Showing 30001 words to 33000 words out of 47249 words
sai da ya gama goge mata hawayen ta sannan ya janye hannun shi ya ce " kin yi breakfast ? "
a hankali ta gyada mishi kai allamun eh
" yaushe ki ka fara yi min ƙariya "
" ni gaskia ce na fada maka , ka tambayi Ammie "
" shikenan , minene matsalar to ? " ya fada ya na dan lekon face din ta
girgiza mishi kai ta yi ta na fadin " babu komai "
" dago ki kale ni to "
ba tare da ta dago kai ba ta ce " yaya Zayd don Allah tashi ka yi tafiyar ka "
dan zaro idanu ya yi ya na kallon ya yi mamakin abun da ta fada
" kora ta ki ke yi ne ? " ya fada
ba ta ce mishi komai ba ta juya ta sauko da kafafun ta kassa ta tashi ta nufi toilet da gudu ta shige ta medo kofar ta rufe
ta na shiga ko ta saki kuka mai cin rai har sai da ya jiyo sautin kukan
da sauri ya diro da ga saman gadon ya nufi toilet din ya tura kofar ashe ba ta sa key ba
ya na shigowa ya tardo ta zaune bakin bath ta sunkuyar da kai ta na kuka
nufar ta ya yi bai ce mata komai ba ya sa hannu ya dauke ta cak kamar baby ya juya ya bar toilet din
ta na jin ya dauke ta ta fara wuntsila kafafu ta na fadin " yaya Zayd ni ka sauke ni "
bai dire ta ko ina ba sai saman bed din ta
sannan ya juya ya nufi door ta dauka fita zai yi kafin sai ta ga ya tura kofar ya rufe ya juyo ya dawo cikin dakin ya nufi bed din
ta na ganin ya nufo ta , ta yi sauri ta mike zaune ta juya daya geffen ta na shirin sauka
kafin ma ta sauko da kafafun ta kassa ya karaso wajen bed din ya riko hannun ta da karfi ya meda ta konta
ya Haye saman gadon , ya riko hannayan duka biyu da hannu guda a saman kan ta saman ya sa dayan hannun ya ware kafafun ta ya shiga tsakiya sannan ya kawo face din shi saitin ta ta
tsuke gera ta yi ta na fadin " yaya Zayd ka sake ni , na tafi "
" yi min shiru , yaushe ki ka fara meda min magana ? " ya fada sam babu wassa a tare da shi
turo dan bakin nan nata ta yi ta kauda kai gefe dan ba ta jure kallon cikin idanun shi
a hankali ya kai bakin shi saitin kunen ta murya cen kassan makoshi ya ce mata " i'm sorry , ba zan sake ba "
ya na gama fadar haka ya ji ta sauke wata nanauyar ajiyar zuciya
slowly ya saki hannayan ta sannan ya sauka da ga saman ta , ya koma gefe ya zauna
ya na sauka ita ma ta mike zaune ta na sa hannu ta na goge face din ta ta ce " ka san ba za ka zo ba shi ne ka ce min za ka zo , tun safe na ke jiran ka , amma ka manta da ni "
" ban manta da ke ba " ya fada ya na riko hannun ta
a hankali ta ta fada jikin shi ta rungume shi ta na fadin " ni na ma yi fushi da kai "
zagayo da hannayan shi ya yi a bayan ta ya rungume ta shi ma sannan ya ce mata " Shikenan sake ni tun da kin yi fushi , ni ma na yi fushi "
yar karamar dariya ta yi ba tare da ta ce komai ba ta lumshe idanun ta
a hankali ya yi geffen damar shi ya konta da ita a jikin shi , a hankali ya fara shafa bayan ta ya lumshe idanun shi , shi ma
nan take kamar da wassa barci ya dauke su a tare a haka su na manne da juna
▪AFTER SOME HOURS
sannu sannu har sai da su ka share wajen good two hours su na barci a haka
a hankali Amir ya bude idanun shi ya na karanto kalmar shahada
ya na bude idanun shi su ka sauka kan Inaya da ke ta faman barcin ta cikin konciyar hankali
a hankali ya zame hannayan shi , ya mike zaune a hankali ya kai hannu ya dauki Sneakers din shi ya saka , sannan ya mike tsaye ya dan juya ya kale ta na dan lokaci kafin ya juya ya fara takawa ya fice dakin , ya na fitowa parlour ya ga babu kowa
bai tsaya neman su ba ya sa kafa ya fice part din
har ya nufi building din su , wata zuciyar ta ce mishi ya tafi wajen MALIKAT AL'UMU
a haka ko ya juya ya nufi part din MALIKAT AL'UMU
bakin shi dauke da sallama cen kassan makoshi ya shigo part din
a tare Rouksar da Tesnim su ka kai kallon su wajen kofar su na amsa mishi sallamar
wani kyawatencen murmushi Rouksar ta saki , ta na shirin yi mishi magana ya riga ta cewa " Tesnim where is mom ? " ya fada ya na kallon Tesnim
" ta na wajen Mamie " ta ba shi amsa
gyada kan shi ya yi a hankali kafin ya juya ya fara takawa
da sauri Rouksar ta mike ta bi bayan shi
Tesnim na kallon ta amma ba ta ce mata komai ba har sai da ta fice
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
💔🥀 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) 💔🥀
👑❤ MALLAKIN MEERAH ❤👑
【THE ROYALTY LOVE 👑🕊💖】
Marubuciyar littafin
【TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺】
【 BOOK …………………… 2 ❤ 👑】
____________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊___________________
PAGE 11 ✍📚
ya na tsaka da tafiyar kawai ya jiyo Muryar Rouksar a bayan shi ta na fadin " Amir ! Amir ! "
ko juyo wa bai yi ba bare ya amsa ta , har yanzu bai manta abun da ta yi wa Inaya ba , ita ba ta san da ya ga komai ba
da sauri ta sha gaban shi ta tare mishi hanya ta na fadin " Amir tun dazu fa na ke biye da kai , ka na ji na ka kyale ni "
kallon ta ya yi na dan lokaci kafin ya ce " ban hanya na wuce " ya fada dan ya fi karfin ya raba ta geffen ta dan ya wuce
kashe mishi murya ta yi ta na cewa " Akhie ni fa kawai gaishe ka na taho yi , ba na samun damar ganin ka , kuma Tesnim ta ce min za ku yi tafiya ko ban kwana ba mu yi ba " ta kai karshen ta na marairaice murya
a hankali ya lumshe idanun shi ya na furza iska da ga bakin shi kafin ya bude idanun shi slowly ya kale ta ya ce " okay ! yanzu zan je na yi sallat , zuwa yamma ki same ni a garden "
dan zaro idanu ta yi ta na washe baki ta ce " Da gaske ? "
gyada mata kai ya yi kafin ya ce " eh , zan iya wucewa yanzu "
da sauri ta koma gefe ta ba shi hanya
" thanks " ya fada cen kassan makoshi kafin ya fara takawa ya bar ta nan tsaye
tsaya wa ta yi ta na bin shi da kallo har dai ya bacewa ganin ta sannan ta saki wani makirin murmushi ta juya ita ma ta koma part din MALIKAT AL'UMU
Shi kuma Amir kai tsaye Part din su ya nufa , bai tsaya ko ina ba sai a floor na uku
ya na shigowa parlour ya tardo Diya zaune tare Malik su na hirar su kamar abokan juna
Malik na ganin shi ya ce " Amir ina ka shiga kuma ban gan ka a mosque ba yau ? "
ko sannu Amir bai ce mishi ba ya nufi corridor ya shige Bedroom din shi
ya na shiga Diya ya bushe da dariya ya na fadin " ran ka shi dade , ai ba zai iya fada muku ba , amma ni na san da ga wajen babyn shi ya ke "
dan tabe baki Malik ya yi ya na fadin " tooooo , abun haka ne ? amma ka ga dan rainin sens ya ke ce min wai shi ba ya son ta "
" Ran ka shi dade wlh ba gaskiya ba ne , Tun lokacin da ya sauke ido saman yarinyar nan ya kamu da son ta tsawon shekara shidda biyar yanzu , ka san yadda Izza ta ke bare ta hadu da Mulki..... " da sauri Diya ya rufe bakin shi ya na dan zaro idanu ya ma manta da wa ya ke magana
yar karamar dariya Malik ya yi kafin ya ce " When LOVE MEETS POWER , ba za ka ji da sauki ba "
ya na kai karshen ya na sakin wani cool murmushi dan abun ya tuno mishi tarihin soyayyar shi da MALIKAT INAS , shi ma da farko haka ta dinga yi mishi irin wannan jan aji , ita ga ta daughter din Malik guda
ya yi nisa cikin tunanin shi ya jiyo Muryar Diya ya na fadin " har yanzu ya kassa yarda da abun da ke cikin zuciyar shi , amma so dai Amir ya na mutuwar son yarinyar nan , izza ce ta yi mishi yawa ba zai iya bude baki ya ce ya na son ta "
" kenan jira ya ke ta ce ta son shi ? "
a hankali Diya ya girgiza mishi kai ya na murmushi ya ce " ta jima da ta fada mishi wannan kalmar ta so , amma bai karba "
cikin nitsuwa Malik ya katse shi da cewa " nan gaba kadan zai karba , tun da har ya karbe ta a matsayin matar shi ta sunna , kuma ya na son ta cikin zuciyar shi , nan gaba kadan zai bude baki ya furta mata wannan kalmar "
" in sha Allah ran ka shi dade , nan gaba kadan za ka fara ganin jikokin ka "
yar karamar dariya Malik ya yi kafin ya ce " haba Diya ina wannan babyn za ta iya daukar Amir , ai shi ya san dalilin da ya sa bai karbi soyayyar ta ba , ba dan ba ya son ta sai dan ya san kan shi , ya san halin kan shi in dai ta wannan fanin ne , ba karamin jarabbabe ba ne , na san haduwa guda za su yi , ku tafi jinyar watanni "
dariya sosai Malik da Diya su ka yi a tare , kai gulma dadi 🤣🤣
hayala yau dai Malik da Diya sai da su ka bude wa Amir na shi zaman
shi kuma Amir ya na Shiga Bedroom din shi ya wuce kai tsaye cikin toilet
jim kadan ya fito daure da towel a kugunshi ya wuce kai tsaye dressing room
nan ma bai wani dauki lokaci ba ya fito sanye da wata jallabiya fara kal mai dogayen sai baza kamshi yake
ya na fitowa ya nufi wajen da daddumar shi ke shinfide ya Haye ya tada sallar shi cikin nitsuwa
bayan ya Kamala ya zauna ya na karatun kur'ani har sai da lokacin sallar la'asar ya zagayo ya tashi ya gabatar da ita
bayan ya Kamala ya yi aduo'in shi , ya mike tsaye ya cire jallabiyar jikin shi ya tila ta saman bed din sannan ya nufi bed din ya Haye ya yi rub da ciki , ya lumshe idanun shi , tun da ya dawo cikin masarautar ya ke jin wata muguwar kasala ta rufe shi , ba shi da aikin yi sai barci
bari mu leko wani bangaran na cikin masarautar kafin ya tashi
* DAMBA
zaune ya ke kassan Bishiyar nan dai , kamar kullum yau ma ya na cikin wadanan bakaken kayan na shi , ya rufe fuskar shi da bakin rawani , idanun shi kadai a ke iya gani
Rouksar na tsaye a gaban shi ta na fadin " Shirin mu ya fara tafiya yadda ya dace "
dan gyada kan shi Damba ya yi kafin ya ce " Tukunna Shirin mu bai fara ba "
cikin rudu Rouksar ta ce mishi " Ban gane abun da ka ke nufi ba , a sani na shirin mu shi ne na janyo hankalin Amir gare ni "
cikin nitsuwa Damba ya daga mata hannu ya katse ta sannan ya ce " Shiri na daban na ki daban , amma nan gaba za ki sani , ke dai ki yi kokari ki shawo hankalin Amir gare ki , tabass zai bukaci macen da za ta kontar mishi da hankali bayan dawowar shi da ga Makkah "
" Ni fa sam ban gane abun da ka ke fada " Rouksar ta fada dan ya na neman ya juya mata shirin da ta yi dangane da Amir
wata shegiyar dariya Damba ya yi sannan ya ce " Za ki gani nan gaba kadan " ya na gama fadar haka ya bace bat a wajen
ya na barin wajen Rouksar ta saki wani dan karamin tsaki ta na fadin " za ka ga abun da na shirya maka ! " ta na gama fadar haka ta saki wani makirin murmushi sannan ta bace bat ita ma
▪AMIR
misalin karfe 8 na yamma su na zaune a cikin dining room din Part din Malik kamar kowa ne dare dan su dining
kowa ya nitsu ya na cin abincin shi
Amir kuwa ya sunkuyar da kai sai juya spoon din shi ya ke cikin Plate din , da allamun hankalin shi na nesa
su na a haka su ka jiyo Muryar Malik ya na fadin " MALIKAT INAS , in sha Allah zuwa gobe za a kai miki kudin da a ke fitar wa sadaka kowace shekara wannan shekarar ke za ki raba "
har hada baki MALIKAT INAS da MALIKAT AL'UMU su ke su na fadin " amma ran ka shi dade ba ....... "
cikin nitsuwa ya daga musu hannu ya katse su sannan ya nuna Amir ya ce " ku tambaye shi , shi ya bada shawarar "
a tare su ka jiyo su ka kali Amir da ke ta faman juya spoon din shi , da allamun ba ya ma tare da su
su na ganin hakan kowace ta ja bakin ta , ta yi shiru dan sun san ko sun yi maganar ba zai amsa musu ba
haka su ka ci gaba da cin abincin su har sai da su ka Kamala kowa ya tashi ya yi tafiyar shi , Amir kuma ya koma bedroom din shi , da allamun yau na miskilancin su ka mishi busa
▪AFTER SOME DAYS
Tun safiya Manya' manyan motoci su ke shigowa Filin Daular
da ga Sarakunan masarautun da ke karkashin Daular saudiya har da ahalin Malik da kan shi da mazaunan fadar da ahalin su , kowa zowa ya ke ya na yi wa Malik da Amir Allah kiyaye hanya , ma su yi tsakani da Allah na yi , ma su muguwar manufa a zuciya su ma na nasu
Malik kuwa farin ciki ba a magana hakan ba karamin dadi ya yi mishi ba , Musaman ya sanya a ka shirya musu wallima dan tarben baƙin shi
▪MISALIN KARFE 10 NA DARE
duk Sarakunan da su ka zo yi wa Su Malik ban kwana kowane ya koma gidan shi , ahalin Malik ne kawai su ka yi saura
a wannan lokacin babu kowa cikin parlourn Malik sai Hussein , da Mohammed tare da Ahalin su , Gimbiya Manisha yarinyar MALIKAT Houda matar Hussein
sai kuma Gimbiya Aysher Yarinyar MALIKAT Youssra matar Mohammed
kowace ta na tare da yarinyar ta guda , da sunnan sun zo yi wa Amir Allah kiyaye hanya
yan mata ne biyu ma su jini a jika renon madara da ice cream ga kuma jinin Sarauta , ba laifi duk sun hadu iya hadu ga kyawo Masha Allah
Muntaz shi ne sunan ta wajen Gimbiya Manisha , a shekaru za ta kai 24 Haka
sannan kuma ta wajen Gimbiya Aysher , Hafsat a shekaru za ta kai 21 years
tun da su ka shigo parlourn Malik babu wanda ta ce ma yar uwar ta ufan wai su ji'ji da kai
sai tsuke fuska su ke su na shan tsami , su kali nan , su kali nan su na duba Amir , amma ina ko hango Bedroom din shi ba su yi
Su na a haka su ka jiyo wani mugun qamshi mai dadi ya daki hancin su , a tare duk su ka kai kallon su wajen da su ka jiyo qamshin
sun dauki wajen good on minutes a haka kafin Su ga Amir ya fito da ga cikin Corridor kai a sunkuye ya na latsa wayar shi
ya na sanye cikin wasu Tracksuit Farare kal , rigar ta na da hula , an Rubuta NIKE da launin Black da ga gaban ta , kafafun shi kuma cikin wasu sneakers Farare