Showing 99001 words to 102000 words out of 122381 words
tai dawnlording sabon WhatsApp app, sai da ta daidaita komai sannan ta lalubosa. Baya online gashi kuma tana buƙatar yau suyi magana ne bawai saƙo take son ajiye masa ba. Sai hakan ya sata jin babu daɗi har walwalarta ta ɓace. “Kona masa flashing?”. Ta faɗa cikin sigar tambayar kanta. Kan ta daga alamar gamsuwa, ta fito a watsap ɗin. A karo na farko tai dailing number ɗin cikin shakku. Harta katse ba'a ɗaga ba, damuwarta ta kara bayyana. Harta sake komawa watsap ɗin ta fito ta sake danna kiran. A hankali ta sauke ajiyar zuciya har ana iya jinta daga can. Tai sallama cikin yar muryarta dake nuna zumuɗin jin an ɗaga, sai dai ba'a amsa mata ba gashi kuma tanajin alamar ana saurarenta.
Danne takaicinta tai ta sake sallamar, nan ma shiru dai babu ma alamar za'a amsa. Cikin suɓutar baki taja tsoki da faɗin. “Nifa a rayuwa na tsani walakanci wlhy, shiyyasa komai nafi yarda naima kaina. Yanzu haka wani ɗan iyan dake ƙarƙashin sa ya ɗaga kiran kamar waccan ranar dana fara kira, ƴan hana ruwa gudu kenan. Nima badan ƙaddarar faɗawa hannun wannan Dodon ba da yanzu ina can ina karatuna na jaridar a daina yarfani. Kai insha ALLAHU kafin naga bayan a azzalumin nan ko sau ɗaya ne sai na hau kujerar karagar mulkin nan nayi tankaɗe da rairaya cikin duk ƴan jaridar ƙasar nan da jami'an tsaro aikin banza......”
Jin kamar sautin fitar murmushi a kunenta ya sata saurin ciro wayar ta kalla. Dai-dai ana yanke wayar. Ido ta kwalalo waje da dafe bakin. Sai kuma ta janye da faɗin, “Kai kamarfa daga cikin wayar ne sautin nan ya fito wlhy. Kai ina”. Ta sake faɗa tana ɗan wawwaigawa babu dai alamar wani a ɗakin sai itan kaɗai. “Oh ni Iffah anya bakin nan nawa bazai yankani ba wataran, yanzu hakama shine yazo ya amshi wayar inata zuba ban sani ba”. Tai tagumi cikin takaicin kanta. Kamar kuma wadda aka ɗan zabura sai ta sake ɗaukar wayar. Cikin sa'a tai tozali da ganinsa online har an amsa mata sallamarta ma. Sai kuma ta shiga kokwanton tayi magana ko kawai ta share. Wata zuciya ta amsa mata da (Kema kin san bashi bane ya ɗaga miki waya. Ki basar kawai). Da alama ta gamsu da shawarar, dan haka ta saki murmushi da buɗe saƙon.
“Sorry kin kirani bana kusa yarona ya amsa”.
Amsar data samu kenan bayan sallamarta da aka amsa. Har cikin rai taji daɗi, dan haka a fili ta furta “Alhamdullah dama naji haka a jikina”. Shi kuma ta bashi amsa da “Babu damuwa Sir”.
“kina da fahimta Shahrbano”.
“Bankai nan ba😣”.
Ta bashi amsa da emojin yamutse fuska. Sharewa yay da faɗin,
“Ta samu ne?”.
Itama sai ta share da bashi amsa da.
“Kusan haka. Sai dai a wannan gaɓar lamarin akwai ban tsoro Sir Ajmaal. Da gaske mutanen nan matsafa ne kuma suna aiki da aljanu”.
“Ya arrahaman! Kamar ya? Har kimsa na tsorata fa”.
“Tab tunma kan na faɗa kenan. To kama cire dan wlhy ba aljanu ba ko bataliyar ifiritai ce sai naga bayan mutumin nan. Wai fa jiya da dare nabar sashen nasa na koma inda sukace nawa kawai yau na wayi gari na ganni an sake maidoni sashen Dodon nan. Ɗakin dana kwana kuwa duk da haɗuwarsa na rantse maka a harmutse kamar anci dambe”.
“Dambe fa?”.
Ya share zancen farko ya amsa na ƙarshe.
“Wlhy kuwa Sir! Sai dai fa ni wannan bai damenba. So nake nasan ta yaya aka ɗakkoni aka maido ni inda ba nan na kwanta ba”.
“Kina da gaskiya dan akwai alamar tambaya kam. Amma ke yanzu wane mataki kika ɗauka?”.
“Komai banyiba har yanzu, nadai fara bincika irin kamshin da naji jikina nayi, inma shine ya aika aljanunsa suka ɗakkoni dan ya kashe ni”.
“🤭”.
Ya bata amsa da emojin rufe baki alamar tare dariya.
“😞Bafa abin dariya bane wannan, abin a dubane. Idan kuma aka halakani kafin ƙwato muku ƴancinku ku kukayi asara Sir Ajmaal”.
“Eh gaskiya hakane kuma ranki ya daɗe. Yanzu dai ƙarasa bani labarin dan in san ina zan kama. Saboda na gama shirye-shiryen buɗe wani sashe na shiri na musamman akan wannan case ɗin, sai dai komai zai kasance cikin hikima”.
“Aiko da naji daɗi Sir, dan gara kam a fara kafin ma na mutu na dinga ji. Dama inason maka zancen wancan tashin bomb ɗin, ko ka san mutumin nan ko damuwa bai nuna ba akan lamarin tsabar bai ɗauki rai bakin komai ba. Wlhy naji kamar na shaƙesa a jiyan kowama ya huta dan takaici”.
“Wai da gaske kike zancen nan ranki ya daɗe?”
“Wlhy kuwa babu wasa. Ni ka daina kirana da wannan sunan bana so”.
“Kiyi haƙuri kin cancanta ne ai. Zawjata-almilk guda ai ba abin wasan mu bace. Nima dai tsaurin ido yasa har nake iya zaman tattaunawa da ke”.
“🙄😏”.
Ta tura masa tana kashe data ɗinta. Daga can Ajmaal ya ƙurama emojis ɗin ido yana mai ƙoƙarin danne dariyarsa amma hakan ya gagara, dole yay faffaɗan murmushi har haƙoransa na bayyana yana ayyana (ƙuruciya daɗi) a zuciyarsa. Ganin ta kashe datan shima sai ya kashe kawai dan yana son sai ya nutsu yay zaman nazari akan abinda suka tattauna ɗin.....
★★..... KAUYEN JUMNA ★......
Alhamdullah dawowar Kaka da tsayuwar daka akan lafiyar Ummu yasa jikinta ƙarayin sauƙi har tana ɗan yin magana. Wani lokacin ma idan suna ƴar hira takan ɗan saka bakinta musamman idan akan Iffah ne da a mafi yawan lokuta take faɗo musu a zukata. Bawai halin da suka shiga kansu Babiy ya mantar da su ita bane, a koda yaushe tana manne a rayukansu, suna kuma binta da addu'a da cigaba da baza kunnen saƙon mutuwarta kamar ƴaƴansu na baya. Duk da dai ga Iffahn na nan shafe wata na uku kenan a daular ruman ɗin.
Yau ma kamar kullum Ummu da Iyyani na a tsakar gida suna aiki wanda kusan Ummu ce keyinsa duk da bana kirki bane. Kaka ya fita tun ɗazun wajen jana'izar mutuwa da akayi ta wani tsoho. Sauri-sauri Ummu ke ƙarasa aikin saboda rana ta ɗaga gata da zafi sosai kasancewar su yankinsu akwai sahara, danma suna ɗan samun sassauci dalilin ruwa ne zagaye da ƙasar tasu. Sai dai kuma zaman Dahab City (Daular ruman) kamar a tsakkiyar ƙasar ta ruman yasa su sunfi samun zafin yashin fiye da sanyin ruwan daya mamaye wasu jahohin dake a gaɓarsa sosai.
Sallamar da akayi ta saka Ummu amsawa tana mai duban ƙofar gidan, Iyyani ta fito tana faɗin, “Inaga mutanen Abbunku ne da basa ƙarewa. Gashi kuma bai dawo ba har yanzu ko yaya zamuyi kenan?”.
“Nima shi nake tunani Iyyani, kona leƙa na gani tunda ba'a sani ba ko baƙon mai muhimmanci ne?”.
Har Iyyani ta buɗe baki zata bama Ummu amsa sallamar Kaka ta katseta. “To Alhamdullah gamashi nan”. Iyyani ta faɗa tana kallon Ummu. Cikin fara'a kaka ya shigo, hakan yasa bayan sun masa sannu Iyyani ke tambayarsa ko lafiya?. Fuskar tasa da murmushi har sannan ya ce “Bani abun zama kedai yaron nan ne Zakariyya makwafcin su Jumimah”. Ya kare maganar da kallon inda Ummu take.
“Ah Masha ALLAH, ALLAH yasa muji alkairi to”. Iyyani ta faɗa tana ɗakko masa abinda ya buƙata har da ruwan sha ma a kofi.......
★★★.... ★★..... ★.....
Iffah kam dake ta faman tsuke fuska ita a dole taji haushi ta jawo rigar ɗazun ta maida a saman gown ɗinta ta fice. Isowarta falon dai-dai isar da sakon Tajwar Eshaan akan sake dafa masa shayi a bakin hadimin nan ga masu dafa abinci. Kai tsaye mamaki ya bayyana ƙarara a kan fuskarta. Amma sai ta dake babu alamarsa a zahiri taima hadiman wani kallo ta ɗauke kai.
Ba ƙaramin razana da ganinta a cikin kicin masu girkin sukai ba. Dan hakan zai iya zamar musu rasa aikinsu. Sai dai yanda tai kicin-kicin da fuska ya sasu kama kansu, kwarjininta da gizagonta na kere yawan shekarunta. Jikinsu har rawa yake lokacin data buƙaci ganin kayan shayin da Tajwar ɗin ke amfani da su. Daki-daki take binsu da kallo cike da nazari, sai da ta gama tsaf kafin ta juya garesu fuska a tsume. “Idan ina buƙatar wasu bayan waɗan nan a yanzun fa?”.
Cikin mamaki da tsoro suka sanar mata za'a kawo da gaggawa.
“Ina buƙatar zama da mai kawowar”.
Ta faɗa a gadarance da juyawa ta fara haɗa kalar shayi da salon dabararta batare da tayi amfani da wanda ake dafa masan ba. Wannan duk cikin shirinta ne na son ƙuntata ma zuciyar Tajwar Eshaan a cewarta. Cikin lokaci ƙalilan ta gama kasancewar ba wani mai yawa bane, ta juyesa a haɗaɗɗen butar shayi tare da haɗa komai na buƙata tai ƙoƙarin ɗauka. Da sauri hadima ɗaya ta miƙe ta amsheta. Bata musaba wajen bata dan dama ba sanin inda zata samesan tai ba.
Hadimar tai tsaye a dai-dai ƙofar ƙaramin falon alamar iyakar ta kenan. Iffah ta fahimci haka, sai kawai ta amsa batare da tace komai ba. Ba tsoro ko shakkar haɗuwa da shi take ba, abinda zai farunne idan ta shiga kawai take tunani. Tsahon minti biyu kafin tai ƙundunbalar shiga dan a ganinta wannan wata dama ce ta biyu a gareta, cikin takunta na nutsuwa da dakewarta ta tura kai bayan ƙofar gilashin ta zuge da kanta batare data tabata ba.........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_42_*
.........Kasancewar Barrister Akeem ba baƙo bane na shigowa gidan masu hidima a gidan suka dinga gaidashi. Amsa musu Barrister Abdallah ya dingayi da fara'a da kuma muryar Barrister Akeem data zama yana kwaikwaya a yanzu kamar yanda aka horar da shi. Ya iso katafaren falon da yaji komai na more rayuwar duniya, ga kamshi na tashi irin wanda aka san duk wani jinin ƙasar ruman da shi. Cikin girmamawa ya kai zaune fuskarsa da murmushi ya shiga gaida babban mutum ɗin dake zaune a falon cikin shigar kayan ƙasar na alfarma.
Da ƴar sakin fuska mutumin ya amsa masa da faɗin, “Barrister sai yau ake ganinka? Bayan kuma tun jiya nasa a sanar maka na dawo ƙasar”.
“Amun afuwa ranka ya daɗe, an ɗan samu wani tazgarone daya riƙeni a dalilin zaman da Boss namu ya kira, nayi zaton zamu tashi akan lokaci harna iso nan ɗin sai hakan bata yiwu ba, ganin dare yayi kawai na wuce gidan dan nasan kana bukatar hutu”.
“Hakane kam. Yaya aikin naku?”.
“Alhamdullh ranka ya daɗe munata bubbugawa”.
Murmushi mutumin yayi, sai kuma ya ɗan gyara zamansa da zuƙar shisha ɗin hanunsa yana gyaɗa kai. Shiru ya biyo baya kasancewar ɗaya daga cikin masu masa hidima ya kawo ma Barrister shayi. Sai da ya kammala ya fice mutumin ya ajiye marikin shisha ɗin da fesar da uban hayaƙin daya tara a bakinsa.
“Barrister dama ina maka wani neman gaggawa ne akan abokinka mai shegen taurin kai Barrister Abdallah Aas”.
“Tofa oga ya ƙara yin wani laifi ne?”.
“Kusan haka kam, dan akwai wani case na aminina dake a rufe sai ƙoƙarin ganin ya buɗosa yake yi. An masa gargaɗi kusan sau uku amma bai ji ba har sai da yajama kansa aka kauda shi kasan mutumin na ka da taurin kai”.
“Kauda shi kuma ranka ya daɗe?”.
Barrister ya faɗa cikin nuna rudanin as shine Barrister Akeem. Murmushi mutumin yayi irin nasu na manya yana ɗage kafaɗa alamar ko'a jikinsa. “To in basu kaudashi ba mi kake so suyi Barrister?. Yana da taurin kai ne gaskiya. Nasan dai kaji zancen tashin bomb ɗin can na jihar Hubab..?”
“Yes Yes ranka ya daɗe, ai kowa ma dake ƙasar nan yaji wannan baƙon al'amari mai tada hankali tunda bai taɓa faruwa ba a wannan ƙasa tamu......”
“To ga abokinka kam yaja ya faru, dan an tada wannan bomb ɗinne da shi kasancewar a cikin motarsa aka sakashi”.
A matuƙar razane Barrister ya furta “What! Ranka ya daɗe abokin nawa?”.
“Kaga kwantar min da hankalinka wannan ba wani abu bane. Sakamakonsa ya amsa a hannunsa. Kaga ko anan gaba masu shirin taurin kai irin nasa sai su kiyaye. Ba wannan ne abin damuwa bisa maƙasudin kiranka nan ba. Muna son ne ka maye gurbinsa a wancan case ɗin ne domin kwaso mana dukkan wasu bayanai da ya haɗa. Mun zaɓoka ne saboda kamaninku ɗaya, har yanzu kuma babu wanda yasan da shi bomb ɗin ya tashi. Kafin masu bincike su gama gano motarsa ce wadda bomb ɗin ya tashi a ciki muke bukatar ka kamla komai”.
“Amma ranka ya daɗe......”
Hannu ya ɗaga masa da sauri. “Karkace komai Barrister, nasan zafin rasashi kakeji, ina maka ta'aziyyar hakan. Sai dai ka sani, wanda ya ɓatar da shi kaima zai iya ɓaddaka kai da duk a halinka wannan yafi shan shayi sauƙi a garesa. Dan haka ka kula. Akwai saƙo na kafin alkalami a motar ka mu yini lafiya🙏”.
Hakan da yay na nufin ya sallamesa. Barrister Abdallah ya miƙe jiki a sanyaye. Gaba ɗaya tunaninsa ya rabu da zuciya da kwakwalwarsa. A yanzu kam ya gagara fahimtar komai gaskiya. Shin idan har waɗan nan ɗin sune mugaye a garesa, waɗan da kuma su yake bibiya a case ɗin su Babiy to sukuma waɗan da suka sakashi wannan aikin fa? Kenan fa kuɓutar da shi sukai a waccan ranar ko mi abinda sukai ɗin ke nufi? Ya ALLAH mike shirin faruwa da ni ni Abdallah?.
Ya tambayi kansa batare da yasan ina zai kama ba har ya ƙaraso jikin motarsa ya shiga. Da ƙyar ya iya tuƙin zuwa waje, yana hawa titi ɗan nesa da gidan aka dakatar da shi akan cewar yay parking ta cikin bluetooth ɗin kunnensa. Hakan ba karamin taimako bane a garesa, dan a yanda yake jinsa tabbas zai iya kife kansa a titin ma gaba ɗaya........
★★.... ★★.....
Babu kowa a ɗakin sai wani irin ƙamshi mai matuƙar saka jiki kasala da sanyin ac. Iffah ta lumshe manyan idanunta tana ambaton sunan ALLAH da sake buɗesu. (Kai kai kai duniya fa na inda take) ta ayyana a zuciya tana dire tray ɗin hannunta saman wani ɗan table dake gaban ƙyaƙyƙyawar kukera ta hutawa. (Dama ce fa wannan) ta zabura dalilin wancan furucin da zuciyarta ta ayyana. “Tabbas dama ce kam”. Ta maimaita a fili tana ɗan waige-waige a nutse cikin hikima kuma ɗan gudun kar ya zam akwai camara a ɗakin kamar yanda aka bazasu ta waje ko'ina a sashen. Adai iya dubanta babu kamar sauran ɗakunan data kwana, dan haka ta cire takalmanta cikin sanɗa ta nufi ƙofar toilet da zuciyarta ke raya mata yana ciki. Tabbas yana cikin kuwa dan jin motsin ruwa. Ta daga hannayenta sama alamar Alhamdullah sannan ta baro wajen. Da ma'ajiyar turarrukan sa ta fara, sai da ta gama ɗagasu ɗaya bayan ɗaya ta shinshina. Sam babu alamar irin wancan, cikin damuwa ta maida ta rufe badan zuciyarta ta wankesa da zargiba har yanzu. Dan ta gama haƙƙaƙewa aljanun tsafinsa ya tura suka ɗakkota a daren na jiya dan ya cika burinsa. Amma ALLAH ya hanashi sa'a shiyyasama taga ɗakin kaca-kaca kamar anyi dambe a cikinsa. Da alama sun gusar mata da hankaline shiyyasama bataji sanda aka ɗakkotan daga can ɗin ba.
Harta juya zata fita zuciyarta ta sake nata shawarar ta ɗan sake duddubawa ko zataga wani shaida da suke buƙata akansa. Cikin yanayin dai ɗan tsoro-tsoro na mara gaskiyar dake gudun a kamasa take ɗan buɗe-buɗen ta, sai dai abin mamaki idan ka cire turarrukan data gama dubawa, da wasu tarin books a