Showing 69001 words to 72000 words out of 122381 words

Chapter 24 - Daudar Gora Book 1 Hausa Novel Complete

25 Dec 2024

414

ɗakin dake jikin wanda suke kwance da waya a hannunsa......

*_ZAWJATA-ALMILK_*

Dukan matakin shawarar da Sir Fawzan ya bata shi tabi, dan tunda sukai bankwana da Daneen Ammarah tai shirin barci ta sakama ƙofarta key. Ta fara da buɗe Watsap, sannan ta lalubo number Ajmaal. Cikin sa'a kuwa yana online, wani farin ciki ne ya ratsata. Taja kakkauran numfashi da godema ALLAH.
_Assalamu alaikum_
Ta fara turawa da fatan samun amsa zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. Tsahon mintuna kusan goma babu alamar zama a buɗe saƙon. Sake tura sallamar tayi a karo na biyu. Ta dasama wayar ido kamar mai irgan fitan numfashinta. Kamar a mafarki taga an buɗe, tai kasare tana jiran taga an amsa sai dai shiru har kusan wasu mintuna goman. A yanzu kam zuciyarta ta sosu, dan duk yanda take buƙatar abu ga mutum ta tsani a wulakantata. Ta cije lips da ƙarfi tana danne fushin dake son mata tasiri.
_Wa'alaikissalam_.
Aka amsa mata a bazata. Nannauyar iska ta furzar, itama ta buɗe saƙon ta share. Da ƙyar ta iya danne zuciyarta mintuna bakwai suka cika.
_Sunana Fareedah bint Zayyan_.
Tsahon mintuna kusan goma yanzu ma sannan aka buɗe.
_Na sani_.
Tai shiru tana kallon amsar, sai kuma taja tsaki na takaici. A fili ta furta, “Aikin banza. Ka sani shine baka san aikinka ba mtsoww!!”.
Sharewa tai, ta rubuta masa.
_Kwanaki na kira, amma akaimun tarbar da har yau ina mamakinta. Shin dama manyan ƴan jarida haka suke da wulaƙanta bukatar marasa ƙarfi?_
Tsahon minti ashirin da buɗe saƙon babu alamar za'a amsata. Hakan yay mata ciwo matuƙa. Sir Fawzan ta kira, bugu biyu kuwa ya ɗaga. A ɗan rikice yace, “Iffah baki ganin akwai matsala yawan kiran nan? Masarauta fa ba irin ko'ina bane sunada hanyoyin tsaro ɓoyayyu ciki harda cctv”.
“Hakane Sir, amma nima dole ce ta sakani kiran. Anya kuwa wannan abokin naka da gaske ɗan jaridar ne? Sam baya ɗaukar al'amarina da muhimmanci, duk ɗan jarida na kwarai zaka samesa da zumuɗi akan labari, musamman ma irin nawa daya kasance babba”.
“Miya faru? Bai amsa saƙonki ba ne?”.
“Ya amsa. Amma yanamun yanga. Harna fara jin gundira a huɗɗa da shi”.
“Karki saurin karaya, amma nayi mamaki dan masan Ajmaal ba mutum bane mai irin wannan siffar wlhy. Inaga dai akwai aikin da yake yi a wannan gaɓar shiyyasa. Kin san su abubuwan nasu da yawa. Kin san kuwa yanda ya ƙagu akan son jinki, dan ɗazun na fara ƙyara masa abinda ke ranki kaɗan”.
Ta ɗanji sassauci daga haushinsa. Taja ajiyar zuciya a fili da faɗin, “Shike nan bara na koma”.
Sallama yay mata ya yanke wayar.
_Am sorry na haɗa wani aikin ne da saurarenki. Yanzu ina jinki_.
Da wannan saƙon taci karo bayan yanke wayar. Sanyi ta ƙaraji a ranta. Cikin ɗan karsashi ta maida amsa.
_Ayya kayi jaƙuri na maka gurguwar fahimta._
_Babu damuwa_
Aka amsa mata cikin ƴan sakanni. Cike da karfin gwiwa ta rubuta.
_Nasan abokinka ya fara maka bayani akan nemanka da nake ido rufe._
_Hakane. A yanzu haka ma munyi dashi zai bani wani yankin rubutunki dake hanunsa._
_Alhamdullahi. A yanzuma akwai cigaban wancan rubutun a hannuna nima. Sai dai ban san ta hanyar da zai zo garesa ba ko gareka_.
_Wannan mai sauƙine ai. Zaki iya turamin shi tanan_
_Wai! Amma typing ɗin zaimun wahala gaskiya_.
_Karki damu ki ɗauki hoto_
Cike da zumuɗi ta miƙe. Gado ta ɗaga ta ɗakko notebook ɗinta, a take ta ɗauka hoton duka rubutun ta tura masa.
_Gashi, insha ALLAHU duk bayan kwanaki uku zaka iya ganin saƙona_
_Masha ALLAH hakan yayi, sai dai a maimakon kwana uku mizai hana muyi mako-mako. Dan wani abun da zai zo yana buƙatar bin diddigi da faɗaɗa bincike mu tanan a garemu._
_Yanda kace haka za'ayi. Ni dai fatana ka kasance ɗan jarida mai gaskiya da riƙon amanar kimar ƙasarsa. ALLAH shine shaidata na baku dukkan yarda kai da Sir Fawzan. Idan akasin nasarata ya biyo bayan yunƙurina ku zan zarga. Duk kuma yarinyar data samu kanta a irin halin da ƴan uwana da ni muka kasance kuma zaku amsa sunan azzalumai ne kamar yanda Shahan-shan ɗin ke amsawa a yanzu. Ku kuma dinga tunawa da mala'iku tare da ku masu rubutawa daga ayyukanku na zahiri da baɗini. ALLAH ya cigaba da tsare ƙasar ruman. Idan kanada wata tambaya zaka iya tura min text message na Barka lafiya_.
Bata jira amsa daga garesa ba ta fita gaba ɗaya. Watsap ɗin ta goge ta kashe wayar gaba ɗayama tana sakin ajiyar zuciya a jajjere. Sai takejin wani kaso na damuwarta da nauyin zuciyarta ya ragu kaɗan. A wani gefe kuma kamannin mutumin can da wanda ta gani a jiya matsayin Shahan-shan ne ke ta faman mata kaikawo babu alamar zai barta ta huta......

★★.... “★★” .....★

“Lafiyarki da tsahon zamani su da ɗa tabbatuwa uwa mai share kukan masu kuka”.
Ta-kurya dake kai gwuyawunta ƙasa ta faɗa sakamakon zuwan Uwa gareta a bazata. Kamar ko yaushe, cikin shigarta ta jajayen kaya, ta gyara zaman ƙasaitar ta. Ƙoƙon dake hanunta ta miƙama ta ƙurya. Hannu biyu ta karɓa, ta kafa kai ta shanye abinda ke ciki.
“Tukuycin cika umarninmu na yanka babbar baƙar dabba da kikai ne. Azamarki da himmarki zaisa bazaki taɓa nema daga garemu ba ki rasa Ta-kurya (Wa'iyazubillah 😭).
“Nagode uwa mai share kukan masu kuka”.
Murmushin daya sake munana fuskarta ta saki tana ƙara kalmashe ƙafafu a kujerarta.
“Karki damu ke mai nasara ce. Minene makomar ayyukan da muka barki da su?”.
“Ina kan yunƙurin ƙarasawa. Na kuma samu ƙyaƙyƙyawan labari a majiya mai ƙarfi yarinyar zata koma sashenta. Sai dai akwai zaman sirri dasu Uwar masu gida sukai wanda babu wanda yasan misuka tattauna. Ina dai ƙyautata zaton duk akan komawar yarinyar ne”.
“Kar tattaunawarsu ta dameki. Tabbatar da ƴan leƙen asirinki cikin hadimanta shine aikinki na gaba. Dan kunada yawa masu wannan burin kema kin sani basai na sanar miki ba. Ina kuma tunatar dake rigar can dake a sashen Uwar masu gida. Da zaran ta tare ki kasance ɗaya daga cikin masu janta a jiki. Yardarta gareki ne zai bamu damar amfani da ita wajen cikar burinmu”.
“Na gode da kasancewar ki haske mai haskamin duk wani surƙuƙin da zai iya zamemin duhuwa uwa”.
“Biyayyarki garemu ita ce tushen share kukanki Ta-kurya. Dan haka bazamu taɓa barin kiyi kuka ba maƙiyanki suyi dariya ba. Sai dai su suyi kuka ke ki kasance cikin dariya a kullum bisa nasararsu. Karki shagala ƴar shilar suda nada taurin kai, Karki zama cikin jerin mutane masu raina allura ta zame musu garma. Muna son tasha madarar nan a ƙalla sau uku daga gareki da zaran ta tare a sashenta”. Ta ƙare maganar da miƙama ta ƙurya ƙoƙon da bata san daga ina ya fito ba. Dan ganinsa kawai tai a hannunta tamkar ƙyaftawar idanu. Hannu biyu tasa a wajen amsa tana jera mata kirari da godiya. A hankali ta fara disashewa a idanunta tamkar baƙin hadarin da masha ruwa (Bakan gizo) ya shanye cikin sakanni.
Ta-ƙurya ta sauke nannauyan ajiyar zuciya. Sai kuma ta miƙe da ƙoƙon da Uwa ta bata. A guri na musamman da na'urar sanyi ke aiki ta ajiye madaran, murmushin jin cigaba da tabbatuwar nasararta na cigaba da ƙawata ƙyaƙykywar fuskarta. Ji take a ranta yanzu ne fa za'a fara wasan na gaskiya. Dan dama idan aski yazo gaban goshi masu iya magana kwance yafi raɗaɗi da zafi. Ta jima bata samu irin wannan damar ga uwa ba a ɗan tsakanin nan da mafi yawan lokuta sukafi ganawa cikin ɓacin rai da rabuwa da ɓacin ran. Amma a yau yanda uwa ta ziyarceta ya sakata jin karsashi da ƙarin kwarin gwiwar cigaba da ruguza duk wanda ya cigaba da yunƙurin shiga gaban nasararta.......✍️


“Humm masu karatu, da gaske fa yanzu ne za'a fara wasan na gaskiya. Ga dai Iffah zata koma ɗakinta. Komawar dake cike da burikan wasu dake zagaye da ita. Buri kuma irin wanda ke kamanceceniya da juna ta fuskar wanzuwa. Manufa kuma kowa da irin tasa. Ita kanta Iffah da nata ƙudirin karku manta. Shin wanene zaiyi nasara ne? Yaya batun su Babiy kuma? Dan maimakon haske komai ƙara cuɗewa yake. Kaka zaiyi wani yunkuri a alamarin kokuwa Barrister zai janye bisa gargaɗin da akai masa shima?. Kumuje zuwa dai dan ba'a fara komai ba sai yanzu😉🥱”.




*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)



𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻


*_30_*


........Kamar yanda su Malikat Haseena suka faɗa a yau aka tashi da gyaran sashen Iffah, sai dai abinda ya Bama kowa mamaki ba inda aka fara kaita bane. Ɗaya daga cikin sabbin sashen da babu wanda ya taɓa rayuwa a cikinsu ne a masarautar. Hasalima an jima ana gutsiri tsomar dalilin gininsu da Tajwar Eshaan yasa ayi batare da ansan dalilinsa ba. Ba kayan ƙawata gida kawai aka zubama sashen ba, harda tarin sitturu da kayan ado na sakawar Iffah.
A karan kanta kuma masu gyaran jiki na musamman ne suka duƙufa kanta a yinin wannan rana. Da dare ta samu hutawa. Washe gari aka cigaba da mata gyaran da ita kanta sai da zuciyarta ta fara shiga wasi-wasi. Koda yake dama a ciki take. Dan gaba ɗaya kwanakin nan aikinta kawai shine nazari da fasalta abubuwa masu yawa a rai da takasa gane bakin zarensu sam. Sai dai shawarar malam Fawzan ta waccan ranar ta ƙara mata ƙwarin gwiwa da maidota a hayyacinta da matsayin shigowarta daular ruman.....

Tsahon kwanaki uku ta gyaru ta ƙara ƙyau tamkar ba'ita tayi fama da jiyya na a kwanakin baya. Ƙamshin dake fita a jikinta ma kawai ya isa ai kiransa na musamman. Ita a karan kanta har gizago canjawar tata ke mata. Jikinta ya murje ta ƙara girma da cika ido tamkar ba autar Ummu da Babiy ba. Ga wani jin kai da takejin ta ƙara masu neman kere shekarunta. Babu shakka kuma hakan nada nasaba da girman da ake bata.

Masarauta da jama'ar cikinta zance ya yaɗu yau za'a maida Zawjata-almilk sabon sashenta tunda ta samu sauƙi. Shaidar haka kuma nada nasaba da walimar da Malikat Haseena suka shirya, acewarsu ta aure ce da ba'aiba sanadin abinda ya faru za'ayi yanzu. Shirya wannan walima ya kawo ƙananun magana matuƙa, dan kuɗi aka kashe tamkar za'a sake wani sabon auren. Abin mamaki sauran mata biyu kafin Iffah ga Tajwar Eshaan sai al'amarin ya sosa musu zuciya duk da har yanzu zaune suke batare da ko Tajwar ɗin sun san kalarsa ba.
Sam Iffah bata san da wani taron walima ba, sai da aka kammala mata shiri cikin wasu ƙawatattun kaya masu tsananin ɗaukar ido da tabbatar da ita amarya ta gaskiya mai amsa sunan Zawjata-almilk kanta ya fara ɗaurewa. A ganinta in har shigace ta iya rakata sashenta baici ace ta ƙawatu har haka ba kodan kasancewar dare ne ma. Kai mutanen nan fa sun fara caja mata ƙwaƙwalwa, ta faraji a ƙasan ranta akwai manufa. Amma dai koma minene zata jure har zuwa lokacin samun ƴancin kanta na komawa sashen nata dan ta shiryawa kowa talalarsa. A kwanakin baya ta kwantar da kai ne ga kowa domin fahimtar manufar wasu koda kalilanne a cikinsu. Alhamdullah kuma ta dace, dan koba komai ta gama samun yardar Daneen Ammarah da masu gayya da aiki Malikat Haseena da Malikat Bushirat. Duk da dai tasan kada mage ba yankata bane. Amma koba komai raina allura yakan sa ta zama garma ga wanda yay sakaci ai.
Taji ba daɗi da barin ɗakin data rayu tsahon kwanaki cike da kewa. Koba komai bazata manta da rayuwar kusan sati uku da tayi a cikinsa ba. Ta koyi ilimi da yawa, harma da darasi data ɓoye matsayin sirrinta. Da wannan tunanin a ranta har aka iso babban ɗakin taro na cikin masarautar, wanda ya ƙunshi duk wani babba mai faɗa aji. Al'ajab ya kama Iffah, amma ta dake zuciyarta na sake tauri na nan dalilin ɓoye mata wannan zaman da akai. Amma a zahiri rashin ƙarfin cewa yasata yin luff kamar yanda ta kasance a kwanakin da suka gabata na samun lafiyarta. Daneen Ammarah data kasance mata ƴar jagora kasancewar fuskarta a sakaye take ta kaita har mazaunin da aka tanada dan ita a cikin ƙaton falon bisa tattausar dardumar da aka shirya walimar. Kamar yanda al'adar take, abinci aka fara ci yayinda Iffah ta gagara kai ko ruwan madara bakinta. Yanda tayi ɗin ya sake burge su Malikat Bushirat, suna ji a ransu sun dace da irin surukar da suke fata. Bayan anci ansha kowa ya nutsu. An fara buɗe taron da addu'a, tare da saƙon maraba ga sabuwar Zawjata-almilk, harma da fatan kasancewar ta abinda kowa ke fata. Kowa dai ya amsa da amin a zahiri, a baɗini kam sanin sirrin wasu sai ALLAH.
A mataki na biyu shine zagayawa da Zawjata-almilk takai gaisuwa ga duk wanda ke wajen, kasancewar kakanni ne makusanta da iyaye, da yayye. A yanzu dai kam da taimakon Jasrah ta motsa, bayan ta janye hular rigar alkyabbar jikinta data hana kowa kallon ainahinta a tun farko. Duk da Iffah taji ta takura, hakan wata damace a gareta na sanin dukkan masu faɗa ajin, zai kuma zama jagoran abinda zai taimakawa nata ƙudirin. Idanunta suka cika da hawaye, a lokacin da take durƙushe gaban Malikat Haseena matsayin bankwana. Tanajin tsohuwar a ranta, ta kuma samu wani kebantaccen ilimin zamantakewa da ita. Ta saka mata albarka tare da yaba ƙyawawan halayenta da jinjinama iyayenta tarbiyyar da sukai mata. Ta ƙare da fatan alkairi da samun zuri'a mai albarka tsakaninta da Shahan-shan. Waɗan nan zantika sun zama abin kaiwa da komawa a zukatan manyan masarauta. Dan kowa na ganin kamar wata isharace Malikat Haseena ta isar cewar ta karɓi Iffah ɗari bisa ɗari matsayin Zawjata-almilk fiye dana baya da suka gabata. Iffah a karan kanta taji tausayin tsohuwar bisa ƙudirinta na shigowa daular ruman data tabbatar yasha banban da fatan da Malikat Haseena tayi gareta a yau gaban duk wanda ya isa a ƙasar ruman ma ba daular ruman ɗin kawai ba. Har yanzu har gobe da jibi tana akan bakanta na ɗaukar fansar rasa ƴan uwanta. Abin harinta kuma ɗaya ne tal shine Tajwar Eshaan, inma da wanda zasu biyo bayansa sai ta gama da babban dodon nasu. Ta samu ƙwarin gwiwar hakanne da tabbacin jin sai an kai matan turakarsa ake fiddosu babu rai. Sai kuma bincike da shaƙiƙansa guda huɗu sukai yunƙurin ɗaurata a yanzu haka. Kenan babu buƙatar wasi-wasi koma minene shike ƙullasa...
Malikat Bushirat ma tayi irin makamancin addu'ar Malikat Haseena ne ga surukar tata. Ta ƙara da faɗin ita ɗiya takejin ta samu ba Suruka kawai ba, tana kuma fatan ta kasance kibiyar ajali ga masu ƙudirin sharri a ciki da wajen daular ruman. Tabbas maganar Malikat Bushirat tafi ta Malikat Haseena ɗumama zukatan wasu, yayinda mugun ƙudirinsu akan Iffah ya ƙara hauhawar farashi a zukatansu, amma duk sai suka ɓoye suma sukai mata irin tarbar data ɓoye dukkan ainahinsu. Dan Miran Jasim ma da akazo kansa har ƙyauta ta musamman ya gabatar ga Zawjata-almilk.
Iffah data kasance cikin ladabi da ƙawata harshenta gaban kowa yayin miƙa gaisuwarta duk da ƙarancin shekarunta kaifin basirarta da wayonta ya bata damar nazari da adana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login