Showing 12001 words to 15000 words out of 47249 words

Chapter 5 - Exiled Prince Book 2 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

286

ya kone , an meda shi sabo amma wannan karan mai hawa hudu a ka yi ya ni ka farko kyawo da girma

Kamar ko Malik ya san abun da ke cikin tunanin yaron na shi sai ya yi dan karamin murmushi ya ce ma driver din su ya kai su building din
Building din tun da a ka gena shi har yanzu babu wanda ya taba shigar shi , dan musaman Malik ya sa a gena shi saboda AMIR na shi ne na musaman , shi kuma Malik a ka yi mishi wani part din daban

Sai driver ya iso bakin kofar part din sannan ya yi parking din motar
Da sauri dogarai da ke tsaron part din su ka karaso gaban motar su ka budewa Malik kofa
Ashe AMIR ne ke zaune a bangaran su na ganin shi su ka yi baya da sauri su na karanto kalmar shahada

Ya na fitowa ya tsaya ya na karewa building din kallo nan take abun da ya faru tsawan shekaru ya dawo mishi sabo

Ya yi nisa cikin tunanin shi ya ji Malik ya dafa kafadar shi ya na fadin " mu shiga ko "

Dawo da kallon shi AMIR ya yi kan Malik cikin nitsuwa ya ce mishi " ka sa a kai matan nan wajen MALIKAT INAS " ya na gama fadar hakan ya daga kafa ya na taku cike da izza ya shiga cikin ginin

Ya na shiga Azim ya karaso wajen ya Zube saman guyiwowin shi ya na gaishe da Malik ya na yi mishi barka da zuwa

Amsa mishi gaisuwar shi Malik ya yi kafin ya ce " akwai wasu mata da ke tare da mu , yaran ka sa a kai su wajen MALIKAT INAS , matar kuma a isa da ita wajen MALIKAT HOUDA " ya na gama fadar hakan ya shiga cikin building din shi ma

Ba musu Azim ya mike dan cika umarnin Malik
Abdoul da Diya kuma ba su ma shigo Daular saudiya ba , Kai tsaye Daular Ottoman su ka nufa

Bayan AMIR ya shiga building din kai tsaye wajen lift ya nufa ya Haye hawa na uku
Kai tsaye lift din da parlourn ya ke sada ka , ya na shigowa ya ji zuciyar shi ta buga da karfi
Cak ya tsaya waje guda ya na karewa wajen kallo , ya na nan kamar yadda ya bar shi , duk kayan da a ka saka mishi sak irin na farko

Ya na a haka ya ji Malik ya dafa kafadar shi
A hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " zan shiga wanka ba ni son kowa ya dame ni " ya na gama fadar haka ya nufi wani corridor da ke saman damar shi
Da kallo Malik ya raka shi sai da ya ga ya shiga bedroom guda da ga na cikin corridor din sannan ya saki wani kyawatencen murmushi ya nufi sofa ya zauna


Ya dauki wajen good 30 minutes a haka kawai ya ji kofar lift ta bude , RIANNA ta fito da ga ciki da gudu ta na hawaye ta nufi Malik ta Zube kassa kussan kafafun shi ta na kuka ta ce " Abbi wai AMIR ya dawo , tun dazu na ke ji cikin masarauta wai sun ga AMIR ya shigo nan , Abbi wai da gaske ne , AMIR di na ne ya dawo , Abbi ku fada min "

Dan karamin murmushi ya yi ya na fadin " ya isa haka RIANNA kukan na minene kuma "

Da sauri ta katse shi da cewa " don Allah Abbi ku fada min da gaske ne wai , Wlh zuciya ta zafi ta ke yi min ji na ke kamar zan mutu , Abbi ina son na ga yan uwa na , na yi kewar shi sosai Abbi kullum da shi na ke kwana da shi na ke tashi cikin zuciya ta why zai tafi ya bar ni Abbi ? " ta kai karshen ta na kontar da kan ta saman cinyar Malik ta na ci gaba da kukan ta

A hankali Malik ya kai hannu ya na shafa kan ta ba tare da ya ce mata komai ba , sai dan karamin murmushi da ya saki ya san abun da ta ke ji cikin zuciyar ta , duk da ba mahaifiyar su guda ba , amma son da RIANNA ke yi wa Amir ko Tesnim da su ke uwa guda ba ta yi mishi shi

Sai da su ka dauki wajen good ten minutes a haka kafin AMIR ya shigo parlourn ya na sanye cikin wasu kayan barcin farare kal masu mugun kyau sai tashin fitinannan kamshi yake yi , ya na tafe kai a sunkuye ya na latsa wayar shi

Kai tsaye wajen wannan kujerar ta gold ta Malik ya nufa ya zauna ya daura kafa daya bisa daya ba tare da ya dago kai ba ya ce " Abbi , ka sa a kawo min Fruits wlh yunwa na ke ji kamar na yi sati ban ci komai ba "

A dubu dari RIANNA ta ware idanun ta ta dago kai ta kali saitin da ta jiyo Muryar shi
Ya na zaune ya yi zaman kasaita, sai da ta ji zuciyar ta ta buga
Lips din ta har kerma su ke yi wajen bude baki ta ce " Akhie !"

Slowly ya dago kan shi idanun shi ba su sauka ko ina ba sai saman ta
Meyar da kan shi ya yi ya sunkuyar kafin ya ce " Ukhtie , please je ki kawo min wani abu na ci wlh yunwa na ke ji "

Malik ne ya amsa mishi da cewa " NAWFEL ban son shirme RIANNA ba ta girme ka ba ita ce za ta kawo maka abinci "

A hankali ya daga kan shi sannan ya ajiye wayar shi saman yar table da ke geffen Chair din sannan ya sauko da kafar shi kassa ya mike tsaye ya na fadin " ai na san hanya ku yi zaman ku " ya fada ya na fara takawa

Da sauri RIANNA ta mike tsaye ta sha gaban shi baki sake ta ke kallon shi ta kassa magana

Dan karamin murmushin geffen fuska ya yi mata kafin ya ce " Lafya kin tare min hanya tun da ba za ki je ba gusa min ni na tafi "

Ita dai ta kassa wani kwakwaran motsi sai kallon shi ta ke yi
Ganin hakan ya sa shi kauda kai gefe kadan ya kali Malik ya ce " sai da na ce maka kar a dame ni "
Bai gama rufe bakin shi ba kofar lift ta bude MALIKAT INAS da MALIKAT HOUDA su ka fito a tare

Cak kowa ce ta tsaya ta na zaro idanu ta na kallon AMIR
Ya na ganin su ya saki wani dan siririn tsaki ya juya ya koma kan Chair din da ya taso ya zauna ya na kauda kai gefe

Sai zaro idanu su ke su na kallon shi , duk sun kassa magana
Sai cen MALIKAT INAS ta karaso wajen Malik ta zauna geffen shi ta na ci gaba da kallon AMIR baki sake nan take idanun ta su ka kawo ruwa

Kamar ya ji a jikin shi ya na juyowa ta fara zubar da hawaye , ya san ta hawayen kusa su ke abu kadan sai ta ta yi kuka kamar karamar yarinya , shi ya sa ya ce a kai su Inaya wajen ta dan ya san duk cikin masarautar babu mai kirki irin nata

Ya na ganin ta fara zubar da hawaye ya saki wani cool murmushi ya ce " Haba Ammie su hawayen na minene "
Wani murmushi mai dan sauti ta yi ta na girgiza mishi allamun ba komai
Shi ma murmushi ya yi mata kafin ya taso da ga saman chair din shi ya koma geffen ta ya zauna kassa ya kontar da kan shi saman cinyar ta ya ce " na yi kewar ki Ammie na "

A hankali ta daga hannun ta har kerma ya ke yi ta daura saman kan shi
Dan lumshe idanun ta ta yi kafin ta bude slowly ta na sauke ajiyar zuciya
[16/09 à 09:57] M.N.M:


❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤


(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥




( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




⚘🕊 MALLAKIN MEERAH 🕊⚘



【 THE ROYALTY LOVE ✌👑🌹】




Marubuciyar littafin :【 TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 】






BOOK .............. 2 🌹👑







________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊________________




PAGE………………… 5 ❤🔥




A hankali RIANNA ta karaso wajen shi ita da MALIKAT HOUDA ta zauna saman sofa
Ita kuma RIANNA ta zauna gaban shi
Ta na shirin magana ya riga ta cewa " kar ki yi min magana , tun dazu na ce miki yunwa na ke ji amma kin share ni "

Ba ta san lokacin da kuka ya kubce mata ba , ta fada jikin shi ta rungume shi
Shi ma rungume ta ya yi tsam nan take idanun shi su ka kawo ruwa amma bai bari sun zubo ba

Sai da ta gaji da kukan na ta sannan ta dago da ga jikin shi ta sa hannu ta na goge hawayen ta saki wani cool murmushi ta ce " na dauka ka tafi har abada "

Da sauri MALIKAT HOUDA ta katse ta da cewa " da ma in an mutu a na dawowa "

Cikin zolaya AMIR ya amsa mata da cewa " eh a na dawowa , na hadu da mijin ki a cen , har ya ce na gaishe ki "

Duk mutanan wajen sai da su ka yi dariya jin abun da ya fada
Cuke fuska AMIR ya yi ya ce mata " ke ni fa da gaske na ke yi miki , amma fa ki yi hakuri ya yi sabuwar amarya a cen wadda ta fi ki kyau "

" ba na son shirme ni tsarar wassan ka ce " ta fada ta na tsuke gera
Jinjina mata kai ya yi kafin ya ce " eh , ni na ma tafiya ta barci na ke ji , Please Ammie na , ku kula da yaran nan dayar ba ta da cikakiyar lafya " ya kai karshen ya na mikewa tsaye

Da sauri MALIKAT INAS ta ce mishi " wai su wanene yaran nan "
Juyo wa ya yi ya kale ta kafin ya ce " sirikan ki ne " ya kai karshen ya na kashe mata ido guda ya juya ya ci gaba da tafiyar shi ya koma bedroom din da ya fito da farko

Da kallo duka su ka raka shi sai da ya shiga sannan Malik shi ma ya mike ya na fadin " ni ma zan shiga sai da safe " ya fada ya na nufar corridor shi ma ya shiga bedroom din da ke kusan ta AMIR

" to sai ku tashi mu tafi " MALIKAT HOUDA ta fada ta na mikewa tsaye
Su ma dai MALIKAT INAS da RIANNA mike wa tsaye su ka yi su ka fice part din kowa ce ta koma part din ta

Kai tsaye ko wace part din ta ta koma , RIANNA kuma ta bi MALIKAT INAS part din ta
Su na shiga su ka ga INAYA da NESRINE zazaune a kassa sun takure waje guda

Dan karamin murmushi RIANNA ta yi kafin ta nufe su ta na sallama
A tare su ka dago kai su na amsa mata sallamar ta kafin su sunkuyar da kai
Zama ta yi gaban su ta na murmushi ta ce " ya sunan ku " ta fada da turanci
A hankali kowace ta bude baki ta fadi sunan ta
" Masha Allah , ku saki jikin ku , ku dauki tamkar yar uwar ku ta jini , saboda duk abun da Dan uwa na ya nuna ya na son shi , to ni ma ina son shi "

Jinjina mata kai su ka yi a tare ba tare da sun ce komai ba
Ta na gama rufe bakin ta wata matar ta shiga parlourn ta na rike da tray shake da abinci ta kawo gaban su Inaya ta ajiye kafin ta mike ta koma inda ta fito
Ta na barin wajen MALIKAT INAS ta shigo parlourn ta na sallama

Wajen su Inaya ta nufa ta zauna saman sofa ta ce " maza kun cinye ba na son ganin komai saman tray din nan "

Su dai Inaya da Nesrine kai a sunkuye sun kassa cewa komai
Dan sunkuyar da kai RIANNA ta yi ta na lekon face din su ta ce " ko kunya ta ku ke ji "
A hankali Inaya ta girgiza mata kai ta na sakin wani marayan kuka ta na cewa " ku kai ni wajen yaya Zayd di na "

Da sauri Nesrine ta rungume ta ta na fadin " ke yi wa mutane shiru ko kunya ba ki ji ba "
Kallon MALIKAT INAS RIANNA ta yi cikin harshen larabci ta ce mata " Momy ina ga ita ce wadda AMIR ke cewa ba ta da lafya "

Gyada mata kai MALIKAT INAS ta yi kafin ta sauko kassa saman carpet geffen Inaya ta daura hannun ta saman shoulder din ta ta na fadin " baby ya isa haka kin ji ko , bari da safe ina kai ki wajen AMIR kin ji ko " ta fada cikin sanyi

Gyada mata kai Inaya ta yi ta na raba jikin ta da na Nesrine ta sa hannu ta na goge hawayen ta

Murmushi kadan MALIKAT INAS ta yi kafin ta kai hannu ta dauki spoon ta fara ba ta abinci da kan ta
Ba kunya ba tsoron Allah Inaya ta bude baki ta na karba kamar wata baby , Nesrine ma sai da RIANNA ta matsa sannan ta dauki spoon ta fara cin abincin , nan take ta zame ta na ci dama yunwa ta ke ji

Ita dai RIANNA kallon su kawai ta ke ta na murmushi nan take ta ji son su ya shiga zuciyar ta

Sai da su ka Kamala sannan MALIKAT INAS ta ce da RIANNA " je ki cewa Lamiya ta karbo musu kayan barci wajen TESNIM "

" no , momy akwai kananan kaya waje na za su yi musu " RIANNA ta fada dan ta san halin TESNIM bayan AMIR ba wanda ta ke ba wa kayan ta

" okay tashi mu je ki yi wanka ku sake kaya sai ku konta ku huta , gobe zan sa a kawo muku kayan saka wa " MALIKAT INAS ta fada ta na mike ta nufi wani corridor da ke fuskantar su ta shiga door ta karshe

Ta na shiga RIANNA ta mike ita ma ta ce musu su tasso
Ba musu su ka tashi su ka bi bayan ta , ta shiga da su bedroom na biyu ta ce su shiga su yi wanka yanzu ta kawo musu kayan sakawa
Da to su ka amsa mata kafin su shiga cikin dakin ita kuma ta wuce na ta bedroom

Su na shiga Nesrine ta yi saurin shiga toilet
Ba ta yi five minutes da shiga ba RIANNA ta dawo rike da wasu kayan guda biyu ta ce su saka sai da safe da ga haka ta juya ta bar musu dakin
Bayan Nesrine ta fito , ita ma Inaya ta shiga ta yi wanka kafin ta fito har Nesrine ta saka kayan ta , ta bi lafiyar gado har barci ya dauke ta
Ita ma kayan ta saka ta Haye gadon ta konta ba jimawa barci ya yi gaba da ita

* MELI

Wani mutun ne sanye da bakaken kaya ya rufe fuskar shi ya sa hannu ya shake wuyan Meli sai zaro idanu ya ke yi " Ba ka ce min AMIR ya mutu ba tsawon shekara 6 , wannan wanene to " ya fada da dan karfi

Murya na kerma Meli ke fadin " wlh ya shugaba na , ni da kai na kunnawa part din wuta kuma ina da tabbacin AMIR na ciki a lokacin ban san yadda a ka yi ya dawo ya shugaba na "

A fusace wannan mutun ya yi wurgi da Meli geffe guda har sai da ya fadi kassa
Da sauri ya riko wuyan shi ya na meda nunfashi kafin ya dago kai mutumin nan ya bace bat babu shi



* WASHE GARI ( misalin karfe 10 na safe )


*AMIR



Konce ya ke saman katafaren bed din shi , ya yi rub da ciki , da ga shi sai short
A hankali ya fara jiyo a na yi mishi knocking , dan karamin tsaki ya ja kafin ya ware idanun shi a hankali ya na kallon door din kafin ya ba da izinin shigowa

Turo kofar Malik ya yi ya na yi mishi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login