Showing 39001 words to 42000 words out of 122381 words

Chapter 14 - Daudar Gora Book 1 Hausa Novel Complete

25 Dec 2024

401

amin afuwa bani da wani zaɓi bayan hakan. Saƙone daga Baba yaro”. Ya ƙare maganar da miƙama Kaka takardar hanunsa. Kaka ya amsa takardar yana ɗan juyata, sai kuma ya nuna hanyar shiga da faɗin, “Kaga shigo daga ciki”.
A tare suka shiga cikin gidan, Kaka ya buɗe takarda yana dubawa, yayinda Iyyani ta kawoma baƙo dake gaisheta ruwa. Kaka ya ɗan murmusa bayan gama karanta takarda tare da girgiza kansa. “Ayyub naga saƙo, sai dai kuma inaga basai naje da kaina ba. Zan baka saƙo ka kai masa nima. Ita kuma ALLAH ya bata lafiya yasa ya zama kaffara a gareta”.
Ɗan jimm Ayyub yayi, sai dai kafin yace wani abu Kaka ya miƙe. Ɗakinsa ya shiga, kusan mintuna ashirin sai gashi ya fito da wata jakkar fata. “Kayi maza ka kai masa wannan. Kace kuma ina gaishesa”.
Cike da girmamawa Ayyub ya amsa da faɗin “Angama Baba. A huta lafiya”. Kai kawai Kaka ya jinjina masa yana murmushi. Sai da ya rakasa har ƙofar gida sannan ya dawo. Iyyani da duk ta shiga damuwa ko zama baiyiba ta jeho masa tambaya, dan tasan ma'anar wannan murmushin nasa bana farin ciki bane, yakan yisane a lokacin da wani abu ke masa ƙuna a zuciya.
“Itama sun taɓata ko?”.
Bai bata amsa ba sai da ya zauna. Ya jawo allurarsa zai cigaba da ɗinkinsa. “Dama ai bazasu barta haka ba saboda wasu dalilai”.
“Dalilai kuma? Nami to?”.
“Kinga sarkin tambaya bani zaren cen dana manta kan bunu”.
Iyyani tasan tambayarce baya son amsa mata, dan haka taja bakinta tai shiru bayan ta kawo masa zaren. Sai dai sam zuciyarta babu nutsuwa......


★★.MASARAUTA.★★

Bayan sallar azhar Ayyub ya iso masarauta. Zuwa yanzun har an fara raɗe raɗin mutuwar Iffah, duk da kuwa ya tadda masu maganin da suka isa suka tumbatsa da matuƙar yawa an tarasu kowa nata gwada ƙoƙarinsa da baiwar da ALLAH ya basa.
Baba Yayaroya furzar da nannauyan numfashi bayan ya amshi saƙon kaka a hanun Ayyub “Dama nasan da wuya Dattijo ya zo”.
“Amma duk da haka ka aika masa Baba?”.
“Ya cancanci a aika masan”.
“To amma miyasa yaƙi zuwa? Bayan kuma alamu sun nuna kai tsaye ma yasan abinda ke faruwa anan ɗin”.
Baba ya tsurama ɗan nasa ido na wasu sakanni, sai kuma ya girgiza kansa. “Ba lallai sani irin wanda kake tunani yayi ba. Dan nidai nasan baida wata alaƙa da abinda ke faruwa anan. Sai dai ya sani ta dalilin baiwar da ALLAH ya masa duk da shi yana gudunta ne”.
“Amma Baba....”
“Kaga Ayyub wannan ba lokacin tambayoyi bane. Bara naje muga ko za'a dace anan.”
Da kallo Ayyub yabi mahaifin nasa. Sai dai ƙasan ransa fal tambayoyine da yasan samun amsarsu zaiyi wuya a lokacin da yake buƙata. Yasan mahaifinsa gawurtaccen masanin magani ne irin na gargajiya dama na gusar da junnu. Shahararsa tasa Daular Ruman ɗaukarsa da bashi matsayin (Mai magani a gonar yaro) amma ya rasa minene dalilinsa na bama wancan dattijon girma mai tsanani duk da shi kowa bai sanshi ba sai da sunan mai ɗinka kayan doki.....

*_ZAWJATA-ALMILKI_*

Zuwa yanzu numfashin Iffah ma yana fitane da taimakon na'urori, yayinda jinin dake fita a jikinta har yanzu yake fita ta kunenta. Na ido da hanci da baki ne kawai likitoci suka samu nasarar tsaidawa. Baba yaro shine shugaba na masu maganin, dan haka ake basa damar shiga kai maganin da duk aka bayar dan ai mata amma da taimakon Jasrah kai tsaye. Yanzu ɗinma dai hakance ta kasance. Bayan neman iso aka bashi iznin shiga inda Iffah take, sai dai babu mai iya ganinta kasancewar zagaye take da glass.....

*_SHAHAN-SHAN_*

Bani kaɗai ba, nasan duk masu karatu tambayarsu zata rinjayane akan wai shin duk abin nan dake faruwa ina _Shahan-shan_ yake ne a matsayinsa na shugaba ga ƙasar ruman baki ɗaya bama daular ruman ba?. To amsar itace yana nan a cikin masarautar, sai dai kuma tun a yammacin jiya bayan dawowa daga sallar juma'a babu wanda ya sakejin motsinsa. Duk da dama fitarsa a zahiri ta zuwa massallaci ce kawai. Yana kuma da ƙofar dake kaisa har massallaci daga sashensa batare daya fito wani ya gansa kai tsaye a masarautar ba. Shiyyasa har zuwa yanzu wanda suka san fuskarsa ko'a cikin masarautar ma ƙalilanne musamman a cikin hadimai. Duk abinda ke faruwa a masarautar kuma kowa nada yaƙinin ya sani, sai dai ba'an miyasa ya zaɓi yin shiru ba.
Kamar jiya yau ma labari yajema Malikat Bushirat akan Shahan-shan bai fito sallaba har ta asubahi. A yanzu kam hankalinta ya tashi ba kamar a jiya ba data ɗauka dan yana fushi da auren da yaso bijiremawa ne. A take ta bada umarnin shirya mata zama da shi. Dan ita a karan kanta na uwa garesa bata da hurumin ganinsa a duk sanda taso ko kai tsaye bisa doka da al'adar masarauta da ƙarfin iko na Shahan-shan. Sai zuwa ɗaya tak na kowanne wata da yakanyi kawai na zahiri. Amma duk da haka Tajwar Eshaan kan saci jiki wani lokacin ya kawo mata ziyarar tsakkiyar dare cikin ɓadda kama batare da wani ya taɓa fahimtaba har yanzu a cikin masarautar.
Shiri ta farayi duk da batada tabbacin samun damar ganin nasa a yanzu, sai dai sanin duk ƴan majalissar fada na'a masarautar yau yasa bata fidda tsammani ba. Cikin sa'a kuwa cikin abinda baifi mintuna ashirin ba Ghazi ya zo ya isar mata da sakon ƙarɓuwar buƙatarta. Dan dama suma ƴan majalisar fadan nada buƙatar samun wanda zai duba shi, hakan kuma bamai yuwuwa bane dan ita dake amsa suna mahaifiyarsa da Malikat Haseena (Kakarsa) da matansa ne kawai ke da wannan hurumin saboda an tabbatar tun jiya baiko zo falo na uku ba. Sannan duk abincin da mai dafa masa ya shirya tun daga kan na daren jiya har safiyar yau da rana haka yake zuwa ya kwashesa ba'a taɓa ba.
Cikin shiri na alfarma da rakkiyar tawagar hadimai maza da mata Malikat Bushirat ta doshi sashen Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed.........✍



*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)



𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻


*_18_*


..........Tuni labari ya kai kunnuwan sauran matan gidan musamman Malikat Ashwaq da Ameera Danish-Ara da Ameera Haifah cewar Malikat Bushirat ta ziyarci Shahan-shan saboda rashin jin motsinsa. Hakama wasu a cikin matan manyan masu faɗa aji a gidan harma da mazan, wasu iyaye, wasu ƴaƴa, wasu jikoki. Hakan yasa aka kafa gungu-gungu na cigaba da tattaunawa tare da sukar cewar yasan tsiyar daya aikata ai shiyyasa ya ɓoye kansa. Kokuma dodon tsafin nasa ne ya bashi wannan umarnin naƙin fitowa har sai yarinyar mutane ta mutu... Wasu kuwa murmushine kawai nasu dan su kaɗai suka san kansu. Yayinda wasu ke tausayama Tajwar Eshaan ɗin da ganin abubuwa ne suka masa zafi da yawa dan suna kallon komai a matsayin makirci da mafi yawa akafi dangantashi da matan ubansa, da kuma ƴan uwan mahaifin nasa na jini masu zawarcin son hawa wannan kujera... (To koma dai miye ALLAHU shine mafi sani).

Duk inda ta gitta hadimai zubewa suke akan gwuyawunsu suna miƙa gaisuwa. Ko sau ɗaya bata ɗaga ido ta kalla kowa ba, sai hadimanta ne ke amsawa duk wanda yay gaisuwar. Tun'a harabar shiga sashen dukkanin hadimanta suka dakata. Sashen Shahan-shan shine mafi ƙyawu da ƙawatuwa na ƙyale-ƙyale a daular ruman. Gini ne da kusan zamuce an yisa da zallar gilashi. Yanada hawa huɗu dan haka sai da lifter. Zaman lissafin dukiya da daular da aka zuba a cikinsa da kuma ainahin fadar da Shahan-shan ke zaman fadanci ma ɓata lokacine. A lokuta da dama duk abinda ke faruwa a cikin masarauta Tajwar na kallo daga cikin sashensa musamman idan a hawa na ƙarshe yake, hatta da wajen masarauta yana iya hangowa. Hadiman dake tsaron sashen matsayin sojoji suka maye gurbinsu wajen take mata baya har falon farko. Anan ɗin ma hadiman zubewa suka dingayi ƙasa kawunansu a risine domin girmamawa a gareta har zuwa falon farko. Wanda suka rakota ciki suka dakata, na falon farkon dake a hawa na ɗaya suka take mata baya har zuwa falo na biyu a hawa na biyu, suma iyakarsu nan, wanda suke a falo na biyu sukai mata rakkiya har zuwa falo na uku dake a hawa na uku. Anan soja ɗaya ne, shine amintacce da yake iya haurawa har zuwa falo na huɗu hawa na huɗu a falon dake can. Anan ma akwai hadimi ƙwara ɗaya sai masu dafa masa abinci su biyu suma. Sune amintattun na ƙarshe dake iya zuwa hawa na can ƙarshe na huɗu kenan, suke iya ganin Tajwar kai tsaye kuma, suke iya sanin a wane ɗaki ya kwana, suke iya shiga ɗakin barcinsa suyi gyara ko kai abinda yake buƙata, ko isar da wani saƙo. Bayan gaisuwa a gareta Ghazi ya nema afuwa da bashi damar zuwa nema mata iso ga Tajwar. Hannu kawai ta iya ɗaga masa.
Mintuna da basu wuce huɗu da shigar tasa ba ya dawo ya zube a gabanta. “ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsahon rai mai amfani, shugaba ya bada damar shiga dake har ciki”. Shiru tai kamar bazata motsa ba, dan a duk sanda ta kama zasu gana anan sashensa yakan fito ne su haɗu a wannan falon ko ƙaramin falon hutawarsa dake a hawa na uku. Wannan kuwa a ƙa'ida ko matarsa bata shigarsa, dan haka jin wannan amasa yasata fahimtar akwai matsalar da gaske.
Bayan buɗe mata ƙofa Ghazi yaja da baya. Cikin takunta na ƙasaita da isa ta ƙarasa shiga cikin matsakaicin falon mai fidda wani irin ƙamshi da wadataccen sanyin na'urar ac. Rashin girman falon ba komai bane, haɗuwarsa da tsaruwarsa ce mafi ɗaukar hankalin mai kallo. Dan an ƙawatashine da wasu irin tausasan tumtum na ainahin sarakan asali, dardumar falon kanta abin kallo ce, komai ya tsaru dai-dai da tsaruwar manyan mutane. A hankali takai zaune tana mai sauke ajiyar zuciya, sosai takejin matuƙar kewar gudan jinin nata, sai dai tsarin masarautar tasu ya tilasta mata haƙura akan dole tamkar kowace uwa ta Tajwar irinta da akai a cikin wannan daula....
Motsin buɗe ƙofa da ƙamshin turarensa mai rige-rigen isowa hancinta da sautin takumsa ya sata ɗago ƙyawawan idanunta ta sauke a kansa. A hankali ya cigaba da takowa cikin ƙasaita da nutsuwa har ya ƙaraso gareta. Daga tsayen da yake ya ɗan risinar da kansa alamar girmamawa. “Amincin ALLAH ya tabbata a gareki *_Ammie!_*”. Nutsatstsiyar muryarsa mai zurfi da rashin hayaniya ta fita a fisge, dan yanda ya motsa lips ɗinsa a hankali zama ka iya ɗauka bashi yay maganar ba. A hankali ta sauke ajiyar zuciya mai haɗe da nannauyan numfashi ta jinjina kanta da lumshe idanunta ta buɗe a kansa alamar amsawa. A nutse ya kai zaune a gefenta, yay zama irin na ƙasaita da kame kai da kuma girmamawa a gareta matsayin mahaifiya. Hanunta ta ɗaura bisa tattausar sumar dake kansa kwance, tare da ɗan ranƙwafawa ta sumbaci goshinsa da yay zafi zau alamar baida lafiya. Lumsassun idanunsa da ƙanƙancewarsu ya hanata ganin hasken cikinsu ya buɗe, ya motsa lips ɗinsa kaɗan alamar murmushi a gareta. Murmushin ta saki itama a karo na farko da gyara zamanta na ƙasaita.
“Kaima amincin ALLAH ya tabbata a gareka *Bugun zuciyar Ammie'n sa*”.
Ɗan luuu yay da idanunsa ya lumshesu tare da sake buɗewa a kanta da ɗan risinar da kai na girmamawa. Sai kuma ya kamo hanunta data janye a saman sumar kansa ya sumbata. Ajiyar zuciya ta sake saukewa mai kauri da jin ƙarin ƙaunar tilon gudan jinin nata da maƙiya suka sako a gaba. Tana matuƙar ƙishirwar rashin ganinsa a kusa da ita ko yaushe, sai dai babu yanda ta'iyane.....
“Ammie kina lafiya?”.
Ya katse mata tunanin da take neman yin nisa a ciki. Numfashi ta ɗan fisga ta fesar alamar dawowa. Sai kuma ta girgiza kanta da raunana fuskarta. “Kasancewarka lafiya itace tawa Saiful-mulk”.
A karo na biyu ya saki murmushi yana ɗan jinjina kansa shima, sai kuma ya ɗago ya ɗan kalleta ya kauda kai. “Ina lafiya Ammie”.
“Ni ba haka na gani a cikin idanunka ba *_Negar_*”.
Baice komaiba kusan minti ɗaya, hakan ya fahintar da ita bazai ce ɗin ba, tai murmushi kawai tana kaɗa kanta. Ta yarda jinin mulki gaskiya ne, dan tana ganinsa yana yawo a cikin gudan jininta. Duk ƙasaita da miskilanci irin na Tajwar Haysam da ita kanta da ake faɗi Eshaan ɗinta ya takasu ya shanye. Irin miskalayen mutanen nan ne shi masu matukar ban mamaki da wuyar sha'ani, dan kai tsaye baka isa gane ainahinsu ba balle farin cikinsu ko damuwarsu kai tsaye, a matsayinta na mahaifiya a garesa da ake ganin yafi sakewa da ita fiye da kowa sukanyi zaman awa guda bai firta jimlar magana sau goma ba, murmushi kam ita da Malikat Haseenah kawai ke gani daga garesa sai mahaifinsa kafin yabar duniya......
Lurar da yay tayi nisa a tunani ya sashi kai hannunsa cikin ƙyaƙyƙyawan bowl ɗin da aka cuɗa dabino da zuba ya ɗakko tsagin dabino ɗaya daya naɗi zuma yay luntsum, ya tare da ɗayan hanunsa ya kai bakinta. A hankali taja numfashi ta sauke alamar dawowa. Babu musu ta matso tare da buɗe bakin ya saka mata. Sai da ta cinye a nutse tana mai kallonsa da murmushi sannan itama ta ɗauka kamar yanda ya bata ta bashi har sau uku. Tasan yunwa yake ji, amma yaƙi cin komai saboda damuwa. Tun yana yaro haka yake, a duk sanda sukaje dubashi a inda ya girma ita da Tajwar Haysam ta wannan hanyar take gane yanada damuwa, ko kuma yana fushi. Dan in har yana jin yunwa yaƙi cin abinci suka matsa masa akan yaci zai ɗiba abincin ya saka a bakinsu, sukuma hakan da yayi zai nusashesu zama su bashi da kansu har sai ya ƙoshi. Tissue tasa ta goge masa bakinsa idonta dake kansa na cika da ƙwalla.
“Kanajin yuwa Negar?”.
Gajeren murmushisa ya sakar mata da kauda kansa gefe maimakon amsar data buƙaci ji daga garesa. Itama bata sake cewa komaiba, sai wayar landline dake gefensa ta ɗauka. (Inba akan Tajwar Eshaan ba waya isa ganin Malikat Bushirat a haka😑). Cikin ƙanƙanin lokaci aka iso da abinda ta buƙata. Shi dai kallonta yake a harɗe kamar yanda itama take zaune a harɗen. Abincine na musamman, wanda tasan shine mafi soyuwa a garesa...
“Idan kana zama da yunwa bazan yafema kaina ba”.
Idanunsa yay kamar zai rufe sai kuma ya buɗe a kanta. Ƙasaita jininsa ce, kamewa da tsumewa nagartarsa ce. Kwarjini da cikar haiba mutuncinsa ne. Miskilanci gadonsa ne. inba ita ɗin bama wake ganin murmushin kojin furucin bakinsa, dan babu abu mafi wahala da girma ga Tajwar Eshaan kamar magana. Dariya kam ko'ita a karan kanta zata iya rantsuwa bata taɓa gani ba tunda ba'a gabanta ya tashi ba, sai lokaci-lokaci suke zuwa su gansa.
Abincin ta haɗa masa a gabansa da kanta, babu musu kuwa ya amsa tausasan idanunsa na kallonta da jin ƙaunarta kamar kowane ɗa akan mahaifiyarsa. Tsahon mintuna yana tsakurar abincin cike da ƙasaita kamar wani magani, kafin ya ɗauka tissue ya goge bakinsa da janye jikinsa da ga kwanikan alamar ya ƙoshi.....
“Ya take yanzun?”.
Tambayar da take son jin tun ɗazu daga bakinsa ta fito tamkar an fisgota. Idanunta ta ɗan kafe kansa, amma sai ya kauda kai gefe kamar bashi ya buƙaci ji ba. Taja numfashi ta fesar, itama batare data sake cewa komai ba ta cigaba da nazartar sa. Kusan mintuna uku tsakani sannan ta nisa...
“Ban san mikafi buƙatar ji ba. Sauƙin ko akasin sa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login