Showing 6001 words to 9000 words out of 74587 words

Chapter 3 - Duniya Biyu Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

12 Dec 2024

462

in ba'a sayo nashi da nakaba bazai karbaba, yaron nan bought this house for me, yasaimin car, handling everything that has to do with me, every end of the month saiyayo min har gobe dudda na nunamai yanzu kana aiki kanada kudin yimin komi but yaron nan yaki, yabaka job a inda yake shima, he carry u along a komi, in yananan he want to see u awurin with him, he did everything for us and look I will forever be grateful to Waleed har karshen rayuwa ta, dabadan Waleed ba da Allah kadai yasan inda muke yanzu maybe muna kwana a kasan gada, ankoremu agidan haya" tai dan shiru tana sauke ajiyan zuciya sanan ta nisa tace "menene aibun fadimaka dayayi cewa lokacin office lokacin aiki ne bana firan abota ba eh? Kowa dake da any dangantaka da Waleed yasan the way his world revolve around gidan marayun nan, kafi kowa sanin irin soyayyan dake tsakanin shi da mahaifin shi, bayan rasuwan shi yabude gidan marayun da sunan mahaifin shi, gabaki daya soyayyan dayakema mahaifin shi yay transferring nashi to gidan marayun ne, Arham idan Waleed wants to do good I think u should be the number person dazai bashi support, banda haka just take a look shima yadamu yana ganina agidan yazo wajena ya tambayan kadawo nace bansani ba, yamaka text kakimai reply, Arham karage zuciyan nan dan Allah karage, yanzu tashi kaje ka shirya katafi he needs u komi na hannunka kaji?" gyadamata kai yayi ahankali, dan murmushi tayi tace "right from day one Waleed has been a rude person but ahaka ai ka kawomin shi Umma ga abokina remember? Ka girmeshi yakamata ace kayi amfani da hankalinka and understand him better than anyone, babba babba ne yarona" dariya yadanyi hakan yasa tace "ko kaifa I sauri ina jiran ka a falo" gyadamata kai yayi tawuce tafita shikuma yatashi ahankali zaiyi wajen wardrobe dinshi wayarshi tadanyi kara juyowa yayi yadawo wajen yadauki wayan yabude sakon da sauri ganin Waleed ne.
_"okay okay, I get it, you want me to say those words right? Sorry blood I know I was rude dazun nan but hey! Don't put too much pressure on me I might break, Ammi ne tamin fada dazu da safen nan but I am sorry for taking it out on you, please kazo su Hasim are driving me nut am about to loose it_
Dan murmushi yayi ya ijiye wayan batare dayamai reply ba yadauko wata bugaggiyar farar shadda ya saka dan akwai kayan dinner dazusu saka anjima da night ya feshe kanshi da turare, sanan yadau makullan motan shi yafito, tuk kafin ya iso Umma ta kafe kofar corridor da ido fitowa yayi hakan yasa ta murmusa tace "abokin ango da kanshi, agama nashi dakafana zanje wajen Ammin Waleed dama ita ke goyamaka baya wlh kokai aure kona bama wanan bazawaran datazo takanas tafadamin tana sonka dan kaji" dariya yayi yace "habadai Big boy irina zaki sadaka dashi Umma" dariya dukansu sukayi tace "dalla bacemin daga gani nisai kuma gobe in Allah yakaimu zan koma gidan" "alright bye Umma" "bye" tamai waving hand yana fita daga dakin, motan shi ya shige ya zauna ya kunna motar sanan yafito ya bude gate yana tunanin yakamata yadauko mai gadi fa fa fitar da motar yayi waje yadawo ya kulle Gate din sanan yadau hanyar gidansu, dayake Umma tariga tafadamai ta bayan layi shima ya zagaya yay parking akofar gidan sanan ya kashe motan yafito yana tafiya dai dai yabude Gate ya shiga gidan, tundaga tsakar gidan wajen yakejin hayaniyan su Hasim girgiza kai kawai yayi yabude kofan ya shiga falon duk waigowa sukayi suna kallonshi, harara ya watsa musu hakan yasa suka fashe da dariya Hasim yace "ga best man din ango nan ya shigo, iyye see the glow" da hannu ya nunamai kunnenshi hakan yasa da sauri Hasim yace "tuba nake Ya Arham" barin falon yayi yadauki hanyar bedroom dinshi ahankali yabude kofa dakin nashi daga Mom har Waleed din datakai spoon bakinshi danya karbi abinci juyowa sukayi suka kalli kofan, ganin Arham ne yasa Mom tasaki wani murmushi, dauke kai yayi daga kallon Waleed din dayadan murmusa kadan ganinshi sanan ya karasa gaban mom yadan rage tsawo cikeda ladabi yace "ina yini Mom" cikin wani irin jin dadi Mom tace "lpy lau Son, barka da zuwa, Allah yamaka albarka kaji, ina yawan fadama abokin ka ai duk duniya bazai taba samun aboki mai amana irinka ba ga girmama nagaba dashi, uwa uba ga kunya, kai Allah dai yabarku tare, kadinga hakuri da halin Waleed, dabi'un Waleed sai du'a'i jinshi yake kaman dan shekara biyu kagafa yanzu abincin nan wlh inda ban bashiba da bayici, ai nagode ma Allah yanzu zaiyi aure nahuta daman Adda tace ninenan nabata shi" tai maganan tana tallo keyanshi, yi yayi kaman zaiyi kuka saikuma yatashi ashagwabe yayi hanyar kofa da sauri Mum tace "ina zaka?" ahankali cikin yanayin maganan shi kaman na wanda yagaji yace "ni ruwa zan dauko" yana fadin haka yawuce yafita, ajiyan zuciya Mom ta dauka sanan ta maida hankalinta kan Arham dahar lokacin bai tashi daga gabanta ba tace "Arham nasanka yarone mai hankali da sanin yakamata ga abokin kanan kacigaba da sashi a hanyar kwarai, kacigaba da hakuri dashi, ka girmeshi, Waleed is still a child kawai girman jiki dayake da shine yasa a kemai kallo kaman wani babba but har yanzu baikai 30ba kaima kasani, Arham always watch his back kaji dan Allah, kafishi wayau always guide him for us kaga shi kadai garemu, Allah muku albarka dukanku, bari kaga nakoma cikin gida in yazo ga abincin shinan kasashi yaci kasan matsalan shi na Ulcer pls, Ulcer shi yatashi batamai da kyau" gyadama Mom kai yayi ta tashi tawuce tafita, tashi yayi ahankali yana kallon hadadden bowl din da pepper soup din fish keciki ga plate na white rice da spoon komi anjera kan tray, girgiza kai kawai yayi yanabin ko ina nadakin da kallo kafin ahankali yadaga kafarshi yay gaban mirror dakin yana tafiya ahankali, tsayawa yayi yana kallon turarukan wajen, hannunshi yamika ahankali yadauko wani da shi kadai ne baisaniba cikin turarukan wajen mai suna "Men of Chastity" ya shiga jujjuya turaren yana kallo kaman mai wani tunani, bude kan turaren yayi yafesa kadan ahannun subhanallah saida ya lumshe ido tsabagen dadin kamshin, bude kofa da akayi yasa yajuyo da sauri rikeda turaren a hannu, Waleed ne ya shigo rikeda bottle water a hannunshi maidan sanyi, binshi yayi da kallo kafin idanunshi su sauka kan turaren da Ammi tabashi jiya as gift, dan murmushi yayi ya shigo dakin yace "wanan turaren kake kallo, Ammi tabani shi jiya da daddare gift, gama kwalin shi nan kasa dazun nan nabude shi" yamai pointing wani hadadden kwali dakenan kusada kafarshi ja akasa a ijiye, tsugunnawa Arham yayi yadau kwalin yadaura kan mirror sanan yabude kwalin ahankali, kwalin kadai abin kallo ne, har zai rufe kwalin idanunshi suka sauka kan receipt din turaren dake cikin kwalin idanunshi suka sauka kan kudin turaren 2.8m, da sauri yace "wanan turaren ne 2.8 million X-man?" batare daya kalleshi ba Waleed ya sauke goran ruwan dake bakinshi yace "eh kaima kaga bai tsada bako?" yafada yana daukan plate din rice trying to see in zai iyaci da kanshi dan bai koshi ba, sosai Arham ke binshi da kallo yama kasa magana he just wish inama ace shine dandan Ammi shikuma Waleed dandan Umman shi, Waleed dan gatane da baitaba ganin irinshi ba tarairayan shi ake kaman egg, bai dauki kudi anything ba sabida yanada su in excess ma, kaman ance yajuyo yajuyo gani yayi har lokacin Arham kallon turaren yake yamayi nisa a tunani dan murmushi yayi yamaida kanshi kan abincin yace "take it blood" maganan shi yadawo da Arham daga duniyan tunani yace "take wat?" cikin halin ko in kula yace "the pef" da sauri Arham yace "are u crazy? Ammi tabaka gift ne zaka wani ce nadauka" murmushi yayi yana chakalan abincin yace "ai itama tasan everything two ake saimin me and u maybe ta manta ne tasayo just one this time around, anyway take it will order akawo min wani" wani irin murmushi Arham yayi yataho wajen da sauri yadan bugi kafadar shi yace "thank you ango, angon Ilham"
dagokai yayi ya kallai tareda ballamai harara hakan yasa Arham yace "to me dalla, common chill, dan gatan Ammi I know yanda Ammi ke sonka dinan will choose the best girl for u, a princess kaman yanda kake a Prince to this family yar gata irinka" tabe baki yayi yatashi yace "nidai mutafi mosque" tashi Arham din yayi suka wuce suka tafi masallaci sallan magrib.
[10/20, 11:40 AM] +234 806 139 0121: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫



✍️ M SHAKUR





4️⃣



FREE PAGE
Direban gidansu Arham yatura dazasuje su dauko Amarya da kawayen ta to the event centre cus 9 za'a fara dinner dasu Hasim da friends dinsu, saida ya tabbatar sun tafi sanan yakoma cikin gidan, Waleed yasamu azaune kan kujera yana aiki da laptop dinshi ko ajikinshi kaman ba shine angon bikin ba, maida kofan Arham yayi yarufe ya karaso cikin dakin tsayawa yayi chak akanshi yace "muje ka shirya mutafi ai ba'a office kakeba yanzu kana gida" dan dagokai yayi ya kalli Arham din wata yar gajeren tsaki yaja yace "Omg wai why did u initiate this dinner stuff at the first place ma eh? Goddd! Mutum cannot rest again yayi abinda yakamata, am so so sick of this wedding, gosh!" girgixa kai Arham yayi ganin yanda yake masifa bil hakki ya karbe laptop din tareda shutting nashi down yarufe yarike ahannu sanan ya mikamai hannu yace "muje mushirya" ahankali yatashi Arham yabishi da kallo yana sanye da faran t-shirt sai wani 3quater short daya tsayamai wajajen gwuiwa shima fari, kafafunshi sanye cikin farin bathroom slippers, gashin kafarnan kwance lub lub irin na mugun dan hutun nan. Ahankali kaman wanda kwai yafashe wa aciki yake tafiya Arham yabude kofar hadadden bedroom dinshi suka shiga ciki, wajen wardrobe dinshi yayi yafito dawasu kaya da bama abude ba yazube su kan gadon sanan yabude ya shiga shiryawa cikin wata white suit na ermenegildo zenga, suit din yamugun fitting nashi daga kasan waje akamai order suit din aka tahomai dashi, sanan yadauki cover shoe dinshi na dinner sabo fil Black, designers shima na Testoni, tsayawa chak Arham yayi yana kallonshi yamugun yin kyau sai kallon kayan yake, juyowa Waleed yayi ya mikamai bow tie din dake hannunshi yace "tayani sawa blood" karban bowtie din Arham yayi yashiga samai kaman ba zaice komiba saikuma yace "amman wanan takalmin da suit din bashi mukaje muka sayo tareba a dunes ko?" girgiza mai kai yayi yace "Uncle yazomin dashi daga Ukraine jiya daya iso" gyadamai kai Arham yayi baisake cewa komiba yana gama samai yawuce yaje wardrobe yaciro wayanda suka sayo tare, yazaro tashi suit din black, dan abokan ango black suit zasu saka shikuma ango white, ya shirya tsaf sanan yataho key motar Waleed ya dauka yace "let's go" fitowa sukayi daga dakin, har zasu fita daga falon Ammi ta shigo dakin sun kusan cin karo, binsu tai da kallo yanda suka mata kyau sosai kafin ta sauke idanunta kan Waleed dayay mata wani irin kyau batasan lokacin data saki wani kayataccen murmushi ba, wucesu tayi tazauna kan sofa sanan takalli Waleed tace "zonan Son" tahowa yayi ahankali kaman wanda baison tafiya yazauna kusada ita inda take nunamai, hannunta takai tai cupping face dinshi tana kallonshi kaman yau tafara ganinshi kafin ta shafa fuskar tace "you look so much like your father today, kayi kyau sosai, Allah ya maka albarka kaji" dan lusme ido yayi yana danne abinda yakeji a zuciyan shi yace "Ameen" purse din data shigo dakin dashi ta ijiye agefenta tadauka tabude taciro rapas nayan dollars guda biyu tamikamai tace "gashi kama y'ata manni dasu" karban kudin yayi ahankali dan baiso yaki karba taji haushi, rungume shi tayi ahankali taredamai kiss akumatu tace "stop being sad, I love you son, kaci abinci kuwa?" juyawa da sauri Arham yayi yafita daga dakin ya shiga mota Waleed din yay zamanshi a mazaunin direba, he just wish inama shine Waleed, kome zaiyi iyayen shi basa tabamai fada komin girman abun, unlike him da kullum abu kadan Umma fada takemai, abu dan kankani sai fada, Waleed ko abinci ma abaki ake bashi, bodyguard ma saida sukai fada da Ammi sosai dan anso kusan 10 sudinga binshi da kyar ya karbi daya wanda yadawo direban shi, bama abari yasha wahalan neman mataba aka samomai yar gidan masu kudi, graduate lawyer fa dudda dai bai taba ganinta ba aka bashi, just look at suit din da uncle dinshi ya kawo mai daga Ukraine, suit din ermenegildo yana costing about 22 to 28000 dollars, suit din jikinshi kadai worth a fortune dan yakai almost 8.8million naira a kudin Nigeria, takalmin kafanshi na Testoni kusan 3m ne shima, gata da dadi is beyond tunanin kowa ko shima inda bai gani da idanunshi ba dabazai taba yarda ana bama yaro gata irin gatan da ake bama Waleed ba, why was he born from the poor home? Maisa Umma ta auri Abban shi wani Malam Muhammad Bala, malamin islamiyya? Yataso ko gidan kansu basuda shi sai gidan haya, gidan dakuna ashirin da biyu da bayi guda biyu daya na kashi daya na fitsari, daga baya kuma yazo yarasu ya barsu cikin talauci, Waleed ne ya shigo rayuwan shi ya chanza mai komi..... Bude motan da akayi yadawo dashi daga daga dogon tunanin dayaje Ammi ne tabude ma Waleed din kofar motan tana kallon Arham tace "son ina gajiya" cikeda kunya dan yafi sakewa da Mom sabida ita tanada raha sosai while Ammi batada raha tanada fada, bata cika wasa da yaraba, aduniya in tana tareda Waleed ne kawai zaka dinga ganin dariyanta da murmushi ta abanza, da farkoma ya dauka bata sonshi ne sai daga baya ya lura haka Allah yayi ta ita kawai bamai yawan wasa da sakema yara fuska bane, cikeda girmamawa ya sauke fuskanshi yace "ina yini Ammi, ya taro" tana kokarin saka Waleed dake mata wani shegen shagwaba a mota tace "Alhamdulillah Arham, ai tuntuni muna tareda mahaifiyarka ma wlh, mamanka akwai kirki, kaga Arham gashinan drive him safe please, saikun dawo, bye Son, have fun okay, if u need anything ka kirani zan aikoma dashi" ta shafa kan Waleed din dake tura mata baki tana murmushi, kunna motar Arham yayi yaja Ammi na daga musu hannu tana murmushi, saida sukadan yi nisa ahanya sanan ya kalli Arham din dayaga yay shiru kuma ba halin shi bane yamika mai rapas din dollars din da Ammi tabashi duka biyun yace "use this" da sauri Arham ya kallai saikuma ya maida kanshi kan tukin yace "a'a, abinda Ammi tabaka zan karba" murmushi yayi kafin ahankali yace "take it inada wanda zanyi amfani dashi already" "shikenan" Arham yafadi ahankali kafin yace "thanks blood" murmushi Waleed yamai baice komiba, ahaka har suka karasa event centre babu wanda yakara magana cikinsu, daman yawanci in suna tare Arham ne mai kawo hira shi Waleed iya kanshi um a'a kokuma yan maganganu kadan, parking yayi yace "ka zauna aciki, I need to confirm in Amarya ta iso dan tare zaku shiga Hall din" bai jira amsanshi ba yamaida kofan yarufe yay wurin entrance din daidai zai shiga Abdul suna saukowa daga elevator tareda Salima suna hira shiru sukayi ganin Arham, Salima tace "you must be Arham ko? Best friend na ango" dan murmushi Arham yayi yana binta da kallo tana sanye cikin asshobi kawayen Amarya pitch yace "yeah nice to meet you Mss Salima" murmushi Salima tayi tana kallonshi ganinshi shima kyakkyawa sosai saidai dudda kyanshi baikai kyawun Dr ba, kuma Dr yafishi kaurin jiki da cikama mutum ido, ganin kallonshi take yasa ya katse shirun yace "ina Amarya? Cus they're going in together" "eh tana wani daki asama where is Dr?" juyawa yayi yace "lemme get him" har wajen motan yaje yabude motan ya kalli Waleed dake dandanna waya yace "let's go ango" ballamai harara Waleed yasakeyi hakan yasa Arham yace "sorry mana ai kuma gaskiya nafadi kai angon ne" ahankali Waleed yafito yana gyara suit din jikinshi su karan kansu su Abdul da Salima kallonshi suke yawani irin yin mugun kyau cikin white suit din dasukai mugun fitting dinshi maida kofar Arham yayi yana kallonshi yace "muje" ahankali suke tafiya har zuwa gaban entrance din Salima takasa daina kallonshi, dan kallonta yayi sanan ya kalli Abdul batare dayace musu komiba, anatse Abdul yace "sannu da zuwa Ya Waleed" bai kallesu ba yacema Arham dake kusadashi "let's go" wucewa sukayi dukansu suka shiga lift din yakaisu 4th floor, wani daki Salima tabude tana kallon Arham dan Waleed mugun cika mata ido yake tace "ku shigo tana nan" shiga ciki tayi suka hada ido da Ilham datasha uban gayu anmata makeup tasaka wani gown white daya mata fitinannen kyau ita kadai zaune kan wani Royal chair tai kyau sosai, cikin tafiyan nan nashi mai daukan ido daidai ya sawo kanshi cikin dakin Arham biyeda shi abaya, ahankali ta mike tsaye tana kallonshi hada ido sukayi hakan yasa ya tsaya chak shima, wani irin dadi ne ya lullubeta batasan lokacin data saki murmushi ba da sauri tazo wajenshi batai wata wataba tafada jikinshi ta rungume shi, ihu dakin ya dauka Arham ya shigo dakin da kyau yana kallonsu yana murmushi, da sauri Salima taciro wayarta tafara musu hotuna, ahankali yadaga hannayenshi ya rungume ta back, wani irin ajiyan zuciya ta sauke ta shige jikinshi sosai tana shakan kamshin dayakeyi, kaman ta jawo gobe takeji ayi a daura musu aure tayi ta dawo matar this ajebota handsome rich kid, "wai anan zamu kwana ne" Abdul yafada yana dariya, ahankali tasake shi cikeda jin kunya hakan yasa shima ya saketa, juyawa tayi suka hada ido da Arham da tundazu yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login