Showing 36001 words to 39000 words out of 122381 words

Chapter 13 - Daudar Gora Book 1 Hausa Novel Complete

25 Dec 2024

407

imani ya zubda mata hawaye, dan sauran Zawjata-almilki na baya mutuwarsu kawai akeji bayan kaisu turakarsa. Amma ita ko kaitanma ba'ayiba, a kwana ɗaya tak da tai a gidan batare da an kammala gagarumin taron bikin da aka shirya ba dominta gata a halin da gara mutuwa da shi...
Bayan idar da sallar isha'i Malikat Bushirat na hakimce a katafaren falonta na uku Malikat Ashwaq ta iso da tawagar hadimanta duba Iffah. Malikat Ashwaq itace mace ta farko ga marigayi Tajwar Haysam ibn Abdull-majeed. Hamshaƙiyar mace ce data isa take kuma amsa suna Malikat. A ƙa'idar Daular ruman matar data haifi yarima mai jiran gado a cikin matan sarkice kawai ake kira da Malikat. Mafi yawanci kuma ana samu ne daga matan farko. Sai dai ga Tajwar Haysam hakan bata faru ba. Dan matarsa ta farko Ameera Ashwaq bata taɓa haihuwa ba kamar sauran matansa, tadai taɓa ɓarin ciki na wata huɗu daga shi kuma bata ƙara ba. A zahiri mace ce isashiya mai baza mulkin da yafi na kowace mace a gidan bayan malikat Bushirat, amma kuma bata da damuwa sam. Ƙaryarka kace ga wani mugun halinta na zahiri saboda tasan kanta. Rana ɗaya aka ɗaura aurenta dana Malikat Bushirat matsayin Zawjata-almilki. Amma itace uwargida. Duk da mulkinta Malikat Bushirat ta fita, ta kuma fita zafi da nuna kishi a zahiri dan sam ita bata da haƙuri, hakan yasa ake matuƙar jin tsoronta fiye da kowace Zawjata-almilki, dan Malikat Bushirat ba kanwar lasa bace ƙwarai da gaske, sai dai mace ce mai son ƙyautatama wanda yay mata da na ƙasa da ita, hakan ya taimaka mata samun soyayyar hadiman gidan. Haihuwar Miran (Yarima) mai jiran gado Eshaan tasa dole sunan Malikat ya koma kan Malikat Bushirat. Wato Sarauniya Bushirat kenan. Amma duk da haka sai Mahaifiyar Tajwar Haysam mai suna Malikat Haseena ta bada umarnin cigaba da kiran Ashwaq da suna Malikat Ashwaq. Hakan ya ƙona ran Malikat Bushirat, sai dai babu yanda zatayi. Amma ta sake tsananta kishin da takema Malikat Ashwaq ɗin fiye da da, yayinda ita kuma Malikat Ashwaq ke nuna tamkar babu komai a zahiri, amma a baɗini hummm....
Koda ta shigo Malikat Bushirat bata nuna tasan da shigowar tata ba. Sai dai ta ɗagama hadimanta yatsu biyu da ya sakasu rige-rigen fara barin falon. Zaune Malikat Ashwaq takai bisa ɗaya daga cikin kujerun falon tanama nata hadiman nuni dasu fita suma. Da sauri suma duk suka fice aka barsu su biyu kawai. A hankali Malikat Ashwaq ta ɗan sakin murmushi daya danne zafin yarfin da Malikat Bushirat ɗin tai mata, ita ta fara gaisheta da tambayar ya mai jiki?. A daƙile Malikat Bishirat da tai kamar zata basar ta amsa mata cike da isa. Nanma Malikat Ashwaq dai murmushi kawai tayi da haɗiye ɓacin ranta. Sosai ta nuna tausayi akan Iffah ta kuma mata doguwar addu'a da bada shawarar mizai hana a kira likita ma ya duba ta ko wani abune daban da wanda ake tunani.
Karan farko Malikat Bushirat ta ɗakko manyan idanunta tai mata kallon tsakkiyar ido. Cikin yamutsa fuska taja numfashi da fesarwa, “Haihuwar magajin Daular ruman daga tsatson Malikat Bushirat rubutacciyar ƙaddara ce da duk yaƙi da gwagwarmayar masu son daƙile hakan. A baya basuci nasara ba, Taya suke tunanin samunta a yanzu kan _Saifulmulk_ ɗi na?. Kamar yanda aka haifesa daga matsayin gudan jinin Shahan-shan, Tajwar Haysam ibn Abdul-majeed. Shima haka za'a samar da Ɗa daga gudan jininsa da izinin UBANGIJI masu lissafi su fara...”
Muƙutt Malikat Ashwaq ta haɗiye yawun dake neman kufce mata, a zahiri kuwa murmushi ta saki da ɗan girgiza kanta. Batare da tace komai ba tai yunƙurin miƙewa domin barin ɗakin tana mai ƙoƙarin danne zuciyarta dake yunƙurowa. Har tayi taku biyu sai kuma ta tsaya, batare data juyi ba ta saki murmushi. “Idan dai har Eshaan ya kasance gudan jinin Shahan-shan ne babu gauraye, muma irin wannan fatanne a bakunanmu garesa kasancewarmu uwaye a wajensa. Fatan alkairi da samuwar lafiya ga Zawjata-almilki.....”
Har tsakkiyar kai kalaman ƙarshe na Malikat Ashwaq suka daki zuciyar Malikat Bushirat, sai dai kafin ta samu wani damar fassarasu sallamar Ameera Danish-Ara da suka kusan kiciɓus da Malikat Ashwaq ya dakatar da ita. Itace mata ta uku ga Tajwar Haysam. itama da tata tawagar hadiman. Kallon juna sukai da Malikat Ashwaq, Ameera Danish-Ara ta saki wani malalacin murmushi a kaikaice. Sai kuma ta matso cikin girmamawa ta gaishe da Malikat Ashwaq ɗin datai mata kallo guda ta ɗauke kanta. Amsa mata tai cike da ƙasaita, kafin ta matsa ta bata hanya ta shige, itama ta fice tawagarta biye da ita.

Saɓanin Malikat Ashwaq ita ta samu tarba daga malikat Bushirat. Dan duk da take mata itama ga Tajwar kuma Malikat Bushirat kishiya a gareta hakan bai hanata risinawa ta gaidata ba da matuƙar girmamawa tana mai tambayar jikin Iffah. Malikat Bushirat dake kishingiɗe har yanzu a yanda Malikat Ashwaq ta barta ta amsa mata da sassauci mai haɗe da jimami. Cike da makirci Ameera Danish-Ara ke nuna tsantsar tausayin Iffah tana mai yin ALLAH wadai ga duk mai hannu akan waɗan nan al'amura.
Malikat Bushirat taɗan jinjina kai irin na ƙasaitattun mata da yamutsa fuska kaɗan, a saman lips ta furta, “Nagode”.
A kaikaice Amera Danish-Ara ta ɗan saƙi murmushi tare da harararta ta ƙasan ido. A zahiri kuwa zamanta ta gyara tare da risinar da kanta. “Wannan abunda ya shafemune ai gaba ɗaya ranki ya daɗe. Domin Zaki ɗammu ne, fatammu dai ALLAH ya warware waɗannan al'amura cikin sauƙi”.
Har cikin zuciya Malikat Bushirat taji daɗin kalaman Amera Danish-Ara, dan haka a lips ta amsa da “amin” tana mai sauke ajiyar zuciya, dan bata cika samun damuwa da ita a gidanba tunma sunada ƙuruciya. Amera Danish-Ara mace ce mai tsananin kissa da ba lallai a lokaci guda ka iya gano wacece ita ba. Duk da kasancewar ita Zawjata-almilki ce a daular ruman zakasha mamakin irin girman da take bama Malikat Ashwaq da Malikat Bushirat a gidan a zahiri tunda ta shigo. Kai hatta da Amera Haifah dake amarya kuma ƙarama a cikinsu ita bata taɓa bari saɓani ya shiga tsakaninsu ba a zahiri. Wannan halin nata yasa sanda surukarsu Malikat Haseena ke da lafiyar ƙafa take sonta da janta a jiki fiye da su Malikat Bushirat. Wani lokacin har kwatance take musu da halin Amera Danish-Ara ɗin wai suyi koyi ta fisu dattako. A yanzu haka da take zaune babu lafiyar ƙafa Ameera Danish-Ara ɗin tafi kowa sintirin zuwa dubata da mata hidima a zahirance, duk da itama Malikat Bushirat na kamantawa sai dai babu ruwanta da sai wani ya gani yace tayi.
Shiru falon ya ɗauka na wasu mintuna, Amera Danish-Ara na son taga Iffah babu fuska ga Malikat Bushirat, dole ta miƙe cikin ƴan kame-kame tana tambayar ko Amera Haifah tazo kuwa?.
Kallon ƙasan ido Malikat Bushirat tai mata tana ƙara tsuke fuska, dan ita duk yanda take da zafi babu wanda zaice ga ranar data zauna maganar wani a cikinsu koda da su Jasrah ne kuwa. A ganinta idan tai hakan sunma isa kenan a wajenta. Murmushin yaƙe Amera Danish-Ara tayi cike da basarwa. Sai dai ƙasƙantaccen kallon da Malikat Bushirat tai mata ya matuƙar sokar mata zuciya. Taɗan risina da faɗin, “Na barki lafiya ranki ya daɗe”.
Kai kawai Malikat Bushirat ta jinjina mata batare data ko ɗago ba. Amera Danish-Ara ta cije baki da ficewa hadimanta dake jiranta daga falo na biyu suka take mata baya.

Sam Amera Danish-Ara bata gaban Malikat Bushirat, kalaman Malikat Ashwaq ne keta faman mata kaikawo a zuciya musamman na ƙarshe. (Fatan alkairi da samuwar lafiya ga Zawjata-almilki) waɗan kalamai bakwai a cikin tarin kalaman Malikat Ashwaq sunfi komi tsayawa Malikat Bushirat a zuciya. Dan kuwa tana fassarasu ne da wani abu daban ne. Haka manyan mutanen masarautar suka cigaba da shigowa duba Iffah daga sassa daban-daban na gidan. wasu iyaye ne, wasu yayu, wasu ƴaƴa harma da kakanni maza da mata duk da basu samun damar shiga ciki iyakarsu wajen Malikat Bushirat. Bata damu kanta ba sai da dare yaja. Koda hadimanta suka dawo sallamarsu tai dan tafi buƙatar kaɗaici a yanzu saboda son ƙara tunani akan kalaman Malikat Ashwaq da suka gagara haɗiyuwa a gareta. Da kuma nazartar kowa daya shigo sashen nata domin duba Iffah. Tun tana a zaune har takai ta miƙe tsaye hannayenta goye da bayanta tana faman kaikawo tamkar mai safa da marwa..........✍



*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*


_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)



𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻


*_17_*


...........Dare yayi nisa, bakajin motsin kowa a daular ruman sai sassanyar iskar dake kaɗa bishiyoyi kaɗan-kaɗan. Sai kuma Hadiman da ake kira Ghazi a masarautar ne kawai ke faman kaikawo domin bada tsaro ta kowacce kusurwa ta gidan musamman a sashen Tajwar Eshaan.
Iffah dake kwance samɓal a katafaran gadon alfarma na Malikat Bushirat idanunta a rufe kai kace batama numfashine ta fara zabura a hankali kamar wadda ake mintsini. Jasrah ce kawai tare da ita a ɗakin, tana daga gefe barci ya ɗan figeta mai cike da wani irin mummunan mafarki. Wata gigitacciyar ƙara da Iffah ta fassa tare da girgizar data saka gadon shima rinƙa girgizawa yasa Jasrah farkawa a kiɗime. Tsalle tai gefe jikinta na rawa ganin yanda Iffah da gadon ke girgiza, hatta shi kansa ɗakin ji Jasrah keyi na mata rawa shida fitulun da suka haskesa, dan sai daukewa suke suna kawowa. Wani irin tari Iffah ta farayi mai tahowa da aman jini ta baka ta hancinta harda ta kunne. Jasrah ta fara ƙwala kiran sunan Malikat Bushirat a matuƙar firgice tana sake manne jikinta da bango hanunta na laluben ƙofa amma ta kasa buɗeta...
Malikat Bushirat da dama ba barci take ba saboda tsabar damuwa ta buɗe idanunta a hankali jin sautin muryar Jasrah tamkar a sararin samaniya tana yawo. Cigaba da jin sautin ya sata miƙewa zaune ta sauka a gadon baki ɗaya. Babu wani hadimi dake da damar shigowa sashen ɗakunan barcinta sai masu gyarawa kawai suma da safe ne, hakan ya sata ɗora abaya kawai a saman kayan barcinta ta fito.... Jasrah da ta gama fita hayyacinta gaba ɗaya ta faɗa jikin Malikat Bushirat, rungume ƴar uwar tata tayi, a hankali ta shiga hura mata iska a kunne tana bubbuga bayanta. Jasrah da ƴar nutsuwa ta fara zuwa mata tai lamo tana sauke numfarfashi a jajjere, sai kuma ta ɗago a hankali hawaye wanke da fuskarta...
“Mike faruwa?”.
Malikat ta faɗa a hankali. Ɗakin Jasrah tabi da kallo, kafin ta fara mata bayanin komai har yanzu hawayenta sun kasa tsayawa. Sosai hankalin Malikat ya ƙara tashi, sai dai kamewarta yasa ba lallai ka fahimta a kan fuskarta ba. Cikin takunta na ƙasaita ta isa gaban gadon inda Iffah take. Kwance take samɓal tamkar ba itace ta gama buge-buge ba yanzun. Idanu ta tsura mata a karan farko, yarinya ce ƙarama sosai kuma ƙyaƙyƙyawa matuƙa, duk da halin ciwo da take ciki da canjawar fatar jikinta ƙyawunta da kwarjininta basu gushe ba, tausayinta mai tsanani da ƙaunarta suka sake ratsa zuciyarta. Zaune ta kai gefen gadon ta kai hannu ta shafa yalwataccen gashin Iffah daya gama bajewa a kan filon.
“Ibnati kiyi haƙuri zaki samu lafiya bazasu taɓa samun galaba ba kinji”.
Iffah da sarai take jin maganar Malikat dan ba barci take ba azaba ce kawai ke ratsata tai murmushin ƙarfin hali a zuciyarta, a karan farko taji ƙaunar matar a ranta da sake ganin kima da girmanta.......

★★_______★★

“Sun jiƙa mana aiki! Sun ɓata mana shiri! Ya ƙwace mana damarmu wadda sake samun samuwarta a garemu cikin sauƙi haka zata iya zame mana mai wahala!!”.
Kakkausar muryar Uwa mai matuƙar rashin daɗin saurare ta fara karaɗe ɗakin cikin amon sauti mai tashi sama. A firgice ta miƙe a zabure tare da zube gwuyawunta ƙasa jikinta na tsuma dan dama zaune take ido biyu tana jiran tsammani. “A gafarce ni uwa ba laifina bane, ni kaina ina cikin damuwar tangarɗar da aka samu”.
“Bana buƙatar jin komai daga gareki Taƙurya. Domin sakacinki ne ya jawo hakan. Nasha faɗa miki ki san suwa zaki bama aikin da ke bazaki iya yinsa kai tsaye ba. Su kuma waɗan can sakarkarun barinsu sukai wayewar gari tamkar rasa sauran damar data rage miki ne....”
Ɗan zabura tayi da nufin cewa wani abu, sai dai tamkar walƙiya Uwa ta ɓace a ɗakin. Hakan na nufin ranta a ɓace yake. Itama kanta ta dafe nata ran na suya da ƙara girmamar baƙin cikinta. Miyasa kowa bai bata matsala ba sai wannan ƴar shilar yarinyar da bata wuce sauron gidanta ba da feshi ɗaya take kawar da shi. Zuciyarta ta fara raya mata Uwa kodai tsoron yarinyar nan takeyi, yo inba tsoro ba taya zata dinga wani gewaye-gewaye bayan bai wuce da ƙyaftawar ido kawai ta shafe babin rayuwarta ba. Dama mutum na gagarar aljani ne banda ta fara maidata susu......


WASHE GARI..

Duk wanda ya kwana ya tashi a masarauta a yau ya tashi ne da tashin hankalin da yafi na jiya sakamakon mawuyacin yanayin da Iffah ta wayi gari. Dole tun gabatowar sallar asuba aka maidata cikin clinic ɗin dake a masarautar saboda ɓallewar jini ta kowane sashe na jikinta. Da farko aman jini ta fara, sai kuma ta hancinta, sai gashi ta ido da kunne harda ma ramin cibiyarta. Hankalin Jasrah da Malikat dake tare da ita ya kai matuƙar ƙololuwar tashi. Duk da kowa yasan ciwo ne bana asibiti ba haka likitoci suka rufu a kanta domin ƙoƙarin ganin sun tsaida jinin amma abu na neman gagara. Har kusan goma na safe a gogon ƙasar babu wani cigaba, jikin Iffah ma ya fara saki alamar jininta yayi ƙasa matuƙa....

★★...

“Bari-Hamshira! Inaga ya kamata a bama masu maganin dake waje dama suma suzo su gwada sa'arsu tunda ba'a dace dana cikin masarauta ba.”
Malikat da damuwar duniya ta tattaro a kanta yau ko fadarta bata iya fitaba tana cikin ɗakin barcinta har zuwa yanzu ta ɗago idanunta dake jajur ta sauke akan ƙanwarta ta uku mai suna Zaimah, cikin nuna sallamawa ta jinjina kanta. “Wannan ma shawara ce mai ƙyau Akia, ruɗewa tasa sam wannan tunanin bai zomin ba. A sanar da Ghazi su faɗama Baba Yaro. Sai dai komai ya kasance cikin sirri da amana dan kar maƙiyanmu suyi amfani da wannan damar wajen ruguza ɗan sauran ƙwarin gwiwar mu akan wannan yarinya”.
Kai Zaimah ta jinjina mata, sai kuma ta miƙe da hanzari domin isar da umarnin.....

*_ƘAUYEN JUMNA_*

Tafiya saurayin yake tamkar zai tashi sama dan gaggawa, wani lokacin har tuntuɓe yakanci sai dai kafin ya kai ƙasa yay azamar taro kansa ta hanyar dafe duk abinda ke kusa da shi. Wurjanjan ya isa ƙofar gidan Dattijon da kowa yafi sani da suna Abu Huzaifah ya kwaɗa sallama da iya ƙarfin muryarsa har sau huɗu babu ko jiran a amsa masa.
Dattijo Abu Huzaifah Da mukafi sani da Kaka ya dakata da ga ɗinkin kwalliyar doki daya duƙufa yi ya dago suka kalla juna da Iyyani dake shara a tsakar gidan. “Kamarfa sallama naji Abu Jamaima a ƙofar gidan nan”
Kafaɗa yaɗan rausayar gefe da ajiye zungureriyar allurar da yake ɗinkin da ita. Kafin ya ce wani abu aka ƙara zungura sallamar a jajjere tamkar yaƙi. Kansa ya ƙara jijjigawa ya miƙe dajan tsaki. “Kai wasu dai mutanen sam basu da lissafi, irin wannan ai saka ɗauka tashin hankali ne”. Kaka ya faɗa cikin mita yana gyara takalmansa. Iyyani da takaici ya ƙulle itama ta bisa da kallo harya fice a soron gidan...
“Ayyub! dama kai ne kake ƙwaɗa irin wannan sallama haka? Lafiya dai ko?”.
“Da sauƙi dai Baba, amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login