Showing 27001 words to 30000 words out of 41393 words

Chapter 10 - Mulki Ko Sarauta Book 1 Complete Hausa Novel

Nawarty   

01 Oct 2025

386

yi ba aiman, meyasa xaka yanke hukunci batare da sanin mu ba, kuskuren ka d'aya na sakin ilham yarima, me kake so iyayen ta su d'auke mu, wane irin kallo kake tunanin xasu mana, na aura ma mace tsawon wannan shekaru baka taba kula ta ba wane irin mutum ne kai, kasan haqqoqi da xamantakewar aure kuwa, kasan hukuncin namijin da ya danne haqqin matar sa idan kai baka neman haqqin ita bata so ne, kaci amanar da na baka aiman, ka kasa kulawa da abinda na d'auko daga wani gari na raba ta da iyayen ta na baka ita ka cutar da ita, baka yiwa Alhaji Ahmed adalci ba daya nema maka wannan yarinyar aka aura maka ita, mata nawa ne a duniyar nan ake raba su da iyayen su ayi masu aure irin naka kuma su xauna lafiya, yarinyar ta xauna tayi wa iyayen ta biyayya amma kai ka kasa mana biyayya?

Daddy kayi haquri, baka fahimce...

Shut up, baxan fahimce ka ba saboda bani da fahimta da hankalin da xan gane abinda ka aikata right.

Aiman ya xuba masa manyan idanuwan sa cikin tsoro da fargaba, ba haka nake nufi ba daddy am so sorry please.

Cikin fusata sarki yace please get out.

Aiman xai yi magana d'aya daga cikin dogari daga waje dake tsaye ya shigo da sauri ya durqusa tare da fad'in.

Ranka shi dad'e gimbiya afiya ce ta aiko tana so ayi mata ixini taga wannan matar da aka rufe a rumfar hukunta bayi.

Aiman ya dube sa cikin bacin rai, ka sanar da ita baa mata ixini ba.

Ni nayi mata ixini taje, je ka sanar da ita hakan, ya fad'a cikin bacin rai.

Godiya take ranka shi dad'e ya tashi ya fice da sauri, aiman ya maida duban sa ga sarki but daddy...

Get out nace ya qara katse sa, jiki a sanyaye ya tashi ya fita mahaifin sa bai taba masa irin haka ba kenan yayi laifi babba na rabuwa da ilham a gurin sarki bai sani ba, meyasa baxai fahimce sa ba, yayi shiru yana kallon yanda ake fito da kayan ilham d'in ana sakawa a mota, ashe saif d'in Ma ya xo yana ganin aiman ya nufe sa da sauri tare da miqa masa hannun sa na dama suka gaisa.

Nagode sosai Doctor bansan da wace irin kalma xan furta ma saboda farin ciki da wannan abin da kayi min ba, na roqi Allah ya saka ma da mafificin alkhairi akan abinda kayi.

Aiman yayi murmushi duk da yana cikin bacin rai bai yi magana ba ya xubawa afiya idanu da ta fito daga sashen ta bayi suna bayan ta, kallo d'aya tayi masu daga shi har saif ta d'auke kanta ta nufi sashen umma, tana shiga ta tarad? da ilham tare da umma,

Fuskar umma ta nuna tana cikin damuwa da alhini sosai tun lokacin da ilham taxo ta sanar da ita maganar xata tafi auren ta ya qare da aiman, haka ma afiya lokacin da taji abin taji wani iri though bata nuna ba sai ma ta fice daga sashen duk yanda ilham taso tayi magana da afiya bata sami fuska a wurin ta ba,

Suna tsaye ilham ta fito, ma'aikatan gidan da bayi duk sun mora mata baya sun mata rakiya, da yawa daga cikin su basu ji dad'in tafiyar ta ba, ilham tana da sauqin kai sosai a gidan bata taba samun matsala da kowa ba kamar yanda mai karatu ke tunanin ko ita d'in mafada'ciya ce.

Falon sarki ta nufa, kallo daya yayi mata yaji tausayin yarinyar sosai tana da haquri da biyayya, baa taba kawo masa qarar ilham cewa tayi wani abin ba dai dai ba kamar yanda ake kawo masa na afiya, tayi haquri boye sirrin ta dana mijin ta batare da ta sanar da kowa irin xaman da take da yarima ba, tabbas ilham ta cancanci lambar yabo a gurin sa, yayi mata kyauta ta musamman mai girma da tsoka sa'anan ya had'a ta da waziri da galadima domin suje gida da ita suyi bayanin abinda ke faruwa da dalili baxaa barta ita kad'ai taje gida da wani ba alhali da kansu suka aika aka d'auko masu ita bayan auren ta da yarima, ya bata haquri sosai tare da yi mata godiya, itama godiyar tayi ta fito.

Kallon aiman tayi Karo na biyu ta sakar mashi murmushi mai qayatarwa, tace nagode da dukkan abinda kayi min na alkhairi baxan manta da kai ba a rayuwa kuma duk wani laifi da kake ganin kayi min na yafe ma har abada.

Yace nima na yafe maki ilham ballantana Ma babu abinda kika min nine Ma nayi maki, ina qara roqon da ki yafe min, ya juya yana kallon Saif ga amanar qanwata ilham idan ka cutar da ita baxan taba yafe ma ba.

Saif yayi murmushi tare da fad'in na karbi wannan amanar da hannu biyu Doctor xanyi qoqarin kulawa da ita gwargwadon iyawa ta insha Allah.

Ilham ta juya ga mutanen da suka mata rakiya tayi masu godiya sosai tare da masu alkhairi itama, aiman da kansa ya bud'e mata motar ta shiga yana murmushi tare da fad'in your Highness ki shiga ki xauna.

Ta shiga motar tana hawaye bayan ta qarewa gidan kallo sosai, su waziri suka shiga tasu motar daban suna bayan su, aiman ya rufe motar tare da sunkuyawa ta glass ya dubi saif ya maida duban sa gare ta, you don't have to cry my dear, saif xai kawo ki watarana I know and again nima xaki ganni naxo maki, kafin Ma kixo ni xan fara xuwa daurin aure idan an gayyace ni.

Ta boye fuskar ta cikin jin nauyin sa ya matsa kad'an shima yana dariya tare da d'aga masu hannu har suka fice, da yawa bayi, fadawa da sauran mutanen dake harabar gidan xubawa aiman idanu suka yi cikin tsananin mamaki ashe yana dariya haka basu taba ganin dariyar sa, bai Ma san suna yi ba bai damu da su ba ya juya ya bar wurin yana jin duk ba dad'i, magen sa ta tafi ta bar sa sarkin son jiki Allah ya so sama da bai biye mata ba da yanxu mai afkuwa ta afku ina maganar sakin ta, baxai taba sakin ta ba komai halaccin saif a gare sa domin yana tsanani kishin wani yabi wannan hanyar da yabi koma ya kalle masa wurin.

Afiya tun da taga halin da nabila take ciki da yanda ta koma hankalinta ya tashi sosai, tsananin tausayi ya saka ta fashewa da kuka musamman da ta tuna ko wacece nabila, yar gayu amma itace a haka yanxu.

Nabila kuwa a xuciya da gangar jiki cike suke da tashin hankalin ganin yanda afiya ta koma kamar ba ita ba, ta xama qasaitacciyar mace mai kyau da aji not like before da take yarinya mai taqama da kud'i, wannan ganin da tayi wa afiya a yanxu ya tabbatar mata da har abada muddin aiman na ganin afiya baxai taba son ta ko kula da ita ba, baxata taba yarda aiman ya rayu da wata ya mace a duniya bayan ita ba da haka gwanda kowa ya rasa, tabbas ilham ba qaramin kyautawa kanta tayi ba da ta bar gidan dan yanxu labari yake xo mata na aiman ya saki ilham, dama xai saki afiya da ta barshi da rayuwar sa wanda take da tabbacin xai so ta tunda ya rasa afiya amma kashe tasan abu mai wahala ne wannan.

A fuska kuwa kuka ta fashe da shi tare da rungumo qafafun afiya tana roqon ta da tayi mata hanyar da xata fitar da ita a gidan tun da dama an rufe ta ne saboda batan ta yau gashi ta dawo cikin yan uwan ta itama tana so a fidda ta.

Babu kyama ko kyankyami afiya ta jawo ta tare da had'a ta da jikinta ta rungume.

Nice sila da wanna yanayin da kike ciki, da ban tafi ba da baa rufe ki anan kika wulaqanta ba, ki yafe min nabila kuma nayi maki alqawari a yau baxa ki qara kwana a wannan wurin ba.

Nabila ta d'ago tana kallon ta kafin tace baki da wani laifi anan afiya, nice na saka kaina a wannan wahala, soyayya ta janyo min wannan uquba nayi qarya akan ina da cikin aiman bayan ba haka bane nayi ne saboda a aura min shi ashe ban sani ba na jawa kaina babban kuskure a rayuwa.

Dama sharri kike masa nabila, afiya ta tambaya cikin mamaki.

Sharri ne nabila ta fad'a tana kuka.

Amma nima kin cuce ni kin cutar da tawa rayuwar na saka ni gujewa iyayena da kuma mijina akan laifin da bashi da masaniya akan sa, duk da baya sona da nuna min qauna hukuncin da na yanke akan sa bai cancance shi ba, meyasa kika yi haka, kin bata duk wata soyayyar aiman a xuciya ta ina masa kallo na d'an iska mazina ci, ina masa kallo na cin amana ta da yayi tare da ke ashe abin ba haka bane, gashi ta dalilina ya kasa xama da matar da aka aura masa, me kike so nayi a ynxu, abinda kika yi ya saka aiman ya so ki ko kuma ya aure ki, menene ribar abinda kika aikata a yanxu.

Tace babu riba afiya, every alley every crossroad I walked 2ru were all meant to lead me to this very place no matter what choices I made I could not avoid this fate, he imprisoned me in the room of eternity, dubi inda nake rayuwa, dubi a inda nake xama nake ci da sha da kwanciya duk gatana da kud'in mahaifina, so laifi ne?

Afiya ta girgixa kanta ba laifi bane amma kaso a soka shine so, na roqe ki da kibar min mijina haka, ki fita rayuwar mu ki manta da aiman da duk wani abu daya shafe sa, xan yi magana da sarki yau a fitar dake daga nan amma daga wannan rana ina qara roqon ki da ki nesanta kanki da mijina, shi kad'ai nake so, shine komai nawa, shine na fara so, xan iya xama dashi na cigaba da rayuwa da shi koda baya sona matuqar baxai qara kula kowacce irin mace bace, kin shigo rayuwar mu kin tarwatsa ta a lokacin da wanxuwar farin cikin xuwan sultan ta shigo, yanxu Ma ina qara roqon ki da ki kwance duk wata niya ko nufi akan mijina ki barshi har abada, ta juya ta fice da sauri batare da ta saurare ta ba, bayin dake tare da ita suka mora mata baya.

Murmushi nabila tayi ta bita da idanu, na bar miki aiman, ashe afiya bata da hankali taya take tunanin nayi wad'annan shekarun a kurkuku su tashi a tutar banxa xamu rasa aiman daga ni har ke.

People always say that love is painful but I have realized that goodbye are even more painful, good bye to our beloved Dr Aiman Merah....... ta fad'a cikin qasaitaccen murmushi.
[2/23, 2:31 PM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Bayan an yi mata iso ga sarki ta shiga, nesa dashi ta xauna kad'an had'e da sunkuyar da kanta.

Barka da yini ta fad'a a hankali bayan ta d'ago tana kallon sa, bai amsa gaisuwar ba maganar da ya jefo ta da ita ne ta saka ta raxana.

Kin saka aiman rabuwa da ilham burin ki ya cika ko.

Ta dafe qirjinta tare da bud'e idanuwan ta tana kallon sa cikin tsananin tsoro,

Taya xan saka shi rabuwa da matar sa bayan tare naxo na same sub, ta dafe kanta cikin rudani jikinta har rawa yake, ko da nayi magana baxan xauna dashi da wata mace ba ina nufin anan gidan ya kaini wani gida daddy amma ni ban saka shi rabuwa da matar sa ba hassalima a gurin umma na fara ji suna maganar da ita.

Sarki yace meyasa tuntuni da baya son ta baiyi yunqurin raba auren ba sai bayan dawowar ki, itama mace ce kamar ki tana da xuciya kamar kowacce mace, sannan itama ya'ce kamar ki, iyayen ta baxa su ji dad'i ba saboda babu mai son mutuwar auren y'ar sa, menene laifin ilham a gurin aiman, bata ganshi tace tana so ba mune muka nema masa ita muka aura masa bata son sa baya son ta, aiman ya san policy na gidan nan game da sakin ilham shiyasa har ya yanke hukunci batare da sanin mu, tabbas xai fuskanci baci rai daga gare ni.

Afiya ta fashe da kuka sosai sanin halin sarki da gaske xai iya hukunta yarima tun da ya fad'a, tace daddy dan Allah kayi haquri yaya aiman yayi laifi amma inaji yayi hakan ne saboda saifullah, saif ya cancanci komai daga wurin aiman saboda shi mutum ne mai karamci, yana da kirki sannan ilham budurwar sa ce yana son ta tana son sa, (ta kwashe komai game da xaman ta da saif da ilham wanda ta sani ta gaya masa), daddy kada ka hukunta shi akan alherin daya aikata pls.

Sarki yayi shiru bai yi magana ba, ta share hawayen fuskarta kanta a sunkuye, As I lived my life I had realized how life can be so unpredictable and how control is just an illusion, babban kuskurena na tafiya batare da sanin ku ba har na tsawon wannan lokacin amma nayi nadama dan Allah daddy ka yafe min.

Still bai yi magana ba illa idanu daya xuba mata hakan ya qara bata damar sake neman alfarma a saki nabila.

Sarki ya saka aka kira mahaifin nabila, bai xo ba sai a washe garin ranar jin sarki ya saki nabila daga xaman kurkuku da take a gidan ya saka abbu tsananin farin ciki sai dai nabila taje da wata buqata cewa tana so a bar ta tayi kwana biyu a gidan ta warware sosai kafin taje gida saboda yanda kamannin ta suka canxa baxata so taje gida a hakan ba.

Abbu ya qara nema mata wannan alfarmar a gurin sarki saboda plan d'in da suke had'awa dole sai ta xauna a gidan.

Sarki ya bada umarnin a kula da nabila na tsawon kwana biyu tare da bata jin dad'i na more rayuwa ko wane iri take so.

Nabila tace ina so na xauna tare da afiya a gidan ta na tsawon wannan kwana biyu d'in.

Afiya tayi murmushi tana kallon ta, a gidana babu gurin sauke baqi irin ku nabila, sarki xai baki wurin xama ko da sashen ilham ne amma ba sashen afiya ba.

Sarki ya jinjina kai yace hakane, akwai wurare da dama a gidan nan xan saka akai ki sai ki xabi duk inda kike so ki xauna kafin ki tafi.

Nabila bata so hakan ba da kyar ta bud'e baki tace ranka shi dad'e a barni a sashen ilham d'in.

Abinda ke faruwa aiman baida masaniya akai domin yana cikin tsananin damuwa tun jiya da ilham ta bar gidan sarki ya canxa mashi, gaisuwar da yaje ya mishi da safe ya hana a barshi ya shiga ya gansa wanda hakan na nuni da sarki na matuqar fushi dashi idan har baya son ganin sa, ya dafe kansa yana kallon mahaifiyar sa kamar yayi kuka saboda tsananin damuwa, mahaifin sa bai taba irin wannan fushin dashi ba shi ke qara saka shi damuwa.

Umma kije ki bashi haquri ni xan maida aure na da ilham gobe xanje katsina.

Ta dafa kansa tana kallon sa, maganar dawo da ilham bashi ne mafita ba, meyasa koda yaushe kake qoqarin yin abu mai girma batare da shawartar iyaye ba yarima, mai martaba sam bai ji dad'in wannan abin ba saboda girma da mutunci na iyayen yarinyar yanxu wane irin kallo kake so suyi masa a matsayin sa na sarki.

Nayi kuskure but ya kamata daddy ya fahimce ni umma, meyasa yake irin wannan fushin dani da ko gani na baya son yi balle gaisuwa ta.

Ta miqa masa tea cup dake hannun ta tare da fad'in xan yi magana dashi xuwa anjima, xama da damuwa ga yunwa bana so yarima maxa ka sha ko tea ne kawai, batare da gardama ba ya karba ya tashi yayi d'akin ta jiki a sanyaye kamar ba shi ba.

They say fear is just an illusion but why is it that this fear of mine wasn't just an illusion it was the creator of all my illusions ya fad'a a hankali bayan ya xauna bakin gadon tare da ajiye tea d'in batare da yasha ba, meyasa yanxu abubuwa suke canxa mishi, meyasa damuwa yanxu take riskar sa, meyasa yanxu gata da tarairaya daya ke samu a wurin mahaifin sa ya daina masa a yanxu, meyasa yake damuwa da macen da bata damu dashi ba, duk me ya janyo hakan?

Abbu ya dubi nabila bayan sun fito kiyi qoqari ki shiga jikin afiya sosai yanda xata sake dake acikin kwana biyun nan kina shiga sashen ta, da hakan buqatar mu xata biya.

Nabila tayi murmushi shikenan abbu amma maganar mummy yaushe xaka maida ta, ya bata fuska tare da fad'in saki biyu nayi mata saboda tana yunqurin tona mana asiri akan abinda taji muna fada a waya na kashe wannan yaron, har kuka take tana min Allah ya isa na kasancewa mijin ta, idan bata had'a hannu dan farin cikin y'ar ta ba menene amfanin xama da ita.

Nabila ta jinjina kanta, mummy kamar ba itace ta haife ni ba abbu.

Yace manta da ita kawai taje tayi ta xawarci a gidan su, mu xamu more rayuwar mu yanda muke so batare da takura ba.

Nabila tayi dariya sosai.

Mami take me to my daddy, ta juya tana kallon sa tare da fad'in har cikin toilet xaka biyo ni da motar kenan?

Ya fita daga cikin motar ya nufe ta, mami take me to my daddy.

Tace kai baka san hanyar xuwa wajen sa ba, ya make kafada I don't want to see that bodyguards they look ugly suna bani tsoro and they don't smile.

Tam ina ruwan ka dasu, dole sai ka kalle su.

Ya soma buga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login