Showing 21001 words to 24000 words out of 47249 words
cin shi
tsawan shekaru yanzu rabon su da su yi diner tare da Amir , musaman Malik ya ba da umarni a shirya duk wani abinci da Amir ke so , Table din a shake ta ke kamar unguwa guda za ta ci abincin , amma su shidda ne kadai wannan uban duniyar
abincin su su ke ci cikin konciyar hankali babu wanda ya ce ko ufan
su na a haka Malik ya katse shirun su da cewa " Ina son ku ba ni hankalin ki duka , zan so na yi muku wata magana "
a tare Malikat Inas da Malikat Al'umu su ka hada baki wajen cewa " Wace magana ce wannan kuma ? "
dan jinkirtawa Malik ya yi kafin ya ce " Daya da ga cikin yaran da Amir ya dawo da su Matar shi , tsawan shekara biyu yanzu da yin auren su , ba na son jin korafin kowa a nan , Malikat Inas MALIKAT AL'UMU ku na ba wa hakin kulla da ita , ina son ku koya mata duk wani abun da ya dace , bayan dawowar mu da ga Makka za ta dawo dakin mijin ta "
baki sake Tesnim da MALIKAT AL'UMU ke kallon Amir su na zaro idanu
RIANNA da MALIKAT INAS ko sai murmushi su ke yi dama sun san da maganar auren
sarai ya lura da su amma bai ce musu ko ufan ba , Ya ci gaba da cin abincin shi
su na a haka su ka jiyo Muryar Malik ya na kiran Azim
da sauri Azim ya karaso wajen Malik ya Zube saman guyiwowin shi cike da girmamawa ya shiga gaishe su baki daya
daga mishi hannu Malik ya yi allamun ya yi shiru sannan ya ce " je ka kira min yarinyar da ke part din MALIKAT INAS , karamar "
ya na gama fadar haka Azim ya mike da gudu ya fice parlourn ya bar building din baki daya ya nufi part din Malikat INAS
ya na barin wajen Malik ya kali Amir ya ce " Nawfel ? "
slowly Amir ya dago kai ya kali Malik ba tare da ya ce komai ba
cike da zolaya Malik ya ce " Ba ka da abokin da zai raka ka dakin amaryar ka , ko na kai ka da kai na "
shiru Amir ya yi bai ce komai ba , a hankali ya tashi da ga saman kujerar shi ya juya
da sauri RIANNA ta ce " Akhie , wassa fa Abbi ke yi maka "
ko juyowa bai yi ba ya ci gaba da takawar shi ya koma parlourn ya zauna saman doguwar sofa ya fido wayar shi da ga cikin aljihun shi ya fara latsawa
yar karamar dariya Malik ya yi kafin ya ce " na ga allamun ke za ki raka shi dakin Amaryar shi ! "
RIANNA na shirin magana TESNIM ta riga ta cewa " a'a Abbi , ni da ita za mu tafi " ta kai karshen ta na kashewa Rianna ido guda
a tare su ka yi yar karamar dariya
duk abun da su ke yi Amir ya na jin su amma bai tanka musu ba
su na a haka Azim ya shigo parlourn ya na sallama Inaya na biye da bayan shi
a tare su ka karaso cikin parlourn ta na ganin Amir ta saki wani kyawatencen murmushi da gudu ta nufe shi ta rungume shi ta na fadin " yaya Zayd tun dazu ina ta jiran ka amma ba ka zo ba "
ajiye wayar shi gefe ya yi a hankali ya sa hannayan shi biyu ya dago ta da ga jikin shi ya ce mata " ba ki ga mutanan da ke wajen ba "
slowly ta juyo da kan ta , ta kali saitin da su Malik ke zaune , sun ko tsare su da idanu babu ko kiftawa
dum Inaya ta ji zuciyar ta buga da sauri ta boye fuskar ta a bayan Amir
" tashi ki je Abbi na son magana da ke " ya fada mata cen kassan makoshi
a hankali ta girgiza mishi kai ba tare da ta ce komai ba allamun ba za ta je ba
" please tashi ki je , ba abun da zai miki "
a hankali ta fido kan ta da ga bayan Amir , ta mike a hankali ta nufi su Malik zuciyar ta na duka uku uku ji ta ke yi kamar ta yi kuka , ko ta juya da gudu ta bar wajen amma ba hali
a haka ta karaso gaban Malik ta sunkuyar da kai Muryar ta har kerma ta ke yi ta ce " Bar.....barka da da da....re "
Malik na shirin magana Tesnim ta ce " Akhie wannan ita ce matar ta ka " ta kai karshen ta na yi ma Inaya wani kallon wulakanci
Da sauri Malik ya taka mata burki ya na cewa " ke Tesnim ki shiga tayi'tayin ki , wannan matar Yayan ki ce "
cikin nitsuwa MALIKAT AL'UMU ta katse shi da cewa " ran ka shi dade , na ga wannan ai ko TESNIM ta girme ta , ta ya za ta zama matar Amir din Saudiya guda "
" Nawfel Hicham Bin Jaabar , ka dauke ta a matsayin matar ka , ko kuwa " Malik ya fada cike da Izza , da Allamun yanzu da Al-MALIK HICHAM BIN JAABAR su ke tare ba mahaifin su ba
yanayin da ya yi maganar ya sa su duk shan ruwan jikin su , su ka sunkuyar da kai
Shiru Amir ya yi bai ce komai ya na kallon kassa
ya na a haka ya sake jiyo Muryar Malik ya na fadin " Nawfel da kai na ke magana "
slowly ya bude baki shi ya ce " eh " a takaice
wani kyawatencen murmushi ne MALIKAT INAS da RIANNA su ka saki a tare sun samu abun da su ke so
Malik kuwa juyo wa ya yi ya kali MALIKAT AL'UMU ya ce " Kin karbe ta a matsayin Sirikar ki ? "
dan karamin murmushi MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta ce " Tun da Amir ya yarda , ni ma ban da ja a kai , na karbe ta "
a hankali Amir ya Lumshe idanun shi ya na sauke ajiyar zuciya , shi dama har ga Allah ya na tsoron su ce ba za su karbe ta a matsayin matar shi ba amma tun da sun karbe ta komai ya yi mishi sauki
haka zalika Malik sai da ya yi wa Allah godiya cikin zuciyar shi
a hankali ya mika wa Inaya hannu
ba musu ta karaso a hankali ta daura hannun ta saman na shi , hannun ta har kerma ya ke yi
dan karamin murmushi Malik ya yi kafin janyo mata chair din da Amir ya tashi ya ce ta zauna ba musu ta zauna ta na sunkuyar da kai
ta na zama Malik ya ce " Ba zan yarda wani ya yi mata ko da kallon da bai dace ba , kin ji dai na fada miki Tesnim " ya kai karshen ya na tsuke fuska dan ya san Halin Tesnim , ba ta da mutunci ko kadan bare in ta girmi mutum
yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " Abbi ni na ma isa , ai tsakanin mu gaisuwa ce kawai "
a hankali Malik ya gyada kan shi kafin ya kali Inaya da ta sunkuyar da kai ya ce " dago kan ki yarinya "
shiru Inaya ta yi ko motsi ba ta yi ba
da sauri RIANNA ta ce ma Malik " Abbi ba ta jin larabci , sai kun yi da Turanci "
gyada mata kai Malik ya yi kafin ya yi mata magana da turanci ya ce " dago kan ki , nan duk sirikan ki ne , kar ki ji tsoro kin ji "
a hankali Inaya ta gyada mishi kai kafin ta dago ta na bin su da kallo daya bayan daya sannan ta saki wani cool murmushi ta meda kan ta ta sunkuyar
" in sha Allah bayan dawowar mu , da ga Makka za a gabatar da ita a matsayin matar Amir , yanzu ina son ku koya mata duk wani abun da ya shafi Daular Saudiya " Malik ya fada
a tare duk su ka hada baki su na cewa " an gama ran ka shi dade "
Inaya kuma a hankali ta dago kai ta kali Malik ta ce " Uncle , zan iya komawa , barci na ke ji " ta kai karshen ta na marairaice fuska
dan karamin murmushi Malik ya yi kafin ya gyada mata kai sannan ya kali Amir cikin harshen larabci ya ce mishi " Nawfel , tashi ka meda ta part din MALIKAT INAS "
a dubu dari Amir ya dago kan shi ya kali Malik ya na zaro idanu
da sauri Malik ya daga mishi hannu ya na fadin " idan ba za ka tashi ba , ni na tashi da kai na "
dan karamin tsaki Amir ya yi ya na kauda kan shi gefe sannan ya tashi ya nufi hanyar fita wajen
yar karamar dariya Malik ya yi kafin ya kali Inaya ya ce " za ki iya tafiyar ki "
dan karamin murmushi Inaya ta yi kafin ta mike da ga saman Chair din ta nufi hanyar fita wajen ta bi bayan Amir
a tare shi da ita su ka baro Building din , ta na tafe ta na hamma allamun ta na jin barcin sosai
duk abun da ta ke ya na lure da ita amma ya kyale ta
a haka har su ka karaso cikin part din MALIKAT INAS
su na shigowa parlour su ka tardo Diya tare da Nesrine su na zaune a kassa su na hirar su gwanin burgewa
Amir ya ganin shi ya kara tsuke fuska , bai ce mishi komai ba su ka nufi corridor har sai da ya raka ta cikin bedroom din ta
Diya na ganin shi amma bai ce mishi komai ba har sai da su ka shiga corridor sannan ya yi wata yar karamar dariya
Amir kuma su na shiga cikin bedroom din ta ya ce mata " sai dai safe " ya kai karshen ya na juyawa
bai yi taku daya ba ya jiyo Muryar ta ta na cewa " yaya Zayd ba za ka zauna ba "
slowly ya juyo ya kale ta ya ce " me za ki ba ni in na zauna ? "
da sauri ta kai hannu ta bude box din bedside drawer ta fido sweet biyu ta nuna mishi ta na murmushi
a hankali ya girgiza mata kai ya ce " ba na shan sweet "
turo dan bakin nan nata ta yi cike da shagwaba ta ce " Don Allah kar ka tafi yaya Zayd " ta kai karshen kamar za ta yi kuka , har sai da idanun ta su ka ciko da ruwa
cikin konciyar hankali ya tako ya karaso bakin gadon ya zauna ba dan ya so ba , ba zai so ya ga kukan ta ne cikin wannan daren , ya san ba zai samu nitsuwar yin barci ba in har ta yi mishi kuka
ta na ganin ya zauna ta yi sauri ita ma ta Haye bed din duka , ta zauna a tsakiya ta yi zaman cin turo
ta na murmushi ta ce " yaya Zayd na gwada maka wani abu "
a hankali ya gyada mata kai allamun eh
da sauri ta daga pillow din gadon ta dauko wata tsadadiyar phone kirar Iphone 14 pro max , mai launin Gold sabuwa fil har wani kyali ta ke yi
dan zaro idanu ya yi ya kai hannu ya karbi wayar ya na fadin " wa ya ba ki wannan ? "
" Aunty RIANNA ce ta saya mana ni da Nesi "
a hankali ya gyada kan shi ya na kunna wayar , nan ya ga akwai card Sim a ciki
contact ya shiga ya ga babu number ko guda a ciki
bai tsaya wani tunanin ba , ya saka number din shi ya yi saving din ta
( ni dai ba zan fada muku sunan da ya saka ba gaskia π€π€π€ )
bayan ya yi Saving ya danna wa kan shi kira
nan take wayar shi da ke cikin aljihun shi ta fara ringing , hannu ya kai ya fido wayar sannan ya kashe kiran
ya mika mata wayar ta , Sannan ya shiga latsa ta shi ya ce mata " Idan na tafi zan dinga kiran ki ga number ta na saka miki , ko ki na bukatar wani abu sai ki kire ni "
" shikenan yaya Zayd " ta fada ta na ajiye wayar saman bedside drawer
meda wayar shi shi ma ya yi cikin Aljihu kafin ya ce " ki dai na kira na da yaya Zayd ba shi ne ba sunana "
a hankali ta matso kusa da shi ta ce " to minene Sunan ka "
" Nawfel " ya fada mata a takaice
" Zayd ba sunan ka ba ne , kuma ai na ji yaya Moussa ya na kiran ka da Amir "
" Zayd sunan kaka na ne , Shi ya sa Diya ba ya iya kira na da sunnan sai dai ya ce Amir "
ya na gama rufe bakin shi ya ji ta zagayo da hannayan ta ta baya ta rungume shi , ta kontar da kan ta saman bayan shi ta na fadin " ni dai da yaya Zayd zan ci gaba da kiran ka , ni da wannan sunnan na san ka , kuma , shi zan rike "
hmm ita ba ta san Amir ya riga da ya bar duniyar mutane
ya na jin ta zagayo da hannayan ta ya dauke kamar wutar nepa
cen cikin zuciyar shi ya ce " yarinyar nan ta na shirin kashe ni wlh "
[16/09 Γ 09:57] M.N.M:
β€β EXILED PRINCE ββ€
(LOVE MEETS POWER ) ππ₯
ππ₯ ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) ππ₯
πβ€ MALLAKIN MEERAH β€π
γTHE ROYALTY LOVE πππγ
Marubuciyar littafin
γTAURIN ZUCIYA πππΊγ
γ BOOK β¦β¦β¦β¦β¦β¦β¦β¦β¦β¦β¦ 2 β€ πβγ
____________________ππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉ___________________
ο½PAGE _______7 β€π₯ο½
yar karamar dariya Abdoul ya yi kafin ya ce " mama ni fa ba tsoron shi na ke ba , kawai dai yanzu ya fi karfin na je a na kiran shi , sai dai shi ya kira mu "
shiru mama ta yi ba ta ce komai ba ta na ci gaba da shafa kan Nesrine da barci ya dauke
βͺAFTER SOME HOURS
βͺAMIR
zaune su ke shi da Malik a cikin parlourn su da ke hawa na uku
su na zaune bakin Glass su na kallon Masarautar
su na a haka kawai su ka ga Inaya ta fito da ga part din MALIKAT INAS , ta na sanye da wata gown fara kal mai mugun kyau ba ta daura Alkyaba ba , ta saki wannan lalawsan gashin kan ta ya zubo mata har tsakar baya ta na tafiyar ta cikin konciyar hankali
tun da ta fito AMIR ya tsare ta da wadanan hazel eyes din na shi har maganar da Malik ke yi mishi komai bai ji ba
a hankali Malik ya juya kan shi ya kali saitin da AMIR ke kallo
nan ya ga Inaya ta na tafiyar ta a hankali cikin masarautar gwanin burgewa
dan karamin murmushi Malik ya saki kafin ya kai hannun saitin fuskar AMIR ya kyasta mishi yatsun
a hankali AMIR ya lumshe idanun shi kafin ya bude su ya juya ya kali Malik ya na daga mishi gera guda allamun minene
" me ka ke kallo ne haka tun dazu na ke yi maka magana amma hankalin ka ba ya tare da ni "
juya kan shi AMIR ya yi ya na fadin " nothing " a takaice
" shikenan fada min me ke tsakanin ka da yarinyar cen da ka tsare da ido " Malik ya fada ya na daga mishi gera kamar ya na kallon shi
dan jinkirtawa AMIR ya yi kafin ya bude bakin shi murya kassa kassa ya ce " She is my wife , your daughter-in-low , ko ka na da ja ? "
a dubu dari Malik ya mike tsaye ya na fadin " what , Matar ka fa ka ce min AMIR , yaushe hakan ta faru "
ba tare da ya juyo ya kale shi ba ya ce " two years , Tsawan shekara biyu yanzu da yin auren "
wani kyawatencen murmushi ne Malik ya saki ya na komawa ya zauna saman chair din shi ya ce " ba banza ka ki dawowa , ashe yarinyar mutane ka samu "
shi dai AMIR shiru ya yi bai ce mishi komai ba ya ci gaba da kallon Inaya
" Bayan dawowar mu da ga Makka za ta dawo part din ka da zama " Malik ya fada ya na kallon AMIR
a hankali AMIR ya juyo ya kali Malik ya ce " Makka kuma ? "
" eh , ko ka manta tafiyar da mu ke yi duk watan azumi ? "
dan lumshe idanun shi AMIR ya yi shi ya ma manta da wannan tafiyar da su ke yi shi da Malik , shi gaskia ba ya jin zai iya yin tafiyar nan ya bar Inaya a cikin masarautar nan