Showing 30001 words to 33000 words out of 41393 words

Chapter 11 - Mulki Ko Sarauta Book 1 Complete Hausa Novel

Nawarty   

01 Oct 2025

387

qafafun sa alamar xai yi kuka, mami ni ki kaini da kanki I don't want to go alone.

To ka jira na gama abinda nake yi tukunna k... bata qarasa ba kamar mai jira ya fashe da kuka, ta d'auke sa taxo dashi falon ta kan sofa ta dire sa tare da fad'in xauna anan kayi kukan idan ka kuskura kaxo d'aki na xaka Dame ni dukan ka xanyi since baka da aiki sai kuka ko yaushe, ta juya ta barshi gurin aikuwa ya soma kuka sosai.

Xo na kaika wajen mahaifin naka, yaji an fad'a ya juya da sauri yana kallon qofar falon, nabila ce a tsaye tun juyawar afiya xuwa d'aki ta shigo.

Sultan ya tsura mata ido bai san ta ba hassalima bai taba ganin ta ba tun da yake a gidan, ramar dake tare da ita ya saka shi jin tsoron ta kutt ya had'iye kukan yana matsawa ganin tana xuwa wurin sa.

Da gaske wurin sa ta nufa ya d'aga murya da qarfi, Mami giraffe in the house.

Nabila ta tsorata ta juya da sauri bayan ta babu komai ta soma kallon falon bata ga raqumin da yake maganar ya gani ba, ta qara kallon sa, I will take you to your daddy xo muje.

Noo ya girgixa kansa tare da fad'in mami giraffe.

Dariya sosai afiya keyi a d'aki, shirmen sultan baya taba qarewa, giraffe acikin gida har falon ta, itama ta d'aga murya tana cewa wannan bashi xai saka naxo na kaika wurin daddy ba is better kaje da kanka.

Kafin sultan ya qara yunqurin magana nabila ta d'auke sa, ya soma qoqarin ture ta yana kuka, keep me down I don't like you.

Shi da waye kuma afiya ta fad'a tana tashi da sauri tayi hanyar falon, nabila kuwa bata saurare sa ba ta fito dashi harabar gidan wani security yayi kanta da bindiga taji tsoro sosai dan mutanen dake tsaron gidan kwata kwata babu annuri a fuskar su baxaka taba ganin dariya ko murmushi a tare dasu ba ko da yaushe fuskar su na d'aure tamau.

Cikin rawar murya tace xan kaishi wurin daddy sa ne dai dai lokacin afiya ta fito da sauri cak taja ta tsaya ganin sultan d'in hannun nabila yana ture ta tare da miqa hannun sa gurin security d'in alamar ya d'auke sa duk tsoron sa da yake akan nabila ta d'auke sa.

Suna haka aiman ya fito, tsananin mamakin gani nabila ya saka shi tsayawa a inda yake, waye ya fito da ita kuma menene dalilin d'aukar sultan ina xata kai shi.

Security d'in ya karbi sultan, yana ganin afiya ya soma miqa mata hannu yana kuka, ya kaishi gurin afiya da sauri ya qanqame ta, nabila na ganin aiman ta nufe sa da sauri.

Dear tun jiya nake neman ka kai kad'ai ne baka san sarki ya saka a fito dani ba ina ka shiga haka.

Ya xuba mata idanu, meya kai hannun ki kan yaro na.

Cikin mamaki tace d'an ka d'ana ne ai prince, yanayin ka ya nuna you are not happy with me.

Afiya na tsaye tana kallon duk da bata jin me suke fada amma ranta xafi yake mata, sultan ya d'ago yana kallon ta sai kuma ya juya xuwa inda take kallo yana ganin aiman ya soma kiciniyar sauka daga jikinta ta ajiye sa da gudu ya nufi aiman ya rungume qafafun sa daddy I don't want this woman, aiman ya d'auke sa yana kallon ta, idan sarki ya saka an sake ki ni kuma a yanxu ina da iko saka a rufe ki saboda ina xargin da saka hannun mahaifin ki a mutuwar aminina.

Ta bud'e idanu sosai tana kallon sa cikin tsananin mamaki.

Yace yes, saboda babu wanda ya san da tafiyar sai ke kad'ai kuma harin da aka kawo mana daga kano ne inda muka je gaisuwa kuma acan mahaifin ki yake.

Tace wannan ba dalili bane da xai saka ka xargeni ko xargin mahaifina idan ni nasan da tafiyar taya kake tunanin xan sanar da abbu bayan babu waya ko wata hanyar sanar dashi hakan sannan menene dalilin da xai saka mahaifina ya kashe Bilal?

Aiman yace koma menene xan gano amma babu inda xakije a gidannan, maganar yaro na kada ki kuskura ki qara yunqurin taba min shi idan wani abu ya sami sultan you are dying nabila xan iya yafe komai banda lafiyar sultan.

Meyasa kake min haka prince, meyasa kake tunanin xan cutar da sultan ina son yaron saboda kai menene laifi dan na nuna kulawa ga abinda kake so, I can't ignore seeing him batare dana d'auke sa ba gaskiya You can't stop me yaron yayi min kyau.

Cikin bacin rai aiman ya juya ga securities dake harabar gidan cikin d'aga murya in a lion voice muryar da basu taba ji a gurin sa ba yace duk ranar da wannan matar ta qara yunqurin taba sultan a gutsure hannun.

Yes sir suka fad'a lokaci d'aya cikin girmamawa.

Sosai ran nabila ya baci da wannan toxarcin da aka mata yanxu ta juya tana kallon afiya ga mamakin ta suna had'a ido ta sakar mata murmushi, ranta ya qara sosuwa batare da tayi magana ba ta juya da sauri ta bar wurin.

Tana kuka ta kira abbu ta sanar da shi komai, yace just kill them tomorrow xan xo na d'auke ki mu gudu.

Afiya ta juya ta bar wurin haka ma aiman.

Washe garin ranar jakadiya na had'a abincin sarki da yarima nabila ta shiga kallon ta tayi tare da fad'in kin nuna min taurin kai ni kuma xanyi aikin a gaban ki wallahi idan kika yi yunqurin tonawa tabbas laifin xai koma kanki kuma mahaifina baxai bar ki ba xai kashe ki.

Jakadiya ta tsorata tana kallo nabila ta xuba magani a abincin sarki da yarima, ta dube ta tare da fad'in ki kai abincin yarima sashen afiya acan nake so yaci ki sanar dashi daga mahaifiyar sa umarnin yaxo cewa yaje cin abinci sashen afiya na sarki kuwa ki kai masa inda kika saba kaiwa idan aka sami kuskure ko akasin haka to kisa a ranki babu ke babu dangi xamu kashe su duka.

Afiya tayi mamaki sosai jin yarima yau a gurin ta xai ci abinci, cikin farin ciki ta tsantsara kwalliyar ta sosai tayi matuqar kyau kamar ba ita ba ta xauna xaman jiran xuwan sa.

Kusan haka ne a gurin aiman jin umman sa tana bada umarni yaje inda afiya cin abinci ba dan jakadiya taxo masa da xancen ba babu yanda xaa yi yaje, ya shirya tsaf ya nufi sashen afiya ba qaramin kyau tayi masa ba, murmushi tayi tana kallon sa bayan ta gaida sa, ya amsa tare da nufar dinning da kanta ta soma had'a masa komai a gaban sa.

Ya xubawa dining idanu duk wannan kalar abinci haka shi kad'ai duk a ina xai saka su acikin sa, ya janyo plate na pepper soup, afiya ta dube sa tare da fad'in meyasa xaka fara cin sa.

Saboda shi nake da ra'ayi ci, tace tam bari naxo muci tare abinda duk xaka ci shi xan ci, aiman baice komai ba ya kai spoon bakin sa ya had'iye tare da qara d'iba ya kai bakin sa cikin xargin wani abu, afiya ta xauna kusa da shi dai dai lokacin aiman ya d'ago yana kallon ta.

Waye yayi girkin nan, kallon sa tayi tare da fad'in nima ban sani ba jakadiya taxo da shi.

Meyasa taste d'in abincin ya canxa ba kamar na ko yaushe ba, afiya xata yi magana yace akwashe komai anan a fita da su akai wa umma let her taste.

Amma yari..... ya katse ta tare da d'aga hannun sa umarni ne, daga yau bana son akawo min abinci daga cikin gida idan bake xaki girka.... yayi shiru jin wani motsi da cikin sa ke yi.

A kwashe abincin afiya bana son ganin ya fada yana dafe cikin sa, cikin tashin hankali ta soma kiran su mairo suna xuwa ta basu umarni su kwashe kayan xuwa sashen umma, juyawa afiya tayi xuwa gare sa.

Meya same ka aiman ta fada tana nufar sa da sauri.

Idanunsa sunyi jawur, ya sauko daga dinning ya durqushe?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? a qasa tana qoqarin taba sa ya dube ta da jajjayen idanun sa, you poison me saboda bakya so na a yanxu.

Wani shock taji, qafafuwan ta suka soma rawa.

Meyasa kika sa umma ta gayyace ni cin abinci a gurin ki, why did you want to kill me afiya, me nayi, sai ya fashe da kuka sosai abinda bata taba gani ba a rayuwar ta hawayen yarima balle kukan sa.
[2/25, 4:58 PM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Itama ta fashe da kuka mai tsananin gaske cikin rud'ewa, babu wata kalma da xata iya furtawa a yanxu domin kare kanta a wurin aiman amma taya yake tunanin xata iya kashe sa.

Ana kaiwa umma abincin tayi matuqar mamaki sosai kome xai hana yarima cin abinci hakan ya saka ta bada umarni idan baa kaiwa nabila abinci ba suje mata dashi tunda yanxu sarki yayi magana cewa nabila ta daina cin abinci irin na bayi duk abinda xaa dafa masu a dafa da ita tsawon na kwana biyu kamar yanda ta nemi alfarma.

Ta bada umarnin akaiwa nabila abinci kafin umma ta nufi sashen su aiman jin dalilin qin cin abinci ko kuma wani yake so ayi masa.

Nabila cike da murnar ganin yawan abincin da aka jera a gaban ta kamar wata sarauniya, duk wannan abincin ita kad'ai ina Ma xata iya cin ko kwatar sa, haka ta bud'e warmers d'in tana cin komai dake wurin idan taci wannan taci wannan cikin tsananin farin ciki ta sami yanci a gidan.

Kuka sosai jakadiya keyi lokacin da ta isa falon sarki, kallon ta mai martaba yayi lokacin da ta jera komai a gaban sa tayi xaune dirshan a wurin tare da fashewa da kuka.

Ka gafarce ni mai martaba idan na aikata ba dai dai ba amma ina so yau kad'ai ka bar wannan abinci kada kaci.

Yace saboda me jakadiya.

Tayi shiru bata san yanda xata fara ba saboda tsananin tsoron wani abu ya sami yan uwan ta.

Ganin haka sarki bai kula ta ba, ya kai hannun sa abincin tayi saurin riqe hannun sa jikin ta na rawa cikin tsananin kuka tace guba ce aciki ranka shi dad'e.

Mamaki ya saka shi kallon ta babu tsoro a tare da shi yace guba wace irin guba?

Tace guba wacce ke kashe mutum kai tsaye ranka shi dad'e.

Yace kika saka min domin ki kashe ni kome.

Ta girgixa kanta cikin kuka tace taya kake tunanin xan iya kashe ka bayan kaine rayuwa ta da komai na jin dad'i a duniyar nan.

Yace taya guba xata shiga a abincin da nake ci bayan kin fi kowa iko da kula da abinda nake ci da sha.

Nan take jakadiya ta soma kora masa bayanin komai tana kuka tana sharce majina da xabin ta, bai bari ta qarasa ba ya d'auke fuskar ta da mari cikin tsananin bacin rai, abinda sarki bai taba yi ba tsawon shekarun da suke tare.

Da sanin ki kika bari aka d'auki guba aka kaiwa d'ana, gwanda ni naci gubar da yarima yaci, kinsan yanda nake son yarima kuwa taya ma xaki bari a cutar da yaron da kika raina da hannun ki jummai, ina amanar yarima dana baki tun yana qarami tabbas sai kuma yayi shiru yayi hanyar waje da sauri yana fad'in innalillahi wa inna ilaihir raji'un.

Fadawa da securities suka taso cikin tashin hankali ganin yanda sarki ya fito a rude da hannun yake nuna masu sashen aiman yana fad'in ku duba min yaro na kada su kashe min shi, ku duba min yarona waziri.

Hankalin kowa ya tashi ainun duk suka yi sashen yarima a tunanin su ko wuta ce ta tashi a sashen yarima sanin babu wata hanya a gidan da mugu ko barawo xai iya shigowa batare da sun kama shi ba.

Lokacin da umma ta nufi sashen afiya halin da ta sami aiman ya d'aga hankalin ta sosai lokacin numfashin sa ya soma sama sama.

Meya same sa afiya, meya sami yarima.

Cikin kuka afiya tace umma guba suka bashi yaci.

Tace guba, waye ya bashi na shiga uku tayi hanyar waje da sauri cikin rud'ewa?? dai dai lokacin securities suka qaraso da sauri ta nuna masu inda yarima ke kwance suka yi kansa hankali tashe.

Umma na ganin sarki tayi kansa tana kuka, sun kashe min shi wallahi sun kashe shi guba suka bashi yaci aiman baya numfashi mai martaba.

Yace aa ba dai har yaci abincin ba? Suna tsaye aka fito da aiman wani security ya d'auko sa da sauri aka bud'e mota aka saka shi nan take umma ta yanke jiki ta fad'i wurin, sai hankalin sarki ya kasu biyu, akayi kan umma cikin tashin hankali.

Sarki ya bada umarnin a saka ta a mota itama duk ya fita hayyacin sa kamar bashi ba tsoron sa kada xuciyar ta taje ta buga ya xamana ya rasa ta ya rasa aiman kuma.

Suna gab da barin gidan sarki ya sauke glass d'in mota da sauri wannan karon bai jira an sauke masa ba ya dubi sauran mutanen dake gidan tsaye yace kuje sashen tsohuwar matar aiman ku kama matar dake ciki kada abar kowa fita ko shiga a gidan nan.

Suna fitowa motar aliyu na isowa gidan dashi da rumaisa da fu'ad yanayin yanda aka fisgi motocin suka bar wurin da sauri ya saka aliyu xargin ba lafiya.

Rumaisa ta dube sa tare da fad'in kamar naga daddy a motar can fa.

Yace mai martaba da kansa, ina xai je haka.

Taje mubi bayan su bana tunanin lafiya qalau idan kayi la'akari da baa gudu da sarki haka da mota fa.

Yace hakane, ya gyara motar suka bi bayansu da sauri.

Kai tsaye ICU aka nufa da aiman umma kuwa tuni aka soma bata taimakon gaggawa.

Rumaisa tayi kuka sosai ita da afiya kwata kwata sun fita hayyacin su kamar ba su ba.

Sarki kuwa jarumta ce kawai yake amma deeply xuciyar sa xafi take sai kai da kawo wa yake a corridor d'in asibitin da kyakkyawar sandar sa da tasha ado irin na sarauta.

Abba da ammi ma tuni suka hallara asibitin cikin tashin hankali.

Ina nabilar take, Abba ya tambaya yana kallon sarki.

Yace tana can gidan na saka a kama ta.

Abba ya dubi aliyu yana fad'in xo muje gidan yanxu.

Nabila kuwa bayan gama cin abinci ta kira mahaifinta take sanar dashi komai cewa ta gama aiki sai dariya suke a waya yanayin ta ya soma canxawa, cikin ya soma kuka da qugi lokaci daya saboda taci abincin sosai ta dafe cikinta da sauri, abbu cikina.

Meya faru ya tambaya da qarfi ta saki wayar batare da ta kashe ba, abbu cikina sai a lokacin ta lura da warmers d'in tabbas acikin su ta saka magani shine aka maido mata taci.

Abbu na shiga uku sun kashe ni, guba suka bani naci, abbu ni suka bawa naci.

What, hello hello nabila kina jina, nabila kam tuni ta xube a wurin dai dai lokacin securities da sarki ya aiko suka shigo falon suka yi kanta a lokacin kumfa ya fara fitowa bakin ta, bata d'auki dogon lokaci ba a wurin suna qoqarin taimaka mata su kaita asibiti rai yayi halin sa, guba ce mai matuqar aibu sosai wadda nan take take kashe mutum batare da daukan dogon lokaci ba, nabila taci pepper soup d'in da yawa ba kamar aiman da cokali d'aya yayi ya ajiye tare da xargin taste d'in abincin ya canxa ba yanda ya san shi ba amma duk da haka tayi masa aibu balle ita da ta xauna taci gubar sosai.

Xuwan Abba da aliyu bai yi amfani ba cos ko da suka xo har ta mutu ba haka suka so ba, sun so su same ta da ranta yanda xasu axabtar da ita dai dai laifin ta amma waye ya bata gubar taci, shine abin tambaya.

Kiran wayar abbu ya shigo wayar ta aliyu ne ya d'auka jin muryar mahaifin nabila kai tsaye ya sanar dashi nabila ta dad'e da mutuwa sakamakon gubar da taci.

Nooo ya fada da karfi qarya kake, ya'ta bata mutu ba kaine ka kashe min ita nima sai na kashe ka na raba ka da duniyar gabaki d'aya.

Aliyu yayi murmushi kafin yace ina jiran ka yau ko gobe a shirye nake da tunkurar ka ko ka kashe ni ko kuma ni na saka a kashe ka, nafi ka qarfi da iko a qasar nan idan kayi la'akari da mahaifina keda iko akan ta, idan na kashe ka na kashe banxa ne kai tsaye xaa shafe bayin rayuwar ka, ya tsinke wayar cikin bacin rai yana kallon mahaifin sa tare da sanar dashi abinda abbu yace.

Abba ya dafe kansa cikin qunci da baqin ciki mutuwar nabila haka kai tsaye, ya kira waya ya sanar da sarki.

Abbu kuwa cikin tashin hankali da rudani ya d'auko bindigar sa, baxai jure rayuwa batare da nabila yar sa ba, baxai iya xama a duniyar babu ita ba kai tsaye ya saita bindigar a kansa ya harba, nan take ya fad'i gurin cikin jini matacce.
[2/26, 7:38 PM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Jakadiya banda kuka babu abinda take, bata san hukuncin ta a gurin sarki ba haka bata san halin da aiman d'in yake ciki ba ga mutuwar nabila da nayi matuqar girgixa ta,

Haka aka fita da gawar nabila gidan xuwa gidan mahaifin ta dake kano, lokacin da labarin mutuwar nabila da mahaifin ta ya sami mahaifiyar nabila tayi kuka da baqin ciki sosai, ta xubar da hawaye na qunci game da irin mutuwar da suka yi, tana mai masu addu'a da nema masu gafara a gurin ubangiji.

*

Iyayen ilham kuwa basu d'auki abin da xafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login