Showing 24001 words to 27000 words out of 122381 words
ta ƙanƙame. Iffah jitai zuciyata ta ƙara hautsunowa, a matuƙar zabure ta sake buɗe baki zatayi magana ya dakatar da ita...
“Ke ƴar talakawa lura da inda kike. Bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane. Idan taƙamarki tsageranci tamkar ƙiftawar ido za'a sauke miki shi, a kuma shafe babinku daga ke har iyayen naki a doron ƙasa”.
Hasala iya hasala Iffah tayi, Kukan da Ummu ta fashe da shi ya hanata cewa komai ta juya gareta jikinta na rawar shiga tsananin ɓacin rai, kanta take juyamata alamar karntace komai.....
“Umm....”
“A'a Iffah! Ina umartarki karki ce komai”.
“Kibarta tace ɗinma yanzu harshenta ya zama datsatstse a gabanki.”
Kafin Ummu dake girgiza kai tace komai Babiy ya shigo tamkar an jehoshi, da alama dai wanine ya sanar masa da zuwan jama'ar masarauta gidan nasa. Ko sau ɗaya basu bashi damar cewa komaiba suka isar masa da saƙon kira daga daular ruman.
“Innalillahi.....” Iffah ta shiga ambata ita da Ummu, dan sunaji a ransu tarihine dai yake ƙoƙarin maimaita kansa, hawaye masu tsananin ƙuna da ɗaci na gangarowa bisa ƙyaƙyƙyawar fuskata Babiy da shima dai yasan labarin gizo bazai wuce ƙoƙi ba. A gaban idonsu aka wuce da Babiy Daular Ruman a karo na uku, tare da barin wasu dakaru a ƙofar gida ta hanyar hana duk wani mai yunƙurin fita daga gidan. Haɗe kai kawai Iffah da Ummu sukai suna kuka, dan shi kaɗai suke da damar yi ɗin..
★Bayan cikar awanni biyu da tafiyar Babiy sai gashi ya dawo, dawowa irin wadda ya saba a duk lokacin da makamancin kira irin wannan ya samesa daga daular Ruman. Yanda ya kafe Iffah da idanunsa dake zubda hawaye ya saka Ummu zubewa ƙasa cikin kuka. “Abu Hanash itama zamu rasata ko? Itama ka ɗaura mata aure da Tajwar.....?”
Hawayene masu ɗumi da ƙuna suka ziraro a idanun Babiy, ya girgizama Ummu kansa a hankali alamar a'a, tare da girgiza kan nasa kuma alamar tayi shiru. Hawayen nata ta share kamar yanda ya buƙata, sai dai jikinta bai bar tsuma ba. Kamar yanda Iffah data kafesa da idanu bata iya ko ƙyaftawa ba. Ummu ta sake gyara zamanta da fuskantar Babiy da ƙyau....
“Idan ba abinda muke tunani bane to minene ya faru?”.
“Ki kwantar da hankalinki babu komai f.....”
“Bazan taɓa yarda babu komai ba. Sai dai idan kana so ka rufeni ne. Hakan kuma shine mafi ƙololuwar kuskuren da banajin zan iya yin afuwa gareka a kanshi. Dan inaji a jikina zuwanka masarauta nada nasaba da rayuwar yarinyata data rage min, idan har zuciyarka ta iya ɓoyewa ƙwayoyin idanunka basu lulluɓe komai ba, garama ka sanar min”.
Babiy ya fahimci idon Ummu ya rufe ta manta Iffah na wajen, dan haka ya cigaba da ƙoƙarin ganin ya kufcema faɗar abinda yazo da shi har sai sun keɓe amma ta dage akan itafa ya faɗa mata a yanzu. So yake ya buɗe ido amma bashi da sauran ƙarfin zuciya a yanzu, dan haka a sanyaye ya rumtse idanunsa da launinsu yay matuƙar komawa ja. “Ba'a ɗaura mata aure da shi ba. Sai dai....” ya kasa ƙarasawa.
“......Sai dai me? Dan ALLAH ka faɗa min”. Ummu ta faɗa tana mai sake fashe masa da kuka mai matuƙar sake ɗaga masa hankali. Miƙewa yay yunƙurin yi tai saurin riƙe masa ƙafa. Babiy ji yake shima kamar ya fashe da kuka ya huta kawai. Ya dawo ya durƙusa gaban Ummu tare da riƙo mata hannu, “Akan abinda suka faɗa munada mafita tunda yasha ban-ban dana baya Jumaima. Dan haka na gama yanke shawarar zamu bar garin nan dama ƙasar gaba ɗaya a daren yau insha ALLAH. Dan sun buƙaci izinin neman auren Iffah ne a gareni, sun kuma bani damar zuwa nai shawara daga nan har zuwa ƙarshen makon nan”.
Kafin Ummu ta samu damar cewa wani abu sulalewa da faɗuwar Iffah a lokaci guda ta riski kunnuwansu. A tare suka zabura kanta jikunansu na matuƙar rawa da tsuma. Ummu ta fashe da kuka dai-dai tana ɗago Iffah dake wanwar a ƙasa taga ta koma yaraf alamar babu rai a tare da ita.....
.....Sosai kukan Iffah ya sake ɗaga hankalin Babiy. Dan tunda aka zuba mata ruwa ta farfaɗo ta haɗe kai da gwiwa. Suma idanu kawai suka zuba mata suna hawayen zuci, rikicin yana a kantane kawai, amma sune suka fita jin raɗaɗin a zuciya saboda ita akwai ƙuruciya tare da ita. A ganinsu bai zama lallai ma tana hange irin wanda su suke matane ba.
Kusan mintuna talatin suna a haka, kafin Babiy yay ƙarfin halin miƙewa suma yay musu umarnin su tashi su koma ciki. Sai da taimakon Ummu Iffah ta iya miƙewa, har sun kusa shiga ɗakin ta tsaya, ɗagowa tai ta dubi Ummu ta juya ta dubi Baby hawaye na sauka da gudu bisa ƙyaƙyƙyawar fuskarta.
“Bazamu gudu ba Babiy, zan aure shi....”
Kaɗan ya rage Babiy yaci uban tuntuɓe saboda firgitaccen furicin Iffah mai kamanceceniya da gawurtaciyar sautin saukar aradu cikin tsakkiyar duhuwar dare. Ummu ma dai da taima Iffah sakin bazata ƙirji ta dafe dukanin idanunta na firfitowa.....
Iffah ta share hawayenta da sakin murmushi a karo na farko. “Ummu! Babiy! ku kwantar da hankalinku, kar kuma ku ɗauka ba'a cikin hayyacina nake ba. Nasan burinku shine ku kuɓutar dani daga mutuwa, sai dai kuma a duk inda zanje ku sani tana tare da nine. Wannan azzalumin ba guje masa ya kamata ayi ba, tunkararsa ya kamata ayi. Kamar yanda kaka ya faɗa, a wasu lokutan gujema ƙaddara ba mafita bace sake kirawowa kai halaka ne. Amma tunkararta gaba da gaba ƙarfafa imani ne sannan jarumtace. Shin idan mun gudu kunada tabbacin zamu iya tsere musu bayan ƙasar a hanunsu take? Sannan idan mun tafi ina zamuje bayan babu inda muka sani sama da ƙasar Ruman. Fir'auna ma da yay nasa zamanin mulkin da ko kama kafarsa wannan shaiɗanin baiyiba UBANGIJI maida ANNABI MUSA (A.S) yay cikin gidansa ya rayu bisa ƙudirarsa da tabbatar masa shine mai iko akan kowa da komai. Azzalumin nan ba gudun masa ya kamata ayi ba, daƙilesa ya kamata ayi, domin idan ni kun kuɓutar dani, su sauran iyayen da zasu iya fuskantar makamancin halin da kuke ciki fa bayanku?. Babiy zanyi biyayya kamar yanda ƴan uwana sukayi, kuma ku sani da iznin ALLAH nice zan kashes........”
Cikin rawar jiki Ummu ta zaburo tare da toshe bakin Iffah. Sai faman waigen bayansu take domin sanin dakarun Daular Ruman na ƙofa gidan har su biyar. Babiy ma gaba ɗaya kalaman Iffah sun sake rikitashi. Sai dai kafin wani cikinsu ya samu damar cewa wani abu ta shige cikin ɗakin. Idanu suka tsirama juna shi da Ummu harna tsahon mintina biyu, kafin Babiy yay ƙarfin halin janyewa yana mai jan nannauyan numfashi da barin wajen ya shige ɗakinsa. Da ƙyar itama Ummu ta sauke numfashin, har zatabi bayan Iffah sai kuma ta fasa ta nufi ɗakin Babiy ɗin itama.
Shigowarta dai-dai dayin sallamarsa waya manne a kunensa. Zaune takai a bakin gadon dake ɗakin dan inba haka ba zata iya zubewa ƙasa saboda yamutsawa da jininta ke mata. Jin sunan Baba da Babiy ya ambatane ya sata maida hankali garesa itama. Komai sai da Babiy ya zayyanema Kaka kafin yay shiru alanar saurarensa.
Daga can Baba yaja nannauyan numfashi bayan gama sauraren surukin nasa mijin ƴarsa tilo data rage masa a raye. Sai kuma yay murmushin ƙarfin hali mai sautin daya isa har cikin kunnen Babiy. “Ni ma ina goyon bayan maganar Fareedatu. Da ace wani rai nada ikon hana tabbatuwar wasu daƙiƙu na gaban rayuwarsa masu tafe da ƙaddara da mutane da yawa sunyi rigakafi kafin cikar adadin waɗan nan daƙiƙu Muhammadu Zayyanu. Amma inaso ku tuna muɗin talakawansu ne, masu rayuwa a ƙarƙashin mulkinsu, bamu da wani ƙarfin iko akan hukuncinsu garemu ko kan ƴaƴanmu. Dan haka ku bita da addu'a kawai itama.”
Tamkar yana gabansa ya jinjina masa kansa, tare da ƙoƙarin danne hawayen da yake na zuciya da ƙunarsu gara ace a zahiri suke zuba bisa ƙyaƙyƙyawar fuskarsa. “Shikenan Baba, amma furucin Iffah ya girgizani, ina tsoron kar zuciya ta ingizata tai yunƙurin aikatawa. Kisa fa! Koda bata aikata ba fitar wannan furucin zuwa kunen wani bayan mu ba ƙaramar magana bace”
“Kar komai ya dameka Muhammad Zayyan. Ta faɗane kawai saboda raɗaɗi da takeji da kuma ƙuruciya, kai dai ka sanar dasu ka amsa daga nan zuwa kwanaki uku. Zan zo a amsa kuɗin auren da ni dama wasu a cikin zuri'an ka insha ALLAHU.........✍
ALLAH sarki Iffah kin bani tausayi🥲
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 90165991
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_11_*
..........Iffah taci kuka matuƙa da ko maƙiyinta ya dubeta sai ya tausaya mata. Sai dai kuma iya juyawa su Babiy sun mata akan su gudu ta kafe akan itafa ta yarda zata aura *_Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-Majeed_*. Sosai hankalinsu yake ƙara tashi da tirjewarta. Gashi gaba ɗaya ta bikice musu ko isashen lafiya babu a tare da ita. A cikin wannan halin Babiy ya sake samun saƙon kira daga masarauta. Yana shirin tafiya sai ga Kaka. Duk sunyi matuƙar mamakin zuwan nasa, dan abune mai wahalar gaske a garesa zuwa inba da wani dalili ba. Sun tarbesa kamar yanda suka saba matsayinsa na uba. Bayan gama gaisawa ya kai dubansa ga Iffah dake kwance cikin bargo duk ta rame ta sake komawa fayau da ita, dama tun rasa ƴan uwanta ɗan jikinta ya zube, dan sam ba siririya bace. Iffah nada jiki murjajje daba za'ace mata siririya ba kuma babu mai sakata a sahun masu ƙiba. Duk da shekarunta har yanzu sunada ƙaranci ALLAH ya bata jiki na manyan mata da'a yanzu komanta yake ciff dai-dai da halittarta. Kaka ya ɗauke idanunsa a hankali tare da maidasu ga Babiy.
“Muhammadu Zayyanu ka sakama ranka nutsuwa ka cire batun barin gidan dan bashine mafita ba. Hasalima tun randa ka amsa kiran masarauta wannan gidan zagaye yake da dakarun daular ruman harta inda baka zata ba. Ko'a tunaninka zasu tunkareka da wannan maganar su baka damar kanka sannan su koma gefe da tunanin kai bazakayi wani yunƙuri ba”.
Daga Babiy har Ummu da Hanash kallon tsoro da mamaki sukema Kaka. Ya ɗan jinjina kansa alamar tabbatarwa. “Karku damu da yanda akai nasan wannan, kai dai kawai kaje ga kiran da sukai maka. Karka kuma nuna wani ja'inja kace ka amince musu suzo neman auren”.
Kuka Ummu ta fashe da shi tana kallon mahaifin nata. Yay ɗan murmushi da ɗauke kansa tamkar bai fahimci mitake nufi ba. Ganin haka Hanash da idanunsa sukai jajur cikin cinkushewar harshe yace, “Amma kaka miyasa ka zaɓa itama mu sake rasata? Wlhy nayi alƙawarin in har itama ta salwanta sai na salwantar da ran Shahan-shan da wannan hanun nawa wajen ɗaukar fansa koda nima za ai gunduwa gunduwa da naman jikina!!”.
“Ba kai ne zaka salwantar da ruhinsa ba, ni nan Fareedah bint Zayyan nice zan karya ƙarfin ikon azzalumi da hannuna, zan masa shaƙa irin wadda har sai ya mutu yana mai kallon tsakkiyar cikin ƙwayar idanuna Hanash Akhi”.
Su duka zuba mata idanu sukayi, dan a yanda take maganar babu alamar tana a cikin hayyacinta. Babiy zaiyi magana Kaka ya girgiza masa kai alamar kar yace komai yaje kawai....
★Kamar yanda Kaka ya umarci Babiy ya amsa kiran masarauta kasancewar a wannan karon an bashi damar zuwa ne shi kaɗai batare da dakaru sun taho da shi ba. A yanda ya samu tarba zai tabbatar maka dama a jirace ake da zuwansa. Kamar ko yaushe a wannan karon ma baiga Tajwar ba, amma dai a karon farko na tarihin rayuwarsa an kaisa har cikin fadar Shahan-shan. Inda yaga tsantsar dukiya da ainahin karagar mulki ta Shahan-shan da akayita da zallar zinare. Hakan ba'abin mamaki bane ba, saboda girman Shahan-shan koda da diamonds akai kujerar mulkinsa bazai zama wani babban al'amari ba, sannan zinare arziƙin ƙasar su ta ruman ne da bare ma kanzo ya ci balle su ƴan ƙasa musamman Shahan-shan. Karo na farko da Babiy yaga karramawa daga dattijan daular ƙasar ruman. Waɗan da ko'a mafarki bai taɓa tunanin gani ba dan su ɗin ma ba'abune mai sauƙi ga duk wani talaka ganinsu ba kai tsaye haka. Duk da a birkicen da yake ALLAH sai ya saka masa nutsuwar yi musu bayani babu ko rawar harshe a tare da shi. Sun masa godiya da tabbacin a gobe idan ALLAH ya kaimu masu neman aure zasu zo. Karramawar da sukai masa ta matuƙar basa mamaki da tsayawa a ransa, sai dai ta wani gefe na zuciya ya tabbatar da sabuwar hanyar yaudarace kawai. Cikin danƙareriyar mota aka maidasa har gida badan yaso haka ba, yayi shiru ne kawai domin bin unarnin mahaifin matarsa, dan duk da bai taɓa ambatawa ba ga kowa ya jima da tsanar duk wani abu daya shafi masarautar daular ruman..
★A wannan dare Babiy yayi zaman kuka irin wanda ake kira kuka a zahiri da baɗinin rayuwa. Har yanaji bazai iya cigaba da yima kaka biyayya ba shikam, zai ɗauke Iffah su gudu daga ruman koda daga shi sai ita ne. Sai dai wani ɓangare na zuciyarsa na tunatar da shi maganar Kaka, yasan gaskiya ya faɗa, dan daular ruman bazata zuba ido na barinsa sakakai ba. Ajiyayyun dakarun dake a ƙofar gidansa ma kawai tabbaci ne....
A ɓangaren Ummu ma bata runtsa ba, sai dai saɓanin Babiy ita kwana tai tsaye tana gayama UBANGIJI damuwarsu da roƙonsa kariya da kuɓuta ga yarinyarta. Shi kuwa Hanash kwana yay ƙulla ta yanda zai halaka Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed da kansa. Hakama Iffah nata shirin nada alaƙa dana Hanash. Ta gama yankema kanta koda zata mutu itama sai dai su mutu tare da Tajwar Eshaan. In yaso a binne gawarta a tsakiyyar ruman matsayin tarihin da za'a dinga tunawa.......
*_WASHE GARI_*
Washe gari data kasance safiyar laraba da misalin ƙarfe biyar na yamma sai ga manyan baƙi daga masarauta ruman. Baƙi masu ban mamaki, dan kuwa wasu manya ne a cikin dattijai masu faɗa aji a daular ruman. Sannan iyaye ga Shahan-shan ta ɓangaren jini makusanta sosai ga mahaifinsa. Tamburan masarauta da ɗunbin tawagar hadimai da jibga-jibgan motoci da suka ƙoshi ne suka tabbatarma da jama'ar anguwa dama maƙwaftan anguwar wace tawagace. Tuni mutane suka fara ƴar rige-rigen fitowa daga gidajensu bama idanunsu abinci.
Sun tarbesu bisa jagoranci Kaka daya tsara komai tare da shimfiɗa kakkauran gargaɗi ga su Babiy. Bayan an musu masauki a cikin lambun Babiy ta ɓangaren garden ɗin da yayi domin farin ciki ga iyalansa aka cika musu gabansu da ƴaƴan itatuwa duk da babu tunanin ko zasu ci. Babiy, Kaka, da wasu dattijai biyu, ɗaya ta ɓangaren Babiy, ɗaya ta ɓangaren Ummu ɗan uwa ga kaka kenan suka zauna da su. Sun miƙa gaisuwa a garesu cikin mutuntawa da nuna tabbacin su ɗin masu ƙarfin iko ne a garesu talakawan ƙasan ruman. Hakan yayima dattijan matuƙar daɗi da yabama su Kaka. Dan haka suma suka nuna mutuntawa a garesu da basu ƙarfi matsayin waɗanda sukazo neman iri wajensu. Hakan ya ɗan bama su kaka mamaki amma sai babu wanda ya nuna. Sun gabatar da buƙatarsu, tare da bada duk wani abu na al'adar aure da ƙasar ruman ta tanada ninki wanda akanyi sau goma. Hakan sai ya ƙara firgita Babiy da bashi tabbacin yanda za'a salwantar da rayuwar ƴarsa ɗaya tilo data rage masa zai zama ƙololuwar girma fiye da ƴan uwanta kenan. To inbaice hakaba mizaice, dan dukiyar da suka kawo kawai tamafi ƙarfin ma sayen Iffah idan sayarwar zaiyi. Bai samu damar cewa wani abu ba, yadai cigaba da kukan zucinsa yabar su Kaka dayin abinda ya dace.
A wannan zama aka ƙarƙare komai har ranar ɗaurin aure dama inda za'a ɗaura auren. Daga haka sukai addu'a suka tafi bayan an shigo da tarin kayayyakin da sukazo da shi. Daga Babiy har Ummu tagumi kawai sukai suna kallon kayan