Showing 54001 words to 57000 words out of 122381 words
ra'ayinta, itako tana amsa mata a kunyace da tsakurar abincin. Suna a haka Daneen Ammarah ta shigo, itama dai ta nuna jin daɗinta na ganin Iffah ɗin tare da jin kaunarrta har cikin rai. Zama tai itama aka ɗora cin abincin da ita suna yar hira jefe-jefi da Malikat Haseena. Iffahn dai nata saurare kawai, sai kuma murmushi. Rabin hankalinta kam nacan wajen tunanin hadima banou da yanayin ta....
★★.... ★.. ★★....
Kamar yanda Barrister yayma su kaka alƙawari ya samo Ibrahim Askari ta hanyar mutumin nan da suka fara zuwa wajensa. Fuskarsa cike da murmushi yake dubansu, dan tun yana can ya sanarma Abu Zainab su haɗu a office. Sai gashi kafin ya iso ma su har sun iso. Ko cikakkiyar gaisuwa basuyi ba ya fara musu bayani.
“Alhamdulh an samo Ibrahim Askari, ya kuma bani cikakken adireshin Dawood ɗin, hasalima yace shiyya sayar masa da gidan daya koma ɗin. Ga adireshin gidan ya bani”.
Sosai farin ciki ya bayyana a fuskar Kaka. Ya dinga jerama Barrister addu'a da fatan alkairi. Shima dai Abu Zainab yayi masa godiya, tare da ɗorawa da faɗin, “Barrister yanzu mune zamuje can ɗin? Kokuwa kai ne?”.
“Mu duka babu wanda zai je Zakariyya”.
Kallonsa sukai su duka, ya jinjina musu kansa da buɗe wani littafi a gefensa ya yago takarda, ɗan rubutu yay da sake ɗagowa ya dubesu. “Kamar yanda na faɗa muku mu duka babu wanda zaije. Domin ita Shari'a takanzo saɓanin hankali. Sannan bamu san nasu shiri ba, zasu iya amfani da duk wani yunkurinmu a yanzu. Dan haka nayi abinda ya dace bayan barina wajen Ibrahim Askari. Akwai wani babban police dana sani kai tsaye naje garesa, nakumayi sa'asar samunsa. Nayi magana dashi da rokonsa ya bincika mana inda zamu iya samun su, Alhamdullah kuma ya amsa, yanzu haka kiransa nake jira kamar yanda yaymin alkawarin kafin cikar awa ɗaya”.
Anan ɗin ma dai farin ciki ne a fuskokin su Kaka, sai faman sauke ajiyar zuciya sukeyi.....
★... ★★.... ★....
Zamu iya cewa gaba ɗaya yinin yau Iffah ta kare shine a neman number Malaminta Fawzan da abokinsa Ajmaal. Amma abin mamaki har yamma amsa ɗaya ce layukansu not available. Gaba ɗaya tayi firingai-firingai na damuwa, duk yanda take ƙoƙarin ɓoyewa da danne hawayenta sai da suka zubo bayan ta idar da salla. Bakomai yasata shiga damuwar akan son samunsu ba sai rashin samun number Babiy da Hanash da batai ba suma. Tana son jin wani abu game da ahalinta, dan yawan faduwar gaban da take da mummunan mafarki yasa tanaji a jikinta akwai matsala. Tama rasa wane tunani zatayi, har text message ta turama Malam Fawzan akan ya taimaketa ya duba mata iyayenta amma shiru kakeji, bama tada tabbacin ya gani ko bai gani ba. Kuka taci sosai a wajen kafin ta mike tana share hawaye bisa shawarar zuciyarta. Wayar ta sake ɗauka ta sake tura sakon data turama Malam Fawzan a layin Ajmaal abokin nasa. Tana fatan ɗaya daga cikinsu yaga saƙon koda bata samu sauran biyan bukatarta ba. Jikin window ta koma ta tsaya tana mai shaƙar iskar dake busowa mai daɗi, kamar ance kalla gefe ta hango Hadima Banou can jikin filawoyin saitin ɗakin Malikat Haseena tsugunne kamar tana tona rami, sai faman waige-waige take alamar rashin gaskiya. Da farko tsura mata idanu Iffah tai, sai kuma ta zabura bisa umarnin zuciyarta. Sai da ta tabbatar wani baiga sanda ta fito a dakinta ba sannan ta fice, kasancewar ta naɗe har fuskarta da ɗan kwalin abayar jikinta yasa babu wanda ya ganeta, balle abayar jikin nata ɗaya daga cikin natane na gida data canja bayan barowarta wajen Malikat Haseena. Da ƙyar ta gane hanyar dazata ɓulla bayan, dai-dai Hadima Banou na ƙoƙarin maida kasar data tone alamar harta saka abinda zata saka. Sauri-sauri takeyi harta kammala, ta ɗago da nufin barin wajen taja ta tsaya a kiɗime ganin mutum tsaye a bayanta. Amma kasancewar ta mai shegen tsurin ido sai ta dake a zahiri tana kallon Iffah da har yanzu bata janye mayafin data yane har fuskar ba....
“K! Ubanwa ya kawoki nan?”.
Ta faɗa da zaton cikin hadimai ne irinta. A hankali iffah ta karasa takowa gabanta, tare da janye mayafin ta saka idanunta cikin nata jajaye marasa ƙyan gani. Sosai hadima banou ta rikice har rawar jikinta ya bayyana. Iffah ta janye idanunta daga kanta ta maida akan ramin,
“Mi kika binne?”.
“Ranki ya daɗe babu komai, w... W... Wani magani ne kawai da nake son yin amfani da shi.....”
“.....Shine kika shuka shi anan cikin rashin gaskiya? Wacece ke? Mi kike kullawa”.
Tambayoyin sunma Banou yawa da tsauri wajen bada amsa, a take ta sake gigicewa duk da tana ƙoƙarin ƙirƙirar jarumtar dole. Wuceta Iffah tai zuwa wajen ramin, ta tsugunna da daukar iccen datai tonan da shi ta shiga sake tone kasar da Bismillah. Firrr wani abu kamar tsintsuwa ya fito a ramin yay sama. Iffah ta mike da sauri ta bisa da kallo harya bace. Juyawa tai da sauri inda Banou take, dai-dai ko tayi shirin silalewa tabar wajen ta dakatar da ita.
Ƙasa tai da kanta jikinta na matukar rawa, Iffah ta kare mata kallo sama da kasa na wasu sakkani, sai kuma ta girgiza kai. “Wani asirinne haka bizne tsuntsuwa da ranta saboda son zuciya? Ko wani ya sakaki biznewar saboda ya isa? Kokuwa ke ɗin kina a cikin jinsin Mayu ne? Dan a cikin ukun nan dana lissafa dole ne a samu ɗaya tattare da ke tsohuwa”.
Kuka Banou ta fashe da shi gwuyawunta a ƙasa. “Ranki ya daɗe ban fahimci abinda kike nufi ba, nifa magani na shuka ki yarda dani”.
“Uhhm wato magani kika shuka, tsohuwa kalleni da kyau ki ganni banyi kama da wanda akema rufa ido ba, amma zan baki lokaci kije, zan nemeki a lokacin daya dace. Idan kika hangi gudu baki da wajen iya ɓoye min, idan cutar dani ne zagaye nake da kariyar UBANGIJINA, idan yunkurin salwantar da rayuwarkine idona biye yake dake tako ina. Shawara ya rage gamai shiga rijiya”.
Da wani irin mummunan kallo hadima banou tabi bayanta da shi, ta cije baki da rumtse jajayen idanunta da karfi.........✍️
🤔 Wannan ƴa ta Babiy ƙarfin halinta da tarar aradu sun mata yawa. Dole dai sai ta kai kanta inda za'a lamushete oh ni Balki😜.
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 90165991
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_24_*
..........Komai daya faru tsakanin Iffah da Hadima Banou akan idon Daneen Ammarah ne, dan itama tayi yunƙurin fitowar ne ganin Banou na tono a bayan windown Mamman sai ta hango Iffah na tahowa. Kasancewar ta ganta da rigar jikinta a ɗazun yasa kai tsaye ta ganeta. Da farko gabantane ya fara faɗuwa da tunani iri-iri, shiyyasa ta tsaya domin ganema idanunta. Sai dai kalaman Iffah da yanayin Hadima Banou ɗin ya sata shiga ruɗanin tunani. Idan har zata auna da hankalinta matsayin babba itama Iffah taga Hadima Banou ne shiyyasa ta fito, a yanayin Banou kuma ya nuna akwai wani ɓoyayyen al'amari na rashin gaskiya tattare da ita. To amma su maiyasa a tsahon shekaru basu taɓa ganin wannan fuskar ta Banou ɗin ba? Wacece Iffah? Anya kuwa ba akwai abinda ya kamata ta sani dangane da yarinyar nan ba?......
★Iffah da al'amarin wannan masarauta ya fara ruɗama tunani tana shiga ɗakin dake matsayin nata yanzu ta murza key. A jikin ƙofar ta jingina da lumshe idanunta tana sauke numfashi. Ita kanta taga ƙarfin halinta yau, dan zata iya rantsewa bata san a ina ta samo wannan jarumtar ba. Idanun ta buɗe tare da riƙe ƙugu ta karyar da kai alamar nazari. In fa har ta canka dai-dai tabbas wannan hadimar mayya ce. Dan bata manta da wani labari da Iyyani ta taɓa basu ba na mayya yar Danƙo datai zamani a kauyen jumna shekarun baya. Babu banbanci da abinda taga matar nan tayi yanzu, dan da alama kurwar wani ta laso tazo ta boye a wajen. “Bahun ubancan, eh da gaske dai ashe lamushe ƴaƴan mutane ake a masarautar nan tunda ga alama harda su bayi an barbaɗa musu muguwar tambaya. Shi baƙin babban dodon nasu nacinye mutanen gari su kuma bayi nacinye junansu a cikin gida”. Tai maganar a fili cikin ƙankance idanu na alamar tunzuruwa...
Murmushi Daneen Ammarah dake bakin ƙofa tsaye ta saki, dan nutsuwar da zuciyarta ta kasa mata ya sata biyo bayan Iffah, har ta kai hannu zatai knoking sai kuma ta fasa da tunanin inhar Iffah nada wani mugun nufi a kansu to baro can zata samu wani abun take aikatawa a yanzu. Dan haka ta ɗan kara kunenta kaɗan jikin ƙofar, cikin Sa'a kuwa ta jiyo mi Iffah ta faɗa saboda yanda tai maganar da ɗan zafi sai ta fita da ɗan karfi kaɗan. Ƙofar ta fasa bugawa ta koma ɗakinta da baya. Itama dai ƙofar tata ta sanyama key duk da tasan babu wanda zai shigo mata. Kai tsaye wadrob ɗin ta ta nufa, a cikin wani akwatin ƙarfe karami mai ƙyau ta fiddo waya bayan ta danna madannan sirri ya buɗe. Wayar ta shiga ƙoƙarin kunnawa tana mai rufo windows ɗin ɗakin nata. Sai da tai danne-danne kusan na mintuna biyu alamar text ta tura. Kira ne ya shigo, sai a ring ɗin karshe ta ɗaga, batare da jiran wani gaisuwa daga wancan ba cikin bada umarni tace,
“Daga yanzu zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu ina buƙatar sanin komai akan Zawjata-almilk ta uku. Idan nace komai yana nufin komai da komai”. Kitt ta yanke kiran tana wani irin murmushi tun kan ma ta samu amsar data bukaci sani. Wayar ta kashe gaba ɗaya ta sake maidata inda ta dakkota......
(🤔Wai su kowa da tasa manufar ne????)
*_MALIKAT BUSHIRAT_*
Zaune take hakimce kamar ko yaushe cikin kwalliya mai matukar ɗaukar idanu. Ga wani sihirtaccen ƙamshi mai ratsa zuciyar duk wani mai shaƙa na tashi. Shi kansa falon kamshinsa na musamman ne. Gefenta na dama Jasrah ce itama cikin kwalliyar, zuwanta kenan sashen sakamakon aiken data samu daga ƴar uwar tata. (Itama dai Jasrah anan cikin masarautar take aure, tana kuma auren ƙanin marigayi Tajwar Haysam ne da suke uba ɗaya. Dan kamar yanda Tajwar Haysam suke su huɗu a ɗakinsu suna kuma da ƴan uba har su kusan tara, sai dai mata sunfi yawa a ciki. Su tarannan kuma ƴaƴan mata uku ne. Mijin Jasrah shine babba a cikin ƴaƴan amaryar Tajwar Haysam da ake kira Ameera Aasfah a masarautar. Mace ce mai kirki da sanin ya kamata, jininsu kuma yay matuƙar haɗuwa da Malikat Haseena. Dan idan ka gansu bazaka taɓa ɗauka kishiyoyi bane a sanda tana raye. Yaranta biyune ita kacal, Miran Arshaan shine babba, shine kuma ɗa na takwas a wajen Tajwar Abdul-majeed, a maza kuma na uku, shine mijin Jasrah a yanzu, sai ƙanwarsa Daneen Fu'ada, a yanzu haka tana aure itama. Ƙaunar dake tsakanin Malikat Haseena da Ameera Aasfah yasa shaƙuwa sosai a tsakanin ƴaƴansu, hakan yasa Tajwar Haysam ke kallon Miran Arshaan tamkar ƙaninsa Miran Nayyar daya rasa, shine ma da kansa ya aura masa Jasrah. Wannan kenan, ALLAH yasa kun gane🥱).
“Akia kince nazo amma kin kasa cewa komai? Wani abun ya sake faruwa ne?”.
Numfashi Malikat Bushirat ta sauke a hankali tana kallon ƴar uwar tata da takema kallo tamkar first born ɗin ta. Kamar bazatai magana ba sai kuma ta nisa cike da kasaita. “Komai bai sake faruwa ba, sai dai ina gudun sake faruwar. Sanin kanki ne Jasrah ba lallai kosu waye su haƙura ba dan yarinyar nan ta kuɓuta a yanzun, sannan ma bayan ita akwai sauran yaran biyu da har yanzu fargaba ta hanamu kaisu turakar Saifulmalik. Kin san kuma rashin kai su zuwa nan da ɗan lokaci sai kinji an fara kace-nace”.
“Hakane Akia. Amma ke mikike son cewa?”.
“Zancen dai ɗaya ne shine inajin tsoro, na biyu kuma da gaske yarinyar nan ta shiga raina fiye da duk matan da aka kawo gidan nan matsayin Zawjata-almilk”.
“Wlhy nima har cikin rai yarinyar ta shiga raina. Gata da tarbiyya daga ganinta, sannan itace mafi ƙanƙanta a duk matan na Son”.
“Wannan yana ɗaya daga cikin abinda ya sake jan hankalina a kanta Jasrah, shiyyasa yanzu da wani tunani yazo min nace bara nai shawara da ke. Shin kina ganin naima Mamma (Malikat Haseena) magana gobe idan ALLAH ya kaimu da Saifulmalik zaije gaisheta a kusanta shi da yarinyar nan suga juna? Sai nake ganin hakan zai canja wani babban al'amari da masu mana yankan baya ke ƙullawa. Tunda kinga dai duk matansa sai an kaisu turaka yake da damar ganinsu kamar yanda kowa yasan dokar kenan ga duk Zawjata-almilk tun ƙarnin baya”.
“Eh gaskiya kuma wannan tunani ne mai ƙyau Akia inhar Mamma zata amince ɗin. Dan Kinga muma a karan kammu wata hanya ce da zamu fuskanci wani abu akan shi kansa..”
“Wannan gaskiya ne. Dan da gaske Jasrah a yanzu har shi kansa zuciyata rawa take ga al'amarinsa, dan abinda ke faruwa dole ne kowa ya zama abin zargi har mu kammu, ke nama takaice miki zance ni kaina yanzu ban yarda da kaina ba”.
Murmushi Jasrah tai har haƙoranta na bayyana. Tace, “Kai Akia kinada abin dariya wlhy wani lokacin. To inke baki yarda da kanki ba mu kuma dawa zamu yarda kenan?. Kawai dai inaji a jikina koma minene ya kusa zuwa ƙarshe ta silar yarinyar nan tunda har ALLAH ya fara nuna musu iyakarsu suka gaza cin nasara a harin farko da suka kai mata. Yanzu dai bamu da lokaci, ki tattauna da Mamma ɗin kawai. Hukuncin data yanke sai mu karɓa kawai”.
Malikat Bushirat ta jinjina kai kaunar ƴar uwar tata na sake ratsata. Koba komai idan ta tattauna da ita takanji sanyi a ranta.......
★★.... ★.... ★★.....
“Wai nikam ɗazu ina ƙoƙarin shiga fada naga kamar motarki ta gitta, kinje wani waje ne?”.
Shayin da take ƙoƙarin zuba masa ta karasa tare da miƙa masa. Sai da ya amsa ta koma ta zauna tana mai ɗan ɗage kafaɗunta. “Kaima kasan fita ta bata wuce wajen Akia ai Abu Harith, wlhy itace fa tai min kiran gaggawa shine ka ganni na fitan. Amma lafiya kuwa har irin wannan lokacin kuna a fada?”.
“Uhm to lafiya lau za'ace, anyi baƙin bazata ne kawai ga Shahan-shan ya rigada ya shige kuma. Dole mu mukai zaman tarbarsu. Amma kiran gaggawa wata matsalar ne ta sake faruwa? Ko jikin Zawjata-almilk ɗinne dai?”.
“No akan dai wadda ake cikine. Jikinta kuma Alhamdullah, idan ma ka ganta yanzu bazakace wani abu ya faru ba. Kawai dai Akia ce ke ganin ya kamata idan Shahan-shan yaje gaida Mamma gobe idan ALLAH ya kaimu Zawjata-almilk ta ziyarcesa ko hakan zai kawo wani sauyi kan abinda har yanzu muka kasa sanin kansa”.
“Amma baƙwa ganin hakan wani ganganci ne? Sannan dokace fa Shahan-shan baya ganin matansa sai a turaka”.
“Eh muma mun duba wannan ɗin, dan haka ma bamu wani yanke shawara ba akace sai an sanarma Mamma. Amma kai ya kake gani akan hakan. Abu Harith wlhy Akia na bani tausayi matuƙa, a yanzu har takai da kanta itama zarginsa take shi yake ɓarnar nan”.
“Ya ALLAH wannan wace irin magana ce haka? Miyasa zatai irin wannan tunanin akan ɗanta. Bana jin Eshaan zai taɓa aikata makamancin hakan. Kawai dai akwai abinda yake ba daidai ba”.
“Sosai kuwa. Amma insha ALLAHU ta sanadin yarinyar nan kowa sai yaci ƙaniyarsa. Dan haka kawai nakeji a jikina ita ɗin haske ce a wannan daula. Tunda