Showing 111001 words to 114000 words out of 122381 words

Chapter 38 - Daudar Gora Book 1 Hausa Novel Complete

25 Dec 2024

420

tare da mikewa ya kai jakar gabansu, cike da farin ciki suka buɗe suna mai fiddo duk takardun ciki. Bayan sun ɗan dudduba su suka ɗago fuskoki cike da murmushi suna yabama Barrister namijin ƙoƙarin sa. Shi dai nashi murmushi ne kawai. Ɗaya daga cikin baƙin da ake kira da Sayeed Harun Al-rashid, babban mutum ne a ƙasar ta ruman, dan riƙƙaƙen ɗan kasuwa ne na gwal da kowa ya sani kasancewar sunansa yayi matuƙar shura a wannan harkar data zama babban tattalin arzikin su na ƙasar, dan Ruman kam bata san iya arziƙin gwal da ALLAH yay mata ba, shiyyasa duk wani riƙƙaƙen ɗan kasuwa zaka samu gwal ɗin ne mafi rinjayen makaminsa kamar dai Sayeed Harun Al-rashid. Ta wani gefen kuma yana riƙe da sarauta sai dai yafi bama kasuwancin muhimmanci matuƙa. Zamansa ya gyara sosai yana fuskantar Barrister. “Barrister yanzu mi kake son ka sani?”.
     “Ranka ya daɗe ba komai bane dama sai akan waɗan da naga case ɗin ya karkata. Na duba dukkan bayanan Barrister Abdallah Aas, sai dai a yanda na fahimta kamar ya gano inda su mutanen dake hannun naku suke, dan kafin ma ya rasa ransa kamar ya fito da ga ƙauyen Lufana ne wajen matar marigayin, abinda nake son cewa anan ina tsoron yazam bayan Barrister ɗin akwai wanda yasan wannan sirrin. In kuwa hakan ta kasance zaman mutanen a station ɗin dana fahimci kun ɓoyesu zai zama barazana ke nan koda anan gaba”.
    Kusan a tare sukai murmushi, Sayeed Harun Al-rashid ya muskuta zamansa cikin nuna damuwa da zancen Barrister. “Maganar ka nakan hanya Barrister shiyyasa tun kafin yau muka gama maganin duk abinda kake gudun. Tun daga farkon wannan case ɗin idanunmu akan komai suke, dan haka ka kwantar da hankalinka. Su kuma tuni basa a police station ɗin, dama mun kai ajiyar su ne domin ɓadda kama bayan kwanaki kuma muka ɗauke su, amma kai a yanzu mi kake son cewa?”.
    Anzo dai-dai gaɓar da Barrister keson azo, dan haka ya ɗan murmusa yana mai ƙara bama kansa nutsuwa. “Alhmdullh kun fahimci inda nake buƙatar akai ranka ya daɗe. Abinda nake son cewa kai tsaye shine ayi duk yanda za'ai cikin kwanaki biyun nan abar ƙasar ruman da mutanen gaba ɗaya”.
        “Eh maganarka abin dubawa ce kam, amma kuma mizai hana kawai a ɓaddasu a wuce wajen, dan abinda ya zama dalilin zuwansu hanunmun ma an sameshi cikin sauƙi yanzu haka”.
    Barrister yay ɗan jimm dan bai fahimta ba, amma sai ya dake bai sake musu wata tambaya ba gudun karsu zargi wani abu. Sai dai ya cigaba da faɗin, “Ɓaddasu bashine mafitaba ranka ya daɗe, dan a ɗan bincike da nayifa akwai babbar matsala game da mutuwar Barrister Aas”.
      Babu wanda zancen bai daka ba a acikinsu, Sayeed Faizul-Anwar daya kafe Barrister da ido yay saurin faɗin, “Barrister bamu fahimce ka ba, mi kake son cewa?”
           “Ranka ya daɗe yanzu zan fahimtar da ku. Idan har kun saurari dukkan labaran dake yawo har yanzu babu wani tabbaci na samun alamar sassan mutum a cikin motar Abdallah, wannan shine yaja hankalina tun a ranar farko bayan nabar nan na fara nazari da bincike. Tabbas Abdallah na raye, sai dai ya ɓoye kansa domin bada ƙafa. Na sanshi nasan mizai iya fiye da tunaninku. Shiyyasa nake ganin kashe mutanen a yanzu bashine mafita ba, muyi nesa da su da ƙasar nan ta yanda babu inda zasuji ɗuriyarmu, sai kuma mu samo wasu a madadinsu a buɗe shari'ar ta yanda zamu ƙona Barrister Abdallah Aas da ransa batare daya farga ba”.
        Dukansu gumi suke na tashin hanakali, sai dai babu wanda ya iya cewa komai har zuwa wani tsahon lokaci. Sayeed Harun Al-rashid ya nisa yana mai share ɗan gumin daya taru masa a goshi. Ƙyaƙyƙyawar fuskarsa fara tas gaba ɗaya ta ƙwaɓe alamar rashin damuwa. “Zartar da hukunci bazai yuwu yanzu ba Barrister, amma kaje zuwa anjima zakaji komai ta waya”.
     “Babu damuwa ranka ya daɗe”. Barrister ya faɗa cikin jimami shima, sai dai acan ƙasan ransa dariya yakeyi, yayinda wani gefe na zuciyarsa ke tabbatar masa akwai wani babba mai alaƙa da case ɗin bayan su, shiyyasa bazasu iya zartar da hukuncin ba kai tsaye. Yau ma dai an rakosa da kuɗi masu yawa har mota.......
  
          
  ★★... BAYAN KWANA BIYU ★★....

     A kwanaki biyun nan abubuwa da yawa sun faru tako wane ɓangare, sai dai marasa daɗi sunfi masu daɗin rinjaye. Zuwa yanzu dai da gaske ƙasar ruman da jama'arta suke basa buƙatar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed matsayin Shahan-shan. Dan tun tsirarun mutane na zanga-zanga a wasu jahohi takai yanzu ƙasar ma gaba ɗaya ta ɗauka. Abu mafi ban mamaki harda wasu a manyan ƙasar na nuna goyon baya ga talakawa, ciki kuwa harda wasu Tajwar na jihohi. Yayinda ta wani gefen kuma hankalin wasu manyan ƙasashen duniya ya fara dawowa kan zanga-zangar dama dalilin yinta.
      Babban abinda ke tunzura jama'a shine biris daga Shahan-shan, yayinda kuma a cikin gida hankalin ƴan majalissar sa ya rabu kaso biyu, wasu na goyen bayan ya saukan wasu na buƙatar karya sauka dan shine kawai ya cancanta da kujerar a ganinsu. A talakawan ma bai rasa tsirarun masoya ba, sai dai basu da ƙarfin ja da masu boren shiyyasa suka koma gefe sukai shiru matsayin masu kallo da ido.

     *_IFFAH!_*

      A kwanaki biyun nan yanda Daular ruman ke a hargitse haka Iffah ke a hargitse. Kuka kam idanunta har sun daina fidda ruwan hawaye. Cikin ƙanƙanin lokaci tayi wata irin rama mai ban tausayi. Haukan da iyalan Sayeed Khairul-Bashar keyi a masarautar da wanda jama'a keyi a waje sai ta ɗaukesa wasan yara. Idan su da suka rasa uba kawai zasu harmutsa masarautar haka ina ga ita data rasa ahalinta duka, a ganinta ita ya cancanci ta hargitse ƙasar ruman baki ɗaya ma ai. Sai dai yanda ƴan zanga-zanga ke daɗa ƙaruwa na saka mata farin ciki, dan abin ban mamaki har wasu a cikin Tajwar na jihohi suma sun ƙara tunzura wuta da bada goyon baya akan saukar Shahan-shan ɗin, hankalin ƙasashe kuma ya fara dawowa ƙasar ruman, da alama dai dama a jirace kowa yake da wannan damar. Hakan na sake tunzura ƙwarin gwiwar ƙudirinta.
      Wutar wannan al'amari na ƙara ruruwane dalilin shirun Tajwar Eshaan. Babu shi babu cewarsa, harma wasu sun fara tunanin anya kuwa yana cikin masarautar ma ko?.... Duk wannan bai damu Iffah ba a yanzu, hankalinta gaba ɗaya ya tattara ne akan ta ina zata samo dafin maciji. Bata da wani amintacce a cikin masarautar, a waje kam sir Fawzan ne kawai, shima kuma zuwa yanzu ta fara shakku akansa saboda tana ganin ya ɓoye mata abinda ya faru da su Babiy ne bisa wata manufa. Idan tace zata fita a sulale daga masarautar taya kuma zata dawo cikinta? Wannan ƙalubalen keta faman mata kaikawo harya gagara samun mafita a kwanaki biyun nan. Tana a bangarenta bata ganin kowa kowa baya ganinta, waɗan da zasu iya ganinta hankalinsu a tashe yake dan kai tsaye su abin ya shafa, shirunsu kuma sai ya bama Iffah damar fassarashi da abinda zuciyarta ta gama tabbatar mata, dan haka itama a yanzu ta haƙƙaƙe bata da lokacinsu.
      
       Kamar yanda ta tsara bayan sallar la'asar ta shirya tsaf cikin abaya data amshi jikinta, dan ma ta rame ga idanunta da suka ɗan kuklumburo amalar taci kuka bana wasa ba. Duk da masarautar a harmutse take haka ta keta cikinta hadimanta na take mata baya har sashen marigayi Sayeed Khairul-Bashar. Tayi matuƙar mamakin tarbar data samu dan batai zaton irinta ba, sai dai abinda bata sani ba shine su kallon tausayi suke mata da tabbatar da itama bawai ta tsira bane a hannun azzalumin. Dan malamin duba da matar Sayeed Khairul-Bashar ɗin ta ziyarta tun lokacin daya ɓata kafin aga gawarsa ya tabbatar mata akwai ƙulli mai girma da Shahan-shan keyi game da rayuwar Iffah shiyyasa itama bata mutu ba a sanda aka kaita sashenshi. A ranar bata ɓoyema ƴaƴanta komai akan zancen nan data jiyo ba, sun kuma yi niyyar samun Iffah har sashenta da batun washe gari aka tashi da wannan tashin hankali. Wannan shine dalilinsu na mata tarbar data bata mamaki. Ita kuma kasancewar zuciyarta a kusa take tana musu ta'aziyya tana share hawaye da handkherciff. Sai hakan ya ƙara mata kima a idon iyalansa. Yayinda ƴan uwansu kuma da basu san komai na ke jin zafin ganin Iffahr da fassarashi matsayin leƙen wani asiri dan a yanzu wasu a cikin ahalin masarautar su kuma suna ma Iffah kallon wata ƴar kaɗafin Tajwar Eshaan ce tunda har ta tsira daga kisan gillarsa..........✍️
       
     

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)



𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻


*_47_*


.........Kamar yanda Iffah tai tunani labarin zuwanta sashen Sayeed Khairul-Bashar ta'aziyya har ya isa kunnen surukarta dama na jikin Tajwar Eshaan irinsu malikat Haseenat da su Daneen Ammarah. Dan tana fitowa kiran Daneen Ammarah ya shigo wayarta. Bata ɗaga ba, aka kuma sake kira nan ma dai ta share kamar bataji ba. Sai da ta koma sashenta da kusan mintuna goma sannan tai kiran Daneen Ammarah ɗin back. A bugu biyu ta ɗaga, Iffah ta taɓe baki cikin rashin damuwa tai sallama da fara gaishe ta. Da kulawa Daneen Ammarah ta amsa. Iffah na jiran jin ta mata batun fitarta sai Daneen Ammarah ta jeho mata tambayar da bata da alaƙa ma da fitar.
        “Ibnati na kiraki ne akan Abni, shirunsa na tadamin hankali matuƙa, gashi yana ƙara harzuƙa mutane ƙasa, kinga dai yanda ƙasar nan ke sake rikicewa. Mu dukanmu mun nemesa a waya amma bamata shiga, na fara zargin anya ma yana cikin masarautar nan?”.
     Murmushin takaici Iffah tayi, amma a zahiri sai ta danne ta fara magana cikin kwantar da murya. “Wannan shine tunani na nima Mamy, sai dai ban san yanda zanyi ba ganin ku manya bakuce komai ba.”
         “Shirun na dole ne Ibnati, bazaki gane babbar sarƙaƙiyar dake cikin masarautar nan ba ne. Amma tabbas akwai matsala, akwai kuma gagarumin al'amarin dake ɓoye amma yana son bayyana kansa a wannan gaɓar.....”
    Cikin zumuɗi Iffah tace, “Mamy minene shi dan ALLAH?”.
   “Humm Fareedah kinyi ƙarama da yawa ba yanzu ba. Ke dai kawai abinda nake so da ke shine ki taimaka ki bincika min idan Abni yana a gidan nan...”
          “To Mamy, amma dai zaiyi wuya tunda kunce idan yana cikin damuwa kulle kansa yakeyi baya kuma sauraren kowa. Sai nake ganin ni taya zai saurare ni”.
     Murmushi Daneen Ammarah tayi mai sauti. “Rashin saurarenmu bashi ke nufin kema bazai saurareki ba Ibnati. Ke dai gwada sa'arki mu gani”.
    Iffah dai ta jita ne kawai, amma sai bata sake musawa ba sukai sallama.....

      ★★.... ★.....

   Miran Jasim ya sauke wayar dake a kunnensa bayan gama sauraren abokin wayar tasa, yanda fuskarsa ta canja daga farin cikin dake shimfiɗe a kanta kafin wayar yasa Miran Arshaan sake maida hankalinsa garesa. “Wani abu ya sake faruwa ne?”.
      “Zai dai faru”.
Cewar Miran Jasim ɗin a fusace yana miƙewa. Miran Arshaan da maganar ta dakesa ya miƙe zumbur shima. “Ban gane mi kake son cewa ba Jasim Akh?”.
     Kamar bazai tanka masa ba sai kuma yaja kakkauran tsaki. “Harun Al-rashid ne dai akan waccan maganar banzar ta ranar, duk yabi ya tashi hankalinsa yana cigaba da damuna nima, tun abin bai tasiri a raina ba har ya fara, wai Barrister da suka bama aikin can kan ɗan iskan can ne ke cigaba da musu bayani dai kan Barrister Abdallah bai mutu ba dai da gaske.”
        “Wai suna nufin shi ya tabbatar da hakan kenan?”.
     “Abinda ke cazamun kai kenan, na rasa wane shirme ne kuma hakan? Taya wanda bomb ya tashi da shi ace bai mutu ba?”.
   “To amma fa kuma maganarsu fa abin a duba ce Jasim Akh. Dan koni naji shakku a randa bomb ɗin nan ya tashi amma jami'an tsaro suka tabbatar babu wani alamar an rasa rai......”
       “Amma shine kai shiru?!”.
Miran Jasim ya katsesa a zafafe. “Mi kake so nayi bayan wanda nayi to? ina son ka tuna tun a ranar na kawo maka wannan zancen amma ka nuna min cewar zata iya yuwuwa ƙarfin tashin nakiyar ya cillashi wani waje ne shiyyasa basu gansa ba. A kuma shekaran jiya da suka kawo maganar na kuma ƙoƙarin maka nuni ka kalli zancensu a shirme”. Shima Miran Arshaan ɗin ya karɓa masa a nasa zafin.
    Shiru Miran Jasim yayi da dafe kansa yana murza goshinsa dan ya tuna tabbas anyi hakan. Amma wannan aikin na cikin gida da rashin sanin mi Tajwar Eshaan ke ciki ya ɗauke hankalinsa bai nutsu yayi nazari kan batunba kasancewar akwai abubuwa da yawa da bawai yana buɗema Miran Arshaan ɗin bane, kamar yanda shima Miran Arshaan ɗin ba komai yake yarda ya buɗe ma Miran Jasim ɗin ba. Sai dai a yanzu dukansu sun fahimci yin kuskure, dan haka kowanne ya ajiye ɓoyayyar manufarsa suka fuskanci juna.
          “Ni ina ganin in har an yarda da aikin Barrister ɗin nan shawararsa ba abar yardawa bace. Sannan dole ne fa mu gaggauta ganawa da yarinyar can in ba hakaba aikinmu zai iya buɗewa. Dan idan ya kasance Barrister Aas na raye bazai samu ɗaki bane ya kulle kansa domin hutu kaima ka sani”.
     Miran Jasim ya gyaɗa kai da faɗin, “Hakane maganarka na kan gaskiya. Yanzu minene abinyi?”.
    “Abinyi ɗaya ne bama Barrister Akeem damar shigewa gaba kafin kwana biyun nan na cikar aikinmu abar ƙasar nan da mutanen. Bayan ka haye karagar mulki shi kuma shegen duk inda yake zamu nemishi ne ya ɗan-ɗana kuɗarsa”.
     “Ina sake godema ALLAH da kasancewar ka kusa da ni, dan kana farkar da ni a duk sanda kaina ya shiga duhuwa ɗan uwana”.
    Murmushi Miran Arshaan ya saki a zahiri, a zuciya kam faɗi yake, (Banza ka gama cusamin ƙayar a rumbu na rufeta da ɗan boto ina daga kwance).
    Ɗaukar wayar Miran Jasim dai-dai da kammala wayar Iffah da Daneen Ammarah daga can......

       ★★.....

     Tana ajiye wayar wani kiran ya sake shigowa, kamar zata share dan bata san number ɗin ba sai kuma dai ta ɗauka da tunanin ko Sir Ajmaal ne kasancewar a saƙonta na ƙarshe ta roƙesa idan ya gani ya kirata. Daga can aka amsa sallamarta kai tsaye, hakan ya sata Ciro wayar a kunenta ta kalla tamkar mai son gano muryar. Miran Jasim da kamar yana ganinta yay gyaran murya, hakan ya sata sake maida wayar.
     “Kina magana da Jasim Ibn Abdull-Majeed Aliy”.
   Kai tsaye Iffah ta ganesa, dan haka ta fara gaidashi da girmamawa. Hakan ya masa daɗi, dan yanda yake amsa mata da kulawa zai baka tabbaci. Shiru ne ya ɗan biyo bayan gaisuwar, kafin ya katsesa da faɗin, “Ibnati inata zaman jiran ji daga gareki amma shiru. Ko baki amince da abinda kika gani bane ba dai?”.
        Iffah da ke jin an taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi hawaye suka shiga rige-rigen sakko mata. Hannu tasa ta sharesu da ɗan jan hanci. “Ba yarda ne banyiba ranka ya daɗe, kawai dai zuciyata na kaikawo ne na son sanin dalilinka na yin hakan a gareni. Idan ban manta ba kai fa Ammi ne garesa, mizaisa ka zaɓeni sama da shi? A barshi ma zaka iya hakan kasancewar ka mai gaskiya ko ƙyamar abinda yake. Amma miyasa su na baya da aka rasa bakuyi wani yunƙuri ba sai ni a kaina bayan akwai ƴaƴan Tajwar mafi rinjaye a cikin wanda ya halaka?”.
     (Kaga ibilishiyar yarinya) ya ayyana a zuciyarsa. A zahiri kam sai yay gyaran murya cike da dattako yana kallon Miran Arshaan da shima ke sauraren komai. “Wato Ibnati duk yanda zan miki bayani a wayar nan ba lallai ki fahimta ba. Amma zan tura miki lokaci da adireshi mu haɗu zai fi”.
          Jimmm Iffah tayi kamar mai shakku, sai kuma ta nisa cikin gyaɗa kai tace, “Okay babu damuwa ina jira”. Daga haka sukai sallama kowa ransa na masa kaikawo...

      ★★....

    Cikin ƴar dariya Miran Arshaan yace, “Amma shegiyar yarinyar nan fa da zata samu dama a masarautar nan ba ƙaramin hatsabibiya za'ai ba. Kaji murya cauy-cauy bata ko tsallaken kalma ga shegen wayo”.
       “Shiyyasa dolene tana kammala aikin nan a kaudata kawai, ai tunda har tana da ƙarfin halin shigowa masarautar nan da ƙudiri irin na kashe Shahan-shan dama nasan zamuga fiye da hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login