Showing 9001 words to 12000 words out of 41393 words

Chapter 4 - Mulki Ko Sarauta Book 1 Complete Hausa Novel

Nawarty   

01 Oct 2025

388

daya bayan babu aure ko wata alaqa ta jini a tsakanin su wace mace xata yarda da hakan, har muka dawo Nigeria tana tare dashi idan tace tana da cikin aiman meyasa baxan yarda ba, nasan baxaku taba goyon bayana ba dalilin ya saka ni guduwa na barku ba dan bana qaunar ku ba wallahi Abba kuna raina bani da wasu a duniyar nan kamar ku dan Allah Abba ka taimake ni ka raba wannan auren.
[2/9, 8:45 PM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Tsura mata idanu yayi, maganar ta har cikin xuciyar ta take and again tabbas tayi masu biyayya na auren wanda bata so, ya riqo ta cikin tausayawa tare da fad'in that doesn't make you to ran away Afiya, kina tunanin mu baxa mu iya maki komai ba?

Sultan ya fashe da kuka ganin yanda mahaifiyar ta sa take kuka tun da yake da ita bai taba ganin kukan ta irin wannan ba, sai ya tsorata tunanin sa ko mutanen xasu cutar da su ne ya qanqame afiya sosai sai ihu yake a falon.

Umma ta shigo tare da sarki, aiman na tsaye a gefe tun d'axu kallo d'aya sarki yayi masu ya d'auke kansa tare da fad'in meke damun wannan yaron ne, xo ya tara hannu da niyar d'aukar sultan amma sai ya qanqame mahaifiyar sa tare da make kafada cikin jin tsoro bai san sarki ba.

Murmushi kawai sarki yayi ya xauna, umma ma ta xauna tare da yiwa aiman alama da ya sami guri ya xauna, da kyar ya motsa qafafun sa xuwa cikin falon yayi qoqarin d'aukar sultan shima yaqi xuwa gare sa, hakan ya saka Abba kyale afiya.

Ya soma jan hannun ta alamar su yi tafiyar su, ta girgixa kanta bayan ta xauna gaban sa tare da fad'in babu inda xamu je sultan wannan shine gidan mu, ya qanqame wuyan ta, no mami lets go back to our home, call uncle saif to save us from them, ya share mata hawaye tare da nuna Abba da yatsa wannan ya saka ki kuka ko mami I will tell my father to inject him kinji.

Ta rungumesa tsam a jikinsa tare da sauke numfashi a hankali ta soma rarrashin sa har aka samu yayi shiru yayi lamo a jikinta sai ajiyar xuciya yake sauke wa.

Sarki yace duk wani laifi na aiman kin riga kin wanke sa afiya dalilin guduwa na tsawon shekara hud'u ki bar iyayen ki da mijin ki batare da kin waiwaye su ba, hukuncin da xamu maki a yanxu shine da daren nan xaki koma gidan mijin ki, kowacce mace da kike gani a gidan auren ta haquri take, iyayen ku ma haquri suke da mu, menene auren idan ba haquri ba, maganar wulaqanci ko akasin sa daga aiman bana son qara ji ko gani idan ka qara kwatanta haka tabbas xaka had'u da fushi na mai tsanani yarima.

Afiya ta rarrafa gurin sarki ta riqe qafafun sa cikin kuka, dan Allah ka mini rai daddy baxan iya qara xama da aiman ba.

Sultan ma ya rarrafa ganin yanda tayi shima sai ya riqa qafafun sarki yana fad'in kayi haquri, Abba ya miqa hannu ya d'auki sultan d'in cikin tsananin son jikan nasa, sultan ya soma kiciniyar saukowa daga jikin sa You beat my mother I don't like you.

Aiman na xaune tun d'axu ya rasa wane irin yanayi yake ciki wai afiya ce take kuka haka saboda a raba auren su bata son xaman ta dashi, me yayi haka da xafi meyasa yanxu ta kasa gane damuwar da yayi saboda ita, he promise to change xai bata farin ciki irin wanda take so ko da kuwa baya son ta baxai qara wulaqanta ta ba, bama wannan ba wai yau kamar shi kuma a gabansa ake furta baa son sa, tun da yake a rayuwa an taba gayamasa magana mai xafi da muni kamar wannan kuwa, duk soyayya da rububin da yan mata suke akan sa a duk lokacin da ya gansu amma yau wata ke bud'e baki tace bata son sa, Anya kuwa shine ko dai gangar wani ce a jikin sa.

Sarki yayi shiru shima kamar ba xai yi magana ba sai can kuma yace xaki je gida inda ammi ne ki xauna kafin na gama yanke hukunci ko kuma anan xaki xauna inda umma?

Kafin afiya tayi magana Abba yayi carab yace rantsuwa nayi ranka shi dad'e rashin komawar ta gidan ta a yau yana nufin nima? na yafe ta kamar yanda ta yafe mu.

Hukuncin yayi tsauri Ahmed daga dawowar ta, baxaa bata kwana biyu ba cewar sarki.

Abba yace babu wani d'aga qafa ko tausayi da xaa nuna mata saboda itama tana yanke nata hukunci batare da tausayin ko mahaifiyar ta ba, wannan shine hukuncin da xan mata a yanxu tayi kuskure xata fuskanci hukunci dai dai lokacin aliyu ya shigo da sallama rumaisa na bayan sa d'auke da nasu yaron fu'ad mai shekara biyar a duniya ya bawa sultan shekara d'aya, idan baku manta ba tun su afiya na Phoenix aka haifi yaron.

Jin muryar aliyu ya saka afiya tashi ta nufe sa, qanqame sa tayi sosai tana kuka kamar ran ta, yaya ka taimake ni sun qi saurare na dan Allah kada ka bari su maida ni gidan yarima.

Aliyu bai yi magana ba yaja hannun ta suka fita daga falon, hankalin aiman ya tashi tun daga lokacin da aliyu ya rungume ta yaji ba dad'i duk da ya san d'an uwan ta ne na jini amma sam he is not happy, ina aliyu xai kai masa mata da yaja ta suka fita, idanun sa suka yi jawur, babu mai raba ka da matar ka yaji muryar Abba daga sama, suka juya suna kallon aiman d'in daya sunkuyar da kansa ransa ba dad'i.

Sarki yace ka axabtar da afiya k.... Abba ya yi saurin katse sa kome aiman yayi mata nasan taurin kai ne irin na ta kowa anan ya san halin afiya na naci da kafiya, mutum da matar sa har sai an shiga lamarin su, ku bar su tare da xuba masu ido xakuyi mamaki, sai kuma wani hanxari ba gudu ba idan afiya ta san da maganar auren aiman fa.

Da sauri aiman ya dube sa tare da fad'in xan saki ilham dama bana son ta.

Abba ya bata rai tare da fad'in ashe kai baka da hankali, saboda wata sai ka saki matar ka, itama matar kace kada ka manta nauyin ta da haqqin ta duka ya rataya kanka idan ka cutar da ita Allah baxai bar ka ba kada na qara jin irin wannan daga bakin ka, kayi qoqarin adalci tsakanin su.

Umma tace baka son ilham ka fara son afiya ne?

Yayi shiru xuciyar sa na bugawa saboda bai san wace irin amsa xai bada ba baya son yiwa iyayen nasa qarya ko kad'an, bai yi magana ba.

Sultan ya sauka jikin Abba yana kiran mami, fu'ad dama tun shigowar su yana jikin sarki, sultan na ganin fu'ad jikin sarki shima sai ya koma jikin Abba ya kwanta suna kallon juna.

*

Afiya ta dawo, dama tana raye tsawon wannan shekarun ta gujewa gidan nan tabbas afiya ta dawo xata riski mutuwar ta anan gidan, taya xan bari yarima ya zauna da wasu matan har guda biyu ina nan?

Wayar ta taje ta ciro a ma'adanar ta tare da soma kiran abbu yana d'auka ta sanar dashi komai cewa afiya ta dawo.

Yace afiya baxata mutu ita kad'ai ba nabila har da yarima duk xaa had'a a kashe su kowa ma ya huta idan baya duniyar xaki manta dashi tare da cire soyayyar sa a xuciyar ki.

Abbu koma menene ayi saboda a raba su da shi bana son xaman sa da afiya nafi kowa sanin irin son da yake mata, ya tsinke wayar tare da fad'in ina xuwa xan saka wani d'aya daga cikin bayin dana siye a gidan ya turo maki jakadiya wannan saqon shi xaki baiwa jakadiya muddin taqi aminta da abinda muke so tabbas xamu kashe ta,

Allah ya bar min kai abbuna, yayi dariya tare da tsinke wayar.
[2/12, 6:50 AM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Awa biyu tsakanin kiran nabila da abbu sai ga jakadiya taxo kamar yanda aka aika kiran nata cewa ana neman ta.

Bayan xuwan ta nabila ta kira abbu a waya ta miqawa jakadiya tare da fad'in xakiyi waya da mahaifina, tsohuwa ta karbi wayar ta Kara a kunne duk tunanin ta mutunci ne xaa yi, bayanin iyalanta da taji abbu na xayyanowa yayi matuqar bata mamaki da rashin sanin me hakan ke nufi ina ya san asalinta da dangin ta bata gama tunanin ba taji yana fad'in muddin kika qi aikata abinda nake so daga gare ki a yanxu tabbas xan wulaqanta ki tare da qulla maki sharrin da xaki mutu a wulaqance kuma yan uwan ki duka xan saka masu wuta na qona su gabaki daya a wannan qauyen.

Cikin tashin hankali jiki na rawa tace menene shi kuke so na aikata nayi hanyar da nabila xata kubuta ne kuke so.

Yace aa wannan hanyar da xaki bi ita xata saka ta kubuta ai, akwai wani garin magani xaki karba hannun nabila ki sakawa aiman da sarki a abinci su ci su mutu.

Bugawa xuciyar ta wannan karon yafi na farko, tsohuwa ta fashe da kuka tace meyasa xaka kashe wad'annan bayin Allah da basu da laifi akan hukuncin nabila sai bayan ita da ta janyowa kanta kuma meyasa ka xabi na aikata hakan batare da ka duba shekaruna ba?

Yace su waye bayin Allah wad'annan axxalumai kike kira da bayin Allah, mutanen da suka cutar da ya'ta suka bata mata rayuwa har kike tunanin xan kyale su, kina mamakin dalilin daya saka na xabe ki saboda yardar da sarki yayi maki ke kad'ai ce amintacciyar da sarki ya yarda da ita bayan matar sa akan abincin sa, ke kad'ai xaki iya aikin muddin kika bijire ko kika yi qoqarin tona asirina tabbas hakan na da nasaba da rasa taki rayuwar ne da ta yan uwan ki.

Jakadiya ta kasa magana sai kuka da take, tana ji tana gani nabila ta tsinke wayar ta bata garin maganin a leda ta juya ta koma makwancin ta, a ranar duk murnar da ake na dawowar afiya banda ita, sarki shine mutum na farko daya soma taimakon ta a rayuwa lokacin da suke tsananin buqatar taimako ita da mahaifiyar ta, mahaifinta ya rasu ya bar su, bata mantawa sarki siyen ta yayi a matsayin baiwa saboda gaskiya da riqon amanar ta da kuma yarda sarki ya yantata har ta dawo jakadiyar sa tun baa haifi aiman ba lokacin yayyun sa ne mata kawai ta sama a gidan, haihuwar aiman rainon sa da kula da shi duk a hannun ta ne bayan ya soma girma ne suka karbe shi amma yarima bai taba wulaqanta ta ko sau daya ba tun daga lokacin da yaji labari game da ita na dawainiyar da tayi nasa, sarki ya kai mahaifiyar ta Makkah kuma ya kaita Makkah sa'anan ya had'a ta aure da d'aya daga cikin dogarin sa, ya'yan su uku ya rasu ya bar ta da dawainiyar su sai ya xamana komai na su sarki shi yake yi, ta aurar da mata biyu namijin ne aka tura shi karatu sannan duk wata lalura ta gida ko yan uwa sarki ke mata komai, meyasa xata kashe wannan bawan Allah da d'ansa da hannuwan ta bayan sune suka d'ago tata rayuwar suka mata alherin da baxata taba mantawa da su ba, taya xata iya raba wad'annan mutanen biyu da rayuwar su da kuma iyalan su, idan taqi aikata abinda suke so daga gare ta wane irin toxarci ne xasu mata a masarautar bayan sun kashe dangin ta?

*

Relax Afiya bana son wannan kukan, idanun ki sun kumbura da yawa duk akan aiman, yarima d'an uwan ki ne na jini, kuma mijin ki meyasa kike haka, duk abinda aiman yayi maki a baya ki manta komai kiyi haquri wannan karon baxaa sami matsala ba kamar yanda kike tunani, bugu da qari Ma yanxu aiman ya damu dake wallahi aiman yana son ki ni shaida ne, aiman har yanxu bai san menene so ba bai san so ne ke dawainiya da xuciyar sa na afiya ba sai dai ya kasa gasgastawa ki yarda da ni kinsan baxan cutar da ke ba.

Tace yaya amma ya kake so nayi da saif, xuciyata ta aminta da shi har na bashi dama yaxo ya ga su Abba, he so caring shi d'in namiji ne da mace take son kasancewa da shi ka yarda da ni bashi da wani hali marar kyau da xai iya hana na aure sa.

Yace ya salam, meke damun ki afiya, me ya shiga rayuwar kine haka, saboda ya kula dake yayi sponsoring karatun ki that doesn't mean he so caring, you can't just make a decision on someone you don't know, had'uwar hanya fa, kinsan waye shi da asalin sa, kinsan wane irin mutum ne shi da har xaki amince masa.

Wallahi yaya saifullah baya daya daga cikin irin wad'annan mutanen da kake tunani, shekara hud'u dashi ba kwana hud'u ko awa hud'u bane, idan ya xo xaka gasgasta abinda nake gayama amma saif xuciyar sa tsarkakkiya ce daga abinda kake tunani yaya.

But afiya taya kika yi rayuwa da namijin da babu alaqa ta jini a tsakanin ku, please tell me wane irin xama kuka yi da saif haka? ta d'ago jajjayen idanuwa ta tana kallon sa,

Yaya idan ka xarge ni kenan kowa ma xai iya xargina a gidannan, kana tunanin xan xauna da wani domin na bata rayuwa ta daga ni har shi duk ba halin mu bane, saif bai taba kwatanta ko riqa hannuna ba saboda ya san da aure a kaina ban boye masa ba yaya.

Kina tunanin iyayen mu xasu yarda da wannan abin da kika bijiro dashi, kina tunanin idan kika bar aiman xai bar ki da sultan ba karban yaron sa xai yi ba, xaki iya barwa wata mace yaron da kika haifa kije kina auren wani a waje, ya kike tunanin rayuwar sa xata kasance xai sami irin tarbiyar da kike gani xaki fi yi masa fiye da wadda xata yi masa, idan sultan ya girma ya tashi a tunanin ki xai ji dad'in mahaifiyar sa ta bar mahaifin sa ta xabi wani bare shi kuma ta banxan tar dashi a gun wata mace, ke da ita wacece xai fi kallo da daraja?

Tabbas abinda aliyu ya fada gaskiya ne, tayi shiru cikin rudanin yanda xata bullowa wannan al'amarin, babu yanda aiman xai bar mata sultan karbe sa xai yi baxata iya rayuwa batare da yaron ta ba, ta d'ago da fuskarta sharkaf da hawaye tana kallon sa, yaya xanyi yaya dan Allah ka taimaka min.

Ya riqa hannunta tare da kafe ta da idanun sa, idan har kin yarda da ni to ki amince cewa aiman yana son ki a yanxu amma ya kasa yarda da xuciyar sa saboda bai san so ba, bai taba soyayya ba, da xaki bi nawa shawarar ki yarda ki xauna da mijin ki tare da dabarun nan naku na mata wanda shi da kansa xai xo ya bayyana maki irin soyayyar da yake maki afiya.

Yaya bana son shi a ynxu bana jin xan iya xama da shi ko da ban auri saif ba.

Yace xaki iya, kina son aiman bacin rai ne afiya and komai xai wuce idan kika kwantar da hankalin ki, aure dama jarabawa ce kowa fa haquri yake da dad'i ko akasin sa, babu auren da babu matsala komai qanqantar sa kuma aka yi haquri aka xauna cikin rufawa juna asiri, ammi tana fushi dake sosai afiya amma idan kika haqura kika xauna xai saka ta sauko daga fushin da take da ke wannan dalili ya saka kika ga ko xuwa bata yi ba.

Yaya ka bata haquri dan Allah.

Yace kada ki damu aike yar autar ammi ce, tafi son ki dani, tashi kije kiyi wanka kici abinci bana son ganin ki cikin damuwa ko kad'an.

Yaya idan ka fita ka turo min rumaisa, ya tashi yana fad'in ok tam.

Haka ta shiga toilet tayi wanka tana fitowa ta sami aiman tsaye tsakiyar d'akin da alama ita yake jira, bata boye mamakin ganin sa ba cos tun da take auren sa bai taba tako qafarsa xuwa d'akin ta ba baya wuce falon ta yaxo yayi abinda xai yi ya fice sai dai ita kullum tana hanyar xuwa turakar sa a duk lokacin daya buqaci hakan, kallo d'aya tayi masa ta gane akwai damuwa tattare a fuskar sa dan bata taba ganin sa cikin wannan yanayin ba, ta tabe baki had'e da rabawa ta gefen sa xata wuce babu xato taji saukar hannun sa a qugunta ya riqo ta, ya kafe ta da manyan idanuwan sa.
[2/12, 3:17 PM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Ta d'ago a fusace tana kallon sa, sai kuma ta soma qoqarin janye jikinta daga riqon da yayi mata, ya riqe ta gam tare da sassauta muryar sa.

Waye Saifullah, Menene tsakanin ki dashi, yaushe kuka had'u kuma wane irin xama kike dashi? Tayi shiru kanta a sunkuye batare da tayi magana ba,

Waye Saifullah ya tambaya wannan karon da kakkausar murya, cikin fargaba batare da ta dube sa ba tace friend.

Friend... ya maimaita tare da kafe ta da manyan idanuwan sa kamar a ranar ya soma ganin ta, abota da wannan baligin kina matar aure, ko kin manta wa kike aure, taya ma xaki had'a soyayyata da wancan yaron, me yake dashi?

Ta d'ago a hankali tana kallon sa, cikin sanyin murya tace shi bashi da kud'i sai rufin asiri, bashi da mulki ko sarauta, bashi da girman kai ko qasaita, shi mutum ne da yasan qima da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login