Showing 39001 words to 42000 words out of 47249 words

Chapter 14 - Exiled Prince Book 2 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

293

jikin ta sai dan wandon ta da bra
da gudu ta juya ta nufi Dressing room ta shige
yar karamar dariya RIANNA ta yi ta na girgiza kan ta kafin ta juya ta fice dakin ta nufi hanyar parlour

ta na fitowa MALIKAT INAS ta ce mata " kin tashe ta ? "
gyada mata kai RIANNA ta yi ta na karasowa cikin parlourn ta na fadin " an riga ni " ta kai karshen ta na zama a kassa saman carpet

ta na zama Inaya ta fito da ga cikin corridor
nan ta tardo Su zaune har da Nesrine saman carpet ka kayan sahour nan tsakiyar su
a haka Inaya ta karaso ta zauna kusan Nesrine ta na faman murza ido da hannu guda

bari na takaice muku labarin , Haka watan Azumi duk ya share Inaya ba ta fito part din MALIKAT INAS ba , da ga Parlour sai bedroom , kullum ta na cikin daki da ga barci sai Sallat da karatun kur'ani , in dare kuma ya yi Amir ya kira ta , tai ta yi mishi zuba ya na sauraron ta , har barci ya dauke ta ba ta sani ba
ranar da a ka fara azumi MALIKAT INAS ta fitar da kayan sadaka duk yadda Amir ya fada mata hakan ta yi ko ,
MALIKAT AL'UMU ma ba baya ba
tun Ranar da Aysher da Hafsat su ka shigo masarautar ba su sake fita ba , ko wace ta na wajen kakar ta wai da sunnan sun zo wajen Amir , mutumin da ba ma ya cikin masarautar
bangaran Amir kuwa ya na sha tsokana wajen Malik , har wata yar rama ya yi duk cikin rashin Inayar shi bawan Allah har ya ban tausayi


▪AFTER ONE MONTH


kwana biyu bayan Sallar Azumi Amir da Malik su ka fara shirye shiryen dawowa Daular Saudiya , a ranar kuma wani mugun Abu ya faru da su


▪INAYA


a hankali ta fito da ga cikin corridor , ta na sanye da wata Abaya Black color mai mugun kyau , babu veil a kan ta , ta saki wannan lalawsan gashin kan shi

ta na shigowa ko Azim ya shigo parlourn ya na Sallama
da sauri ya nufi gaban MALIKAT INAS ya Zube saman guyiwowin shi , murya na kerma ya ce mata " Gaisuwa na ke ran ki shi dade , Amir na bukatar ganin ku da gagawa a fada "

kallon juna su ka yi MALIKAT INAS da RIANNA su ka yi cikin rudu MALIKAT INAS ta ce " Amir har ya dawo ? "

" eh ranki shi dade , kuma ya na bukatar ganin ku a fada yanzun nan , tare da AMIRA RIANNA "

gyada kan ta a hankali RIANNA ta yi kafin ta ce " Za ka iya tafiya , mu na nan zuwa "
ta na gama fadar haka ta ga Azim ya mike da gudu ya juya ya fice parlourn
mikewa tsaye RIANNA ta yi ta na fadin " mu je ko Ammie , Baby ki jira mu ina zuwa kin ji ko ? "
da to Inaya ta amsa mata kafin ta juya ta koma cikin corridor ta koma bedroom din ta

ta na komawa MALIKAT INAS ta mike ta bi bayan RIANNA su ka fice part din baki daya

kai tsaye babbar Fada su ka nufa
tun da su ka karaso bakin kofar Fadar , su ne jin koke² , da muryoyi su na tashi

a dubu dari RIANNA ta shiga fadar babu ko sallama
ta na shiga ko sai saman , Gawar Malik konce Tsakiyar Fadar , an rufe shi da wani Farin Tissu
ga Amir tsaye Bayan shi ya zuba mishi ido , ya na rike da hannayan shi a baya

wata irin razananiyar kara ce RIANNA ta saki ta nufi Gawar Malik , kafin ma ta karaso wajen gawar ta silale a kassa sumamiya
MALIKAT INAS kuwa ta yi sumar tsaye ta tsare gawar Malik da ido babu ko kiftawa

ga MALIKAT AL'UMU da gefe guda ita ma ta yi Zugum
TESNIM kuwa Rouksar na rungume da ita sai kuka ta ke yi
MALIKAT HOUDA , MALIKAT DJAOUDATT da MALIKAT YOUSSRA suma su na gefe guda sun yi zugum , ba me cewa komai

Su na a haka Amir ya bude baki murya a shaƙe ya ce " Azim , kun san abun da za ku yi , General ina son ganin ka ! " ya na gama fadar haka Ya daga kafa ya raba ta geffen Malik ya fice fadar ya bar su nan

ya na fita General ya mike da sauri ya bi bayan shi
su na fita Mohammed Sarkin bayi ya ce " Azim ku fara shiri mu kai shi gidan shi na karshe , Allah ya jikan shi ya yi mishi rahama , su kuma wanda su ka yi hakan Allah ya bayanar da su " ya kai karshen hawaye na zubo mishi har da sa rigar shi ya rufe fuskar shi
amma ta ciki na ciki , ba shi daya ba , duk rabin su


▪AMIR


ya na barin wajen Kai tsaye Part din shi ya nufa
ya na isa ya haye floor na uku , ya na shiga ya tsaya a parlour ya bawa kofar baya ya rike hannayan shi a baya

ya na tsaye General ya shigo , cikin girmamawa ya karaso bayan shi kadan ya tsaya ba tare da ya ce komai ba

sai da Amir ya dan dauki lokaci kafin ya ce " ina son ka fara bincike a kan abun da ya faru , ina son ka kamo ko wanene ya yi harbin nan "

dan sunkuyar da kai Amir ya yi kafin ya ce " an gama ran ka shi dade , in sha Allah bayan jana'izar Malik za mu fara bincike a kai "

gyada kan shi kawai Amir ya yi ba tare da ya ce komai ba
A hankali General ya juya har ya yi taku hudu ya tsaya ya juyo a hankali ya ce " ran ka shi dade mu je ko ? "

ba tare da ya juyo ba ya ce " Za ka iya tafiya "
tsaya wa General ya yi ya kale shi ba dan lokaci kafin ya juya ya ficewar shi
ya na barin wajen Amir ya fara takawa ya nufi corridor ya shige abun shi

a haka a ka jana'izar Malik , a ka yi mishi wanka a ka kai shi gidan shi na karshe , duk wani Na cikin masarautar idan ya rasu akwai cemetery a bayan masarautar nan a ke bisine shi , haka zalika shi ma Malik
amma abun mamaki Ko hanyar Amir bai leko ba , kowa sai dai ya halarta ban da Amir

bayan Jana'izar Malik , Duk wani wanda ke cikin Fada sai da ya nufi part din Amir dan jin dalilin da ya hana shi zuwa
Amma tun da ga floor na farko a ka tsaida su , da cewa Amir ya ce kar a bar kowa ya shigo ko da MALIKAT AL'UMU ce da kan ta
😭😭😭DAMA HAKAN YA KE GUDU , GA SHI KUMA SUN RABA SHI DA MAHAIFINSHI , DOLE YA CE BA YA SON GANIN KOWA , 😭😭 NI YANZU TAMBAYAR ITA CE WA YA YI WA MALIK WANNAN AIKIN , DUK YADDA A KA YI WANDA YA YI HAKAN YA NA SANE DA TAFIYAR SU MALIK MAKKAH , DA KUMA RANAR DAWOWAR SU , DAN DA GA GANI MUTUWAR MALIK A SHIRYE TA KE TUN KAFIN SU TAFI 😭😭✌ NI DAI NA TAFI NA YI RARRASHIN AMIR DIN MU


[21/09 à 19:00] +234 913 527 7685:





❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤


(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥




💔🥀 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) 💔🥀





👑❤ MALLAKIN MEERAH ❤👑



【THE ROYALTY LOVE 👑🕊💖】




Marubuciyar littafin

【TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺】





【 BOOK …………………… 2 ❤ 👑】





____________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊___________________




PAGE 14 ✍📚





bangaran Amir kuwa ya na shiga kai tsaye bedroom din shi ya wuce ya shiga Toilet ya yi Wanka ya yo Alwalla sannan ya fito ya wuce dressing room

jim kadan ya fito sanye da wata Jallabiya Fara kal mai mugun kyau ya sako wannan Smooth hair din na shi , yanzu tsawon shi ya fi na farko , ya zubo mishi saman shoulder har zuwa kirji , sai tashin kamshi ya ke yi

ya na fitowa kai tsaye ya nufi daddumar shi ya tada Sallat , ko da ya Kamala bai tashi da ga saman daddumar ba , sai da ya zauna ya dinga jero wa Malik aduo'i , sannan ya dauki alwashin ba zai zubar da kwalla daya ba har sai ya ga bayan wanda ya kashe mishi mahaifin shi , kuma ya san dole a cikin masarautar ya ke amma ba zai iya fadin wanene ba


▪INAYA


bayan ta koma bedroom din ta , kai tsaye ta haye bed din ta , ko minti biyu ba ta yi ba , barci ya yi gaba da ita

ba ta farka ba , sai Wajen sallar magriba , ko da ta tashi , ta shiga toilet ta yi wanka ta yi Alwalla sannan ta fito ta shiga dressing room
jim kadan ta fito sanye da wata dankareriar Abaya Fara kal mai mugun kyau , ta yi Rowling veil din ta a kai sai tashin kamshi ta ke kamar wanda ta fito da ga cikin kwalbar perfume

ta na fitowa kai tsaye ta nufi daddumar ta , ta fara gabatar da sallar ta
ko da ta Kamala ba ta tashi ba , sai da ta tsaya karatun kur'ani har lokacin sallar isha ya zagayo ta tashi ta gabatar da ita

bayan ta Kamala ta tashi ta fito dakin
ko da shigo corridor ta tardo RIANNA zaune saman carpet ta kontar da kan ta saman Cinyar MALIKAT INAS da ke zaune saman Sofa ta jingina bayan ta a jikin sofar ta daga kai ta kurewa waje guda ido
ga busashun hawaye nan konce saman face din su baki daya

karasowa wajen Inaya ta yi ta na fadin " Aunty RIANNA me ya faru da ke haka ? " ta fada dai'dai lokacin da ta ke zama gaban ta saman carpet ita ma

a hankali RIANNA ta dago kan ta , ta riko hannun Inaya ta ce " Baby tashi ki je wajen mijin ki , zai bukaci kulawar ki a wannan lokacin , ki tsaya ki kula da shi yadda ya dace , na san yanzu ya na cikin damuwa , ganin ki zai sa ya rage radadin da ya ke ji kin ji ko ? "

gyada mata kai Inaya ta yi ta na fadin " shikenan Aunty RIANNA , amma ba ki fada min abun da ke damun ki ba , ga hawaye nan konce saman fuskar ki , Ammie ku ma ga hawaye nan saman Fuskar ku " ta fada ta na dawo da kallon ta kan MALIKAT INAS

sai a lokacin MALIKAT INAS ta dawo cikin hayacin ta , a hankali ta juyo ta kali Inaya cikin disashashiyar Muryar ta , ta ce " ba komai baby , tashi ki je wajen Mijin ki , ya fi bukatar ki fiye da mu "

da to Inaya ta amsa musu sannan ta tashi ta nufi kofar fita parlourn zuciyar duk ba dadi ganin yanayin da su RIANNA ke ciki

a haka ta fito part din ta nufi Building din Amir , duk da so guda ta taba tafiya , amma ta san hanya ta kuma san yadda za ta yi ta shiga

abun mamaki kuma ta na zuwa guards din da ke tsarin wajen ko tare ta ba su yi ba
a haka ta shiga building din , kai tsaye ta shiga lift ta nufi floor na uku zuciyar ta na duka uku uku

bakin ta dauke da sallama ta shigo parlourn
nan ta tardo Rouksar , Aysher da Hafsat duk tsaye cikin parlour , Azim ya tare musu hanyar shiga corridor

A hankali Inaya ta karaso wajen ta tsaya ta na bin su da kallo ta na so ta tambayi abun da ke faruwa amma sam ba su ba ta fuska ba
asali ma kowa ce sai kallon wulakanci ke yi wa Inaya

kallon Azim ta yi ta ce " Uncle , yaya Zayd ya na nan ? "
dan karamin murmushi Azim ya yi kafin ya gyada mata kai ya ba ta hanya Sannan ya fada mata a wane bedroom za ta same shi
a hankali ta daga kafa ta wuce ta na tafiya kamar wadda a ka zarewa lakar jiki

Aysher na ganin Inaya ta wuce ta sa hannayan ta dukka biyu ta ture Azim gefe ta na fadin " fin mu ta yi da za ka ba ta hanya ta wuce , ba abun da zai hana ni ganin Amir " ta fada ta na wucewa
da sauri Rouksar da Hafsat su ka bi bayan ta har su ka kamo Inaya su ka wuce ta , su ka nufi Bedroom din Amir

babu ko Sallama su ka fado mishi a tare

Amir kuwa ya na konce bakin gadon shi , ya sauko da kafafun shi kassa
da sauri Rouksar ta karaso tsakiyar dakin ta marairaice murya ta ce " Akhie ! "

slowly ya bude idanun shi ya mike zaune ya dan lumshe idanun shi kadan kamar mai maye , ga gashin nan na shi ya zubo mishi har saman kirji , dukkan su sai da su ka hadiye yawu ba karamin kyau ya yi musu ba

har Rouksar ta bude baki za ta yi magana ya daga mata hannu allamun ta yi shiru
ba musu ko ta yi shiru ta tsaya ta na kallon shi , ta na kara yabawa kyawo irin na Amir , ni ta ke kamar ta hadiye shi

a hankali ya yi kassa da hannun shi dai'dai lokacin da Inaya ta shigo cikin dakin ta na sallama da wannan siririyar murya ta ta

ya na jin muryar ta ya ji wani mugun sanyi lokaci guda , har sai da ya dan lumshe idanun shi ya sake bude su a hankali kafin ya juya ya kale ta , ta na ganin ya kale ta , ta sakin mishi wani cool murmushi cike da shauƙi

ya na juyawa ko Azim shi ma ya shigo cikin dakin da sauri , ya na yin karo da idanun ya sha jinin jikin shi

tun kafin ya yi magana Amir ya riga shi cewa " Me na fada maka ? " ya fada cikin wata murya cen kassan makoshi kamar an busa sarewa dan dadi ,
har sai da Rouksar ta dan lumshe idanun ta a hankali cikin zuciyar ta ta na fadin " Masha Allah , ya Allah na roke ka , ka sa ya zama nawa " ta kai karshen ta na bude idanun ta

jikin Azim har kerma ya fara yi , ya na fadin " ina neman Afuwa ran ka shi dade wlh sun matsa ne sai s...."

cikin nitsuwa Amir ya katse shi da cewa " ku fita ku ban waje ba na son ganin kowa " ya kai karshen ya na sunkuyar da kan shi

Inaya na jin abun da ya fada ta dan sunkuyar da kai ta juya za ta fice
kamar da ga sama ta jiyo Muryar shi ya na fadin " Cutie ban da ke " ya fada da hausa dan ya san ita kadai ke jin hausa

wani cool murmushi ta saki kafin ta juyo ta tako a hankali ta karaso geffen Rouksar ta tsaya ta na kallon shi

ta na tsayawa Azim ya ce ma su Hafsat su fita , ba musu su ka juya su ka fice kowace ta na cika ta na batsewa
riko hannun Inaya Rouksar ta yi , ta na fadin " wuce mu tafi ke kuma ya ce ba ya son ganin kowa "

ba ta kai ga rufe bakin ta ba ta jiyo Muryar shi ya na fadin " sake hannun ta ki fice min da ga nan "

dan zaro idanu Rouksar ta yi ta na sakin baki har da cewa " Amir kai fa ka ce ba ka son ganin k....."

a dubu dari ya dago kai ya daka mata wata gigitaciyar tsawa ya na fadin " I say get out , Azim duk wanda ya sake shigowa ko da parlour ne sai na ɗaure ka da kai na "
nan take idanun shi su ka koma jazir , duk jiyojin jikin shi sai da su ka fito baro baro

ba shiri Rouksar ta saki hannun Inaya ta juya da gudu ta bar Bedroom din Azim na biye da bayan ta da gudu dan shi kan shi ya ji tsoron irin wannan tsawar da Amir

Rouksar kuma ta na baro wajen kai tsaye lift ta nufa ta shiga
kofar lift din na rufewa ta bace bat a cikin lift din

Amir kuwa ya na ganin sun bar wajen , ya kai hannu wajen bedside drawer ya dauki wata remote ya danna wasu button sannan ya ajiye ta
ya na ajiye ta , kofar dakin ta koma da kan ta ta rufe kan ta , ta saka security

sai da ya kofar ta rufe sannan ya juyo ya kali Inaya da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login