Showing 15001 words to 18000 words out of 47249 words

Chapter 6 - Exiled Prince Book 2 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

292

sallama
Da kallo AMIR ya raka shi ba tare da ya motsa ba har sai da Malik ya karaso bakin gadon
Murmushi kadan Malik ya yi kafin ya ce " To sai ka tashi safiya ta yi "
" Saboda shi ne ka zo min tun da safe " AMIR ya fada cikin wata zazzakar murya cike da nitsuwa
Mika mishi wayar hannun shi Malik ya yi kafin ya ce " Amshi to , Ammien ka ce ke son yin magana da kai "

A hankali ya dago hannun shi ya karbi wayar ya kai ta a kunne ya na sallama kafin ya ce " barka da safya Ammie "

Ba ta amsa mishi sallamar shi ba ta ce " AMIR ka na ina , don Allah ka zo part di na yanzun nan " ta na gama fadar haka ta katse kiran

Yanayin da ta yi maganar ba karamin tada mishi hankali ya yi ba
A dubu dari ya mike zaune ya diro da ga saman gadon ya shiga dressing room da gudu
Shi dai Malik ya na karbar wayar shi ya juya ya bar bedroom din dan a na jiran shi a fada
Bai yi one minute ba ya fito sanye da wata jallabiya fara kal har kassa da sauri ya sa kafa ya fice bedroom din
Har hada wa ya ke yi da gudu cikin zuciyar shi ya na rokon Allah ya sa ba wani abu ya samu Inaya da Nesrine ba

A haka ya fito building din , duk dogarai da ke tsatsaye cikin masarautar idan ya yi arba da shi sai ya shiga karanto kalmar shahada saboda wasu ba su san da AMIR ya dawo ba ga shi kuma ya sanye da Farar jallabiya sai su ka yi tunanin ko fatalwar shi ce

Bai bi ta kan su ba ya wuce kai tsaye part din MALIKAT INAS ya wuce na MALIKAT AL'UMU

Ko sallama babu ya shigo parlourn ya na kwalla mata kira , nan ya ga Nesrine zaune saman sofa
Ta na ganin shi ta mike tsaye ta na yi mishi barka da safya
Gaban ta ya karaso cikin fitar hayaci ya na tambayar ta ina Inaya , da yatsa kawai ta nuna mishi corridor ba tare da ta ce komai ba

Da sauri ya juya ya na shirin shiga corridor din har ya yi taku biyu ya tsaya cak ya na kallon ta baki sake
A hankali ta ke takowa kai a sunkuye
Ta na sanye cikin wata kyakyawar gown Pink colour mai mugun kyau ta sha ruwan stone da ga kassa
Ta daura wata Alkyaba fara kal da ga sama , en yi mata zanen flower da zare mai launin gold amma ba ta saka hular ba , ta bar wannan lalawsan gashin kan na ta ya zubo mata gefe guda saman shoulder
Ba ta wani yi make up kawai lips balm ne ta shafa sai tashin fitinannan qamshi ta ke , ba karamin kyau ta yi ba kamar ka sace ta ka gudu


Duk sai ya ji ya tsargu da kallon ta ya kassa janye idanun shi da ga saman ta
Har sai da ta karaso gaban shi ta tsaya , slowly ta dago kai ta kali cikin idanun shi sannan ta saki wani cool murmushi cikin shagwaba ta ce mishi " ina kwana yaya Zayd "

Shi dai da ido kawai ya ke bin ta ya kassa wani kwakwaran motsi ko idanun shi ya kassa kiftawa

Su a haka ya jiyo Muryar MALIKAT INAS ta na fadin " tun asubahi ta tashe mu da kuka wai a kai ta wajen yaya Zayd din ta "

A hankali ya daga kan shi ya kali saitin da ya jiyo Muryar MALIKAT INAS
Ta na tsaye ita da RIANNA sai murmushi su ke yi
A hankali ya daga kai sama ya lumshe idanun shi ya ce " ya rahman " kassa kassa kafin ya juya ya nufi sofa ya zauna ya daura hannayan shi biyu sannan face din shi kafin ya janye ya dago kai ya kali MALIKAT INAS ya ce " kun san irin tsoron da ku ka ba ni ko wanka fa ban yi ba na fito kamar wani zarrare "

Yar karamar dariya RIANNA ta yi kafin ta karaso geffen shi ta zauna ta dafa shoulder din shi cike da zolaya ta ce mishi " minene laifin mu dan Gimbiya na son ganin Yariman ta , mu taimaka mata kawai mu ka yi "

A hankali ita ma MALIKAT INAS ta karaso ta zauna daya geffen na shi ta riko hannun shi ta ce " AMIR fada min gaskia me ke tsakanin ka da wannan yarinyar " ta fada da larabci dan kar Inaya ta ji abun da su ke fada

Slowly ya dago kai ya kali Inaya da ke tsaye har yanzu ta sunkuyar da kai ta riko hannayan ta

Sai da ya dauki dan lokaci ya na kallon ta kafin ya bude bakin shi a hankali ya ce " We are married "

RIANNA ba ta san lokacin da ta saki wata yar siririyar kara sai da ta sa hannu ta toshe bakin ta
Hararrar ta MALIKAT INAS ta yi kafin ta kali AMIR ta ce " Malik ya san da wannan zancen "
" no , ina fada mishi yanzu idan na koma " ya fada ya na mikewa tsaye ya nufi hanyar fita
Har ya kai bakin kofar ya jiyo Muryar Inaya ta na kiran shi
Slowly ya dan juyo da kan shi ya na kallon ta ta geffen ido

Cike da shagwaba ta ce mishi " yaya Zayd ka dawo amma ko " ta fada da haoussa
Gyada mata kai kawai ya yi da ga haka ya juya ya bar wajen
Dan karamin murmushi ta yi ta na sunkuyar da kai

Bangaran AMIR kuma ya na fitowa ya ci karo da Azim
Da sauri Azim ya Zube saman guyiwowin shi ya na fadin " gaisuwa na ke ya shugaba na , Allah karre mana yarima , dan sarki jikan sarki , duk mai taba ka mutuwa ce makomar shi "

Cikin nitsuwa AMIR ya katse shi da cewa " ya isa haka Azim , me ke tafe da kai "
" ya shugaba na , MALIKAT AL'UMU na son magana da kai "
Takawa AMIR ya yi ya fara yin gaba , da sauri Azim ya mike ya bi bayan shi dan nesa kadan dan kar su zo dai'dai

Sai da su ka dan yi nisa da part din MALIKAT INAS , ya wuce part din MALIKAT AL'UMU sannan ya ce ma Azim " ka shirya min zama da ita a garden ina zuwa "
" an gama ya shugaba na " Azim ya fada ya na sunkuyar da kai kafin ya juya

Shi kuma AMIR ya nufi Building din shi , kai tsaye hawa na uku ya nufa ya koma bedroom din shi , ya na shiga ya wuce toilet dan ya yi wanka

After some minutes ya fito sanye da bathrobe , ya wuce dressing room
Jim kadan ya fito sanye da trouser Navy blue , da Shirt white color , ya daura wata alkyaba fara kal da ga sama , duk da bai da gashi dayawa a yanzu sai da ya sa wata yar pin ya daure shi a baya sannan ya daura hular Alkyabar shi , sai tashin fitinannan kamshi yake yi

A haka ya sa kafa ya fito bedroom din , kai tsaye part din ya fice baki daya
Duk inda ya wuce sai ma su tsaro sun zube saman guyiwowin su , su na gaishe da shi
Bai bi ta kan gaisuwar su ba ya nufi wani tanpasheshen garden
Cike ya ke da ciyayi da flowers , sai wata yar hanya da za ta sada ka da wata katuwar runfa dauke da wasu lamusasun sofas farare kal guda hudu uku two seaters , daya kuma three seaters , geffen kowa ce sofa akwai wata yar karamar table ta glass , da ga tsakiyar su kuma an shinfida wani kyakyawan carpet Fari kal mai ratsin ruwan gold gwanin burgewa
Duk wajen zagaye ya ke da dogarai , da guards rike da gun

A haka ya karaso kassan runfar inda ya tardo MALIKAT AL'UMU zaune saman sofa three seaters , ga yar karamar table gaban ta dauke da wani tray shake da fruits

A hankali ya motsa lips din shi ya na sallama , wadda shi kadai ya ji kayan shi
Sannan ya nufi sofa two seaters ya zauna ya na fadin " Good morning momy "
Daga mishi hannu ta yi ta na matse fuska ta ce " na yi fushi da kai "
Cikin sanyin murya ya ce mata " Momy me kuma na yi ? "
Hararrar wassa ta yi mishi kafin ta ce " where is My morning Hug ? "

Maganar ta ta , ta so ta ba shi dariya ma amma sai ya danne kayan shi ya tasso a hankali ya koma geffen ta zauna sannan ya rungume ta

Wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta ce " Na yi kewar sosai ka sani ko ? "
Ya na shirin dagowa da jikin ta , kawai ya ji an fado mishi a baya
Ko bai duba ba ya san ko wanene hakan ya sa shi cewa " tashi kar ki karaya min baya "

A hankali ta tashi ta na yar karamar dariya ta ce " ina kwana Akhie "
Raba jikin shi ya yi da na MALIKAT AL'UMU kafin ya tashi ya koma saman sofar da ya taso

" Akhie wai su wanene yaran nan da ka taho da su ? " TESNIM ta tambayeshi ta na gyara zaman ta saman sofar

Koma wa ya yi ya jingina bayan shi a jikin forehead din sofar ya daura kafa daya sama daya ya kale ta sannan ya ce " saman kan ki su ke ne ? "

Ta na shirin magana Diya ya shiga wajen ya na sallama Abdoul na tare da shi
Da sauri TESNIM ta mike tsaye ta na yar kara ta nufi wata yar budurwa da ke tsaye bayan Diya ta rungume ta ta na fadin " oyoyo , Rouksar , why ba ki fada min ba za ki zo "

Yarinyar da ta kira da Rouksar fara ce kal a shekaru za ta kai 22 haka , ta na da kyau dai'dai gorgaudo , ta so ta yi kama da Diya , amma fa kama ta jini da ga gani ka san kanwar shi ce
Rungume TESNIM ta yi ita ma ta na fadin " ni ma ban shirya tahowar ba , na ga Akhie ne zai tahowa shi ne na biyo shi dan na gan ki na yi kewar ki sosai my TESNIM "

Da ga haka su ka raba jikin su Rouksar ta nufi MALIKAT AL'UMU ta rungume ta ta na fadin " Barka da wannan lokaci Momy "
Dan bubuga bayan ta MALIKAT AL'UMU ta yi kafin su raba jikin su ta koma geffen ta ta zauna , TESNIM ita ma ta koma geffen ta ta zauna

Diya da Abdoul kuma su ka nufi dayar sofa two seaters su ka zauna
Abdoul dai tun da ya zo ya ke karewa AMIR kallo duk sai ya ga lokaci guda ya sauya mishi

Da haoussa Diya ya yi wa AMIR magana ya ce " AMIR ina ????? " ya kai karshen ya na daga mishi gera guda

A hankali AMIR ya juya kan shi ya kali TESNIM ya ce mata " TESNIM je ki kira min yaran nan "

Tsuke fuska ta yi ta na kauda kai gefe wai ita ba za ta je ba
" Idan ki ka bari na maimaita abun da na ce , jikin ki zai fada miki " ya fada cike da izza

Da sauri ta mike tsaye ta na dan gunguni ta fara takawa ta bar wajen ta na tafe ta na kunbura fuska wai ita ta ji haushi

Ta na barin wajen Rouksar ta saki wani kyawatencen murmushi ta na kallon AMIR ta ce " AMIR ba ka ganin ba ne tun dazu ka kyale ni "

" ke Rouksar ban son shirme AMIR din ne ki ke jira ya fara gaishe ki " Diya ya fada cikin tsare gida

Dan sunkuyar da kai ta yi ta na fadin " ka yi hakuri Akhie , ina kwana " ta fada cikin girmamawa
Gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce mata komai ba
Da ga haka ba wanda ya sake cewa komai har sai da TESNIM ta dawo tare da Inaya da Nesrine su ka shigo cikin runfar su na sallama

Da sauri Inaya da Nesrine su ka nufi Abdoul su ka rungume shi su na yar dariya
Rungume su shi ma ya yi ya na fadin " my sisters , da fatan na same ku lafya ? "
Inaya ce ta riga Nesrine cewa " Lafya lau yaya Abdoul , ina ka tafi ka bar mu jiya tun bayan fitowar mu jirgi ban gan ka ba " ta kai karshen ta na raba jikin ta da na shi ta koma saman sofar da AMIR ke zaune ta zauna geffen shi

Ita kuma Nesrine ta zauna kassa saman carpet geffen shi
A tare TESNIM da Rouksar su ka zaro idanu su na kallon Inaya ta na zaune saman sofar da AMIR ke zaune kuma bai ce mata komai ba , ko ita TESNIM yanzu in a ka ce mata ta yi hakan ba za ta iya ba
Ita dai MALIKAT AL'UMU ko a jikin ta sai ma tashi da ta yi ta bar wajen ta nufi part din ta

Ta na barin wajen AMIR ya juyo da kan shi ya kali Inaya kassa kassa ya ce mata " kun yi breakfast ? "

Juyowa ta yi ta kaleshi ita ma ta na murmushi ta gyada mishi kai
" za ki sha fruits " ya tambaye ta
Yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " no ni na koshi , sai dai in so ka ke ciki na fashe " ta fada cikin shagwaba

Girgiza mata kai ya yi kafin ya kali Nesrine ya ce mata " Nesrine ina son yin magana da ke " ya kai karshen ya na mikewa ya fara takawa ya fice runfar
Da sauri Nesrine ta tashi ta bi bayan shi

Su na barin wajen Rouksar ta kali Inaya sama da kassa kafin ta kali Diya ta ce " Akhie su wanene wannan ?" Ta kai karshen ta yi wa Inaya kallon kaskanci

Nuna ta da yan yatsa Diya ya yi kafin ya ce " saurare ni da kyau Rouksar na san abun da ya kawo ki masarautar nan , tun wuri ki sauke idanun ki da ga saman yarinyar nan , wlh ko gashin ta ki ka taba AMIR zai iya kashe ki , kuma ba abun da zai faru "

Da sauri TESNIM ta katse shi da cewa " Dalilin mi Akhie zai kashe ta saboda wannan dan babyn ? " ta kai karshen ta na nuna Inaya da dan yatsa

Yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " bari in ya dawo sai ki tambaye shi ai kun fi kusa "

Duk maganar nan da su ke yi a kunnen Abdoul dan shi ya na jin larabci ba kamar Inaya ba , abun da bai sani ba ita ma ta na jin larabcin amma sama sama , duk maganar nan da su ka yi ta dan gane rabin ta amma sai ta nuna kamar ba ta ji su ba , sai da ta bari sun Kamala sannan ta tashi ta dauki Apple guda da ke saman table din gaban sofar su TESNIM sannan ta koma ta zauna ta na cin Apple din ta


[16/09 à 09:57] M.N.M:



❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤


(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥




( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




⚘🕊 MALLAKIN MEERAH 🕊⚘



【 THE ROYALTY LOVE ✌👑🌹】




Marubuciyar littafin :【 TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 】




YOU CAN FOLLOW MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i





BOOK .............. 2 🌹👑







________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊________________





PAGE ……………………6 ❤🔥







Bangaran AMIR kuma , a tare su ka baro wajen shi da Nesrine su ka sauka da ga saman Hanyar ya shiga cikin ciyayin sannan ya tsaya ya rike hannayan shi a baya ita kuma ta na tsaye geffen shi


Sai da ya dan dauki lokaci kafin ya ce mata " kin san dalilin da ya sa na kira ki ?"
Girgiza mishi kai ta yi ta na fadin " a'a yaya Zayd "
A hankali ya dan lumshe idanun shi ya bude kafin ya dan juyo da kan shi ya kale ta ya ce " da farko ki daina kira na da yaya Zayd , ki kira ni da Akhie ko kuma AMIR "
Da to ta amsa mishi

Shiru ya yi na dan lokaci kafin ya ce " na san malam ya fada miki auren da ke tsakanin da Diya kafin ya rasu "

Sunkuyar da kai ta yi kafin ta ce " Eh ya fada min , ranar da wadanan mutanan su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login