Showing 18001 words to 21000 words out of 41393 words

Chapter 7 - Mulki Ko Sarauta Book 1 Complete Hausa Novel

Nawarty   

01 Oct 2025

384

numfashi da qarfi idanunsa na kawo kwalla.

Kallon sa take a tsorace na rashin gane me yake magana akan Bilal, meya sami Bilal, fada suka yi suka rabu kome, tace ina Bilal bangan shi ba tunda naxo.

Ya matse ta a jikinsa gam tare da xura hannun sa cikin rigar ta yana yawo dashi a hankali a gadon bayan ta, we lost him, sun kashe shi, taji komai ya tsaya mata cak, hankalinta sosai ya tashi bata san sanda kuka yaxo mata ba, aiman ya bata labarin komai har dalilin sa na xuwa Jordan, bayan wani lokaci ya bar d'akin da sauri ya bar ta anan xaune cikin jimami da alhini na rashin Bilal harda matar sa da bata san ta ba.

Ta tuna kalaman Bilal a Phoenix, Afiya kada kiga laifin aiman duk inda sarauta take dole akwai qasaita, sarauta bata xuwa ko ina sai da qasaita, aiman qasaitaccen mutum ne dake ji da mulki kece xaki canxa shi, kece xaki janyo raayin sa gare ki, kece xaki koya masa yanda xai so ki domin nasan watarana sai aiman ya so ki, ki daina damuwa da nabila aiman baxai taba sonta ba baxai taba kulawa da ita ba..... bata mantawa a daren ranar aiman ya sauko yana kallon su fuska a yatsine tare da fad'in qananan maganganun ku suna damuna sun hanamin barci a wannan daren idan fira xakuyi ku fita daga gidan gabaki d'aya.

Baxata taba manta wannan ranar ba cos a ranar ta gasgasta maganar Bilal na cewa ba ita kad'ai yake wa wulaqanci ba kowa Ma xai iya wulaqantawa batare da ya damu ba, ta yarda daga yanda taga aiman d'in ya kora Bilal na cewa yana damun sa ita kuma ya nuna mata hanyar d'akin ta batare da magana ba wanda kai tsaye da gudu ta nufi d'akin ta cikin tsoron sa.

Bata manta ganin sa na qarshe da tayi kwana biyu da haihuwar sultan ba, suna xaune falo yana d'auke da sultan ta dube sa.

Yaya Bilal, yarima sau d'aya yaxo duba sultan shima sai da aka tilasta mishi kenan har da abinda na haifa ma baya so?

Inji waye, ya fada yana kallon ta ganin yanda afiya ta damu, aiman yana son jinjirin nan fiye da tunanin ki, nauyi da girman kai ke hana masa nuna hakan amma ya damu da baby shi da bakin sa ya fada afiya kuma dalilin kasancewar ki mahaifiyar abinda yake so har matsayi ya baki a xuciyar sa kinsan da wannan?

Ta girgixa kanta cikin farin ciki, ya qara da cewa abu d'aya nake so kimin afiya, kada ki bijirewa aiman ki cigaba da xama da haquri dashi ki kuma kula da yaron ki batare da nuna damuwa akan aiman ba, ni na gayamiki aiman xai so ki fiye da tunanin ki.... ta fashe da kuka wannan shine ganin ta dashi na qarshe, Allah ya gafarta maka Bilal.

Da kyar ta tashi tayi wanka tayi sallah, daren ranar komai ya jagule mata harda tsoron duniyar ma da baa bakin komai take ba, taji tana so taje ga iyayen ta gobe ta roqe su gafara akan kuskuren da tayi a baya ta kuma roqi aiman akan laifin da tayi masa, xata rarrashi xuciyar ta na xama dashi tayi ta haquri ko da baya son ta d'in kamar yanda tayiwa Bilal alqawari amma abu mai wuya ne ta jure xama dashi da wata mace dama xai fitar da ita daga wannan gidan ne ya kaita wani daban ita da yaron ta, da wannan shawara ta tashi ta shirya kanta cikin jar rigar da ya nemi alfarmar ta saka mashi ta same sa a daren ranar.

Dai dai wannan lokacin ilham ma ta gama nata shirin sosai tayi kyau acikin kayan barcin, ta feshe jikin ta da turare masu qamshi da sanyin shaqa kana ta d'ora kyakkyawar alkyabbar ta, ta fice daga sashen da wasu bayi biyu a bayanta xasu mata rakiya.

Afiya ma ta gama shirin nata sosai tayi kyau, wani sihirtaccen qamshi ke tashi ta lungu da saqo na jikin ta, simple make up ya fito da ita kamar wace xata je gasar kyawawa, ta juya ta gaban mirror d'in tana kallon jikin ta yanda rigar tabi jikinta ta kwanta saboda tsantsin ta duk ta fitar mata da halittar jikinta, haka ta d'ora sabuwar alkyabba akai duk da haka taji bata kammalu ba saboda babu lalle a hannu da qafafun ta gobe xata saka ayi mata, bata nemi rakiyar kowa ba tayi hanyar sashen aiman.

Aiman na tsaye ya??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na saka botiran rigar barcin sa ilham ta shiga da sallama, juyawa yayi yana kallon ta itama shi take kallo tare da janye alkyabbar jikin ta, ya tsurawa qugunta ido har xuwa qirjinta kafin ya maida duban sa kan kwayar idonta yana jin kansa wani iri tabbas ba qaramin rudashi tayi da wannan salon kwalliyar ta taba, ganin ya shagala kallon ta ta soma tafiya a hankali cikin qasaita duk da tana son yi masa maganar kayan da ya siyawa afiya bai siya mata amma tana tsoron tayi wata katobarar da xai korata a yanxu xata haqura ta bari sai xuwa gobe.

Afiya tana xuwa falo bayanan, to surprise him sai ta cire alkyabbar tun anan falon nasa ta juya tana kallon falon duk hotunan tane akai wani da ciki wani babu ciki, ta qara yarda tana da matsayi a xuciyar aiman, komai na falon an canxa daga yanda ta sanshi before duk da itama nata sashen anyi gyara sosai an canxa mata furnitures da komai bai kai kyau da tsari irin na aiman ba, tayi murmushi ta nufi hanyar d'akin sa duk da wata irin fad'uwar gaba da take ji a tare da ita.

Ilham tana kaiwa wurin sa ta janyo hannunsa ta d'ora a qugunta kana ta kai hannuwanta ta xagaya dasu ta wuyansa, tace naxo nayi ma goodnight I can't sleep without seeing you, I love you so much ta fada tana hura iskan bakin ta a kunnen sa.

Wani iri yaji, komai na gangar jikinsa ya amsa a wannan karon dama a buqace yake, ya lumshe idanun sa a hankali kafin ya qara budewa sai akan fuskar afiya da ta turo qofar d'akin ta shigo, cak taja ta tsaya.

Tsoro da tashin hankali da bai san su ba suka kaiwa xuciyar sa kamu lokaci d'aya...
[2/17, 7:12 PM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Da sauri ta juya ta bar d'akin kafin ilham d'in ta ankara da ita, a falo ta d'auki alkyabbar ta tana tafe tana sakawa xuciyar ta cike da qunci, aiman rungume da wata mace ba ita ba, wace rayuwa ce wannan.

Hankalin sa inyayi dubu ya tashi Karo na farko daya soma tsintar kansa cikin tashin hankali, da sauri ya hankade ilham daga jikin sa yabi bayan afiya.

Kallon mamaki ilham tabi sa da shi kome ke damun sa ta fad'a tare da tabe bakin ta, tana fitowa falon bata same sa ba ina ya nufa ta tambaya tana qara duba ko ina na falon.

Sauri sauri gudu gudu haka take had'a tafiyar ta tana kuka aiman na bayanta yana kiran sunan ta, jin muryar sa ya saka ta qara saurin tafiyar ta kada ya same ta, bata son qara ganin sa ko kad'an?? tana gab da shiga sashen ta taji ya riqo hannun ta, a fusace ta kwace hannun tare da turasa da qarfi yayi baya ta juya ta barshi gurin, tana shiga falon ta rufe gam tare da saka key ta jingina jikin qofar ta had'a kanta da gwiwa tana kuka sosai kamar ranta.

Ya soma buga qofar a hankali yana kiran sunan ta, rarrashi da ban baki babu wanda bai yi ba a daren taqi sauraren sa daga baya ma barin qofar tayi ta nufi d'akin ta, yana tsaye gurin ilham ta fito kallo d'aya tayi masa ta d'auke kai tare da jan tsaki kad'an kada yaji an dai ji kunya, duk girman sarautar da ake tutiya dashi sai a ganka a qofar mace a labe anqi bud'e ma ai girma ya fad'i ta fice, sarai yaji ta sai a lokacin ma ya tuna da halin da yake ciki, wani bawa ya gansa a haka cikin wannan daren yana buga qofa ai girma ya fad'i, sai ya juya da sauri ya nufi sashen sa, extra key ya d'auko kai tsaye ya bud'e qofar ya shiga har bedroom d'in ta, tana kwance tsakiyar gadon tana kuka sosai, yana ganin ta yaja numfashi da kyar ya taka a hankali xuwa inda take gefen ta ya kwanta tare da birkito ta xuwa qirjinsa, ta soma qoqarin kwace jikinta ya riqe ta gam sosai a jikinsa, listen afiya ya fada a hankali kamar baya son magana, taqi ta kula shi hakan ya saka ya birkitar da ita ya koma saman ta tayi saurin rumtse idanun ta har lokacin hawaye basu daina bin kuncin ta ba ya tsura mata idanu daga bisani ya soma magana a hankali, kiyi haquri afiya you mean everything to me baxaki qara gani na da ilham ba, ita mace ce da bana so kuma ban damu da ita ba amma afiya mace ce dana damu da ita bana son ta, trust me pls.

Qarfin ta duka ta tattaro ta ture sa daga jikin ta kafin ta tashi da sauri ta nufi toilet cike da qunci ido da ido aiman ke gayamata baya son ta bayan cin amana da cin mutunci da yayi mata na rungumar wata mace, soyayyar da yake nuna mata a wurin kwanciya kenan itama ilham yana nuna mata, those sweet kisses, hugs, romances duka yayi wa ilham ina baxata iya ba, baxata iya xama da maci amana irin sa ba, baxata jure ganin aiman da wata macen ba, ta cigaba da kukan xuciyar ta na mata xafi sosai.

Aiman kuwa idan ransa yayi dubu duk ya baci da irin wulaqancin da afiya take masa yana biye mata, bai qara bi ta kanta ba ya juya ya fice ransa a matuqar bace, tana jin fitar sa ta fito idanun ta jawur.

Washe garin ranar da sassafe ta soma had'a kayan ta dana sultan bata jin xata iya qara xama a gidan, bata jin xata iya raba kwana da aiman da wata mace, bata jin xata jure ganin wata mace a jikin mijin ta is better tasan bata auren sa, xataje gida kome ammi xata mata sai dai ta mata amma baxata yarda da xama da aiman a haka ba.

Mairo.., Mairo...

Na'am ranki shi dad'e ta fada lokacin da take xubewa a gaban afiya.

Kiyi magana da jakadiya ta kawo min sultan yanxu ina jira.

An gama ranki shi dad'e ta fad'a tana tashi da sauri ta bar sashen.

Ranki shi dad'e Afiya ce ta turo axo mata da sultan yanxu jakadiya ta fad'a bayan ta russunar da kanta qasa.

Yanxu da sassafe haka, meyasa take neman sultan lafiya kuwa jakadiya?

Nima bani da masaniya akan komai ranki shi dad'e mairo aka aiko ta gayamin.

Umma ta tashi tana fad'in sultan d'in ma barci yake bai tashi ba a hakan take so a bata shi.

Uwar d'akina ki kawo shi a kai mata shi a hakan ina jin akwai matsala ne tsakanin ta da yarima jiya na ganshi ya fito sashen ta ransa a matuqar bace na gaida sa ma bai kula ba.

Umma tayi jim kafin tace jiya da wane lokaci jakadiya?

Da dare ne sosai da yawa a gidannan ma sun yi barci.

Tace jeki kawai ni bari na kai sultan d'in daga can sai naji meke faruwa tsakanin su.

Afiya na xaune taga shigowar umma da sultan a kafadar ta yana barci, ba haka taso ba gabanta na fad'uwa ta tashi.

Um.. Umma ina kwana, ashe kin tashi.

Ta ajiye sultan akan sofa tana kallon ta, meyasa kika aika a d'auko sultan yanxu.

Afiya ta kauda kanta kafin tace gida xanje umma.

Saboda me? ta tambaya idanun ta akan ta.

Kai tsaye afiya tace saboda baxan iya xama da waccan yarinya da aiman ba, ni bana son kishiya dan haka baxan xauna ba.

Umma tace ni da nake xaune da kishiya meya same ni afiya.

Afiya ta dube ta tare da fad'in umma kefa auro ki aka yi aka kawo wa wata bafa auro maki aka yi ba, an kawo kine saboda waccan tana haihuwar ya'ya mata bata da namiji, bayan xuwan ki aka sami yarima da rumaisa, kin sami soyayya da xuciyar sarki fiye da mama matar sa ta farko har ta bar duniya, yanxu ke kad'ai kike xaune da sarki ba kishiya ammi ma bata da kishiya, rumaisa bata da kishiya sai ni kad'ai, saboda ni babu wanda ya damu da rayuwa ta bayan duk abinda aiman yayi min na jure, meyasa kuke tunanin sai kun aurawa aiman mata shine kun hukunta ni, is better a dake ni ayi min hukunci mai tsauri akan abinda na aikata da na xauna da wata a matsayin matar aiman baxan iya ba.

Tun da baxaki iya ba shikenan sai kije, ilham babu inda xata je ko kin so ko baki so ba dole xata xauna da aiman a matsayin mata, itama macece kuma ya' a gurin wasu, bamu d'auko ta dan wulaqantata ko cin xarafin ta saboda yarmu afiya ba kin fahimta.

cikin kuka afiya tace amma um..

Don't call me umma again, tun da ban isa na fad'a kiji ba ko mahaifiyar ki tana min biyayya a matsayin ta na qanwata balle ke yar cikin ta, ta juya tana kiran wata baiwa daga waje ina neman yarima yanxu.

Afiya ta dafe kanta tana kuka sosai, a hakan sultan ya tashi ya dubi umma kafin ya diro yayi inda afiya baiyi magana ba sai ya kwanta jikinta sosai yana sauraren kukan da take tare da kallon kayan dake xube a tsakiyar falon.

Aiman ya jima sosai kafin yaxo, fuskar nan tasa babu annuri kamar can farko da kyar ya iya gaida umma shima fuska a yatsine, inda afiya take ma bai kalla ba, sultan ya nufe sa da gudu yana nuna masa afiya.

Daddy wannan umma ta daki mami na, xaka rama mata.

Aiman bai yi magana ba, ya d'auki sultan d'in har lokacin bai saki fuska ba, shima sultan d'in ya qanqame shi.

Umma tayi masa bayanin xancen da afiya taxo da shi na tafiya akan baxata xauna da kishiya ba, kamar baxai yi magana ba saboda ransa dake qara baci game da afiya yace let her go umma.

Ba umma ba hatta afiya tayi mamakin jin kalamansa, tayi tsammanin xai rarrashe ta ne yace babu inda xata je amma har shi da kansa ke maganar taje d'in, da gaske aiman baya son ta ya xabi ya xauna da ilham akan ya xauna da ita.

Umma tace why yarima.

Yace ina xuwa umma ya juya ya fita d'auke da sultan bai jima ba ya dawo da wasu dogari kusan hud'u a bayan sa ya nuna masu kayan dake tsakiyar falon tare da fad'in ku fita dasu ku saka a mota, nan suka soma fita da kayan.

D'aya daga cikin bayin ilham take sanar da ita taga ana fita da kayan afiya qila yarima ya sake tane.

Ilham ta diro cikin farin ciki da jin dad'i sai gata a farfajiyar gidan umma tuni ta bar sashen afiya, bayan ta gama shirin ta miqa hannu xata karbi sultan hannun sa yayi mata wani kallon a wulaqance.

Da sultan aka kawo ki gidan nan ne, inaji anan kika same sa kuma anan xaki barsa cos na karbi d'ana, bai jira cewar ta ba ya fito farfajiyar gidan sosai yayi mamakin ganin harda ilham a wurin.

Afiya mace ce wayayyiya tasan gida irin na sarauta akwai xargi da qananun magana musamman idan suka ga ana fita da kayan, tunanin ta ya bata idan ta fita da fuskar haka tana kuka xasu tabbatar lallai aiman ya sake ta ne amma idan ta gyara fuskar ta fita fa, haka ta gyara fuskar kamar ba ita ba ta fito sai dai qasan xuciyar ta wani xafi da radadi take mata game da yaron ta sultan komai daren dadewa tasan sultan sai yaxo gare ta Dan bashi da yarda da kowa.

Abinda na qara daurewa ilham kai bata ga alamar tashin hankali a gurin afiya ba.

Afiya domin ta kau da wani xargi a gurin mutanen dake harabar gidan ta qarasa gurin aiman ta sumbaci sultan kana a hankali ta kaiwa aiman sumbata a kumatu, babu xato yaji saukar bakin ta a lips d'in sa, ya lumshe ido ya bud'e tare da xuba su a fuskar afiya kallo d'aya yayi mata yasan qarfin hali ne kawai take kwayar idanun ta tana nuna tana cikin damuwa sosai, murmushi yayi mata itama tayi murmushin tare da d'auke kanta gefe.

Wannan murmushi duka sun yi sane iya fatar baki kawai ba har xuciya ba saboda damuwa da bacin rai dake cin kowane daga cikin su sabanin mutanen dake wurin suna kallon murmushin a matsayin tsantsar soyayya da ma'auratan suke wa junan su.

Sosai ilham kamar ta nutse gurin saboda kunya da dana sanin fitowar ta, tana qoqarin barin wurin aka hangame qaton gate d'in gidan, tsadaddiyar mota ce ta kunno kai a harabar gidan duk gurin sun maida hankali kan motar.

Uncle saif suka ji muryar sultan ya fada lokacin daya soma kiciniyar saukowa jikin aiman, da gudu ya nufe sa, Afiya ta juya tana kallon saif cikin farin ciki da ganin sa.

Me saifullah yaxo yi gidan nan, ilham ta tambayi kanta, ta taka a hankali ta qarasa gurin sa dai dai lokacin afiya ta nufe sa.

Saifullah yaji muryar ta har cikin kansa, baxai taba mantawa da wannan muryar ba ya juya da sauri yana kallon ilham d'in cikin tashin hankali me take yi a gidan?

Cak afiya ta tsaya jin ilham ta ambaci saifullah d'in.

Aiman kuwa hankalinsa ya tashi sosai tare da mamakin duka matan sa biyu suna qoqarin xuwa inda saif tare da ambatar sunan sa, bayan afiya menene hadin saif da kuma ilham ya tambayi kansa?
[2/18, 7:36 PM] Nawarty:

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login