Showing 9001 words to 12000 words out of 47249 words

Chapter 4 - Exiled Prince Book 2 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

288

karamar dariya DIYA ya yi kafin ya ce " AMIR na ce maka da ga Daular Ottoman na ke , tambayar da za ta fito da ga bakin ka shi ne in ina da ruwa , a ka je kashe ka a ka turo ni kassan ka na da makiya dayawa a saudiya "

" ku ta shafa , ko kashe ni ka zo yi , ko ma minene matsalar ka ce , ka na da ruwan ne ? "

Girgiza mishi kai DIYA ya yi ya na fadin " ba ni da , ban fito da komai ba sai kaya na , shi ma wani uziri ne ya biyo da ni masarautar Saudia , da tun da ga cikin masarautar Ottoman zan shi ga jirgi na bar kassar nan "

Jinjina kan shi AMIR ya yi bai ce mishi komai ba
Sai da su ka iso airport din a haka kafin ya ce mishi " yanzu wace kassa za ka je ? "

Sai da DIYA ya yi parking din motar shi a parking space sannan ya juyo ya kali AMIR ya ce " gaskia ban sani ba , duk inda duniya ta kai ni , ba zan maka karya ba ina son adventure , dalilin da ya sa ma baro Daular Ottoman "
bude kofar shi AMIR ya yi kafin ya ce " shikenan tashi mu je "
Da sauri DIYA ya ce mishi " ina kuma za mu je yi Ran ka shi dade "

Juyo wa AMIR ya yi ya kali DIYA sannan ya ce "ka ce min ba ka san inda za ka je ba , ni ma ban san inda zan je ba , dan haka ka tashi mu tafi inda kaddara za ta kai mu , idan kuma ba za ka bi ni ba okay , sai wata rana in mun hadu " ya kai karshen ya na sauka da ga cikin motar

Da sauri shi ma DIYA ya sauko ya bude gidan baya ya sauko da trolley din shi da wata jakar sannan ya rufe ya bi bayan AMIR da sauri

Dai'dai lokacin da ya ke shiga cikin airport din DIYA na biye da bayan shi
Ya yi sa'a ko wajen babu kowa sai wasu security guda hudu da ke tsaron wajen , su na ganin shi duka su ka daga hannu su na sara mishi

Bai bi ta kan su ba ya nufi wajen sayan ticket
Receptionist na ganin shi ta mike da sauri ta na gaishe shi

Bai bi ta kan gaisuwar ta ba ya ce " akwai jirgin da zai tashi yanzu "
Cikin girmamawa ta ce mishi " yes Sir , amma AFRICA-Nigeria ya nufa "
" ba laifi shi za mu shiga " ya kai karshen ya na bude jakar shi ya ciro bandir din Dollar uku ya ajiye gaban ta

Murya na kerma ta ce mishi " I'm sorry Sir , jirgin ya cika , sai dai ku jira gobe akwai wanda zai tashi karfe 5 na yamma "

Matse gera AMIR ya yi ya wurga mata wannan mugun kallon na shi cike da izza ya ce mata " ko da saman kan pilot ne zan zauna , idan ki ka bari jirgin nan ya tashi babu ni a ciki , ki tabbatar gobe ba za ka ki dawo aikin nan ba , dan haka gwara ki dauki kudin nan ki ja bakin ki yi shiru ki ba mu ticket tun ina miki cikin ruwan sanyi , idan kuma ki ka bari rai na ya baci za ki ji karkashin kassa "

Wasu yawu ta hadiye da karfi murya na kerma ta ce " i'm so......rry sir "
Ta na gama fadar haka ta shiga shirya musu ticket
Babu ko na gode AMIR ya dauki ticket din nan ya yi gaba abin shi
Shi dai DIYA ya na biye da bayan shi ba ya da abun cewa karfin ikon AMIR ya fi na shi nesa ba kusa ba
A haka su ka shiga cikin jirgin nan duk da a cike ya ke , bangaran Flight attendant , su ka zauna har sai da jirgin ya daga A karfe 3 dai'dai ya nufi Nigeria ba tare da sun san abun da ke jiran su a cen ba
[16/09 à 09:57] M.N.M:


❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤


(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥




( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




⚘🕊 MALLAKIN MEERAH 🕊⚘



【 THE ROYALTY LOVE ✌👑🌹】






Marubuciyar littafin :【 TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 】







BOOK .............. 2 🌹👑







________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊________________




PAGE ________4 ❤🔥




* PRESENT DAY


* ZAYD



" bayan mun baro Saudiya mu ka shigo Nigeria , da farko a Abuja mu ka sauka , bayan mun yi wasu yan kwanaki , na saye wani company na sarrafa bakin oil da a ka saka a kasuwa , da ya ke su na jin turanci sai abun bai zo da matsala ba , bayan wasu watanni mu ka koma Kano da zama cikin wata yar karamar unguwa , amma duk mutanan wajen daya biyu ne ke jin Larabci da Turanci , hakan ko ba karamin dadi ya yi min don ko magana mutun ya yi min ba na gane wa sai na yi shiru na , da ga haka har su ke min daukar kurma , da makaho saboda yawwan saka glass da na ke dan boye idanu na , sannu sannu Har DIYA ya koyi haoussa ta zauna a harshen shi , ya koya min ni ma amma duk da hakan ba na yi wa kowa magana duk da a yanzu ina gane abun da su ke fada , a shekarar da mu ka dawo Kano ,Allah ya hada ni da wannan family inda su ka dauke mu kamar yan uwan su , ban san abun da ya sa wannan familyn ke kaunar mu haka dan har abincin dare su ke aiko mana idan kuma DIYA ba ya nan mai gidan da kan shi ya ke zowa ya gayace ni zuwa gidan shi dan na ci , a haka rayuwa ta ci gaba , amma har ga Allah kullum ina tunanin ku , ina kuma tunanin komawa gida , kawai lokacin ne sai yanzu ya zo " ya kai karshen ya na dago kai ya kali mutanan cikin dakin

Kuka Ne ya kubce ma TESNIM ta sa hannayan ta biyu ta rungume shi ta na fadin " Akhie why za ka tafi ka barni , ka san irin kewar ka da na yi "

Dan bubuga bayan ta ya yi ya na shirin magana Malik ya riga shi cewa " kenan part di na da a ka kona kai ka ba da umarnin hakan "

Girgiza mishi kai Zayd ya yi kafin ya ce " no ba ni ba ne , a ranar bayan na baro dining room na tafi parlourn , na zaune saman sofa na jiyo Muryar Wasu da ga cikin masarautar su na fadin yadda za a yi su kona part din Malik , amma su tabbatar da AMIR na ciki , jin hakan ne ya sa na tashi na koma saman kujerar ka na zauna ina kallon duk wani abu da su ke yi , amma ban ga face din su ba saboda sun saka rawani , nan ne wata Idea ta zo min , na yi anfani da wannan damar dan na bar masarautar , Saboda pressure ta yi min yawwa , ba ni da yancin kai na a cikin masarautar nan , duk wani abu da na fada maka ina so ba ka saurare na , sai ka ce min wai dole sai na hau mulki , al'halin na fada maka ba ni so ba ni so "

Ya kai karshen ya na kauda kai gefe , nan ya ga Inaya ta kure shi da idanu sai zubar da hawaye ta ke
Nan take idanun su , su ka sarkafe cikin na juna

Ya na a haka ya jiyo Muryar Malik na fadin " Ka yi hakuri AMIR , na san da na saurare ka da duk wannan abun bai faru ba "

Cikin nitsuwa ya katse shi da cewa " no Dad , gwara hakan da ta faru ko ba komai na samu damar haduwa da wannan ahalin "

Dan karamin murmushi Malik ya yi kafin ya ce " Shikenan yanzu sai ka tashi mu koma gida , mun ci gaba da kula da kai a cen "

" no Dad , ka yi hakuri ba zan iya tafiya na bar Family na a nan "

Malik na shirin magana MALIKAT AL'UMU ta daura hannun ta saman na shi
Dawo da kallon shi ya yi gare ta
Nan ta girgiza mishi kai kafin ta juya ta kali ZAYD ta ce " AMIR duk yadda ka ke so haka za a yi , amma nan da one hour za mu bar garin nan "

Gyada mata kai ya yi kafin ya daga ya kali DIYA ya ce " to kai malam , sai ku koma gida kai da ABDOUL ou shirya mana kayan mu , ku taho da mama , sai mun hade a airport "

Dan sunkuyar da kai DIYA ya yi cike da zolaya ya ce " an gama ya shugaba na "
Dariya sosai MALIK da TESNIM su ka yi
Sannan DIYA ya ce ma ABDOUL su tafi , ba musu ABDOUL ya bi shi su ka fice dakin

Su na fita ita ma Inaya ta mike Slowly ta bar dakin
Da sauri Nesrine ta tashi ta bi bayan ta dan ta ga allamun ba cikin hayacin ta ta ke ba

Da kallo Zayd ya raka su har sai da su ka fita sannan ya raba jikin shi da na TESNIM ya mike a hankali ya fice shi ma

Da kallo Malik ya raka shi har sai da ya fita sannan ya yi yar karamar dariya yi ce " MALIKAT ina ga ba a banza yaron ki ya ki tafiya ba , ya fada tarko ne "

Cike da rudu TESNIM ta ce " Abbi wane irin tarko kuma "
" na soyayya " ya fada a takaice
Yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mishi " haba Abbi, wannan babyn ? Ko ni fa na girme mata ba ma ita ba duka su biyu "

" TESNIM ba ki san soyayya ba ne , ba ruwan ta da shekaru , amma za ki gane hakan duk ranar da ki ka fada soyayya ke ma "
Dan tabe baki TESNIM ta yi ta na girgiza kan ta ba tare da ta ce komai ba

Bangaran Inaya kuma , ta na fitowa ta zauna saman Waiting chair da ke bakin kofar dakin
Ta na zama Nesrine ta karaso gaban ta ta tsaya ta na kiran sunan ta
Kamar da ga sama ta jiyo Muryar Zayd ya na fadin " Cutie are you okay ? "

Slowly ta dago kai ta kale shi , ya na tsaye geffen Nesrine
Dan karamin murmushi ta saki kafin ta jinjina mishi kai, ta mayar ta sunkuyar da shi
A hankali ya kira sunan Nesrine
" na'am " ta fada ta na juyawa ta kale shi
Da kai ya yi mata allamun ta koma cikin dakin , ba musu ta juya ta koma cikin dakin ta ba su waje

Da kallo ya rakata har sai da ta shiga dakin sannan ya tako a hankali ya zauna saman chair din da ya ke geffen ta
Cikin sanyin murya ya ce mata " cutie fada min me ya ke faruwa , ko yanzu kin daina so na ne tun da kin ji ko ni wanene ? "

Murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " soyayyar ka ta zama wani bangare na cikin zuciya ta , mutuwa ce kadai za ta iya fitar da shi , kawai dai na ji dalilin da ya sa ba za ka iya so na ba , ni ba ajin ka ba ce , sai dai na zama mai maka shara da wanke wanke , ka fi karfi na yaya Zayd , don Allah ka yi hakuri ka yi tafiyar ka , ka bar mu a nan , ko ba komai zan rage radadin soyayyar da ba zan taba samu ba "

A hankali ya lumshe idanun shi ya bude su sannan ya ce mata " ba zan iya tafiya na bar ku a nan ba gaskiya , inda ma a ce malam na raye , amma ba ya nan , ban san irin abun da zai faru da ku bayan tafiya ta ba , ni fa ba shawara na ke ba ki ba umarni ne "

Yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " nan fa ba masarautar ta ka ba ce , ba ka da ikon ba ni umarni "

Cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " amma ina iya ba ki umarni a matsayi na na mijin ki "

Wani cool murmushi ta saki ta dago kai slowly ta kale shi ba tare da ta ce komai ba
Sai da ta gaji da kallon shi sannan ta meda kan ta , ta sunkuyar
A hankali ya dan sunkuyar da kai ya leko face din ta ya ce " Wannan murmushin kuma na meye , ko ba za ki bi mijin ki ba "
Kauda kai gefe ta yi ta na ci gaba da murmushin ta wanda ita kadai ta san na minene
Ta na haka kawai ta ji ya rungumota ya hada kan ta da kirjin shi cikin sanyin murya ya ce " na ji dadi da babu abun da ya same ki , ba ki san irin sanyin da na ji cikin zuciya ta lokacin da na bude ido na gan ki "
Dan karamin murmushi ta saki ta na kara lafewa a jikin shi

Sai da su ka dauki lokaci a haka kafin ya sake ya tashi ya ce su koma ciki
Noke mishi kafada ta yi cikin shagwaba ta ce mishi " ni ba zan koma ba "
A hankali ya koma saman chair din ya zauna ba tare da ya ce mata komai ba ya san bai wuce ta ce ta na jin kunyar Malik ba

A haka su ka zauna a wajen ba wanda ya sake cewa uppan har sai da Diya da Abdoul su ka dawo su ka same su a nan

A tare su ka saki wani kyawatencen murmushi kafin Diya ya ce " AMIR za mu iya tafiya ko sai ka ida hira da babyn ka ne "

Dan karamin tsaki Zayd ya yi kafin ya mike tsaye ya fara takawa ya yi gaba
Ya na barin wajen Diya ya kali Inaya ya ce " Gimbiya , tashi ku je "
Jinjina mishi kai kawai ta yi kafin ta mike a hankali ta bi bayan shi , ta na fitowa ta hango shi tsaye wajen wata dankareriar mota fara kal , mama na ciki zaune ya na yi mata magana ,
Wajen su Inaya ta karaso , ta na tsayuwa wajen ya ce mata ta shiga motar
Ba musu ta bude ta shiga motar , shi kuma ya juya ya nufi wata motar daban ya shiga
Abdoul da Diya kuma su ka nufi cikin dakin , Diya ya ce wa Malik za su iya tafiya yanzu

Ba musu duka su ka tashi su ka fito dakin su ka baro Hospital din , cikin wasu irin manyan motoci ma su nunfashi
Inaya da Nesrine su ka shiga mota guda tare da mama
TESNIM da MALIKAT su ka shiga mota guda
Abdoul shi kuma tare da Diya
Sannan Malik da AMIR su ka shiga mota guda su ka bar Hospital din
Kai tsaye airport su ka nufa cikin konciyar hankali
Su na isa ko ten minutes ba su yi ba jirgin su ya daga dama cikin private jet din su Malik su ka zo , to cikin shi kuma su ka bar Nigeria


* AFTER SOME HOURS


* SAUDI ARABIA

Misalin karfe 9 na dare jirgin su ya sauka a kassar Saudiya
Airport din cike ya ke da ga Sojoji da dogarai , duk mutanan wajen da idanun su su ka sauka kan AMIR sai da su ka sha jinin jikin su
Shi kuma AMIR ko a jikin shi , ko kallo ba su ishe ba kai tsaye ya nufi wajen motocin da a ka tanada musu , kowa ya shiga su ka bar airport din da mugun gudu kamar za su tashi sama

Cikin abun da bai fi ten minutes su ka iso Daular saudiya
Ba su Inaya kadai ba , har shi AMIR sai da ya yi mamakin ganin irin gyaran da a ka yi wa Daular ta zamo mishi kamar sabuwa
Har building din Malik da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login