Showing 1 words to 3000 words out of 47249 words

Chapter 1 - Exiled Prince Book 2 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

284

 ❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤

(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥




( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




⚘🕊 MALLAKIN MEERAH 🕊⚘

【 CUTIE PIE 】



Marubuciyar littafin :【 TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 】



YOU CAN FOLLOW MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i



BOOK .............. 2 🌹👑




THE ROYALTY LOVE ✌👑🌹




♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡




PAGE 1 ❤🔥





DAULAR SAUDIYA 🔥👑




Tarihin kassar saudiya a matsayin kassa ya fara ne a karni na 1727 da hawan Malik Al Saud wanda ya kafa masarautar Saudiya wanda kuma shi ne sarki na farko a saudiya , wannan yankin an san shi da tsofin al'adu da kuma na zamani , ya na da mahimmacin ga alamun ayukan dan Adam na farko, Musulimci wanda ya kunno kai a karni na 7 , ya ga saurin fadada sauran yankunan bayan mutuwar Muhammad ( S.A.W ) a shekara ta 632 , wanda ya kai ga kafa daular larabawa masu tasiri Yanku na hudu su ka kafa saudiyya ta zamani : Hejaz , Najd , Gabashin Arabiya , da Gudancin larabawa , wanda ABDOULAZIZ BIN ABDOUL RAHMAN ( IBN SAUD ) da ga Al Saud ya hade a 1832 inda ya kafa saudiya a cikakiyar masarauta wanda ya hau mulkin ta , gano man fetur a shekara 1838 ya mayar da shi babban hako
A shekara ta 1840 yanku nan hudu bisa jagoranci uban gida jen su , su ka nemi hawa Mulkin saudiya baki Dayan ta, Hakan ko ya tada wani gagarumin yaki a tsakanin masarautar nan hudu , Daular Ottoman da ta kafu tsakanin yankin Hejaz da Gudancin larabawa bisa shugabancin AHMED ABU-TALIB , sannan Daular Saudiya da ta kafu tsakanin yankin Najd da Gabashin Arabiya bisa Shugabancin ABDOULAZIZ IBN SAUD
Sun yi gagarumin yaki wanda Daular saudiya ta fito a matsayin mai nasara sakamakon Manya manya warriors din ta , wanda ba su ja da baya a kashe ko akashe su
ABDOULAZIZ IBN SAUD ya hau mulkin Saudiya baki daya wanda kuma ya hau a matsayin shugaban kassar , duk wasu shawarwarori na administration a hannun sarkin Saudiya ta ke
ABDOULAZIZ BIN SAUD ya na da diya uku biyu mace dayan namiji ZAYD ABDOULAZIZ BIN SAUD wanda ya hau mulkin Saudiya Bayan rasuwar mahaifin shi a 1883
Bayan hayan ZAYD BIN SAUD Daular saudiya ta kara habaka , duk wasu masarautu da su ke Gabashin Saudiya da Arewacin ta da Yammacin ta duk saida su ka dawo a karkashin mulkin Daular Saudiya , Banda Gudancin wanda ke hannun Daular Ottoman
Bayan Hawan Mulkin ZAYD BIN SAUD ya auri mata hudu wanda su ka fito da ga gidajen saurata da ke karkashin Daular Saudiya , ta hudun kuma da ga Daular Ottoman dan rage tsananin da ke tsakanin wadanan Daular hakan ko ba karamin tasiri ya yi ba dan tun bayan hakan zumunci ya kulu tsakanin wadanan gidan sarauta biyu
cikin wani ikon ubangiji duk cikin matan ZAYD BIN SAUD Gimbiya Hindi ta Daular Ottoman kadai ta haifi yaron ta daya tilo namiji , duk ukun Mata ne su ka haifa
A shekara ta 1948 ABDOUL LATIF BIN SAUD da tilo ga ZAYD BIN SAUD ya hau karagar mulkin DAULAR SAUDIYA bayan rasuwar mahaifin shi da mahaifiyar shi sakamakon wani hari da yan leken asiri su ka kai musu a cikin masarautar a lokacin ya na da shekara 26
Bayan hawar garar mulkin ABDOUL LATIF BIN SAUD ya auri mata Biyu , ta farko Gimbiya HOUDA da ga masarautar Rouma , da kuma Gimbiya YOUSRA da ga masarautar Jordan
Cikin wani ikon Allah Duk yaran da su ka haifa mata ne , ko wace sai da ta haifi yara mata biyar amma babu namiji
Amma duk sauran yara mata na ZAYD BIN SAUD da su ka auri Manya Manyan yan kasuwa da kuma yaran sarki sai da su ka samu da namiji Banda ABDOUL LATIF BIN SAUD
A shekara ta 1985 MALIK ABDOUL LATIF BIN SAUD ya auri matar shi ta uku Gimbiya DJAOUDATT
da kudurin ta samar mishi da namiji wanda zai gaje shi
Amma ita ma Gimbiya DJAOUDATT diya mata kawai ta haifa
Ganin yadda shekaru su ka ja ya sa MALIK ABDOUL LATIF BIN SAUD yanke shawarar duk cikin yaran shi mata , wadda ta fara aure , mijin ta zai zama MALIK a bayan ran shi
Cikin wani ikon Allah Autar ABDOUL LATIF BIN SAUD Gimbiya INAS diyar MALIKAT DJAOUDATT ta fara fido da mijin aure a lokacin ta na da shekara 18
Ba a bata lokaci ba MALIK ya aurawa Gimbiya INAS wani yaron babban dan Kasuwa a cikin masarautar Saudia HICHAM BIN JAABAR
Shekara uku bayan auren su su ka haifa kyakyawar diyar su mace wadda ta ci sunan RIANNA BIN JAABAR
Sati daya bayan shigowar ta duniya MALIK ABDOUL LATIF BIN SAUD ya bar duniya shi kuma , MALIK HICHAM BIN JAABAR ya hau karagar mulki
Amma bayan hawan shi mulki ba su kara samun haihuwa ba shi da MALIKAT INAS
Abun ya janyo kananan magaganun a cikin masarautar baki daya , hakan ya sa MALIK HICHAM BIN JAABAR yanke shawarar karo aure
A wannan karan kuma ya auri Gimbiya MOUSSINA babbar y'a ga ABDOUL MUJEEB BIN AHMED sarkin Daular Ottoman a lokacin
Cikin wani ikon Yaron su na farko da namiji ne wanda ya ci sunan AMIR NAWFEL
Shekaru shida bayan shigowar shi duniya su ka sake samun yarinya mace mai sunan AMIRA TESNIM da ga ita ba su sake samun haihuwa ba
Bayan AMIR NAWFEL ya cika shekara 18 MALIK HICHAM BIN JAABAR ya gabatar da shi a matsayin magajin shi , MALIKAT MOUSSINA kuma ta zamo MALIKAT AL'UMU wato mahaifiyar yarima mai jiran gado wanda karfin ikon ta ya fi na MALIKAT INAS
Duk wanna abun da ke faruwa Daular Ottoman na gefe na kallo su na jiran lokacin buga game din na su dan har yanzu ba su hakura da mulkin saudiya baki daya ba , a wannan karnin mulkin saudiya dole zai koma hannun Daular Ottoman
( TSAGAITA CEN LABARI A KAN DAULAR SAUDIYA DAN KAR KU RIKICE DA GA GABA , ALLAH YA SA KUN GANE YAWWA 😴😴😴🤙 )



SIX YEARS BEFORE



DAULAR SAUDIYA 🔥👑



* AMIR NAWFEL



Zaune ya ke cikin wani katafaren garden kun san yadda gidajen saurata su ke , musaman masu mulki da kudi to be sai na kai ga yi muku wasu bayanai ba

Ya na sanye da wasu kaya masu bala'in kyau irin na sarauta ya daura wata Alkyaba fara kal da ga sama
Ya na zaune saman wata sofa mai mugun kyau da laushi , gaban shi kuma wata table ce ta glass shake da fruits da juice , ga uban dogarai a zagaye da shi ta ko ina ko wane ya na rike da wata katuwar sword kamar wanda za su yaki

Shi kuma AMIR NAWFEL ya daga kan shi sama ya lumshe idanun shi kamar mai tunanin wani abu
AMIR NAWFEL hadaden namiji ne , Fari kal da shi kamar ka taba jini ya fito , ya na da dogon hanci kamar pencil , da dan karamin baki , lips din shi red colour ne , shape din na sama ya firo kamar heart , ya na da gashi sosai so smooth mai laushi kuma baki kirin da shi har wani kyali ya ke yi da ga gani ka san ana kula da wannan gashin , ga wani kontancen saje a geffen fuskar shi , a shekaru zai kai 24 haka
A geffen wuyan shi na dama ya na da wani bakin zane ya fito kamar crown an dasa mata Sword a tsakiya , allamun tambarin masarautar ne

Ya na a haka ya ji daura mishi kai saman cinyar shi
Dan karamin murmushi ya saki dan ya san ko wanene , a hankali ya ware idanun shi ya na kallon sama kafin ya sauko da kan shi slowly
Ya na da dara daren idanun idanun farare kal kamar madara , kwayar cikin su kuma Hazel ce mai bala'in kyau kamar mirror

Cikin wata irin zazzakar Murya cike da nitsuwa ya ce " what are you doing here ? " ya fada da turanci

Wata kyakyawar yarinya ce fara kal da ita cikakiyar balaraba , kamanin ta daya da AMIR NAWFEL sai dai ita launin idanun ta baki ne kal a shekaru ba za ta wuce 17 ba , Al-AMIRA TESNIM kenan , Auta ga Malik HICHAM BIN JAABAR

Cikin shagwaba ta fara magana da harshen larabci ta ce " Akhie , wai yaushe za mu tafi wajen papi ne "

Hannun shi ya daura saman kan ta ya na shafawa a hankali
Sai da ya dauki lokaci ya ce " za ki iya tafiya ni dai ba zan je ba "
Ya na gama fadar hakan ya meda kan shi saman ya lumshe idanun shi

Dago kan ta ta yi , ta mike zaune ta na kallon shi ta ce " uhumm uhummm Akhie ni fa........ "
Da sauri ya daga mata hannu ya katse ta , a hankali ya ware idanun ya sauko da kan shi kassa kafin ya mike ya fara takawa ya bar wajen ba tare da ya ce mata komai ba

Da sauri wasu dakarai guda hudu su ka bi bayan shi , ya bar yarinyar nan zaune da sauran dakaran , sai faman hura hanci ta ke

AMIR kuma a hankali ya ke tafiya cike izza kai a sunkuye , da ga ganin takun shi ka san izza a jinin shi ta ke

Ya na tsaka da tafiyar shi , wata arrow ta fado dab da kafar shi
cak ya tsaya , Kallon arrow din ya yi na dan lokaci kafin ya duka a hankali ya dauke ta ya na bin ta da kallo

A hankali ya saki wani cool murmushi , ba tare da ya dago kai ba ya ce ma dakarun shi su je su bashi wuri

Sunkuyar da kai su ka yi cikin girmamawa kafin kowane ya juya ya koma bakin aikin shi

Su na barin wajen ya dago kai ya fara bin wajen da kallo , amma bai ga komai ba
A hankali ya ci gaba da takawar shi har ya nufi wani dan building mai mugun kyau , ga wasu jibga jibgan dakaru zagaye da wajen

Ya na isa wajen duk dakarun su ka zube saman guyiwowin su su na gaishe da shi
Bai bi ta kan gaisuwar su ba ya shiga wajen kai tsaye ya na sallama kassa kassa babu wanda ya ji ta sai shi da ya yi abun shi

Ya na shigowa wajen idanun shi su ka sauka kan wata mace sanye da wando palazzo Fari kal da riga ita ma fara ta na da madauri da ga tsakiya , ta saki wani lalawsan gashin kan ta baki kirin har tsakiyar bayan ta
Ta juyawa kofar shigowa baya , ta na kallo ta cikin wata katuwar Window ta glass

A hankali ya ci gaba da takawa , ya sa hannu ya cire alkyabar shi ya ajiye saman wata table ya daura arrow din a sama

Kamar ta san da shigowar shi , ba tare da ta juyo ba ta ce " calm down , ni ba da niyar fada na kira ka ba " ta fada da larabci

Ya na shirin daukar takobi ta fadi hakan
Ya na jin abun da ta fada ya juya ya fara takawa ya karaso geffen ta ya tsaya ya nade hanayan shi a kirji ya na kallon cikin Window din shi ma

Sai da su ka dauki lokaci a hakan kafin ta juyo slowly ta kale shi
Kyakyawar budurwa ce mai jini a jika , ta so ta dan yi kama da NAWFEL , amma kuma kama ta jini , sannan launin idanun ta hazel ne kamar na shi bayan haka ba abun da ya yi kama tsakanin su , a shekaru za ta kai 27 haka ina kyautata zaton wannan ita ce RIANNA BIN JAABAR

Cikin sanyi murya ta ce " Amir , wai me ya ke damun ka ? "

Girgiza mata kai ya yi ba tare da ya kale ta ba allamun ba komai
Hannu ta kai ta shako wuyan shi ta kai mishi bugu a ciki , ta na fadin " Wa za ka yiwa miskilanci , kar ka manta na girme ka fa "

" Please Ukhtie let me " ya fada cikin siririyar murya
Sakin shi ta yi kafin ta sa hannu ta tura shi kadan har ya yi baya zai fadi
Cikin zafin nama ya taro kan shi ya mike tsaye ya na kallon ta

Nade hanayan ta ta yi a kirji ta na kallon shi ta ce " za ka fada min ko sai na karaya ma ka hannu " ta kai karshen ta na daga mishi gera guda

Ajiyar zuciya ya sauke , kafin ya ce " wlh ki na son takura min dayawa ni na fada miki ba abun da ke damu na "
Ya kai karshen ya juya , ya fara takawa ya na neman ya bar wajen

Da sauri ta sa kafa ta tade shi , ya fadi dib ga kassa
A hankali ya dago ya mike zaune ya na kallon ta ya shagwabe fuska kamar karamin yaro ya ce " wai me na yi miki da za ki dake ni haka in da kin ji min ciwo wlh sai na fadawa Abbi "

Yar karamar dariya Ta yi kafin ta zaune kassa ita ma ta na kallon shi ta ce " ban son shirme AMIR wa za ka yi wa shagwaba , ko kunya ta ba ka ji , ni yanzu fada min , mi ke damun little brother di na " ta kai karshen cikin zolaya

Kauda kai gefe ya yi ya na dan turo karamin bakin nan nashi ya ce " ni kyale ni ba abun da ke damu na "
Dariya sosai ta yi , ta na kallon shi ta ma rasa abun da za ta ce mishi
[16/09 à 09:57] M.N.M:

❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤

(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥





( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




⚘🕊 MALLAKIN MEERAH 🕊⚘

【 CUTIE PIE 】




Marubuciyar littafin :【 TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 】




YOU CAN FOLLOW MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i




BOOK .............. 2 🌹👑





【 THE ROYALTY LOVE ✌👑🌹】





________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊________________





P A G E 2 ❤ 🔥





Dawo kallon shi ya yi kan ta ya na matse gera ya ce " ki bar min wannan dariyar ta ki ta keta "

Tsagaita dariyar ta ta yi kafin ta ce " okay , okay , Akhie fada min me ya ke damun ka "

Sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " Ukhtie , Abbi ya ce gobe zan fara bin shi fada , dan in ga yadda ke kula da masarauta "

" okay , minene matsalar to , ko ba ka son zuwa " ta tambayeshi

" ni fa na fada mishi ba ni son zama MALIK bayan shi amma ya ki sauraro na " ya fada cikin sanyi

Daura hannun ta ta yi saman kafadar shi ta ce " in tambaye ka , in ba ka hau mulkin Saudiya ba , me za ka yi , kai kadai ne fa yarima cikin ahalin mu "
Dan turo baki ya yi cikin shagwaba ya ce mata " ni na fada mishi company Sarrafa petroleum na ke son budewa , kar ki manta ko a school business na ke karantawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login