Showing 3001 words to 6000 words out of 41393 words

Chapter 2 - Mulki Ko Sarauta Book 1 Complete Hausa Novel

Nawarty   

01 Oct 2025

390

dafe kanta oh Allah wai me afiya take nufi damu iyayen ta ne haka sai yaushe xata dawo gare mu, tace ka sanar da sarki? Aiman ya girgixa kansa, tace to ka sanar dashi yanxu amma afiya ce ta koma haka lallai duniya tayi wa afiya dad'i dole baxata nemi ta dawo? gida ba.

Abba da sarki sun yi mamakin jin wannan batun, afiya tana Jordan kenan da gaske bata son dawowa cikin su shiyasa har bata son su san da inda take.

Aiman kam ya damu ranar da kyar yayi barci wanda ya rasa dalili akai akai yake janyo wayar yana kallon pics d'in afiya, sosai ta canxa tayi kyau tayi jiki kad'an ba kamar da da bata da jiki ba, fatar jikinta ta qara haske da sheqi ya qagu yaji hukuncin sarki na cewa yaje da kansa Jordan neman afiya duk da bai san ta inda xai fara ba amma yana da yaqinin xai gan ta.

Washe gari pics d'in ya saka gaban sa yana kallo, babu xato babu tsammanin sai ya tsinci kansa a mai sumbatar pic d'in tare da lumshe idanuwan sa.

Ilham dake shigowa falon ta ja turus ta tsaya a gabansa cikin mamakin menene aiman yake wa kiss a waya, ko dai.. ko dai... sai kuma tayi saurin basar da xancen xuciyar ta tare da gyaran murya a hankali domin aiman ya ankara da xuwan ta.

A hankali ya bud'e idanuwan sa yana kallon ta, idanun ta suka sauka akan hoton kyakkyawar macen dake kan screen d'in wayar, hankalin ta ya tashi gaban ta ya fad'i wannan kamar matar wayar can da ta taba gani tare da wani yaro da cake, me ya had'a mijin ta da hoton ta dubi aiman dake kallon ta qasa qasa.

Tace yarima wacece wannan da har kake sumbatar ta, menene alaqar ka da ita, ka san ta kuwa.

Kai tsaye yace da ita Afiya ce matar Aiman menene laifi aciki dan na sumbaci matata?

Bugun xuciyar ta ya tsananta ta qare ware idanun ta sosai akan hoton tabbas afiya ce cos tana ganin hotunan ta manne a bangon falon umma da aiman amma kwata kwata anan ta canxa kamar ba ita ba ta qara kyau da waye wa kallo daya xaka mata kasan hutu ya xauna a jikin ta dole ta canxa bata tare da damuwa, nan take wani baqin ciki da kishi suka taso suka toshe xuciyar ta har bata san sanda ta xauna akan sofa tare da jan numfashi mai nauyi ba.

Aiman ya dube ta tare da fad'in ki tayani da addu'a afiya ta yarda ta biyo ni mu dawo tare, xan kula da ita tare da bata jin dad'in da ta rasa a baya, yanxu a shirye nake dana dauwamar da ita cikin wannan farin ciki batare da wulaqanci ba ko da bana son ta tabbas afiya tana da matsayi mai girma sosai wanda baxan iya misalta shi ba.

Duk maganganun da yake sosai suke qona xuciyar ta wai namijin da ta mutu kan sa yau shi yake gaya mata yanda ya damu da wata banxar mace can daban, ashe kuwa xaa yi ta duk ranar da afiya ta dawo gidan dan baxata yarda da wannan wulaqancin da toxarcin ba.

Amma ni menene matsayina a gidan nan yarima, ko sau d'aya ban taba jin ka kira ni da matar ka ko matar gidan ba, dan Allah bana baka tausayi tsawon shekara biyu d'innan da nayi ina haqurin xama da kai.

Yace what? ni kike haqurin xama dani, an aura min ke ban gani nace ina so ba, nayi biyayyar xama dake ni bance ina haquri dake ba? amma kike gayamin maganar kina haqurin xama dani..... tayi saurin katse sa jikin ta na rawa ba haka nake nufi ba mijina ka fahimce ni dan Allah kayi haquri ta fada tana russunawa qasa cikin roqon sa, ni nasan ban isa ka so ni ko ka kula dani ba but atleast ina da haqqi akan ka fa.

Bai qara magana ba gani yake yarinyar ta soma raina masa da wayo banda iskanci ita me ta taba yi masa na haqqin aure, girki, gyaran sashen sa ko kula da shi me ta taba yi bata da xance sai haqqin aure jarababbiya abinda kike nema a gurina baxaki samu ba, yaja qaramin tsaki yana fad'in get out pls bana son damuwa kin soma bani headache.

Batare da damuwa ba ta tashi ta fice ya bita da kallo mace har mace amma ita ke roqona haqqin ta anya yarinyar nan qalau take kuwa yanda kanta yake rawa haka, wani tunani ya shige sa wanda ya san baya kyautawa tabbas tayi haqurin xama da shi wulaqanci da rashin mutunci babu wanda bai mata ba ko afiya yayi Ma hakan amma bata taba magana ko complain ba sai dai tayi ta kallon sa da abin ko kuma ta gayawa Bilal shi yayi masa magana, ga ilham duk abinda yake mata bata da wanda xata gayama sai dai ta tunkare shi da maganar haka kuma bata taba yunqurin sanar da iyayen sa ko wani d'an uwanta halin da take ciki a gidan auren ta ba.

Meke damun rayuwa ta, ilham ta cancanci ya bata kulawa ko da baxai so ta ba kamar yanda bai so afiya ba, xai bata matsayi kad'an? a matsayin ta na matar sa domin kare mutuncin ta ga sauran mutanen gida haka kuma yana tunanin rashin kulawar ilham gare sa yana da nasa ba ne daga yanda baya sake mata fuska, idan ya mutu me xai gayawa Allah akan haqqin da bai sauke na y'ar mutane ba bayan bata da laifi ko kad'an a auren kamar yanda aka masa dole ita Ma dole aka mata dan ba ganin sa tayi tace tana so ba sai bayan an bayyanar dashi gare ta ne ta furta tana son sa, menene xafi da rad'ad'in so?

Sosai jikin sa yayi sanyi yaji a ranar yana son sauke wannan nauyin dake kansa kwata kwata ya manta da xancen afiya, kai tsaye ya tura kiran jekadiya duk da maganar da nauyi hakan bai hana masa daure fuska ba tare da fad'in a shirya ilham yau xuwa turakar sa.

Wani murmushi mai bayyane da farin ciki ya bayyana a tare da jakadiya abinda suka dad'e suna jira kenan duk da har yau bayan jekadiya da su maauratan babu wanda ya san har lokacin aiman bai taba saduwa da matar sa ba.

Ya qara da cewa bana son kowa ya san da xancen xuwan ilham d'in ki riqe wannan sirrin.

Insha Allah ranka shi dad'e, gimbiya ilham godiya take sai mun xo ta tashi ta fice cikin tsananin farin ciki saboda tasan idan har ilham ta kawo budurcin ta xaa mata babbar kyauta a fadar dan ko na afiya da baa qasar aka gudanar dashi ba bata taba mantawa sai da ya kira ta ya bata kyautar wani xoben xinari, kome xata samu a wannan karon?

Ba qaramin farin ciki ilham tayi da jin xancen da jakadiya taxo mata dashi ba, nan take tayiwa jakadiya kyautar manya manyan lace guda biyu masu kyau da tsada, innalillahi ta kasa boye farin cikin ta a wannan lokacin yau xata kwanta tare da yarima a qirjinsa, wannan lips d'in nasa xata jisu a bakin ta abinda ta dad'e tana kwadayin samu, his soft hands on her body ta rumtse idanun ta cikin matsinancin kunya kamar yana gaban ta a wurin.

Daren ranar jakadiya ta rakata har falon aiman sai qamshi mai dad'i da sanyi take xubawa ta kowacce kusurwa ta jikin ta, bakin qofar d'akin nasa jakadiya ta kaita kafin ta juya ta bar sashen gabaki d'aya.

Ta dad'e tsaye a qofar d'akin bata shiga ba kafin ta rumtse idanun ta tayi addu'a tare da murza qofar d'akin ta shiga tare da sallama.

Wani sanyi da qamshi suka xiyarci hancin ta, ta lumshe idanun ta kad'an ta bud'e tana kallon aiman dake xaune akan gadon sa idanun sa akan wayar nan ta d'axu ya d'ago a hankali suka had'a ido, kallon ta yayi qasa da sama kamar baxai yi magana ya amsa sallamar.

Ta tako a hankali cikin takun ta na d'aukar hankali ganin irin kallon da yake mata, alkyabbar dake jikinta ta cire a hankali kayan barcin ta suka bayyana.

Ya kasa d'auke idanun sa akan kyakkyawar surar ta dake rikida tana koma masa tamkar afiya ce tsaye a gabansa har bai san sanda ya fisgota ta fado jikinsa tare da kwantar da ita akan luntsumemen gadon sa bayan ya rage hasken d'akin.

Ya kai tsinin hancin sa dai dai wuyanta yana shaqar qamshin jikinta wanda nan take ta soma jin wani iri a jikin ta tare da kai hannun ta gadon bayan sa ta rungumesa tsam kamar xaa kwace mata shi....
[2/7, 3:26 AM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

A hankali ya janye jikinsa daga nata tare da dafe kansa da yake jin yana juya masa, baxai iya ba baxai iya aikata wannan ba idan ba da afiya ba, baxai iya bari wata macen ta san sirrin shi ko jin yanda yake ba bayan afiya beside Ma ilham baya jin xai so ta ko kuma cigaba da xama da ita duk da yana cikin wani yanayi na buqata a yanxu amma dole xai haqura, ya sauka daga bed d'in ya nufi toilet batare da ya qara waiwayen ta ba.

Ilham kuwa da kallo ta bisa har lokacin da ya shige toile ta kasa gane me hakan ke nufi da yayi, sai da ya gama tado mata da tsumi ya gama jagula ta sannan xai tashi ya bar jikin ta batare da buqata ta biya ba wallahi bai isa ba, kamar ta fashe da kuka haka take ji.

Fiye da minti talatin da shigar sa sai gashi ya fito d'aure da towel alamar wanka yayi kenan, ya qara hasken d'akin suka had'a ido da ita da kyar yace kallon na menene.

Tace kai xan yiwa wannan tambayar meyasa ka tashi.

Yayi Jim kad'an kafin yace na tabbata akan ki kenan, ta sunkuyar da kanta qasa tana fad'in ba haka nake nufi ba amma kasan yau ne daren mu na farko.

Yayi mata kurr da ido cikin mamakin rashin ta ido irin na yarinyar, ko ta san kan abin ne take zaquwa haka, ya tambayi kansa sam sai yaji bai yarda da ita ba, ina baxai qara iya rabar jikin ta ba cos bai san iya adadin mutanen da tayi huld'a da su ba, ya gama shirin barcin sa ya raba ta gefen ta ya kwanta bayan ya shige lallausan duvet d'in sa.

Cikin baqin ciki da takaici ta sauka daga gadon, alkyabbar ta kawai ta saka ta lullube jikin ta da kyau ta fice daga sashen gaba ki d'aya, ranar tayi kuka sosai iya ranta har tana ganin babu amfanin auren nata, ita mace ce mai lafiya dole tana da buqata duk da bata taba tsintar kanta aciki ba amma a yau yanda aiman ya tafiyar da ita ya jefata wani hali, ya tafi wata duniya da ita wadda batayi tunanin dawowar ta ba, meyasa xai mata haka?

Washe garin ranar sai ga jakadiya taxo sashen ilham, bayan gaishe gaishe ta qara russunar da kanta tare da fad'in ranki shi dad'e yanxu na fito sashen yarima shine ya sanar dani kin dawo sashen ki.

Cikin fad'uwar gaba ta dubi jakadiya tana sauraren me xai fito bakin ta idan aiman d'in ba sanar da ita wulaqancin da yayi mata yayi ba.

Yarima ya sanar dani al'adar mu ta mata ce taxo maki, sam abin bai min dad'i.

Ilham ta lumshe idanu a hankali tare da sauke ajiyar xuciya.

Jakadiya tace amma gimbiya yaushe ne abin yake tafiya ina nufin kwana nawa ne.

Da kyar tace kwana biyar ne.

Allah ya nuna mana lokacin, jakadiya ta fad'a.

*

Qila tare fa xamu je Nigeria d'innan, na gama komai a qasar Portugal na karbi duka abinda nake so bani da wani sauran xama acan dama saboda ke na dawo kuma gashi kin balaguro kin dawo Jordan.

Afiya tayi murmushi tana fad'in insha Allah cikin satin nan xamu je, ni saboda karatun sultan ma.

Yace haka ne idan muka sauka Nigeria a abuja d'in xan wuce katsina ba sai na tsaya raka ki gida ba.

Murmushi ta qara yi tace nayi xaton xaka bini muje tare har gida ne sai na gabatar da kai matsayin wanda nake so a yanxu.

Yace rufa min asiri afiya kada nayi xaman rumfar hukunta bayi, ina ni ina jayayya da Dr Aiman.

Dariya tayi tare da fad'in ra'ayina xaa tambaya kuma xan fad'a, baxan cigaba da xama da mutumin da bai san daraja ta baya sona ba, dama sultan ne qaddarar auren, anyi min dole a auren farko yanxu kuwa babu wanda xai tilasta min xama da yarima, bana son shi a yanxu saif.

Saif ya ja numfashi a hankali tare da fad'in Allah ya xaba mana mafi alkhairi.

Sultan ya kwanta jikinta yana fad'in Mami ki kaini inda suzana ni bana son wannan gidan.

Tam shikenan very soon xamu barshi muje inda suzana tun da kafi son can.

Kuma mami xaki kaini asibiti inda New friend d'ina.

Lol, sultan xaka gaji da wannan friend d'in naka very soon cos you will be with him har abada.

*

Daddy kamar yanda muka yi magana jiya yau xanje Jordan nemo afiya.

Sarki yace tare da Alhaji Ahmed xaku je munyi magana dashi saboda babu ta yanda afiya xata yarda ta biyo ka.

Yace haka ne daddy nima nasani bani da wannan daraja yanxu a wurin ta.

Yace amma yarima yanxu kana son afiya kuwa?

Ya dubi mahaifin nasa yayi Jim kafin ya bud'e baki da kyar yace har yanxu ban sani ba daddy na san na damu da ita a yanxu amma wannan son har yanxu bana jin feelings d'in shi ban san ta yanda xan gane ba, pray for me.

Sarki ya jinjina kansa ya rasa meke damun aiman kamar wani mai aljannu, idan ya dawo daga tafiyar xai saka a duba sa idan ba aljana take auren sa tana hana masa son ko wacce mace ba.

Aiman da Abba a tare suka xo qasar Jordan a kullum cikin bincike suke suna raba hannu wajen neman afiya.

Kwanan su biyu a qasar babu ta babu labarin ta, duk girman kai da ajin aiman ya ajiye sa a gefe da kansa yake fita yawon neman ta ya dawo a gajiye cike da bacin rai wahalar da bai taba tunanin xai yi ba.

Ranar kamar baxai fita ba sai kuwa ya had'u da saif mutumin da baxai manta fuskar sa ba a ko ina ne duk da bai san sunan sa ba.

Saif bai san aiman na biye da shi ba har suka xo hotel d'in da afiya take xaune, yanayin parking aiman ya tsayar da mai taxi d'in dake driving d'in sa, har xai fito ya tunkare sa yayi masa magana sai kuma ya ganshi ya fito riqe da hannun sultan, ya tuna shine dalilin daya saka afiya gujewa Portugal bayan yaje ya sanar da ita ya ganshi, hakan ya saka yaji baya son ya ganshi, ya riqa binsa a baya har suka shiga hotel d'in sai surutun sultan yake ji wanda yake yiwa saifullah d'in.

Yana ganin d'akin da suka shiga ya dawo cikin mota ya shiga ya xauna, xuciyarsa cunkushe ya rasa dalilin daya sa yake jin tayi masa nauyi dalilin wannan saif d'in ne kome, mecece alaqar afiya da wannan qaton dake yawo da d'ansa kuma yake xuwa yana samun ta a masaukin ta, wace irin shaquwa ko sabo ne tsakanin su Anya afiya bata manta da maganar auren sa a kanta ba da ta xabi tayi rayuwa da wani qaton banxa fiye dashi? Idanun sa suka yi jawur.

Mami munje yawo da uncle mun sha ice cream ashe garin yana da kyau haka.

Tayi murmushi tana fad'in yanxu kenan babu maganar komawa Portugal ko.

Yace aa mami xamu koma ni bana son wannan qasar, bana so kina min wanka nafi son na suzana.

Tam shikenan ashe xamu d'auki suzana muje da ita gida Nigeria saboda ta riqa yima wanka ko.

Ina ne Nigeria mami?

Nigeria qasar mu ce sultan, nan mun xo muna xama ne kawai amma yanxu xamu koma xaka ji dad'in ta fiye da nan qasar.

Ya shagwabe fuska tare da make kafada, ni baxan je ba ki barni inda uncle kiyi tafiyar ki.

Saifullah ya soma dariya, tace don't you know baban ka yana can Nigeria baka son ganin sa ne kamar ko yaushe da kake maganar sa, grannies are all there waiting for their beloved grandson, kasan gata da jin dad'i dake jiran ka acan kuwa?

Mami ni bana so let daddy come here ki kira sa.

Tace tam shikenan, uncle saif ai kai kam baxaka xauna qasar da ba taka ba ko, xaka je gida ka sami mummy and daddy su saka ka a school, a siya ma ball, ya kai ka skul, buying luxuries kayan wasa, ga horses a gida.

Saifullah ya gyad'a kansa tare da fad'in kuma xai kaini wurin wasa nayi New friends etc

Sultan ya riqa hannunta a sanyaye tare da fad'in mami nima daddy na xai siyamin horse na hau akai.

Ta gyad'a kai tana fad'in daddy yana da horses masu yawa idan xaka je gun sa xai saka kullum a d'ora ka akai.

Yaji dad'i sosai, saif ya tashi yayi mata sallama xai tafi akan gobe xai dawo suyi maganar komawar? su Nigeria.

Bayan ya fice ta dubi sultan tana fad'in only game banda barna xan shiga wanka na fito yanxu, idan kaji anyi knocking don't open kaji ko.

Ya gyad'a kansa, ta qara maimaita mishi kafin ta shiga wanka.

Aiman na xaune a mota ya ga fitowar saif, sai da ya tabbatar ya bar hotel d'in kafin ya fita daga motar ya nufi cikin hotel har d'akin da afiya take.

Knocking yayi a hankali kamar wanda aka masa dole.

Sultan dake xaune gaban computer yana game yaji yaqi kulawa saboda gargadin afiya.

Knocking aiman ya qara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login