Showing 6001 words to 9000 words out of 41393 words

Chapter 3 - Mulki Ko Sarauta Book 1 Complete Hausa Novel

Nawarty   

01 Oct 2025

389

yi wannan karon da qarfi,

Waye? Sultan ya tambaya daga inda yake xaune, aiman yayi masa shiru, afiya tun da ta soma jin knocking ta soma wankan a gurguje ko masu aikin hotel d'in ne suka xo kawo abinci sanin yanxu saif ya bar d'akin.

Who is that? Sultan ya qara tamba??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ya, da kyar aiman yace xo ka bud'e qofar.

Ya make kafada kamar yana ganin sa yace mami tace kada na kuskura na bud'e wa kowa qofar.

Aiman yace xo ka bud'e I have some chocolate for you.

Sultan yace bana so, mami ta siya min ina da su.

Aiman ya dafe kansa kafin ya sassauta muryarsa a hankali yace sultan xo ka bud'e qofar its your hospital friend from Portugal ka tuna.

Shiru sultan yayi na dan wani lokaci sai kuma ya tashi yaje da sauri ya d'ora stool a qofar d'akin ya hau ya bud'e qofar yana ganin aiman ya ware ido cikin mamaki tare da fad'in friend.

Aiman ya d'auke sa cak tare da rungumeshi kyam a jikinsa, wani sanyi yake ji a xuciyar sa ya kaiwa sultan peck a kumatu yana lumshe idanuwan sa, d'agowar da xai yi suka yi ido hud'u da afiya da ta fito wanka a gurguje daure da towel jin sultan ya bud'e qofar da ta hane sa da kada ya bud'e.
[2/8, 3:42 AM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Lokaci d'aya zukatan su suka buga tare da tsurawa juna ido kamar a ranar suka soma ganin juna.

Sultan ya dube ta tare da fad'in mami shine yace na bud'e masa, shine wannan friend d'in nawa na asibiti kinga shikenan ba sai kin kai ni ba.

Aiman ya sauke sultan, Afiya kuwa juyawa tayi da sauri ta koma bedroom ya bi ta da kallo.

Ya kasa yarda yau shine a gaban afiya, Afiya ta canxa sosai daga yanda ya san ta, sultan ya riqa hannun sa yana fad'in friend xo muje na kai ka gurin mami na, she is nice and she will like you cos kullum ina bata labarin ka kuma tace xata kaini inda kake a Portugal.

Yanda sultan d'in ke jansa ya saka aiman bin bayan sultan d'in yana riqe da hannun sa har cikin d'akin da afiya take, tana gaban mirror ta ga shigowar su, juyowa tayi a fusace cikin bacin rai fuska a daure har ta bud'e baki xatayi magana sai kuma ta fasa a ganin ta ba itace ya kamata ta fara yi masa magana ba, ya same ta gidan ta meke tafe dashi waye ya nuna masa inda take sannan menene dalilin sa na xuwa har bedroom nata batare da yayi sallama ba.

Aiman ma shiru yayi ya xuba mata idanu yana jiran ta soma yi masa magana, yana ganin idan ya fara mata magana a matsayin sa na mijin ta kuma babba a gare ta girma ya fad'i.

Mami ga New friend d'ina wanda nake gayamiki yaxo ya gaida ki.

Ta maida duban ta gare sa a fusace kamar mai jira tace sai kuma akace ka shigo min da mutum har tsakiyar d'akina kamar gidan uban ka?

Sosai Aiman yaji xafin kalaman ta duk da ya lura acikin xafi take, menene laifin sa a wurin afiya haka da kusan shekara hud'u ta kasa mantawa take jin xafin sa har yanxu? Kallon Sultan yayi da kyar ya bud'e baki ya soma magana a hankali dama dabi'ar sa ce baka taba jin yayi magana cikin d'aga murya ko hayaniya kome bacin ran dake xuciyar sa, yace sultan tell your mother, your father's mansion is better than wannan rumfar d'akin da take hargowa a kansa ake kira d'aki ya fad'a yana kallon d'akin a wulaqance cikin tabe baki.

A maimakon sultan ya fad'i abinda akace sai ya juya sosai yana kallon aiman, ka san daddy na, a ina yake, xaka kaini gurin sa, mami tace very soon xata kaini gurin sa xai siya min ball, ya kaini parks, tace kuma yana da horses a gida xaa d'ora ni akai, a canxa min school, wai haka ne?

Aiman ya gyad'a kai batare da yayi magana ba sai ya dubi afiya har xai yi magana sai kuma ya juya ya fice tare da fad'in ina jiran ki a wannan banxan falon da kika biya kud'in sa har kike wa mutane fade.

Ta daga murya kad'an yanda xai jiyo ta, kada ka jirani kana batawa kanka lokaci is better ka koma inda ka fito, wannan gurin xama ne ni nake da iko da shi ka tafi pls.

Ransa ya baci ya dubi wurin da afiya take goran ta mashi a yau, sai ya soma kwankwanto a xuciyar sa cewa wannan ba afiyar sa bace da ya sani years ago, a rayuwar sa banda sarki da umma akwai wanda ya taba korar sa a guri kuwa, balle akan abinda yake da iko dashi ko afiya ta manta matsayin sa a gun ta ne.

Ke matata ce ko kin manta? Afiya ta ware idanu tana kallon sa da mamakin jin ya kira ta da matar sa tun da take dashi har ta barshi bai taba kiran ta da sunan matar sa ba sai dai yace cousin duk wanda xai tambaye sa ko friends ne a skul sai dai yace qanwar sa ko kuma cousin menene dalilin bata wannan matsayi na matar sa a yanxu.

Tace xaka bani takardar saki na ne.

Yayi murmushi yana kallon tsakiyar idanun ta sai kuma ta ga ya ciro wayar sa, bata san dawa yake wayar ba taji yana fad'in na ganta sai kuma taji ya bada sunan hotel d'in da take, Allah yasa ba Abba bane yake kira, shi da waye suka xo?

A maimakon ya fita sai ya sami guri ya xauna a saman gadon ya miqe qafafun sa tamkar a d'akin sa batare da ya qara kallon ta ko nuna damuwa da tsayuwar ta a gurin ba, amma a xuciyar sa tamkar an masa albishir ne ya kasa tantance wane irin farin ciki xuciyar sa take ciki na ganin afiya a yau, me xai yi ya burge ta dan ta sauko daga fushin da take dashi, inama xata amince dashi a yanxu cewa ya canxa xai kula da ita.

Bata qara bi ta kansa ba tayi shigewar ta toilet dama doguwar riga ce a jikin ta, tana gama shirin ta a ciki ta fito daga d'akin xuwa falo tayi xaune xuciyar ta a cunkushe, waye aiman ya kira a waya,? ashe har yanxu aiman bai canxa ba, wannan qasaitar da jan aji har yanxu suna nan, har yanxu baya son ta bai damu da ita ba kenan tunda bata ga alamar hakan a tare dashi ba, ina baxata iya wannan xaman dashi ba a yanxu baxata iya cigaba da rayuwa dashi cikin wulaqanci da nuna isa ba, saifullah shine dai dai da tawa rayuwar ta fada a hankali batare da tasan maganar ta fito a xucci ba.

Waye saifullah, menene tsakanin ki dashi, da aure na akan ki kike dai dai ta rayuwar ki da wani qaton banxa, wace irin rayuwa kika yi bayan barin ki Nigeria? taji muryar da kamar daga sama a bayanta, hankalin ta ya tashi xuciyar ta ta soma bugawa sai dai bata nuna ba, ko motsi bata yi daga inda take xaune ba balle ya saka ran amsawar ta.

Waye saifullah ya qara tambayar ta, Sultan ya matso yana kallon sa tare da fad'in shine uncle d'ina wanda muka je asibiti da shi, yana da kirki kullum yana xuwa inda mami ya d'auke ni muje yawo, yana kaini skul idan suzana tana aiki sosai kuma yana d'auko ni, at school ya ce he is my father idan muka dawo gida ya xama uncle d'ina, friend tell me meyasa yake hakan?

Aiman xai yi magana wayar sa ta d'auki qara, ganin wanda ya kira sa yayi saurin karawa a kunne.

Afiya tana ji yana bada room number na d'akin sai dai ita xuciyar ta a jagule take ta kasa fahimtar me aiman ke yi kuma waye yake nufin ya shigo, bata gama tunanin da take ba taji ana knocking.

Aiman ya dubi sultan tare da fad'in open the door.

Mami wai na bud'e door d'in, tayi masa shiru aka qara knocking sai sultan ya nufi qofar da gudu ya bud'e.

Who are you? Sultan ya tambaya yana kallon Abba dake qoqarin shigowa.

Afiya ta d'ago tana kallon ko waye ya shigo, lokaci d'aya ta tashi tsaye cikin matsinancin fad'uwar gaba ta xuba wa fuskarsa ido shima ita yake kallo, Aiman na kishingide yana kallon su, ga mamakin afiya maimakon taga abban ta ya d'auki xafi a kanta sai ta ganshi ya qaraso a hankali tare da ware mata hannuwansa, ba shiri kuwa ta fad'a jikinsa tare da fashewa da kuka, ya rungume ta a hankali yana buga bayan ta cikin shigar rarrashi, sultan da bai san abinda ke faruwa ba ganin ta rungume Abba shima sai yaje ya rungume qafafun Abba.
[2/8, 3:07 PM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

We are leaving afiya yanxu, ta d'ago a hankali daga qirjinsa tana kallon sa.

Abba yanxu b.... Shshshshs ya d'ora yatsansa akan labbanta, umarni ne nake baki, shiga ciki ki had'o kayan ki.

Aiman dake xaune yaji dad'in wannan hukuncin na Abba ganin taqi tafiya kamar yanda aka umurce ta sai aiman ya tashi da kansa ya shiga bedroom na ta ya soma had'a kayan da kan sa, bayan ta shigo d'akin ta jingina da qofar tana hawayen baqin ciki bata son kasancewa da yarima baxata taba yarda su maida ta ba ko da kuwa hakan na nufin barin duniyar ta kenan, baxata qara yarda da xaman qunci da wulaqanci ga mutumin da bai san darajar ta baya qaunar ta ba, ta share hawayen kafin ta qara sa shiga ta soma had'a wasu kayan batare da ta kula da shi ba, yarima mamaki yake bata yanda yake had'a kayan a natse ba kamar ita da xuba su kawai take a jaka ba, bata taba tunanin girman kai irin na yarima xai barshi ya had'a mata kaya ba, ta tabe baki tare da fad'in koma menene baxan xauna dashi ba, d'agowar da xata yi yayi dai dai da shima ya juya bisa rashin sanin sai suka bigi juna, baya tayi xata fad'i yayi saurin taro ta xuwa qirjin sa, idanun ta a rufe a tunanin ta xata ji ta ne a qasa sai taji ta a faffadan qirjin sa, ta kwace jikin ta cikin xafi da baqin cikin da? rungumar da yayi mata, ta ja qaramin tsaki bata ankara ba taji saukar yatsun sa a qaramin bakin ta ya mintsine ta a hankali tare da fad'in har kin manta policy d'ina, bana son tsaki Afiya kin sani, batare da ya jira cewar ta ba ya juya janye da trolly d'in ta, ta bishi da idanu tare da dafe kanta da hannuwan ta duka biyu tana fad'in na shiga uku har yanxu aiman bai canxa ba, a haka Abba yake son tilasta min na xauna da shi, ina baxan iya ba baxan iya cigaba da rayuwa ta a haka batare da jin dad'i na aure ba, xan gabatar masu da saif a matsayin wanda xan aura ko da basa son sa ni xan aure sa saboda jin dad'i da kwanciyar hankali da xan samu a gurin sa nima na dandana soyayyar d'a namiji tare da ni, na sami kulawa da tarairaya tare da nuna min tsantsan so a gurin namijin da nake aure, ya Allah ka duba min ka cika min wannan burin nawa.

Cikin qanqanin lokaci ta gama shirin ta had'a komai ta fito ko da taxo Abba da sultan basa falon sai aiman kad'ai xaune kamar wanda aka saka tsaron ta, ta d'auki wayar ta dake kan sofa ta soma laluben wayar saifullah ringing d'aya biyu ya d'auka, tayi Jim kafin tace we are leaving Saif.

Jin ta ambaci saif ya saka aiman d'agowa yana kallon ta tare da jin fad'uwar gaba.

Yau kuma afiya, meya faru.
Ta share wasu kwallah tare da fad'in mu had'u Nigeria kada ka manta insha Allah komai ya xo qarshe, I want to be with you forever in my life.

Saifullah ya tsorata meya sami afiya bayan barin sa hotel d'in yanda muryar ta ke rawa ya tabbatar masa da kuka take, yace just wait for me afiya I will be on my way yanxu pls.

Bai xama dole ka same ni ba, ka fahimce ni ba tafiyar kaina bace, Abba ne ya xo sai ta fashe da kuka mai tsanani tare da tsinke wayar.

Aiman na xaune ya rasa a wace duniya yake ya rasa xafin menene yake ji a xuciyar sa da kuma dalilin xafin tun daga lokacin da ya ji ta furta tana son kasancewa da wani qato bayan da auren sa akan ta, ko da yake menene nasa Ma na damuwa da shaanin ta bayan ya san baya son ta kuma baxai iya son wata mace ba bayan umman sa, meyasa wayar da take yi da wani xai saka shi damuwa bayan ya san soyayyar afiya bata gaban shi kuma bai damu da ita ba, har Abba da sultan suka dawo yana cikin damuwa.

Ko da suka shiga jirgi shi da sultan suka xauna guri daya afiya da Abba, duk yanda ya so kauda damuwar afiya da saif ya kasa bai san dalili ba, kwata kwata baya jin dad'in rayuwar sa a rana ya kasa tantance a wane yanayi yake murnar samun afiya a yau ko kuma baqin cikin rataya afiya da wani banxa wanda yake gani dole xai d'auki mataki babba a gurin wannan saif d'in a duk lokacin da ya tako Nigeria har masarautar su da sunan yaxo ganin afiya kamar yanda yaji ta fada a waya yana jiran lokacin.

Ko da suka iso airport tuni motocin sarki sun cika airport d'in sun xo tarbar su.

Ilham kam ta kasa samun nutsuwa a yau tun lokacin da taji jakadiya na sanar da umma a d'axu xuwan afiya saboda su yarima sun same ta, ga mamakin yanda maaikatan gidan manya da qanana ke nuna tsantsan farin ciki da dawowar afiya masarautar merah, wane irin farin jini ne da afiya haka, wane irin matsayi take dashi a gidan, wace irin mace ce haka, meyasa kowa ya damu da ita musamman? har da rumaisa yau gata a gidan tana tuna tun lokacin da aka kawo ta gidan sau d'aya qanwar mijin nata ta taba yi mata magana bayan shi bata qara karantawa ba duk yanda ta so kuwa bata sami fuska a wurin rumaisa dake nuna mata qiyayya a fili ba, wane irin malami ko boka ne afiya tayi amfani dashi wurin siye xuciyar mutanen gidan da basa ganin kowa sai ita?

Tana jin sautin busan sarewa ya canxa ta tabbatar da xuwan su, da sauri ta nufi window tana kallon su taga fitowar aiman riqe da qaramin yaro a hannun sa, daga baya Abba ya fito, ta xuba ido sosai tana tsumayen fitowar afiya bata san tun bud'e gate d'in gidan ba afiya ta fice daga motar tayi cikin gida inda umma tana kuka sosai.

Shiru shiru babu alamar fitowar afiya har ta gaji da jira ta bar wurin sai dai xuciyar ta a cunkushe take da alamar tambaya kan yaron da ta gani hannun mijin ta mai kama dashi tamkar an tsaga Kara.

Mami ina ne nan, lets go back ni bana son nan garin kinji.

Tace lemme pray sai mu koma ai dama we are not going to leave here.

Ya xauna a takure yana kallon ta tana sallah he feel bad baya son qasar ko kad'an yana jin xafin ta sannan mutanen da yake gani gidan tsoro suke bashi musamman wad'anda yake gani da xungureriyar bulala wasu da bindiga da dai sauran su.

Tana cikin sallah Abba ya shigo falon jin tana d'akin umma tana sallah ya saka shi xama a falon yana jiran ta bayan ta gama wata baiwa ta sanar da ita xuwan mahaifin na ta, ta riqa hannun sultan suka fita tare.

Kallon ta yayi fuska a d'aure kamar ba shi ba, yace xan tafi daga nan ki koma d'akin mijin ki idan kika saba umarni na ban yafe maki ba xaki iya guduwa ki bar duniyar gaba ki d'aya ma.

Shine abinda aiman yaji lokacin da yayi stepping cikin falon.

Kuka afiya ta fashe dashi, ta riqe sa gam kamar wacce tayi believing cewa rayuwar ta tana hannun sa xai gudu da rayuwar.

Abba ka taimake ni dan Allah kayi haquri wallahi bana son yarima baxan iya xama da shi ba wallahi bana son s..... tayi shiru sakamakon marin da Abba ya d'auke ta dashi aiman ya rumtse idanuwan sa jin kalaman afiya.

Idan bakya son sa uban wa kike so, yanxu kika san ni uban ki ne kike neman taimako na, menene laifin aiman daga sharrin da waccan axxalumar mace tayi masa da xai saka ki gudu ki bar qasa batare da tunanin halin da xai shiga ko mu iyayen naki xamu shiga ba, meyasa baki je gida ba inda mahaifiyar ki ita kad'ai baxata iya share maki hawayen ki ba batare da mu mun dani ba, ki sani idan baki koma gidan ki ba babu ni babu ke ya juya xai fice ta sake riqo sa a Karo na biyu, ya juyo a fusace da niyar kai mata duka suna had'a ido jikinsa yayi sanyi kuka take mai tsuma xuciya.

Abba aura min shi kuka yi bana son sa na xauna dashi nayi biyayya saboda ku, Abba na bishi qasar da ban da kowa acan bayan Bilal, ya hukunta ni acan ya wulaqantani acan batare da tunani nima qanwar sa bace koda baya min kallon matar sa, Abba aiman bai taba sona ba ya gayamin baxai taba sona ba, Abba wannan nabilar xaune take a gidan sa batare da ya d'auki mataki ba, na jure xama da wata mace tare da mijina a gida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login