Showing 15001 words to 18000 words out of 41393 words

Chapter 6 - Mulki Ko Sarauta Book 1 Complete Hausa Novel

Nawarty   

01 Oct 2025

382

auri saif xan fi samun kwanciyar hankali da jin nima mace ce a gurin sa, xanfi jin dad'in aure a gurin sa fiye da kai.

Tell me afiya me yake tayar da hankalin ki a gidan nan, waye yake hana miki kwanciyar hankali na raba shi da rayuwar ki.

Ta fashe da kuka tare da fad'in kaine aiman dan allah ka bar rayuwa ta ka barni haka, shima yaji kamar yayi kukan saboda xafin kukan nata da yake ji a xuciyar sa, ta tashi da sauri xata bar d'akin yayi saurin riqo ta.

Xan saki ilham a yau koma yanxu just to make you happy afiya, ban taba son ta ba, bana mata kallo a matsayin matata ke kad'ai ce matar aiman ki daina tunanin akwai wani abu da xai raba mu a yanxu bayan mutuwa.

Tace babu ruwana a maganar auren ka aiman, ta fisge hannun ta tare da barin d'akin umma na xaune falon taga fitowar afiya tana kuka dama ta san sai anyi haka yanda afiya ta tsani mace ta rabi aiman haka ta tsani mutuwar ta tunda har xata iya barin qasa saboda mace menene baxata iya ba akan kishi, sai dai ita sam bata ganin laifin afiya dan ta nuna wannan kishi da so ga d'an ta.

Afiya na barin sashen ta nufi nata sashen ta rufe kanta aciki.
[2/14, 10:12 PM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Mami.. Mami... Sultan ya soma kiran sunan ta bayan ya tashi daga barci, ya bud'e idanun sa yana kallon d'akin babu ta, Mami ya qara kiran sunan ta yana qoqarin yin kuka, aiman ya bud'e masa hannuwan sa sultan ya rarrafa a hankali ya isa gare sa.

Friend Take me to mami, ina mami na taje?

Am not your friend, aiman ya fad'a yana had'a goshin sa dana yaron, call me daddy.

You are not my father ya fad'a a hankali kamar yanda yaga aiman d'in na magana, mami tace my father is a doctor ya iya allura, yana da horses kuma yana can Nigeria, yana da big mansion.

Aiman ya sumbace sa tare da fad'in bata gayama you are a prince ba, bata gayama.... Sultan ya katse sa tare da fad'in am not a Prince, my father is a doctor not king.

Aiman ya tabe bakin sa, ya tashi d'auke da shi sultan d'in ya qanqame sa, yana jin yaron fiye da kowa da komai a rayuwar sa, suna fitowa umma ta dube sa, wai jakadiya ake sanar dani yanxu tun jiya take kuka kuma taqi magana.

Ya dube ta kafin yace kukan me kuma umma, ko dai wani abu ne ta bangaren yan uwan ta.

Na tura wata baiwa ita nake jira shiru har yanxu tukunna idan Ma matsalar daga gida ne ai ba zama xata yi tana kuka ba, jakadiya ta wuce wannan yanxu.

Aiman yace umma kuka bashi da yaro ko babba ko tsoho, kuka yana xuwa ne domin samun sauqin damuwa dake tare da xuciya, wani xaki ganshi cikin hali na baqin ciki yana so yayi kukan domin ya sami sassauci a xuciya amma kukan sai yaqi xuwa, a barta tayi kukan idan xata ji sauqin damuwa daga baya sai a tambaye ta dalili.

Umma tayi shiru cikin tunani, aiman ya nunawa sultan umma yana fad'in grandma, father's mother, Sultan ya dube ta kafin ya dubi aiman but she is not old to be a granny, umma tayi dariya aiman ma murmushi yayi tare da jan hancin sultan wato kana so kaga umma tsohuwa, murmushi sultan yayi.

Sanda aiman ya gabatar masa da sarki bud'e baki sultan yayi lah shi sarki ne, aiman ya gyad'a kansa, yace ina babana I want to see him, aiman ya ja hancinsa baka ji abinda na gayama d'axu ba, ni ba friend d'in ka bane ni mahaifin ka ne call me daddy, sultan ya sauka daga jikinsa ya nufi sarki yana fad'in granny wai friend ya xama daddy na a yanxu, sarki ya gyad'a masa kansa.

Sultan yace what about uncle saif shima kaine baban sa kuma kaine baban mami?

Nan da nan annurin fuskar aiman ya canxa jin ya ambaci saif, bai amsa masa ba ya riqa hannun sa suka fice daga falon sarki, kai tsaye daga nan mota suka shiga ya nufi gidan su afiya da shi, ammi tayi tsananin farin ciki da ganin sultan jikanta yaron da autar ta afiya ta haifa, sai ta rasa inda xata saka shi saboda tsananin farin ciki.

Sun dad'e suna xagaya yan uwa yana gayamasu matsayin su duk da yasan ba lallai bane ya iya riqewa da sannu dai, sanda suka had'u da fu'ad yaron rumaisa sai da suka yi rigima dan fu'ad yaqi bari ko kad'an sultan d'in ya taba masa kayan wasa ko da ball d'in sa.

Sultan sai kuka yake akan sai an basa keke ya hau fu'ad duk ya tattara ya hana harda motocin sa ma, duk yanda Aliyu yayi akan ya arawa d'an uwansa kayan ya qanqame ya hana, rumaisa na qoqarin karbe masa keke da qarfi aiman ya hana ta tare da tashi da sultan a jikinsa ya soma qoqarin saukowa.

Yace bana son rigima sultan xo muje kaima yau xaa siya maka naka, cikin kuka sultan yace bana so ni wannan nake so, fu'ad kuwa ajiye kayan yayi yaxo da gudu inda aiman yana fad'in daddy nima xaka siya min wasu New ones bana son wannan a bashi ya fada yana nuna sultan d'in.

Sultan na jin fu'ad ya kira aiman da daddy ya qara yarda sunan friend d'in sa daddy ne, sai ya daina kiciniyar saukowa ya qara qanqame aiman yana fad'in bana so nima sabo nake so daddy.

Aiman ya dube sa jin ya ambace sa da sunan daddy, ya shafi sumar kansa yana murmushi kafin ya dubi fu'ad yace tam shikenan wait for me yanxu xan dawo.

Aliyu yace ashe baka da kunya fu'ad, to baxaa siya ma ba.

Aiman murmushi kawai yayi ya fice aliyu da rumaisa suka bi bayan sa, yana fitowa harabar gidan mutanen sa na tsaye suna jiran sa suna ganin sa suka bud'e mota? bayan aiman ya shiga motar rumaisa ta sunkuya tana kallon sa.

Yaya ka kawo sultan amma banda afiya yaushe xaka kawo ta.

Ya qago murmushin yaqe yace kamar yanda kika ganni da sultan yau haka itama xaki ganmu tare mun xo.

Tayi murmushi cikin jin dad'i ganin bai gwale ta ko sakar mata magana mai xafi ba a yau, tace tam yaya ina gaidata kafin naxo.

Bai amsa mata ba yayi wa Aliyu hannu kana ya d'aga glass d'in motar a xuciyar sa fad'i yake how I wish xan ganni tare da afiya cikin jin dad'i kamar aliyu da qanwata, menene matsala ta da afiya ta kasa yarda da dani ko kuma saboda ilham ne?

Basu koma gida ba sai da suka biya shopping, siyayya sosai yayi wa sultan tun daga kayan sakawa, ci da wasa kamar xaa bud'a shago.

Sultan sai murna yake daddy ya siyamin daddy ya siyamin, duk inda aiman ya jefa qafar sa yana biye dashi aiman kuwa ba qaramin jin dad'in hakan yake ba yanda yaron ya yarda dashi sosai, shaquwa ta musamman ce ta shiga tsakanin d'a da uba, baa taba siya masa kaya haka kamar yanda aiman ya siya masa ba hassalima kayan wasan sa acan duk bai wuce ball da bindiga da uncle saif ya siya masa ba, amma anan babu abinda mahaifin nasa bai jido masa ba sai wanda bai gani ba, nan take ya bada umarni acikin gidan a ware wa sultan wurin wasa a gyara shi tare da xuba masa motocin sa, mashin da keke da jiragen daya siya masa, ya bada umarni a saka lilo na wasan yara kala kala a wurin, wad'annan abubuwan suka qara mantar da sultan ga kukan su koma Portugal kwata kwata ya manta Ma da afiya ko tunanin ta baya yi, sauran kayan aka fara shiga dasu sashen afiya duka ilham tana tsaye harabar gidan tana kallon sabon al'amari, ba wannan ba kayan menene aka shiga dasu sashen afiya batare da ita an shiga da nata ba, me aiman ke nufi ko ya manta itama cewa matar sa ce tana da haqqin akan duk abinda ya siyawa afiya dole itama ya siya mata.

Afiya na xaune tana waya da ammi wanda da kyar ta samu ta d'auka tayi kuka tayi roqo amma ammi taqi sauraren ta sai ma kashe wayar da tayi, tana tsakar da share hawayen nata aka soma shigowa da kayan tsakiyar falon ta sai kuma sultan daya shigo da gudu yana kiran sunan ta, ya fad'a jikin ta tare da fad'in mami ni baxan koma Portugal ba ke kad'ai xaki je, friend d'ina ya siya min kayan wasa yace shi babana ne na riqa kiran sa daddy wai hakane mami?

d'agowar da xatayi suka yi ido hud'u da aiman dake tsaye yana kallon ta, ta maida kan ta sunkuyar tare da share hawayen ta da sauri, sultan muje ayi wanka kayi dirty da yawa ya akayi ka bata jikin ka haka.

Sultan ya soma kallon jikinsa kafin ya d'ago yana kallon ta tare da make kafada.

Ni bana son wanka banyi datti ba, sai dai ki canxa min kaya.

Tace ni baxan canxa ma kaya ba idan ba wanka kayi ba sai dai ka xauna da kayan haka a jikin ka kowa yana kallon ka qaxami.

Yana jin ta kirasa qaxami ya soma kiciniyar cire wandon sa yana fad'in ai daddy ma ya siya min wasu masu kyau, ya cire wandon ya jefar tare da nufar kayan yana qoqarin bud'e wa, aiman ya riqe sa yana kallon gaban sa.

Oh God ashe babu kaciya baa yi ma ba.

Sultan ya turo gaban sa yana nuna wa aiman ai mami tace sai na girma xaa min circumcision lokacin da akayiwa John neighbor d'in mu a Portugal shima ya xama babba kuma yayi kuka sosai, uncle saif yace baxaa min ba tunda bana so.

Duk yanda yake cikin farin ciki da zarar yaji an ambaci saifullah ya kan rasa jin dad'in sa, yaja hannun sultan yana kiran wata baiwa.

Da sauri ta qaraso tare da sunkuyawa har qasa tana fad'in gani ranka shi dad'e.

Yace ki kai shi inda umma ta saka ayi masa wanka yanxu, sultan ya boye bayan sa yana fad'in I don't want her daddy, bana so na taba jikinta, aiman bai saurare sa ba ya d'auke sa yana fitowa ya sami wani security ya miqa mashi sultan tare da fad'in ka kaiwa jakadiya shi ayi masa wanka yanxu.

Yana dawo wa ya xauna gefen ta tare da janyo wata jaka xuwa gaban ta a hankali kamar mai tsoron afiya yace wannan kayan kine ki duba idan akwai abinda kike so babu anan sai kiyi magana har cikin kayan sultan Ma.

Batare da ta dube sa ko duba kayan ba tace nagode amma ina da wadatattun kaya bana buqata.

Yayi jim kad'an cikin tunani bai taba bada kyauta akace masa baa so ba komi qanqantar sa, meyasa afiya take masa haka ne, kayan nan ya dad'e wurin xaba mata masu kyau ya hana kowa na tare dashi Ma suga irin kayan da ya siya mata bata ga kayan ta yaba ba sai kawai tace bata so, sai ya sami kansa da riqo hannunta ta d'ago da sauri tana kallon sa fuska babu walwala.

Yace look afiya na kashe kud'i da yawa wurin siya kayan nan, na bata lokaci wurin xaba maki su, ban taba xuwa yin siyayya ba sai dalilin ki da sultan don't you appreciate?

Tace for what aiman, saboda wannan kayan kake tunanin kayi abinda xaka faranta min, nawa ka kashe akaina da yarona na biya?

Stop saying that afiya, sultan ba yaron ki bane nawa ne jinina ne, I produce him y.... tayi saurin katsesa, are you telling me that you produce sultan, ya gyad'a kansa yana kallon ta, innalillahi ta fad'a a hankali ya saki hannun ta tare da bud'e kayan yana cirowa yana d'ora mata a jiki,

Wata nighty ya ciro ja mai matuqar kyau sai d'aukar ido take ya dube ta tare da fad'in tayi min kyau sosai nafi son ta duka akan kayan, ina so na ganki sanye da ita anjima da dare please afiya ya fada tare da langabar da kansa wai shine ke roqon mace akan ta saka masa kaya.

Kallon rigar tayi kafin ta dube sa cikin yatsina fuska, baxan saka ba.

Ya matsa sosai cikin jikinta tare da saka hannu ta qugunta, ya kai kansa a hankali a qirjin ta, kiyi haquri afiya for all abinda nayi please...
[2/15, 7:58 PM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Ta d'auke kanta gefe, wani baqin ciki take ji a xuciyar ta wanda ta kasa tantance ko a wane hali take ciki tun lokacin da ta baro sashen umma jin auren yarima.

Tana qoqarin tashi yayi saurin maida ta jikinsa, ta lumshe idanuwan ta xuciyar ta sai bugawa take ta lumshe idanuwan ta, a hankali yake hura fuskar ta da iskar bakin sa, duk yanda taso jurewa kasawa tayi akwai soyayyar aiman a xuciyar ta da baxata iya cire sa lokaci d'aya ba, sai ta bud'e idanunta a hankali tana kallon sa shima sai ya tsura mata idanu, yana ji a xuciyarsa babu wanda ya kaisa farin ciki kasancewar gashi a jikin afiya tana kallon sa yana kallon ta, yana jin wani nishadi sosai a ransa, tabbas babu abinda xai raba sa da afiya sai mutuwa, yana manta kowa da komai a duk lokacin da ya kasance tare da ita, yana jin ta sosai a xuciyar sa sai dai ya kasa yarda da kansa cewa yana son ta yana danganta hakan da cewa kawai ya damu da ita ne.

A hankali ya kai lips d'in sa kan nata, ya sumbace ta, ta lumshe idanun ta cikin wani yanayi da baxata iya fassara shi ba, ashe itama tana da muradi kamar kowane lafiyayyen d'an adam sai taji ta kasa hanasa hakan ya bashi damar kissing d'in ta passionately, ganin yana soma wuce gona da iri ya saka ta saurin janye jikinta da sauri tare da matsawa nesa da shi kad'an tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudun dambe, Aiman xuba mata manyan idanuwan sa yayi yana kallon ta bai san meyasa yake rasa hankalin sa yaji baya iya controlling kansa ba duk lokacin da yake da afiya abinda baya ji a gurin ilham.

Karka sake yunqurin qara taba ni da wannan jikin da ke cundanya da mata, yaji muryar ta daga sama tana magana.

Har lokacin bai d'auke idanun sa akan ta ba, da kyar ya bud'e baki yace me kike nufi.

Cikin bata fuska tace ina nufin nabila da amaryar ka.

Ransa ya soma baci jin tana had'a sa da nabila ma ai gwara ilham da ita, yace bana son maganar nabila.

Tace saboda ta haifa maka shege kome?

Ransa in yayi dubu ya baci sosai, bai qara qoqarin qara magana ba ya tashi yana gyara shaddar jikinsa da ta yamutse, yana qoqarin fita tasha gaban sa tare da d'ora hannayen ta a qugunta, babu inda xaka je sai ka sallame ni, baxan xauna nayi kishi da wannan yarinyar ba, bana son ta bana son ganin ka aiman ka sake ni.

Da kyar yace saboda me xan sake ki, saboda kin gudu da aure na kinje kina rayuwa da wani qaton a wata qasa ko kuma saboda kina so na sake ki saboda kije ki cigaba da xama dashi, ransa ya qara baci.

Look afiya bana son qara jin xancen nabila a bakin ki if not xaki sha mamaki na, ko dan saboda ina rarrashin ki har xaki gayamin an haifa min shege ni nayi kama da d'an iska ne, ko kinga nayi kama da irin maxan dake bibiyar kowacce irin mace ce? Ya raba ta gefen ta xai wuce tayi saurin riqo hannun sa, babu inda xaka je aiman sai ka bani saki na baxan xauna da wannan yarinyar ba nima ka barni naje na auri wanda nake so.

Yayi shiru yana kallon ta batare da ya tankata ba ganin haka sai ta soma dukan qirjin sa tana kuka sosai.

Sai ka sake ni, baxan xauna da kai ba tunda kaci amana ta, idan har da gaske baka son kowa kuma baxaka iya son mace ba meyasa ka yarda ka aure ta, meyasa kake xaune da ita, meyasa kake kiran ta xuwa sashen ka kowane dare, kana nuna ka damu dani alhali kana cin amanata, wannan ne farin cikin da kake cewa xaka sanyani.

Yanda take dukan qirjinsa ya saka shi riqe hannuwan gam ya maida su bayanta, ya jingina ta da bangon d'akin batare da yayi magana ba ya qara had'a bakin sa da nata, duk yanda taso kwace kanta ta kasa qarfi ba d'aya ba musamman hannayen ta daya maida bayan ta, sai da ya gaji dan kansa kafin ya d'ago yana kallon ta, ya kai bakin sa dai dai kunnen ta cikin sanyi yace ke kanki shaida ce cewa a yanxu na damu da ke fiye da kowa da komai, kina da matsayi a xuciyata ko da bana son ki Afiya, before idan kika min wannan rashin kunyar tattakaki xanyi kin sani amma yanxu ban san meyasa bana iya fushi da afiya ba ko me xata min, ya janye jikinsa kad'an yana maida numfashi a hankali, abinda kika yi yaci ace na hukunta ki akan sa afiya but sai naqi na bawa kaina laifin komai, na xauna babu mata babu aboki, babu wannan abokin da xai min fada ko bani shawara akan abinda ya dace dani, na xauna ina rayuwata batare da wani aboki ba kuma ba dan bani da friends d'in ba sai dan nafi amincewa da Bilal nafi shaquwa da yarda dashi kamar yanda sarki ya yarda da shi, yau afiya tana neman guduna na a lokacin da babu Bilal a tare da ni, na rasa wannan aminin nawa... yaja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login