Showing 27001 words to 30000 words out of 47249 words

Chapter 10 - Exiled Prince Book 2 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

290

▪AMIR


ya na baro part din MALIKAT INAS bai tsaya ko ina ba sai building din su
ya na shigowa parlourn su na uku ya tardo Malik zaune da wasu mutanan guda hudu , babu ko sallama ya shigo wajen ya nufi corridor
da sauri Malik ya ce " Amir dawo ina son magana da kai "

cak ya tsaya da tafiyar shi , har ya kai bakin corridor din , sannan ya juyo a hankali ya karaso cikin parlourn ya nufi sofa one seater ya zauna ya na kallon Malik

ya na zama Malik ya mika mishi wasu takardun da ke gaban shi saman table
da sauri Azim ya taso ya karaso wajen ya karbi takardun ya nufi Amir ya mika mishi cikin girmamawa

a hankali Amir ya kai hannu ya karba ya na fadin " na minene wannan ? "

kallon mutanan Hudu Malik ya yi ya ce " Wadanan dai ka san su ba sai na fada maka ba " ya fada ya na nuna Sarkin bayi , da Sarkin dogarai

sannan ya nuna wanda ke kusan sarkin Bayi ya ce " wannan kuma shi ne Miram bin Salman , mai kula da Bankin Daular "

sannan ya nuna na karshen ya ce " wannan kuma ,General Abdallah Mohamed , Shugaban masu tsaro , General of Army kuma , duk su na cikin mutanan Fadar Malik , kamar ko wace shekara kafin a fara azumi a na fitar da Ten Milliard , da ga Bankin Daular , dan a rabawa Al'uma , to wadanan Takardun ne ! ka san ban da gobe za mu tafi makkah , shi ya sa su ka zo dan mu tatauna a kai , zan so na ji ra'ayin ka yadda za a raba kudin "

shiru Amir ya yi ya na kallon takardun ya na karantawa

sai da ya karanta takardun tsab sannan ya ajiye takardun a kassa sannan ya jingina bayan shi a jikin sofar ya kali Malik ya ce " wa ke kula da raba kudin kowace shekara ? "

" Sarkin bayi " Malik ya fada a takaice

a hankali AMIR ya juyo ya kali Sarkin bayi ba tare da ya ce komai ba
sai da ya dauki wajen good five minutes ya na kallon sarkin bayi babu ko kiftawa kafin ya ce " a ba wa MALIKAT INAS kudin wannan shekarar "

" what ? " Sarkin bayi da Miram su ka fada a tare
sannan Sarkin bayi ya ɗaura da cewa " tare da dukkan girmamawa Amir , Kowace shekara mu mu ke kula da wannan ta ya za a tashi rana guda a bawa wani , wanin ma....... "

cikin nitsuwa Amir ya katse ta hanyar daga mishi hannu sannan ya kali Malik ya ce " ra'ayi na ka ce na fada kuma shi zan fada , ina son a duba cikin prisoner Din masarautar nan , wanda ya kusa kai karshen zaman shi , ko da ya haura wata biyar a sake shi , su koma gida jen su , zancen kudi kuma na san dalilin da ya sa na ce a bawa MALIKAT INAS , ita za ta fi sannin yadda za a yi da kudin , na san kowace shekara , da ga bayi sai dogaran masarautar nan ke samun kudin , shi ya sa na ce A kai wa MALIKAT INAS , ba ku sani ba amma yawwan cin mata sun fi wasu kaifin tunani da sanin abun da ya dace , Idan shawara ta ba ta yi muku ba , ku yi yadda ku ke so " ya na gama fadar haka ya tashi ya nufi corridor ya shige bedroom din shi

ya na barin wajen Mohammed ya kali Malik ya ce " Ran ka shi dade ni dai ban yarda da wannan shawarar ba "

ya na gama rufe baki Miram ya ɗaura da cewa " haka ne ya shugaba na , kowa ce shekara mu ka ke bawa ragamar kula da raba kudin nan ta ya rana guda a ce an sauya , kuma a ce mace za ta raba kudin "

kallon Hussein Malik ya yi kafin ya ce " Hussein , General , me za ku ce a kai ? "

" ran ka shi dade ina ga abun da Amir ya Fada dai'dai ne , ko wace shekara tsarin Raba kudin nan duk ɗaya , canjin da Amir ya kawo hakan ba karamin ɗaukaka shi zai yi , specially da ya ce a saki sauran prisoner , ko ba haka ba General " Hussein ya fada ya na kallon General

gyada kan shi General ya yi kafin ya ce " Haka ne yadda ka fada , magana ta rage gare ka ran ka shi dade "

a tare duk su ka kai kallon su kan Malik su na jiran su ji abun da zai ce

dan jinkirtawa Malik ya yi kafin ya ce " a yi yadda Amir ya fada , za ku iya tafiya "

cikin girmamawa su ka mike dukkan su , su na yi wa Malik sai da safe sannan su ka nufi hanyar fita building din baki daya


▪ MIRAM


Tsaye ya ke shi da Mohammed a cikin garden din cike da bacin rai Miram ya ce ma Mohammed " Mohamed , yanzu ya za mu yi , Wacen sakaran Amir ya bata mana shirin mu "

" Miram kontar da hankalin ka " Mohammed ya fada cikin nitsuwa
" ta ya za ka ce na kontar da hankalin na , ni dama na San kallon nan da ya yi min ba na banza ba ne , mun jima mu na jiran wannan damar yanzu ya bata komai "

wata shegiyar dariya Mohammed ya yi ya fara takawa ya yi gaba ya na fadin " kar ka damu , wannan ne na farko kuma na karshe , dan babu wanda zai dawo da ga Makka a cikin su , kai dai ka tsayar da maganar auren ka da RIANNA kafin Malik ya bar kassar nan "
haka dai su ka ci gaba da tafiyar su su na hirar su ta makirci


▪AMIR


Ya na jin su Miram sun fita , ya dawo cikin parlourn
Malik ya na zaune inda ya ke ko motsi bai yi ba

a hankali Amir ya karaso cikin parlourn ya nufi sofar da ya tashi ya koma ya zauna ya na fadin " Ina son mu yi wata Magana "

a hankali Malik ya juyo ya kale shi ya ce " wace magana ? "

" wanene ya nemi auren RIANNA lokacin da ba na nan "

" Miram ne ! amma ta ce ba ta son shi , yanzu dai Akwai Sarki Abdoul Mujeeb ya nema wa yaron shi babba , Aymane auren ta , kuma mahaifiyar ku ta ce ta yarda ka san Abdoul Mujeeb yayan ta ne "

cikin nitsuwa Amir ya katse shi da cewa " na san da wannan dukka , ina son na ga Yaron , MALIKAT INAS da ita RIANNA sun yarda ? "

" yanzu dai ba ya cikin saudiya , ya tafi wani aiki a kassar Turkey , bayan Azumi ya dawo , RIANNA ta ce sai ta gan shi kafin ta yanke shawara , ka san yar uwar ta ka da mugun son maza ma su kyau shi ya sa ta ki yarda da Miram wai ya yi mata tsufa " ya kai karshen ya na yar karamar dariya

" kennan babban yayan Diya ne ? " ya fada cikin zuciyar shi

ya yi nisa cikin duniyar shi ya jiyo Muryar Malik ya na fadin " ya kamata ka je ka yi wa matar ban kwana yadda ya dace "

slowly ya juyo da kan shi ya kali Malik ya daga mishi gera guda ya na fadin " What do you mean ? "

yar karamar dariya Malik ya yi kafin ya ce " ka na nufin ba za ka yi mata ban kwana ba , kar ka manta cikin daren gobe za mu tafi "

" goben idan ta yi na yi mata " ya kai karshen ya na tashi da ga saman sofar ya nufi corridor
da kallo Malik ya raka shi har sai da ya shiga sannan ya saki wani dan karamin murmushi



❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤


(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥




💔🥀 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) 💔🥀





👑❤ MALLAKIN MEERAH ❤👑



【THE ROYALTY LOVE 👑🕊💖】




Marubuciyar littafin
【TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺】





【 BOOK …………………… 2 ❤ 👑】





____________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊___________________



PAGE 10 ❤🔥






Amir kuma bayan ya koma bedroom din shi kai tsaye toilet ya nufa
jim kadan ya fito sanye da bathrobe da Allamun wanka ya yi
ya na fitowa ya nufi dressing room ya shiga
ko two minutes ba bai yi ba , ya fito da ga shi sai short , kai tsaye ya nufi katafaren bed din shi ya Haye ya yi rub da ciki , ya kai hannu ya kashe wutar dakin baki daya sannan ya lumshe idanun shi

ya dauki wajen good 30 minutes a haka kafin ya jiyo wayar shi ta yi ruri allamun shigowar sako , daman ba barcin ya ke ba

da farko har ya so ya share , amma wata zuciyar ta ce ya duba kar a je abu mai mahimanci ne

dan karamin tsaki ya ja kafin ya bude idanun shi ya kai hannu ya dauki wayar ya kunna ya kali screen din

wata number ce da a ka yi saving da sunnan * MY BELOVED ❤💍*
🤔🤔🤔 ku tsaya beloved ya na nufin masoyina ko na yi batan kai ? tommm wacece wanan beloved kuma 🤔🤔

a hankali ya kai hannu ya cire password din wayar ya shiga wajen Text ya fara karanto sakon ta kamar * Good night yaya Zayd di na ❤😚 *

text din ta ba karamin sanyaya mishi zuciya ya yi ba , har sai da lips din shi su ka dan motsa allamun ya so ya yi murmushi amma ya danne

a hankali ya fara typing shi ma ya yi mata reply da * Thanks ❤ Good night *
ni na zata da ya tura mata zai kashe wayar , kawai sai ya tsaya ya na kallon screen din har sai da ta yi mishi reply kamar haka " Thanks 💋 *
reply ya yi mata da * Okay ajiye waya yanzu tafi ki yi barci *

ko one minute ba ta yi ba ta yi mishi reply da cewa * kai ma ka tafi ka yi barci 😑 *
* shikenan sai da safe *
* yaya Zayd gobe za ka zo mu yi breakfast tare ? 🥺🥺 *
* eh zan zo *
* 🥳🥳🥳 yawwa yaya Zayd ni da kai na zan shirya mana breakfast , na tafi ma dan na samu na tashi da wuri , I LOVE YOU byeeeeee ❤ *
* bye *
ya na gama rubuta hakan ya kashe wayar ya ajiye saman bedside drawer ya na kallon wayar
da allamun ya na jiran sakon ta
sannu sannu har barci mai dadi ya dauke shi bai sani ba


* WASHE GARI ( misalin karfe 10 )


" Amir ! tashi Ammien ka na son magana da kai " Malik ya fada ya na dan bubuga kafar Amir da ke ta faman sharar barcin shi

a hankali ya fara motsi ya na karato adu'ar tashi da ga barci sannan ya ware idanun shi a hankali sai saman Malik da ke tsaye ya tsare shi da wadanan Hazel eyes din na shi

cikin magagin barci Amir ya ce " wai malam lafiya ka tashe ni ? "
" iyeeeee , lalle idon ka ya bude Amir , yanzu ni ka ke wa wannan tambayar ? Shikenan Tashi ka tafi Ammie din ka ce ke son yin magana da kai , ni zan wuce fada " ya kai karshen ya na juyawa ya fice bedroom din

ya na fita Amir ya sauko da kafafun shi kassa ya mike tsaye ya fara takawa ya nufi Toilet
jim kadan ya fito daure da towel a kugunshi , ya nufi dressing room kai tsaye
nan ma bai wani dauki lokaci ba ya fito sanye da jeans brown color da T-shirt white color , kafafun shi kuma , cikin wasu sneakers farare kal , ya saki wannan smooth hair din na shi , gashin shi yanzu tubarikallah ya toho har ya kai shoulder din shi , sai tashin kamshi ya ke

bedside drawer ya nufa ya dauki wayar shi ko duba ta bai yi ba ya saka ta cikin aljihu ya fice dakin ya fito corridor ya shigo parlour , kai tsaye ya nufi lift ya shiga ya sauko kai tsaye ya baro building din

ya nufi part din MALIKAT INAS
duk inda ya wuce sai dogarai sun sunkuyar da kai su na yi mishi barka da safya
in kuma bayi ne , sai sun zube saman guyiwowin su , su na gaishe shi har ya wuce sannan su tashi su ci gaba da tafiyar su

shi ko daya bai bi ta kan gaisuwar su ba ya nufi part din MALIKAT INAS , hankalin shi na wata duniyar ji ya ke kamar ya manta da wani abu mai mahimanci

a hankali ya motsa lips din shi ya na sallama ya shigo parlourn MALIKAT INAS
nan ya tardo ta zaune , ita da RIANNA da Nesrine duk sun yi zugum waje guda
su na jiyo sallamar shi su ka dago kai a tare su ka kali saitin kofar su na amsa mishi sallamar shi sannan RIANNA ta daura da cewa " Amir ina ka tsaya wai tun dazu mu na ta kiran ka a waya "

karasowa ya yi cikin parlourn ya na fadin " What happening ku ke kira na tun da safe ? "
RIANNA na shirin magana MALIKAT INAS ta daga mata hannu ta yi shiru sannan MALIKAT INAS ta ce " Je ka , ka gani da idon ka " ta fada ta na nuna mishi hanyar corridor

a hankali ya juya ya kali corridor din sannan ya juyo ya kali MALIKAT INAS ya na son ya yi magana ya shanye ya nufi corridor din kamar yadda ta ce

kai tsaye bedroom din Inaya ya nufa
a hankali ya sa hannu ya tura kofar ya na sallama cen kassan makoshi

ya na shigowa ya gan ta zaune tsakiyar gadon ta juya wa kofar baya ta sunkuyar da kai
a hankali ya fara jiyo Muryar ta cen kassa kassa allamun waka ta ke
karasowa ya yi cikin dakin ya tsaya dab da gadon ya na rike da hannayan shi a baya

murya kassa kassa ya ce mata " Barka da safya "
ba tare da ta juyo ba ta ce mishi " barka " a takaice sannan ta ci gaba da wakar ta

tsaya wa ya yi ya na kallon ta na wani dan lokaci kafin ya juya a hankali ya fice dakin
kai tsaye parlour ya dawo , ya nufi MALIKAT INAS ya tambaye " lafiya wai ku ka kiro ni tun da safe haka ? "

cikin bacin rai MALIKAT INAS ta ce mishi " Amir yanzun ne tun da safe , karfe 11 har da mintina ? "

shiru ya yi ya tsaya ya na kallon ta , tabbas ta na cikin fushi ba kadan ba , ga Dukkan allamu kuma da shi ta ke fushin

cikin nitsuwa ya ce mata " Ammie please calm down , me ya ke faruwa ne ? "

nuna mishi Dining room ta yi ta na fadin " tun karfe 6 ta shiga kitchen dan ta shirya maka breakfast , amma ba ka zo ba " Ta na gama rufe bakin ta ta ga juya a hankali ya koma cikin corridor din

bedroom din Inaya ya koma shi har ga Allah wlh ya manta da zancen breakfast din da za su yi tare , bare yau wani barci mai dadi ya dauke shi , ba dan Malik ya tashe shi ba da wuya ya tashi yanzu

a hankali ya sa hannu ya tura kofar dakin ya shigo ya na sallama cen kassan makoshi
ko motsawa ba ta yi ba ta na nan yadda ya bar ta , ta na wakar ta kassa kassa

gaban gadon ya karaso ya tsaya kamar dai da farko bai ce mata komai ba ya na kallon ta
sai da ya dauki lokaci a haka kafin ya zauna bakin gadon ya kai hannu ya daura saman shoulder din ta ya na fadin " Cutie ! "

" uhm " ta fada ba tare da ta juyo ba
" ba za ki juyo ba " ya fada ya na janye hannun shi da ga saman shoulder din ta

a hankali ta girgiza mishi kai ba tare da ya ce komai ba
hannu ya sa ya cire sneakers din kafafun shi sannan ya Haye saman gadon shi ma , ya koma gaban ta su na fuskantar juna ya yi irin zaman cin tuwo shi ma

ya na kallon face din ta ya ga uban hawayen da ke konce sama , ga wasu nan na zubawa bibiyu ga shi kuma ba kukan ta ke ba hawayen ne kadai ke zubowa

a hankali ya kai ya goge mata hawayen ta ya na fadin " hawayen minene wannan ? "
" komai ! " ta fada a takaice ba tare da ta kale shi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login