Showing 33001 words to 36000 words out of 74587 words

Chapter 12 - Duniya Biyu Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

12 Dec 2024

471

bishi da sauri yanadan dariya yace "wlh kacika rigiman banza, kawai daga ganin dan kunne shikenan" Waleed baice mai komiba har sukaje children section din, zai shiga ciki saikuma ya kalli Arham yace "lemme go and get Khadija and change" gyadamai kai Arham yayi Waleed yawuce.
Knocking yayi tareda bude dakin yashiga, daidai lokacin Ilham tafito daga bayi tana sanye da hadadden jeans din daya kawomata as gift jiya da crop top din da hakanan yadauko let's just say he's use to seeing ladies yan gayu dress in them so practically he wants to see his wife dress like that, tana ganinshi ta taho da gudu zata fada jikinshi ta rungumeshi yakoma baya yace "am wet baki gani" binshi tayi da kallo cikeda mamaki zatamai tambaya yawuce bayi, fitowa yayi daure da towel yazo ya chanza kaya, tajowa wajenshi tayi da sauri saikuma tarike waist tamai wani irin juyi tace "bakace nayi kyauba, nayi kyau?" dan murmushi yayi kawai yakarasa bakin gado ya zauna bayan ya chanza kayan yace "is nice" wani irin blushing tayi ta taho da gudu ta zauna kan laps dinshi sanan ta manna mai kiss a lips dinshi tace "thank you" gyadamata kai yayi kawai sukia shiru, ganin yamata shiru yasa tace "Dr jirgin na landing awajen nanne dazu naji karan jirgi kaman akaina" ahankali yace "it just came and yakuma juya" gyadamai kai tayi tana kallon yanda yake maganan yace "get dress let's go out" cikeda wani irin murna ta dagashi wardrobe taje da sauri taciro gyale mai kyau dazai shiga da jeans din sanan takoma gaban mirror ta yaryada uban kwalliya tasa jan baki sanan ta yafa gyalen awuya tajuyo ta kallai yana danna waya tace "na shirya" dagokai yayi ya kalleta dauke kai yayi yace "change into something native" wani iri taji taso sufita ahaka ko Arham yaga shape dinta da kyau saikuma ta share tai gaban wardrobe din dakin wata pink atampa taciro da aka mata riga da skirt ta shirya tsaf ciki kayan sun mugun kamata suranta yafito sosai, tayafa gyalen daya shiga da kayan tasaka flat shoe sanan tazo gabanshi tace "Baby let's go" dagokai yayi ya kalleta sai kawai yamike tsaye yamaida wayan aljihu yay gaba, bude mata kofa yayi tafito sanan shima yafito yamaida kofan yafita, ahankali suke tafiya har zuwa children section atare suka shiga wajen, da Arham tafara hada ido da sauri ta dauke kai kujera yabata tazauna yace "am coming" gaishe da ita staff dinshi suka shigayi tana ansansu ayangance shikuma yawuce inda Arham yake yace "am taking her out blood she has been indoors tunda mukazo" batare da Arham yakalleshi ba yace "saikun dawo" juyawa Waleed yayi yaje wajen ta suka fice inda bodyguard dinshi ke tukasu, cikin Bauchi suka shiga shi bai wani surutu da ita amman kome takeso tana fadi zai siyamata daga bayama supermarket yakaita yasami waje ya zauna tadauki duk abinda takeso sai dadi takeji sanan suka dawo mota, da magrib sukaje wani eatry bayan ya tsaya sunyi salla a masallaci, sosai ranan taji dadi tasamu sunyi pics sosai dashi komi yasai mata saitai snapping asamu na nunama friends a status sai wajajen 10 nadare suka dawo, baje tsaraban ta tayi a kasan dakinsu tana dubawa tana snapping shikuma yatabe fuska ya shiga bathroom abinshi wanka yayi yazo ya shirya cikin pj yakoma kan gado yabude system dinshi yana aiki, harya gama yay bacci yabarta tana daddanna waya ana saka status ana amsa comment din kawaye.
***




Ahankali motar data kwaso mutane kusan goma sha hudu ta God is good take tafiya sabida yanda motar ke over heating, passengers din cikin motar sai tsaki suke suna korafi daga Abuja da suke, yanzun nan suka baro Abuja Benin zasu amman shine tun yanzu sun tsaya yakai sau uku wanan wani irin abune, daidai sun shiga MURTALA MUHAMMADU BRIDGE dake nan hanyar lokoja gaban motan yafara hayaki hakan yasa dole direban yayi paki tareda tsaki yafito, bude kofa passengers sukayi dan sufito sudansha iska indamai fitsari yaje yayi, wata matace dake rikeda yarinyar da at least zatakai 7yrs ne tace "Mummy I want to ease myself" kallon Bridge din matan tayi duk titine ga maza kuma itama fitsarin takeji agaban su zasuyi tunanin hakan yasa takama hannun yarta tarike tareda rataya Jakarta akafada suka sauka daga Bridge din zuwa kasa, sauka sukayi suna tafiya, tanacikin tafiya taji ana tafiya da sauri matar ta juyo ganin wata yar matashiya yasa da sauri matashiyar tace "me to I want to piss madam, sorry if I scare you" juyawa matar tayi tace "no problem" sauka sosai sukayi suna dandarawa har zuwa gaban ruwan da ake cewa anan River Niger da river Benue suka hade, cirema yarta wando tayi tace "tsugunna kiyi, bari indan matsa ta chan is like na pupu dey worry me sef, since ba yanzu motar nan zatai cooling down ba gwara nai kayana our journey still fa, if u finish just stand here I dey come" gyadamata kai yarinya tayi itakuma Maman ta shiga cikin ciyayi sabida yadan kareta, yayinda itama dayan budurwa tashiga cikin ciyayi kowa yashiga biyan bukatun sa. Wani irin ihu da yarinyar ta kwala ba matan kadaiba har mutanen dake chan wajen mota saida yay calling attention nasu. "Mummmmmmyyyyy!" azabure uwar ta tashi ko kashin bata wanke ba tafito tanajan pant dinta sama same with dayar budurwan, da sauri Maman tai wajen yarta dake tsaye tana kallonta tace "wat is it Engozi?" daidai dayan budurwan itama tazo tace "wats the matter why are you shouting beautiful girl?" duk suka tsaya kan yarinyar suna tambayarta ganin yanda take shaking, ahankali tadaga hannunta tamusu pointing 👉 rafin duk suka juya suka kalli inda take pointing atare maman da budurwan suka hada baki suka kwala wani irin ihu. "ahhh hhhhhhhhhh hhhhhhhhhh!" within 1min suka hada mutane wajen ciki harda direban su dan ihun yay yawa sun zaci macijine ma ya sarezu, yanda yan tafiye tafiye sukaga direbobi na sauka kasa ana ihu yasa aka shiga parking mota ana sassakkowa dan anzaci hatsari ne kafin kace me mutane sunfi dari dayan kai awajen, matsar da mataye biyun akayi dake rangada uban ihu, daya daga cikin mazan da duk suka tsaya suna kallo yace "are you sure this one is alive" daya daga cikin mutanen wajen ne yace "acirota please wanchan bishiyan daya rike mata riga ne da yanzu ruwan yakara sweeping nata away" wani ne yace "waya iya ruwa dan Allah anan?" daidai lokacin wasu rundunan mutanen sun iso wajen daya daga cikinsu yace "na iya na iya" da sauri matan wajen sukahau cewa "oga pray o, this river they chop people wey no be from here" murmushi kawai mutamin yamata yace "this na my work in my state" kayanshi yatube agabansu yarage dagashi sai boxer yamikama wani dasuke tare dayake nan kaman kaninshi kawai yay iyo cikin ruwan, mutane akahau salati masu kiran jesus nakira masu ciro waya na video nayi, cikin hukuncin ubangiji mutumin yakai inda take sanan yafito da kanshi hamdala akahau yi, karasawa yayi wajen ichen daya rike riganta sanan ya damke rigan kafin yazare daga jikin icen, yakarasa wajen yarike ta gangan ajikinshi yashiga iyo da ita yana zuwa baki bakin rafin maza kusan shida suka saka hannu suka karbeta aka cirota ana ihu mutane fam awajen wasu na cewa she don die, this one don die, wasu na cewa na Mamy water, kwantar da ita akai akasa aka danne cikinta amman batai aman ruwa ba, babu wani abu da ba'a mataba, wani direba ne da yanadaga cikin wayanda ke kanta yace "please waye likita anan ko nurse koda na gargajiya ne? Yakamata asan ko tana raye kota mace gashi kanta a fashe yake gabaki daya ta baya please in akwai Dr yazo" yay maganan yana ihu sabida aji hakan yasa aka shiga passing information din har zuwa kan titi inda tulin mutane suke tsaye dan basu samu wurin shigowa ba sabida acike, ciki ikon Allah aka samu wata mota da Dr keciki da sauri aka sauko dashi akai making mishi way har zuwa kan wacce aka tsinta a ruwan tsugunnawa yayi akanta gabanshi na faduwa yace "kai anya wanan bil adama ce?" yay maganan shikadai saikuma yace "ta zubar da any ruwa" atare duks samarin sukace "mum mata komi amman bata fito da ruwaba" soyake ya daga dogon gashinta dat is lying akasa dayaga yakai har cinya ta amman harga Allah tsoro yake baison abinda zai hanashi bacci, tunda yake a Nigeria baitaba ganin mace mai gashi hakaba, hannunta yakama yarike danyay feeling pulse dinta, almost 3min yana saurara amman baiji komiba yana shirin zare hannunshi yaji pulse dinta but very slow and weak a dimauce yace "sh.....she's alive" wani irin kabbarta wajen yadauka. "Allahu Akbar" kiristocin sukahau cewa. "thank you jesus" tashi yayi yace "amman a kaita any nearby hospital this girl or whatever she is need to be saves quick inba hakaba za'a iya loosing nata, machine za'a sata dazai zuko ruwan" da sauri wani yace "wayasan any nearby asibiti?" shiru duk akayi duk asibitin da za'a fadi nacikin garine saikuma wani tsoho yace "ku kaita WARBAI ORPHANAGE HOME AND HOME OF THE DISABLED ko tsintuwa fa akayi gwamnati ta halatta mana kai abinda aka tsinta awajen, akwai asibiti da kwararrun likitoci a gidan, kana zuwa za'a karbeta, banda haka asibitin ne kadai zaku kaita ko sisi baza'a chajeku ba sanan kubarta awajen baruwan ku sune zasu dauka daga wajen, in nemo iyayenta ne inma menene duk su zasuyi, kuma ma ai babu wani nisa yana nan hanyar fita daga Abuja zakuga dankareren gini wane University ga sunan baro baro ajiki ga sojoji" addu'a akahauma tsohon maza suka dauketa wani bawan Allah dazaiyi Abuja yay volunteer motarshi mutane uku suka bishi sabida zamanin nan ba'a yarda da kowa tafiya kusan minti hamsin yakaisu gaban WARBAI ORPHANAGE HOME AND HOME OF THE DISABLES, sojoji suka taresu saida aka duba motan tsaf bayan sun nuna abinda suka tsinta sanan sukai ciki har asibitin aka kaita soja biyedasu.






Suna shiga sukai parking gaban dankareren asibitin dako wani asibitin cikin gari albarka, already nurses harsun gunguro gado dan sojoji sun riga sun sanar dasu, daura ta mazan sukayi akan gado nurses din na kallonta suka gungurata ciki, Sojan daya biyosu ciki yace "we will take it from here thank you" yanuna musu motarsu, komawa cikin motar sukayi sukabar orphanage din.
Wanan kenan!!!




Assignment din dazasuje yau shine hiking with benefit, sunan dasuka bashi kenan, chan wani mouthain zasu da tun jiya Waleed yatura maaiktan shi akaje dan dubawa dacire duk wani abu dazai cutar mai da yara sanan akai planting various gift awajaje daban daban dan za'ayi treasure hunt duk wanda yasamu wani abu yazama nashi halak malak saisa aka sama hiking din suna _Hiking with benefits_, yaran sai jin dadi suke, they're super excited, gabaki dayansu yau sun saka sport wears da p-cap harda yan matan cikinsu, bayan kowani t-shirt anrubata sunan gidan marayun koda yaro zai bata za'a iya dawo dashi, ko tracing daga inda yake, kasancewan Ilham tacemai zata bishi yasa sune last to arrive venue din, bodyguard dinshi ya tukosu, tunda taga harda yan mata da sun isa aure a marayun yasa taji tama tsani aikin, sanye take da jeans da riga da sneakers amman saida yasa tadaura after dress akai, shikuma yana sanye da jeans da riga sai canvas da p cap akai, yay bala'in kyau idanunshi sanye cikin bakin glasses dan rana tafara fitowa takwas ne na safe dayan mintuna, Arham kawai suka samu akasa bai riga yafara hawa ba gabanshi da manya manyan jaka guda biyu wanda bottles water ke ciki da glucose incase wani yaro yagaji, kallo daya Ilham tamai tadauke kai tace "Barka da asuba" Barka yacemata yana kallonta saikuma yay murmushi ganin bata iya kallonshi tun bayan abinda yawakana tsakaninsu yace "blood your wife tayi kyau sosai cikin english wears dinan da sneakers menawani sa tasaka after dress akai?" jaka daya Waleed yadauka yagoya abaya sanan yace "she is married ba kyau ana ganin jikin matan aure, let's go" yay maganan yanayin gaba yafara hawa kan dutsen, dan kallonta Arham yayi suka hada baki, lashe lips yayi irin kinyi kyau dinan u look yummy sanan yabi bayan Waleed, murmushi tayi ganin yanda ya mutu akan gayun shiko Waleed koya cemata tai kyau baiyyiba, ajere suke tafiya Waleed nagaba Arham atsakiya sai ita abaya, ahaka har sukakai saman mountain din kafanta kaman zai katse ta gaji, sauke jakan Waleed yayi yana murmushi ya kalli yanda yaran suka zuzzube akasa suna haki sai zufa suke nanko dazu sunfi kowa kosawa a tafi yace "are you tired children tun yanzu?" atare sukace eh, dariya yayi yashiga ciro rowan yana raba musu suna karba sauran ma'aikatan ma nabasu ruwawwakin dan kowa saida ya goyo jakan ruwan cikin maaikatan, wayanshi dayashiga kara yasa yamikama wani staff dinshi yamai alamu yacigaba da raba musu sanan ya matsa gefe yaciro wayan, ganin daga orphanage dinshi ake kiranshi Dr Kemi yasa da sauri yay picking yakai kunnenshi yace "talk to me Dr Kemi" anatse matan tace "Sir we have an emergency case, we need you here ASAP" bayan shi Dr Kemi is the second best Dr yakedashi a hospital dinshi, ganin ita da kanta tana fadomai akwai emergency ana bukatan shi yasa yace "what happen? Who is sick?" anatse tace "Sir a patient was brought into the hospital few minutes ago...." da sauri yace "is it a BID (brought in death) case"? Da sauri tace "no no sir, is not a BID case amman close to BID" "kaman ya close to BID? Dr Kemi skip the talk and cut to the chase" ajiyan zuciya tasauke tace "Dr Warbai 4 men suka kawo yarinyar nan cewan an tsinceta acikin ruwa, karkashin gadan murtala Muhammad Bridge in zaka lokoja, I believe them cause the evidence was obvious" anatse yace "did she sustain any injury?" "yes sir, yes, akwai bruises ajikinta ko'ina, sanan kanta yafashe" "what is kanta yafashe? Da kanta yafashe da BID za'a shigo da ita, tell me the exact lobe a head dinta daya fashe, is it the temporal lobe, frontal lobe, parietal lobe, ko occipital lobe, wanne ne yafashe?" anatse tace "occipital lobe dinta ne tasami injury, wajajen keya, wajen yatsage yafashe, the problem now is I believe water yay finding his way to her cerebellum, naduba eyes dinta sun karkace, I think her vision sight has been distorted" cikeda damuwa yace "that's metamorphopsia, yawanci head injury nasaka hakan" ajiyan zuciya Dr kemi tasauke tace "she is unconscious, pulse dinta kadan ne sir" wani irin ajiyan zuciya yasauke yama kasa magana saikuma yace "I will be on my way just stabilise her condition" da sauri tace "ejo, mabinu Sir, listen sir" ahankali yace "yes! Kince"? anatse tace "Sir am the only Dr on duty am sorry bazan iya duba yarinyar nan ba trust ne indai yarinyar nan bayar ruwa bace to mami water ce, I just got married, I don't want my husband to loose me" wani mugun tsaki yayi ya katse wayan yajuya ya kalli Arham daketa rabo itama Ilham na rabon, karasawa wajen yayi ya kirashi "blood" da sauri Arham yadago ganin yakira shi yasa ya ijiyema yaran snacks din yataho wajenshi yana kallon idanunshi yace "yanaga idanunka sun chanza? Menene?" ahankali Waleed yace "akwai emergency a orphanage a clinic, Dr Kemi isn't helping matters, I need to be there now, but once nashawo kan case din zan dawo koda gobe ne, please don't tell Ammi nakoma Abuja koda takirata, I don't want her to know, zanbar Ilham ma anan, dankoda nace zanje da ita zata mayarmin aiki bayane ko?" da sauri Arham yace "yes kabarta anan aiduk muna tare she will be fine, but tell her first kafin katafi sabida karta damu kasan tana sonka dayawa, don't worry I will take care of her, go and save life Allah sa muji alkhairi" side hug Waleed yabashi yace "thanks blood" sanan yakira Ilham dake wajen yara. "Khadija" da sauri Ilham tadago kanta saikuma ta tashi tazo inda yake tana kallon fuskarshi ganin kaman yanayinshi ya chanza tace "baby menene"? For the first time yakai hannunshi kan fuskarta kaman mai son lallashinta yace "I need to go to Abuja yanzun nan Ilham, ga Blood na he will take care of you, anything you need just let him know, zan dawo once nai stabilising case din, take care of yourself okay" gyadamai kai tayi kaman zatai kuka tace "Allah ya kiyaye" fuskanta yadan shafa yace "Ameen bye" gyadamai kai tayi, bye yama Arham yawuce, bodyguard dinshi yabishi mota ya shiga already akwai wallet dinshi ajikinshi daman, Airport yakaishi direct yabi available flight to Abuja baima sami business class ba haka yay managi da economy, yana kaiwa yadau drop direct to his orphanage, sojojinsu zasu taresu yasaukar da glass suna ganin shine aka bude gate da sauri ana gaidashi motan yawuce ya shiga, har gaban clinic dinshi yafito yabama direban kudaden dabaisan iya adadinsu ba.

Shiga cikin clinic din yayi da Dr kemi yafara haduwa a reception baibi takanta ba yawuce washhand basin dake reception dinshi ya wanke hanunshi da hand-wash sanan yatare senitizer yay amfani dashi yajuyo lab-coat dinshi Dr Kemi ta mikamai cikeda girmamawa tace "welcome Sir" gyadamata kai yayi yakarbi lab coat din yasaka daidai lokacin wata nurse takawo mai faranti da handglove kekai, dauka yayi yasaka sanan yace "where is the patient Dr Kemi" adan daburce Dr Kemi tace "ICU Dr" tafiya yafara yay hanyar ICU tana biyeda shi da nurse guda daya, Dr Kemi tace "Sir ko nurses dinmu sunce karmu tabata, kaganta wlh she is the definition of ba mutum bace" tsaki yayi baice musu komiba tsabagen takaici har sukakai gaban ICU din, ahankali yadaura hannunshi kan handle din kofan ya murda kafin ahankali yatura kofan.
[10/18, 1:05 PM] +234 703 278 9649: ✍️ M SHAKUR





1️⃣5️⃣


Ahankali yatura kofan ICU kaman wanda bayaso yatura, wasu fararen kafa yagani farare tass

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login