Showing 21001 words to 24000 words out of 41393 words

Chapter 8 - Mulki Ko Sarauta Book 1 Complete Hausa Novel

Nawarty   

01 Oct 2025

385

Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Afiya taja ta tsaya ganin ilham ta nufe sa kuma a yanda ta lura duka hankalin sa na gurin ilham d'in ne.

Motar da aka xuba kayan ta ciki ta nufa xuciyar ta a jagule, tana shiga ta bada umarni su tafi sai a lokacin hankalin saif yayi gurin motar ya nufe ta da sauri kafin motar ta tashi.

Ta sauke glass tana kallon sa wani iri.

Saboda ke naxo afiya kuma xaki tafi ki barni kamar baki ganni ba.

Tace saboda ni kaxo amma shine ka maida hankalin ka ga waccan yarinyar.

Ya dubi ilham dake tsaye tana kallon ikon Allah meya had'a saif kuma da afiya?

Yace ina xaki je haka.

Tayi jim kad'an, ka biyo ni a baya gida xanje tayi saurin maida glass jin hawaye suna shirin xubo mata, yaja kad'an jiki a sanyaye bai qara kallon ilham ba ya shiga motar sa.

Uncle saif nima xanje sultan ke fad'a yana tumami a hannun maina daya riqe sa gam cikin bacin rai, daddy leave me sultan ya qara fada yana kallon aiman.

Motar su afiya na fita ta saifullah na baya, hankalin aiman ya kasa kwanciya saifullah yabi afiya me suke nufi sam sai yaji ya kasa samun nutsuwa wanda ya xama dole ya bisu.

Bayan saukar afiya a gida Abba baya nan kuma bata sami fuska a gurin ammi ba ko gaisuwar ta bata amsa ba, tsawon shekara hud'u tayi kewar mahaifiyar ta ba kad'an ba shi kansa saif bai ji dad'in yanda ammi tayi wa afiya ba.

Meke faruwa afiya?

Ta dafe kanta da hannuwan ta duka biyu kafin ta fashe da kuka sosai, ta rasa inda xata saka xuciyar ta taji sauqi dama bata dawo qasar ba, iyayen ta sun kasa fahimtar ta sannan ga baqin cikin mijinta dame xata ji.

Tace saif tunda naxo sun qi su bani dama su saurare ni, a ranar dana dawo a ranar aka tilastamin komawa gidan aiman, ta dube sa da jajjayen idanuwan ta saifullah har yanxu yarima baya sona har yanxu yarima bai canxa ba yana qara gayamin baya sona da bakin sa sannan kuma ya qara aure shekara biyu yanxu.

Ilham yake aure ko? yayi tambayar kamar wani xautacce, ta gyad'a kai tana share hawayen fuskar ta.

Yace kiyi kuka afiya baxan hana ki ba nima nayi kuka a lokacin dana dawo na tarad ilham ta auri wani, afiya ta qara kallon sa cikin mamaki, ya gyad'a kansa tare da fad'in ilham itace yarinyar da nake baki labari Afiya.

Yanxu ya xaa yi? ta tambaya.

Murmushi yayi tare da fad'in tuni na kankare ta a xuciya ta, mu daina maganar Ma saboda tana da aure yanxu, ke kanki naxo mu gaisa ne kawai saboda yanda kika matsa min amma wannan maganar ki bar ta afiya ki xauna da yarima am sure watarana xai so ki xai nuna maki so fiye da wanda xan nuna maki, matsala d'aya ki gyara zamantakewar ki da iyayen ki, ki nemi afuwar su domin kinyi ba dai dai kamar yanda nasha gayamiki a baya, xaki faranta masu ne idan kika koma d'akin ki tare da amincewa xaki xauna da wanda suke so d'in, kiyi haquri afiya.

Aiman dake qofar falon yana sauraren su ya shiga da sallama dai dai lokacin afiya ta fashe da kuka a yau ta qara yarda ta rasa saif baxai taba auren ta ba kamar yanda take so domin huce haushi akan abinda aiman yayi mata, tana jin sallamar sa ta tashi ta bar falon.

Kallon kallon ne tsakanin aiman da saif kowane da tunanin dake xuciyar sa game da d'an uwan sa, saif ya fara miqa masa hannu domin su gaisa aiman ma ya miqa nasa suka harde.

Ammi dan Allah kiyi haquri ki yafe min, dan Allah ammi, afiya ta fada yayin da take durqushe gaban mahaifiyar ta.

Ammi ki daina tuna komai akan kuskuren da nayi a baya na guduwa batare da sanin ku ba, ki yafe min xan koma na xauna da yarima idan hakan shine farin cikin ki.

Har lokacin mahaifiyar bata tanka ta ba, hakan ya saka afiya tashi daga durqushen da take ta fito harabar gidan babu motar saif babu ta aiman.

Ammi kallo ta bita da shi sosai take tausayawa halin da yar ta ke ciki tana yin haka ne saboda kada ta bata damar da xata qi xama da aiman, idan ta sake mata fuska a yanxu tabbas kafuwa da shagwabar afiya baxata barta ta koma ba wanda abban ta xai iya goyon bayan ta a yanxu amma tuni ta dad'e da yafe mata tun daga lokacin da ta kira ta a waya tana kuka.

Driver tayi wa magana da ya kwaso kayan da taxo dasu yaxo ya maida ta, ta bud'e motar ta shiga kanta sai ciwo yake ga wani jiri da take ji, tun safe babu abinda ta sakawa cikin ta banda kuka da take fama dashi.

Bayan driver ya gama loda kayan a booth yaxo yaja motar suka fice.

Suna yin parking ta fito idanunta basu sauka ko ina ba sai wurin wasar da aka tanadarwa sultan, ilham, aiman da sultan ta gani suna wasa kowane fuskar sa d'auke da nishadi.

Nan take taji kanta na qara juya mata, haushi da tsanar aiman suka dirar mata lokaci daya tare da nadamar dawowar ta gidan a yanxu da batayi wannan ganin ba, dama yana son matar sa yake boye mata cewa baya son ta, duk wanda ya gansu a wannan yanayin ya san tsantsar soyayya ce a tsakanin su.

Ilham bata ankara da ita ba, aiman kuwa kallo d'aya yayi mata ya d'auke kansa gefe, a hankali taja qafafun ta xuwa sashen umma.

Umma ta boye mamakin ganin ta sai dai yanayin afiya ya tabbatar mata babu lafiya tana xaune ta wuce ta xuwa d'akin ta, bata yi yunqurin bin ta ba ta bar ta.

Nan da nan zazzabi mai xafi ya rufe ta saboda tsananin damuwa da ta sakawa xuciyar ta da kuma rashin cin abinci, ta lumshe idanun ta tana hawaye sosai gani take kowa baya qaunar ta a yanxu.

Tun da yaga dawowar afiya yaji hankalin sa ya koma kanta wasar ta fice masa a rai, ya bar sultan da ilham a wurin ya nufi sashen sa, bai yi yunqurin xuwa inda take ba sanin halin ta xata iya wulaqanta shi a gaban umma Ma.

Wanka yayi ya shirya kana ya fice daga gidan xuwa asibiti, bayan ya gama ward round ya nufi office d'in sa, xaman sa keda wuya metron nafee ta shigo da sallama.

Kallon ta yayi tare da fad'in menene?

Uhm dama dama wata patient ce ke vomiting yanxu shine naxo na gayama.

Dan tana vomiting sai me, me xan mata ko xuwa xan yi na kwashe ne?

Ta girgixa kanta tana sunkuyar da kai sorry sir I was confused ne ta juya da sauri ta bar office d'in ganin yanda ya d'aure fuska.

She was confused for what ya tambaya, mtsew ya cigaba da aikin dake gaban sa.

Meke damun ki afiya, umma ta tambaya tana kai hannu jikin afiya ganin yanda ta takure gefe d'aya tana barci.

Jikin ta xafi gau, ta duba taga afiya barci take ta janye hannun ta tare da fad'in sai ki jefa kanki cikin matsala saboda kishi, ta soma kiran sunan ta a hankali afiya afiya.

Da kyar ta bud'e idanun ta jawur tana kallon umma batare da ta amsa ba, tace zazzabi ke damun ki, ta gyad'a kai a hankali, kinsha magani? ta girgixa kanta.

Kinci abinci ma kuwa? Nan ma ta girgixa kanta, umma ta xauna tare da fad'in sai ki hana kanki abinci saboda kishi kina neman halaka kanki, kamar wacce ke jira ta soma hawaye, umma ta kwantar da murya sanin afiya tace banda abin ki wake fushi da miji saboda kishiya har kike neman yaji, waya gayamiki ana barwa kishiya miji, a maimakon kiyi qoqarin janyo hankalin sa xuwa gare ki kike qoqarin janye kanki daga gare sa meyasa afiya.

Umma yaya aiman baya sona.

Inji waye?

Cikin kuka afiya tace shi ya fad'a da bakin sa umma ya gayamin baya sona, ya xabi waccan akaina.

Umma tace aa aiman baxai so ilham saboda ke ba, ki kwantar da hankalin ki idan kika bisa xaki same sa a yanda kike so fad'a ko fushi baxai yi tasiri akan yarima ba kinsan xai iya fita sha'anin ki, bana son haka ki tashi kici abinci kisha magani.

Afiya ta girgixa kanta tare da maida idanuwan ta ta lumshe, wahalallen barci yayi awon gaba da ita, umma ta qara taba jikin har lokacin xafi rau, ta d'auki waya ta kira aiman ta shaida masa ciwon afiya.

Ok kawai yace ya tsinke wayar, bai damu ba ya cigaba da aikin gaban sa cos ya kwana biyu bai shiga asibitin ba.

Bai dawo gidan ba har bayan magrib, sai da yayi wanka yaci abinci kafin ya nufi sashen umma har lokacin afiya bata tashi barci ba ko sallah bata samu tayi ba.

Yayi tsaye kanta hannayen sa xube a aljihu ya xubawa fuskar ta ido, yini d'aya har tayi wata rama kamar ba ita ba, my stubborn wife ya fad'a a hankali tare da xama kusa da ita, hannun sa ya kai jikinta yaji xafi rau ya tashi ya nufi toilet bai jima ba ya fito da qaramin towel da ruwa, kusa da ita ya qara xama tare da jiqo towel d'in ya d'ora a goshin ta, sanyin sa ya saka ta jan numfashi tare da bud'e idanun ta a hankali.

Da sauri ta maida ta rufe saboda bata son ganin sa a yanxu, bai damu ba ya cigaba da jiqa towel d'in yana shafa mata a jiki, tana ji tana gani ya cire rigar jikinta, hannun ta takai da sauri ta rufe qirjinta, ya d'ora nasa hannun akan nata ya janye tare da fad'in karki qara maida hannun.?
[2/19, 3:18 PM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Ta bata fuska tare da janye hannun sa Karo na biyu,

Bana so I don't need your help.

Fine and good ya fad'a yana tashi daga kusa da ita, ba xuwan kaina bane umma ta matsa min, daga haka ya juya batare da ya qara kallon ta ba.

What is wrong with me, ta fad'a tana tashi xaune da kyar saboda wani nauyi da kanta ke mata, ta dafe kanta tana kallon agogon dake d'aure a d'ayan siririn hannun ta, xumbur ta tashi ganin lokaci ashe har sallah anyi tana ta barci bata sani ba.

A gurguje ta fad'a toilet...

Mami mami, sultan ya shigo yana kiran sunan ta dai dai lokacin ta fito daga toilet ta dauro arwallah.

Kallon sa tayi a wahalce saboda xaxxabin dake damun ta, ya riqo hannun ta yana fad'in mami ina kika je kika barni.

Tace lemme pray first, ta saka hijab ta soma sallah.

Tana sallame sallah kamar mai jira ya kwanto ta bayan ta, mami yaushe xamu je gidan mu inda suzana?

Tayi masa shiru saboda lazimin da take, ya fara buga qafafun sa alamar xai yi kuka, tana jinsa taqi kula shi har sai da ta kammala tayi addu'a dai dai lokacin ya fashe da kuka sosai.

Ta jawo shi ta rungume shi sosai a jikinta tana dariya tare da fad'in I miss my love, sarkin rigima, meya faru kuma yanxu kake son muje gida da wannan daren.

Mami muje gida bana son wannan gida, ta jawo hannun sa ta d'ora a wuyan ta tare da fad'in kaji mami babu lafiya bana son damuwa pls sultan.

Yayi shiru yana kallon ta, itama kallon sa take kafin ta d'ora hannun ta a cikinsa tana fad'in kaci abinci kuwa wannan ciki haka.

Ya girgixa kansa, tace meyasa sultan.

Mami bana so muje gida, tace d'auko waya kaxo mu kira uncle saif.

Yana jin haka ya tashi da sauri yaje ya d'auko wayar a bed side ya dawo ya xauna a qafafun ta ya bata wayar tare da cewa mami ki gayamasa yaxo da babbar mota harda kayan wasana xamu je dasu.

Tayi murmushi tana dialing number saif, bugu d'aya biyu ya d'auka sultan na jin muryar sa tun batayi magana ba yayi sauri uncle kaxo mu tafi gida bana son wannan gidan.

Oh my boy, baka son ka xauna da su daddy da granny ne. Sultan ya shagwabe fuska kamar yana ganin sa yace ni bana so.

Saif yace tam gobe xan xo na d'auke ka mu tafi abin mu suzana tana jiran mu sai mu bar mami a gurin daddy ko.

Sultan yaji dad'i ya soma murna, afiya ta karbi wayar ta soma magana a hankali saboda yanayin jikin ta tace ko da na fito d'axu ban same ka ba ya kuka yi da yarima.

Yace mun gaisa kawai sai kuma kowa ya fita abun sa, me kike tunanin xai faru.

Tace nasan halin yarima ne, amma gida ka koma ko kana gari.

Yace ina nan ban tafi ba tukunna qila gobe xan shigo muyi ban kwana shikenan baxa mu sake had'uwa ba.

Meyasa kace baxamu sake had'uwa ba, ta tambaya muryar ta na rawa saboda tsananin tashin hankali.

Babu amfanin xaman mu kina matar aure afiya, wanda muka yi a baya nayi ne saboda taimako har wata alaqa ta soyayya ta soma shiga tsakanin mu, yanxu kina tare da mijin ki idan har ina son ki da aure dole na qaurace maki saboda gudun xargi daga mijin ki, ina maki kallo yanxu a matsayin qanwa kiyi haquri afiya.

Dama kukan na kusa sai ta fashe masa da kuka, yayi shiru yana jin wani xafi a ransa baya son damuwar afiya ko yaya ne balle kukan ta da kyar ya bud'e baki yayi magana yace kuka xaki min na kashe wayar ne.

Tace aa amma kayi tunani bana son muyi wannan rabuwar Saif na xabi na xauna da kai fiye da aiman hankalina xai fi kwanciya idan ina tare da kai.

Aiman yafi dacewa da afiya sosai fiye da ni yau na qara tabbatarwa ba dan bani da kud'i ba nima aa sai dan ina da tabbacin soyayyar ki ta kama xuciyar aiman batare da ya sani ba, ganin da nayi masa a d'axu ya bani mamaki kishin ki ya saka shi biyo mu har gida afiya ni naga idanun sa a lokacin ko bai fito ya furta maki so a baki ba tabbas xuciyar sa na muradin afiya, sannan afiya ma tana son aiman sosai idan har xaki iya gujewa qasar ki saboda aiman na tsawon shekara hud'u meyasa kike tunanin barin sa a yanxu na har abada, fushi da kishin aiman yake saka bakya son xama dashi kin xabi ki xauna dani amma soyayyar ki aiman kad'ai kike wa afiya na sani, taya kike tunanin xan shigo rayuwar ki nayi qoqarin raba ki da farin cikin ki kuma uban d'an ki saboda ni na same ki kenan akwai son xuciya a tare dani, kamar yanda kike min kuka a yanxu haka ilham ta kira ni d'axu tana min wannan kukan itama na taimake ta, ban yi tunanin har wannan lokacin ilham tana da numbata ba kuma bata boye min komai na game da auren ta da yarima ba, bayan wulaqancin da tayi min harda laifin iyayen ta na tursasa mata auren sa tun bata so har ta fara son sa saboda yarima namiji ne da ko wace mace take burin mallakar sa, ta gayamin komai a yanxu game da irin xaman ta da yarima duk da nasan akwai abinda take boye min amma duk da haka ta tabbatar min da babu abinda ya shiga tsakanin ta da yarima and she need my help akan na dawo rayuwar ta kuma kinsan ina son ta, sai dai ban san taya xan same ta ba nima I need your help afiya.

Sai kanta ya d'aure da kyar tace ni me xan iya saif a yanxu.

Yace ki saka aiman ya barmin ilham.

Tace bani da qarfin wannan ikon saif shi kansa aiman bai isa ba batare da sarki ba, al'adar gidan nan baa sakin mace komai laifin ta sai idan taxo da al'fasha ilham kuwa babu abinda tayi da xai saka yarima sakin ta.

Da kyar yace Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.

Amin ta amsa a sanyaye kafin ta tsinke wayar ta dubi sultan tare da fad'in bari nayi isha'i kaji.

Meyasa kike kuka mami, uncle saif yace baxai je dake ba.

Ta share wasu hawaye da suka xubo mata cikin rawar murya tace bari nayi sallah sultan sai muje kaci abinci kaji, yayi shiru yana kallon ta tana sallah yanayin mamin tasa ya saka sam bayajin dad'in jikin sa yana qara tsanar garin da yake ganin tun xuwan su yake ganin mamin sa ke kuka, tana gama sallah ta cire hijab ta d'auke sa suka nufi falo, dai dai lokacin umma ta shigo tare da bayi a bayanta da alama inda sarki ta fito.

Kallon afiya tayi ko bata fad'a ba idanun ta sun nuna tayi kuka ta girgixa kanta kawai.

Me ya sami sultan d'in shi kuma.

Wai yunwa yake ji yaqi yaci abinci shine nake so na bashi yanxu.

Umma tace yaron da kafuwa kamar iyayen sa tun acan naga sarki yayi dashi yaci abinci yaqi sai dai yaxo inda mami su tafi gidan su.

Afiya tayi murmushi batare da tayi magana ba ta soma bud'e masa warmers dake dining tana nuna masa, me kake so na xuba ma kaci, ya dubi kalolin abincin dake wurin kafin ya girgixa kansa alamar baya so.

Afiya ta sauko daga dining tana fad'in nagaji ina son kwanciya sultan.

Umma tace kuma baxaa barshi ya kwanta da yunwa ba ko hollandia ne ki samu yasha kad'an.

Yace Golden Morn nake so.

Umma tace duk jirgi d'aya ne da fu'ad haka shima yake shiyasa sarki ya saka duk aka siyo ire iren wad'annan kayan aka ajiye, ki had'a ki bashi ya sha kafin yayi barci naga idanun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login