Showing 36001 words to 39000 words out of 41393 words

Chapter 13 - Mulki Ko Sarauta Book 1 Complete Hausa Novel

Nawarty   

01 Oct 2025

393

ya dube sa tare da yin murmushi ana shopping dasu, ana bawa masu buqatan taimako.

Yace daddy nima kabani, kayi me dasu aiman ya tambaya.

Nima naje nayi shopping, aiman ya girgixa kansa alamar baxai bashi ba, sultan kuwa ya shagwabe fuska kamar xai yi kuka dai dai lokacin suka shiga falon umma.

Baxan yarda ba sai kabani, aiman ya kyale sa bai kula sa ba, yaron ya soma kiciniyar saukowa jikin sa yana kuka ka bani kud'i.

Kayi me dasu, umma ta tambaya tana kallon su.

Aiman kallon ta yayi kafin ya maida duban sa ga sultan dake ture sa alamar ya ajiye sa yace taya kake tsammanin xan baka kud'i bayan mahaifiyar ka bata nuna maka kud'in ba, baka san kud'in bama sai yau ta dalilina dan haka ko kwandala baxan baka ba at your age ban san me xaka yi da kud'i ba.

Sultan ya qara sautin kukan sa tare da fad'in ni sai ka bani kud'i, aiman ya kyale sa babu xato yaji cixo a qirjin sa sultan ya kai masa, yana d'ago da fuskar sa ya kai masa lafiyayyen mari ransa a matuqar bace dai dai lokacin Afiya ta shigo, umma ta tashi da sauri ta nufe sa tare da fad'in sai ka mare sa yarima wannan qaramin yaron,

Umma cixo na fa yayi, umma ta karbi sultan da tuni numfashin sa ya d'auke saboda tsananin tsoro baa taba dukan sa ba balle mari sai dai tsoratarwa da saif keyi masa da bulala duk sanda yayi laifi ko baya jin magana.

Baya numfashi aiman, jin haka yasa gaban afiya fad'uwa ta qarasa falon, kallon ta aiman yayi kafin ya maida kallon sa ga umma tare da fad'in kisa masa ruwa xai tashi.

Duk da hankalin afiya a tashe yake sosai sai bata nuna ba, ta qarasa gurin aiman tare da fad'in bai ji maka ciwo sosai ba ko.

Aiman ya soma balle maballin rigar sa tare da fad'in nima ban sani ba amma akwai xafi.

Umma da kyar ta samu sultan ya farfado sai fada sosai take yiwa aiman, sultan kuwa sosai ya qanqame ta yana kuka koda aiman ya bud'e gurin yayi jawur sosai a farar fatar jikin sa, bai san xafin cixo ba sai yau akan sultan.

Daddy ya mare ni,? shine abinda kawai yake fad'a yana nuna wa umma fuskar sa, aiman ya juya ya bar falon afiya tabi bayan sa.
[2/29, 8:25 AM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Sashen sa ya nufa kai tsaye bedroom d'in sa, ya cire rigar gabaki d'aya yana kallon inda sultan ya cije sa ta madubi, jin motsi ya saka sa saurin juyawa yana kallon qofar shigowa tare da tunanin waye xai shigo masa babu neman ixini.

Kallo d'aya yayi mata ya d'auke kansa a hankali, afiya ta taka har xuwa inda yake tsaye suka tsurawa juna idanu ta madubi, da kyar ya bud'e baki yayi magana a hankali kamar wanda baya so.

Yace ilham tana da juna biyu.

Ji tayi komai na ta ya tsaya cak, duk wata jijiya ta jikinta ta daina aiki tana tsaye ta kafe sa da manyan idanuwan ta cikin son gasgasta xancen sa, ya juyo gabaki d'aya yana fuskantar ta, ban san da xancen ba Saif ke gayamin bayan yaxo asibiti shekaranjiya.

Cikin rawar murya ta bud'e baki da kyar, amma kace baka d'ora mata iddah ba, baka taba kwanciya da ita ba, ina ta sami cikin, wannan cikin ba naka bane aiman ta fad'a tana kafe sa da idanun ta da suka cika da kwallah.

Ciki na ne ya fad'a yana riqo hannun ta, ni dutse ne afiya? I have feelings right, and ilham is my wife, maganar wannan cikin da ya bullo yanxu ya saka xan maida ilham ta dawo gidan nan tamin rainon baby ta haihu a hannuna muyi rainon baby tare, dalilin wannan cikin na ilham xaki iya guduwa ki bar duniyar ma gabaki d'aya I don't care.

Ya juya yana cigaba da abinda yake babu xato yaji ta rungume shi ta baya cikin matsinancin kuka sosai, baka isa ba baxaka dawo da ita ba, idan har xaka dawo da ita ta haifa ma wannan cikin sai dai ka kashe ni, kaci amanata aiman.

Murmushi yayi tare da juyo da ita gabansa, ya d'ora hannun sa a qugunta tare da matse ta a jikinsa gam yana shaqar qamshin jikinta ya lumshe idanunsa a hankali kafin yace baxan kashe afiya da hannuna ba nafiso ta gudu ta barni da ilham kamar yanda tayi a baya ta barni da nabila, nasan ilham tana sona duk abinda xanyi anan gaba baxai saka ta rabuwa dani ko tunanin taje ta barni har tsawon wani lokaci ba, ya bud'e idanunsa yana kallon ta sun yi jawur sosai na roqe ki idan xaki je a wannan karon kada kije da sultan ki barshi tare da mahaifin sa.

Ta qanqame shi cikin kuka sosai why aiman, meyasa ka kasa sona sai ilham, meyasa kake min haka, ta soma dukan qirjinsa, ya riqe hannuwan gabaki daya tare da fad'in kada ki jimin ciwo ke ki daka d'anki kuma ya cixa, laifina ko naki ashe baxaki iya xama dani ki rufa min asiri ba koda kuwa nabila tana d'auke da cikina, meyasa xaki gudu ki barni idan har kina sona da gaske.

Tace cos you show me hatred aiman, ka nuna bani da girma ko wani matsayi a tare da kai, ka wulaqanta ni a gaban friends da masu aikin mu, ka nuna wa duniya baka son afiya kuma baxaka taba son ta ba, na tafi ne domin na sami sauqin damuwa ko da xan manta da kai na cire soyayyar ka a xuciya ta but I can't, I didn't know how to stop loving someone as dangerous, tainted and flawed as you, naso kasancewa da saif saboda na huce baqin cikin da har bayan dawowa ta aiman is still telling me baya son afiya but he cares, meyasa su ammi suka kasa fahimta ta suke tursasa min xama da kai?

Murmushi aiman yayi tare da tallabo fuskarta ya sumbaci bakinta kad'an kafin yace saboda sun san aiman xai so afiya kuma aiman yana son afiya, ta bud'e idanun ta sosai tana kallon sa, ya gyad'a kai cikin tabbatarwa, yace nayi kuka rashin amini kuma aboki afiya, nayi rashin Bilal he stand by my side ko yaushe, shi kad'ai ke iya kallon idanuna ya gayamin gsky, ya gayamin xan so afiya fiye da yanda take so na, na wayi gari ina matuqar son afiya a lokacin da Bilal baya duniyar, nayi kuka rashin afiya a kusa dani ranar da Bilal ya barni, nayi kuka alokacin da afiya ke kallon idanuna ta gayamin tana son wani daban, yaja numfashi kad'an xuciya tana xafi da rad'ad'i afiya a duk sanda wannan Kalmar ta fito daga bakin ki, you change me, bansan so ko akasin sa ba sai akan ki, ban san damuwa da baqin ciki ba sai ta dalilin ki.

Xatayi magana ya d'ora yatsansa akan bakin ta yayi shiru yana kallon ta, ta lumshe idanuwan ta, ya cigaba da fad'in a gaban kowa xan iya nuna soyayyata da afiya, xan iya sanar da duniya dimbin soyayya da aiman ya kasance acikin ta, ki min afuwa da abinda ya faru a baya ba laifina bane.

Ta bud'e idanunta a hankali tana kallon sa da kyar.

Taya xan amince da abinda kake gayamin.

Yace na taba maki qarya ne?

Ta girgixa kanta a hankali tare da fad'in cikin dake jikin ilham fa, baka son ta har hakan ta faru? Ka kasa riqe amana da yarda da nayi ma aiman idan har xaka iya kasancewa da wata macen bayan ni,

Shiru yayi yana kallon qaramin bakin ta banda tsananin kishi babu abinda yake gani a furucin nata wanda ke fitar da bitterness na maganar da take, ya janyo hannunta ya d'ora a santar xuciyar sa batare da yayi magana ba.

Yace ina roqon Allah ya bani ikon riqe ki da amana da soyayyar da bata yin rauni sai ranar da na bar numfashi da duniyar gabaki d'aya, babu cikina a jikin ilham ban taba kasancewa da wata mace ba, baxan sami farinciki da nutsuwa a gurin kowa ba bayan afiya saboda ita ta fara bani wannan jin dad'in, ta canxa min rayuwa ina son kasancewa da afiya har tsawon rayuwa ta.

Ta d'ago fararen idanunta tana kallonsa, kwayar idanunta narai narai da hawaye, kwayar idanun sa ta tabbatar mata da abinda ya fad'a, haka yake har xuciyar sa ta lumshe idanuwan ta had'e da d'ora kanta a qirjinsa, Ya rungumeta tsam suna sauke numfashi a hankali....

Asuba ta gari Aiman & Afiya....

Washe garin ranar Afiya da kanta ta shiga kitchen tare da jakadiya suka had'a breakfast.

Fitowar aiman ya saka jakadiya nufar sa, kamar ko yaushe bayan ta gaidashi ta qara da cewa kayi min afuwa akan laifina yarima dan Allah ka yafe min ka kuma roqa min sarki ya yafe min daga hukuncin da yake son yi min.

Wane irin hukunci kuma jakadiya? Aiman ya tambaya yana kallon ta cikin mamaki.

Cikin hawaye tace nima ban sani ba amma tun daga ranar har yau sarki bai qara amsa gaisuwa ta ba bai qara nema na saka ni wani abu daya shafe sa ba kamar kullum, ina cikin damuwa dan Allah ka saka min baki yarima.

Yace shikenan ba damuwa, axo min da sultan yanxu.

Ta tashi da sauri ta fice tare da fad'in an gama ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ranka shi dad'e.

Yana xaune a wurin jakadiya ta dawo d'auke da sultan har lokacin afiya bata gama shiri ta fito ba, sultan na ganin aiman ya qanqame jakadiya sosai yana ihu baya xuwa dai dai lokacin afiya ta fito ba qaramin kyau tayi ba cikin simple make up d'in ta, sultan na ganin ta ya sauka jikin jakadiya ya nufe ta da gudu ya rungume qafafun ta kamar xata fad'i.

Miye haka sultan, xaka sa na fad'i.

Mami take me away from him, duka na xai yi I don't want to see him again, ta d'auke sa tana murmushi, meyasa xaka cije sa.

Yayi shiru yana kallon ta kafin yace mami take me back to granny ni bana son nan.

Daga can aiman yace babu inda xaa je da kai and idan naji ka bud'e wannan bakin xaka min kuka ko.....

Jin muryar aiman ya saka shi qanqame afiya sosai yana sheshshekar kuka, da gaske tsorace yake da aiman sosai, afiya ta dube sa tana murmushi tare da fad'in kaxo kayi breakfast d'in tun d'axu kake maganar xaka je asibiti ko ka fasa ne.

Aa ya bata amsa yana tashi tare da nufar dinning, tayi qoqarin ajiye sultan d'in kan dinning yaqi sauka ta dube sa.

Taya xanyi serving ka maqale min haka ka xauna mana.

Mami take me to uncle saif, I don't like this house let's go back to our house.

Sauka daga jikin ta ka xauna anan aiman ya fada fuska a murtuqe tare da nuna masa kusa da shi.

Babu musu jiki a sanyaye ya sauko cikin tsananin tsoro ya nufo inda aiman d'in ya xauna inda ya nuna masa cikin takura, Afiya tayi murmushi ta soma serving d'in su itama kusa da aiman ta xauna, sultan ya soma qoqarin sauka ya nufe ta aiman ya harare sa ba shiri ya koma ya xauna suna had'a ido da afiya ya fashe da kuka tare da nufar da gudu.

Karki d'auke sa aiman ya fada cikin bacin rai tare da saka hannu ya fisgo sa ya maida shi inda yake xaune.

Ka min shiru, duk wanda ka qara cixo a gidan nan xan maka abinda yafi wancan, fara breakfast kada na ji maka ciwo yanxu.

Hannun sa na rawa ya d'auki plantain sai dai ya kasa kaiwa bakin sa, sallamar da umma tayi ya saka su juyawa gabaki daya suna kallon qofar shigowa falon, sultan na ganin ta ya nufe ta da gudu yana kuka sosai kamar ransa, ran aiman ya baci matuqa ya tashi ya nufi inda umma tare da qoqarin karban sultan d'in a hannun ta ai kuwa ya qanqame umma yana ihu sosai akan baxai je ba he don't like aiman.

Tace me kake yi haka yarima.

Yace umma yaron nan baya jin magana, na xaunar dashi nace kada ya tashi shine xai tashi ni xai nuna wa stubbornness, xan yi maganin sa kuwa.

Tace dukan sa xaka yi kome? Baya jin magana kai kana jin magana ne menene baka yi a gidannan ba aka haqura aka xauna da kai akwai wanda ya takura ma ko ya dake ka, ka fita daga idona yarima allow him bana son damuwar sa, and again kaxo tare da afiya yanxu sarki yana son ganin ku, ta juya d'auke da sultan ta fice sai ajiyar xuciya yake sauke wa.

Afiya ta taso ta nufo sa, mu qarasa breakfast d'in tukunna sai muje, yace aa akwai matsala sarki xai aiko umma taxo kiran mu.

Ta dube sa cikin fad'uwar gaba, ai bamu yi wani laifin ba ko.

Aiman yayi shiru yana tunani sai kuma ya dube ta ki saka alkyabba da sauri ina jiran ki.

Ko da suka isa falon sarki sultan na xaune gaban sa suna breakfast tare sai labarin daddy sa yake basa jiya ya dake sa, umma na gefen su ga mamakin su aiman har da su ammi da Abba a falon ko yaushe suka xo.

Ya gaidasu kafin ya juya ya gaida sarki, afiya ma ta nufi iyayen nata cikin farin cikin ganin su.

Sultan ya nunawa sarki aiman tare da fad'in shine daddy na daya dake ni jiya, let him go kace kar ya qara duka na kuma.

Aiman baiyi magana ba ya sami guri ya xauna jiki a sanyaye, sarki kuwa murmushi yayi wa sultan tare da gyad'a masa kai.

Abba ya dubi aiman tare da fad'in mun xo mu tafi da afiya.

Ba aiman ba hatta afiya sai da ta dubi mahaifin nata a raxane.

Aiman ya dubi iyayen sa sai wasa suke da sultan tamkar basu ji abinda Abba d'in fad'a ba kafin ya juya yana kallon Abba cikin tsananin mamaki yace Abba ina xaku je da ita.

Abba yace lokaci yayi da xaa raba auren ku da afiya saboda ta auri wanda take so, iya biyayya tayi mana na xama da kai alhali baka son ta kuma baxaka taba son ta ba dalilin haka ya sanya xamu d'auke ta, takardar sakin ta sai ka bawa mai martaba.

Cikin tsananin rudani aiman ya nufe sa, Abba before kake magana yanxu ba haka bane, ina son afiya itama shaida ce.

Is too late Abba ya fad'a yana tashi tsaye tare da kallon afiya ke tashi mu tafi.

Aiman ya rude ya nufi sarki, daddy talk to them su barmin matata ina son ta da gaske abinda nayi a baya kuskure ne amma sincerely speaking bansan menene so ba sai akan afiya dan Allah kar ka barsu su rabani da ita.

Afiya ma hankalin ta ya tashi sosai ta riqe hannun ammi, tace ammi kice Abba ya barni da aiman xan iya xama da shi har qarshen rayuwa ta koda baxai so ni ba.

Tace saboda baki san ciwon kanki ba ko, tashi mu tafi inaji last xuwan ki da kuka kika je akan sai an raba auren bakya son xama da aiman ai har da kayan ki kika tafi dasu yanxu kuma xamu yi maku abinda kuke so aiman baya son ki kema bakya son xama da shi shikenan an raba ku.

Umma please talk to them aiman ya fada cikin tashin hankali, sarki ya dubi Abba tare da fad'in babu abinda xan ce sai godiya akan abinda kayi na kyautatawa aiman, ka bashi mata Karo na farko bai riqe ta da daraja ba bai bata kulawa irin wacce mace xata buqata a gurin mijin ta ba sai wulaqanci da ji da sarauta, ka d'auki mata Karo na biyu ka bashi tsawon shekara biyu bai riqe ta da daraja ba sai kawai ya sake ta, ni na goyi bayan ka tafi da afiya takardar ta xata xo daga baya aiman sai yaje ya nemi irin macen da yake so ya aura.

Daddy wallahi Afiya nake so, ita kad'ai nake so please daddy kayi haquri, ya nufi Abba tare da riqe hannun sa kayi haquri ka yafe min for my mistakes amma kada ka raba ni da afiya ina son ta.

Ammi ta fisgi hannun afiya ta ja ta cikin bacin rai sosai afiya ta soma kuka, Abba komai bai ce ba yabi bayan su, aiman ya juya yana kallon sarki kamar ya fashe da kuka saboda xafin da yake ji kafin ya juya da sauri yabi bayan su, bai damu da bayi da fadawa dake harabar gidan ba, wannan karon babu MULKI KO SARAUTA babu qasaita babu ji da kai duk ya tattara ya watsar da su babu abinda yake so kamar a bar mishi afiya, ya riqe hannun Abba.

Please Abba give me second chance idan nayi kuskure ko na bata ran afiya na yarda kaxo ka tafi da ita.

Abba ya fisge hannun sa tare da nuna sa da qaramin yatsansa don't touch me again, yanxu ne kasan ina da muhimmanci a gurin ka, kuma na gayama kada ka kuskura ka taka qafafun ka gidana You will regret.

Afiya tayi jim tana kallon Abba da aiman sai taji sosai abban ta ya burge ta a wannan karon daga yanda yayi wa aiman cos babu wanda ya taba wulaqanta shi haka, aiman bai san kuskure ko bada haquri akan wani laifi ba, yanxu ne ya kamata ya san muhimmanci da darajar ta idan har da gaske yana son ta kamar yanda ya fad'a mata jiya ya kuma fada a gaban iyayen su to xai jure duk wani wulaqanci da xai biyo baya, ta sa hannu ta goge hawayen fuskarta.

Afiya please don't follow them ki gayamasu dani kike son xama ya fada gwani ban tausayi yana kallon ta ga mamakin sa sai yaga ta tabe bakin ta tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login