda nason tasami jika kota iya maida sunan mahaifin kaba, kome zakayi kasama ranka u are doing it for your mother wlh Allah zai baka ladan hakan, u are doing it for your mum, repeat after me I am doing this for my mother" dan shiru yayi kafin ahankali yace "I am doing this for my mother" murmushi Mom tayi tace "yauwa Dan Yaro, tashi to" tai maganan tana dago kanshi daga kan kafadar ta sanan ta sumbaci goshin shi ahankali kafin tasake shi, hulan shi tadauka ta shiga karyamai tace "ka kwashi kudin dazaka basu?" da sauri yace "su wa?" dan baisan suwa zaibama kudi ba, dan dariya Mom tayi ta kafamai hulan aka tace "zaka bama kawayen Amarya kudi suyi duk wata hidiman daya rage kagane" gyadamata kai yayi yatashi tareda bude drawer gefen gadon yadau kudi yan 1k rapa guda biyar yasa a aljihu Mom sai binshi da kallo take dan tadade bataga yay kyau hakaba kodan yawanci suit yake sawa oho, sanan yajuyo ya kalleta, murmushi tamai tace "muje" fitowa sukayi atare su Hasim na ganinshi sukahau ihu Mom takama baki tana kallonsu sanan ta kalli Waleed tace "ahhhh lallai Waleed kwana biyu baka lallasa marasa kunyan nan ba" harara Waleed ya watsa musu sanan yajefama Hasim key yace "let's go, u drive" tashi sukayi, Abdul yace "bye Mom" bye tamusu suka wuce suka fita gwanin ban sha'awa, Waleed na dudduba wayanshi ganin har yanzu Arham bai kirashi ba wanda inda normal ne da yanzu sunyi waya sama dasau uku, ijiye wayan yayi gefenshi yana yan tunane tunane, Hasim da Abdul sai hiransu sukeyi dan sune gaban mota har sukakai Wuse, agaban wani tangamemen gida sukai parking, shima gidan cikeda jama'a gate abude event ma akeyi dan sai raye raye ake, kashe motan Hasim yayi yajuyo ya kalli Waleed yace "ya Waleed kirata" wayarshi yadauka yay dailing number data kirashi dazu dayay saving da Ilham, ringing daya aka dauka kafin yamayi magana muryan wata mace ta ratsa kunnenshi. "Baby, Hello Baby, Dr" batare daya amsata ba yace "muna kofar gidanku" wani irin ajiyan zuciya ta sauke da saida yaji daga wayan tace "Omg, innalillahi, Baby na da gaske kana kofar gidan mu?" jin yay shiru bai bata amsaba takuma san bazai bata amsanba yasa tace "okay okay, bari naturo Salima ta shigo daku, ni bana gidanmu ina gidan Anty, amaryan Dady the next house na gaban gidanmu, uhmmnm bari, bari Salima tazo ta shigo daku" tafada sounding super excited tsabagen murna, kasan cewa yasan gidan amaryan baban nata yasa yacema Hasim ya gangara gidan gaban gidansu, hakan akayi Hasim yay parking gaban gidan, ko minti daya basuyi da parking ba wata budurwa doguwan tafito tana sanye da wata atampan biki taci makeup tazo gaban motan taredasa hannu tai knocking glass din motar dan bata iya ganin mutanen ciki, bude mota su Hasim dake gaba sukayi suka fito, cikeda fara'a tace "sannu ku da zuwa ina yininku" cikin fara'a Abdul yace "kawayen Amarya ansha kyau" dan dariya tayi tace "ina Dr? Amarya nachan takosa ta daura mijinta a ido" duk dariya sukayi Hasim yabude mai kofa, anatse yafito dan ko kadan baida garaje yana dan daddanna waya dan sako yake turama Arham, binshi Salima tayi da kallo dan all this while labarin shi takeji bata taba sa Dr a idoba, now she see abinda Ilham tagani ta mutum mai, guy din yahadu. "Hi Dr" tai maganan ayangance tareda mai waving hannu, dagokai Waleed yayi ya kalleta saikuma ya dauke kai yamaida hankalin shi kan abinda yake typing awaya yace "Hey" faduwa gabanta yayi ayanda yayi maganan cikin izza akuma kasalance sai taji ya mugun cikamata ido ga shakkan shi dataji all at a time, juyawa tayi ta kalli su Hasim tace "to bismillan ku, ku shigo" ta shiga gaba su Hasim biyeda ita, saida yatura sakon sanan yamaida wayan aljihu yabisu yana taku dai dai suka shiga gidan, yan mata ne dayawa a compound din ana yan abubuwa, wasu na pictures wasu na cin abinci sunci gayu sosai kowacce tasha makeup suna ganin su Hasim akadau guda ango ango, dariya Salima tayi tabude musu kofar falon da tuni kowacce mace tafice babu kowa ciki agyare tsaf suka shiga ta nuna musu kujure, sanan tawuce kitchen drinks takawo musu na alfarma tadan saci kallon Waleed dahar lokacin wayanshi yake daddannawa tace "ga drinks kusha bari nakawo amarya" sanan ta juya tai stairs, wani daki tabude ta shiga inda wata kyakkyawan yarinya ke zaune akan kujera da a kalla bazata wuce 25-26 years ba ana mata makeup, tana sanye da wata doguwan rigan ashobi white dayay mata shegen kyau mai makeup din na daura mata head da kyau, tana ganin Salima tace "kin shigo dasu Salima?" gyadamata kai Salima tayi tace "eh suna falo, ke Khadija dama haka Dr naki yake? My God he is damn cute but yanada wulakanci sosai wlh" murmushi amaryan tayi tareda juya idanu tace "don't tell me u expect handsome rich guy mai status nashi yazama kaman all this random guys you use to know on the street? Angaya miki irinsu Mubarak dinki ne? Cheap guys?" ta bushe da dariya mai makeup din itama tafashe da dariya, ganin mocking dinta Ilham keyi yasa Salima ta tashi ko kadan bataji dadin abinda Ilham tamata ba, tasaba da halinta dan sabawa amma ta tsani tacimata fuska agaban wasu, ganin ta tashi zata fita batare data cemusu komiba yasa da sauri Ilham tace "me haka kekuma daga wasa dadina dake saurin fushi Salima, yakuri to pls dawo kinga fa ke zaki kaini kasa bai kamata na sauka kasa nikadai ba kekuma wai bazaki gama min daurin bane?" da sauri mai makeup din tadauki pin tana sosokewa a ashoken.




Dawowa Salima tayi ta tsaya akanta, karasa soke daurin tayi Ilham tamike ta kalli Salima ganin ta daddaure fuska yasa tawani fada jikinta tareda rungumota tace "dalla na face miki sorry please karki damu anjima zan baki labarin Dr kinji ni yanzu kiyakuri dan Allah" yanda duk takaiga fushi saida tai murmushi tace "shikenan" tace "kinga yanda kikai kyau kuwa kaman bakeba Ilham" murmushi tayi tace "yi sauri muje naga Dr dina" hannunta Salima takama sanan tabude kofan suka fita sau daya tasaci kallonshi ta sunnar da kanta kasa ganin bashi kadai bane, shi hankalinshi ma nakan wayan hannunshi yana danne danne yay wani irin kyau da saida taji gabanta yafadi hakanan taji wani kishi yataso mata yanzu duka matan dasuka cika gidan nan su ganshi ahaka, da kyar ta iya ta danne kishin suka cigaba da sauka daga stairs ahankali, Hasim ne da Abdul suka tashi suna murmushi "wow, Amaryan Ya Waleed" karasa sauko da ita Salima tayi tana musu murmushi sanan takaita harkan kujeran da Waleed ke zaune two sitter ta xaunar da ita a gefenshi tace "Dr ga amaryan ka nan nakawo maka yanzu kwa barni nahuta" maganan dayaji yasa yadan dagokai ya kallesu sanan yadauke kai, juyawa Salima tayi tai waving su Hasim tace "bari naje waje" da sauri Abdul yace "bari muma mubiyoki mubama love birds some space" dan dagokai Waleed yayi ya watsa musu harara suka kyalkyace da dariya suka fice abinsu falon yarage dagashi sai Ilham dake zaune kusada shi dukansu sunyi shiru.



Almost 5min suna zaune basucema junansu komiba sanin zasu iya kwana ahaka bai cemata kalaba dan tasan magana wuya takemai yasa ahankali tamika hannunta dayasha lalle ta daura kan hannunshi daya ijiye kan laps dinshi ta kama hannun gam, atare suka dagokai suka kalli juna, tasake matse hannunshi dat feels so soft kaman hannun mace smiling, ahankali tace "Dr is our wedding are u not excited? I feel so happy because am getting married to love of my life, I love you so much Dr Waleed Warbai" tai maganan hawaye na gangarowa daga cikin idanunta, dauke kai yayi da sauri he don't really know abinda ma zai cemata, ko 1 single feeling baidashi akanta, ganin baice mata komi ba yasa cikeda son janshi zance tace "waye best friend din naka cikin wayan nan da kazo dasu?" ahankali yace "bayanan, this are my siblings" murmushi tayi tareda lumshe ido tana bala'in son jin yana magana, maganan shi dadi sosai wlh, voice dinshi bala'in dadi, murmushi tayi tace "yana ina shi? Maisa baizo tareda kaiba?" dan dagokai yayi ya kalleta suka hada ido sanan yace "I left him in the office you will see him later" gyadamai kai tayi cikeda sonshi tace "kayi kyau sosai" dauke kai yayi yace "thanks" yadanyi shiru saikuma yace "you look beautiful as well" wani irin cikakken murmushi tasaki cikeda jin dadi sosai tace "nagode Dr" sukai shiru, agogon hannunshi ya kalla sanan yadago kai ya kalleta hada ido suka sakeyi dan idanunta na kanshi har lokacin, hannunshi yatura cikin aljihu yaciro duka rapan kudin daya taho dasu ya ijiye mata akan cinya yace "use it for anything you need, will see you later" gyadamai kai tayi ya mike tsaye tashi itama tsaye tayi itama batai wata wataba tafada jikinshi ta rungume shi tsam tsam murya chan kasa tace "thank you Dr, sai anjiman kaji" sanan tasake shi d sauri yajuya yafita daga dakin batare daya kalleta ba yafita daga gidan.

[10/20, 11:40 AM] +234 806 139 0121: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫



✍️ M SHAKUR





3️⃣



FREE PAGE
Wuraren 4 yafito daga office dinshi ko kallon office din Waleed baiyiba yasauko yay wajen hadaddiyar motarshi ya shige yaja motar yadau hanyar barin gidan marayun, agaban wani gida dan madaidaici mai kyan gaske yay parking ya sauko, shiga gidan yayi yabude gate din sanan yakoma mota yaja motar zuwa cikin gida, parking yayi sanan yafito yaje yamaida gate din ya kulle yana bin tsakar gidan da kallo dayasha flowers ga interlock akasa dudda gidan baida wani girma sosai but yanada kyau, karasawa yayi ya shiga flat babba kwara daya da shi kadaine atsakar gidan, bude kofa yayi ya shiga falon da babu kowa ciki sai TV dake aiki gawasu hadaddun setin kujeru dasuka zagaye falon suka karama falon haske da kyawu, wucewa yayi ya shiga wata yar corridor da dakuna uku ke ciki, ahankali yake tafiya har yakai gaban dakin dashine last room din corridor yabude kofar dakin ya shiga, dakine mai kyau sai kamshi yake, ga Royal bed aciki sai kujera daya 3sitter komi na dakin fari harda curtains din dakin, wani babban frame na hotonshi ne ajikin bango, rage kayan jikinshi yayi yawuce yashiga bathroom din dake cikin dakin, wanka yayo yafito ya shirya cikin wata yar 3quater da farin singlet yazauna kan gado, wayarshi dayaga tana dan kawo wuta yasa yagane anyomai message, mika hannunshi yayi yadauki wayar ya danna, sako yagani daga Waleed.
"Where are you My P.A🤣?" yay emojin dariya agaba alamun tsokana yake, tsaki Arham yayi ya cillar da wayan yay kwanciyar shi akan gadon tareda lumshe idanu yana sauke ajiyan zuciya.







"Arham" muryan wata yar dattijuwa ta kwalamai kira, "Arham" aka sake kiran sunan nashi ana bude kofar dakin gabaki daya, bude idanunshi yayi dasuka dan chanza launi dan bacci yasomaji, wata mata ce da a kalla zatafi fifty ta shigo dakin tana sanye da doguwan rigan atampa dayasha stone work hannunta rike da charbi, tsayawa tayi chak ajikin kofa tana kallonshi cikeda mamaki ganinma bacci yasoma yi shida keda biki saikuma tace "ka shigo gidan kafi karfin ka shigo ka gaidani ko Arham" murmushi yayi na rashin gaskiya yana kokarin tashi ya zauna yace "yakuri Umma, danaga baki falo nasan kina ciki kina salla saisa nayo dakin straight dannai wanka, inayin wankan kuma shine na kwanta" gyadamai kai tayi alamun ta gamsu da bayanin shi tace "yana ganka adaki kaida yakamata kana tareda Waleed yanzu, banma dade da dawowa daga gidan nasuba munata yan aikace akace achan" shiru yayi baice mata komiba, hakanan ranta yabata wani abu ganin yasauke kai yasa tace "kai ba magana nake maka ba" juyowa yayi ya kalleta cikeda takaici yace "bazani bikin ba yaje yay bikin shi shikadai su Abdul samai komi" yanda yay maganan yasa Umma ta shigo dakin da kyau tayo kanshi tace "me kake cewa ne haka? Wai Arham maisa kai gabaki dayanka bahaggon mutum ne eh? Kadaisan Waleed bazai taba iya komi batare dakaiba ko? Kakuma fi kowa sanin cewa duk duniyan nan Waleed baida aboki saikai ko? Kana cewa su Abdul, wani irin su Abdul abinda zai fadamaka comfortably bazai taba gayama su Abdul kannenku ba, Arham abokin ka kokuma ma nace dan uwanka dakuka taso tare yau bikinshi shine zaka juyamai baya eh?" daure fuska yayi tamau baice komiba, ganin da gaske fushi Arham yake yasa ta zauna ahankali gefenshi, hannunta tadaura akanshi ta shafa kan ahankali cikeda lallashi kafin ahankali tace "maiya hadaku Arham? Kuda komu iyayenku bamu isa muji tsakanin kuba shine yau kakeso ajiku, maiya hadaku tell me" shiru yayi kaman bazaiyi magana ba saikuma yace "Umma Waleed is rude, very rude, yana controlling dina anyhow, yau ya shigo office so moody shine....." harya gama bama Umma labarin kallonshi take saikuma tai murmushi tareda sauke ajiyan zuciya tace "Arham nasha gayama ka chanza halin nan nak......." cikin fushi yace "dama nasan side dinshi zaki dauka saisa banso na gayamiki bama, nasan u will always support Waleed sabida sunada kud....." wani mugun kallo da Umma tamai yasa yakasa karasa maganan yasaukar da kanshi kasa yana wasa da yatsu, ahankali tace "Arham harga Allah am not happy da wanan dabi'un naka, abu kadan kadauke shi da zafi, Arham do I need to explain yanda yaron nan yake sonka? Saina fadamaka? Kaida bakinka kasha fadan Umma Waleed nasona, Waleed na sona, Arham akwai abinda Waleed baima aduniyan nan ba? He saw u on the street kana 7yrs old kana tallan ayaba, yaron nan kullum saiya fito yabika kuje ku saida ayaban tare kudawo, tun iyaye basu saniba har suka sani, Arham yaron nan Allah ya jikan mahaifinshi, Allah yakai haske kabarinshi saida yasa mahaifinshi by fire by force yasaka a school din dayake the biggest school a Abuja then, Turkish, adaukeku a mota adawo daku a mota, Arham kadawo dan gayu, kuka gama yasa kuka tafi same University a kasan waje ka karanta business administration shikuma medicine, baitaba aboki ba cus yasha fadamin Umma Arham is my everything, Arham is my blood, Arham is my this and dat, yaron nan kome zai saya kome za'a sayamai agida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login