Showing 24001 words to 27000 words out of 41393 words

Chapter 9 - Mulki Ko Sarauta Book 1 Complete Hausa Novel

Nawarty   

01 Oct 2025

383

sun yi ja sosai.

Mami muje gidan mu suzana xata had'a min bana son nan.

Xama bai same ki ba afiya ko ki had'a kije dashi can sashen ki sai ki rarrashe sa naga har ynxu bayan ke da yarima bai sake da kowa ba kamar tsoron mu yake.

Umma baxan iya kwanciya acan ba gaskiya.

Tace idan yayi barci ki dawo dashi kuma ki tabbatar da kinci abinci kada ki kuskura ki kwanta baki ci komai ba.

Afiya ta had'a golden morn d'in, ta d'auke sa suka fita, sashen ta komai a gyare sai qamshi ke tashi ta ko ina ta sauke sa ya qanqame ta alamar baxai sauka ba.

Wai me kake nufi ne?
Yace bana son nan muje gida.

Tace gidan uban ka, akwai inda yafi maka nan ne, wallahi dukan ka xanyi yanxu.

Ya fashe da kuka tare da fad'in take me to my daddy.

Ta ajiye cup d'in tare da hankade sa a jikinta matsamin can kaje kayi ta kukan idan ka takurani jikin ka kuma xai gayama yanxu.

Ya matsa nesa da ita yana cigaba da kukan tare da buga qafafun sa take me to my daddy, ta kwanta tare da lumshe idanuwan ta duk da tasan kukan nasa ba barin ta hutawa xai yi ba.

Wancan yaron da fitinar tsiya yake da daren Ma baxai barmu ba sai yayi kuka, sarki ya fad'a yana kallon aiman dake xaune kusa dashi.

Murmushi aiman yayi tare da fad'in ko axo maka da shi ya taya ka barci yau.

Yace aa sam fu'ad bashi da rigima kamar wannan idan kaji kukan fu'ad a gidan nan an taba sa ne.

Aiman yace tam shima taba sa akayi baya kuka sai da dalili.

Aa tun d'axu anan yake fitinar sai an kaishi gidan su wannan ba gidan su bane, abinci babu yanda banyi dashi ba yaqi karba.

Aiman yayi jim kad'an kafin yace daddy an gama had'a komai cikin takardun nan.

Yace komai an had'a amma ka barsu xan qara dubawa nagani.

Aiman ya tashi yana fad'in goodnight.

Sarki yace idan ka fita turo min waziri yanxu.

Ya juya ya fice, har ya nufi sashen umma sai yaji sautin kukan ba daga can yake fitowa ba kenan afiya tana sashen ta, yana shiga yayi tsaye cikin mamakin tana kwance abinta sultan na kuka tare da fad'in take me to my daddy, d'aukar sa yayi sultan na ganin sa ya qanqame sa yana ajiyar xuciya da qarfi.

Jin yayi shiru yana sauke numfashi ya saka ta bud'e idanun da kyar ganin aiman ya saka ta maida idanun da sauri, shima bai kula ta ba ya juya xai bar falon sultan yayi saurin nuna masa Cup d'in Golden morn d'in sa dake ajiye kusa da afiya, ya d'auki cup d'in ya fice tare dashi.

Da kyar ta tashi tana so ta bar sashen xuwa sashen umma amma ta kasa tashi wannan karon kanta yayi mata nauyi sosai ga jiri da take gani, ga xuciyar ta dake tashi kamar xata yi amai haka ta sake kwanciya ba dan ta so ba.

Aiman da kansa ya baiwa sultan Golden morn d'in kuma ya sha sosai saboda akwai yunwa tare dashi, ya d'auko fresh yo ya bashi ya sha kad'an ya ajiye tare da kwanciya jikin aiman cikin lokaci qanqanin barci yayi awon gaba dashi.

Aimaan ya tsura masa ido da gaske fa maganar sarki yaron akwai rigima sosai ya kai yatsansa kan lips d'in sa wannan bakin surutun cikin sa na baiwa mutum mamaki a matsayin shekarun sa idan haka ne dole a saka shi makaranta kuwa.

My footballer aiman ya fad'a yana kallon qafafun sultan d'in, sai kuma ya tashi dashi ya nufi sashen afiya domin kai mata shi yana so ya kwanta da wuri yau.

Bata falon ta ya nufi d'akin ta acan ya soma jin kakarin amai da take yi a toilet, ya ajiye sultan ya nufi toilet d'in.

Do you need my help? ya tambaya yana kallon ta, a galabaice ta d'ago tana kallon sa tayi luuu kamar xata fad'i yayi saurin taro ta xuwa jikin sa, shi ya gyara mata jikinta ya fito da ita ya kwantar da ita ya fita xuwa sashen sa tea ya had'a mata mai xafi ya d'auko magani yaxo dashi, da kyar ya samu ta sha tea d'in ya bata magani ta sha ya dube ta yana fad'in waya gayamiki ana fushi da abinci saboda wani dalili naki na banxa, idan saboda ilham ne before nayi niyar rabuwa da ita saboda ke amma yanxu baxan iya ba ilham tayi haquri dani kuma ta cancanci na xauna da ita ko da bana son ta kuma sarki baxai taba yarda na saki ilham ba, kin sani afiya kinsan halin sarki kuma baxan iya jayayya da shi ba.

Ta maida idanun ta ta lumshe sai ga hawaye kamar fanfo suna fitowa a idanun ta, yasa hannu yana share hawayen tare da kai lips d'in sa kan nata ya sumbata a hankali, cikin murya qasa qasa yace na damu dake fiye da yanda kike tunani, ina son kasancewa dake a kowane lokaci ki kula dani batare da kin damu da ilham ba, ki soni like before I promise to be with you.
[2/21, 8:13 PM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Ta d'auke kanta gefe batare da tayi magana ba, sai can ta bud'e baki da kyar tace ina so na tafi.

Yace xuwa ina?
Tace inda umma.

Yasa hannu ya juyo da fuskar ta yana fuskantar ta, me xaki je yi inda umma yanxu bayan dare yayi.

Tayi masa shiru tana lumshe idanu a hankali saboda wani barci dake son d'auke ta.

Ganin ta soma xufa ya kunna AC alamar xaxxabin ya soma sauka, ya tashi ya d'auki sultan ya fice da shi daga d'akin xuwa sashen umma, tana xaune a falo kuwa xaman afiya sai ga aiman ya shigo d'auke da sultan.

Tace afiya fa, ya d'auke kansa daga gare ta tare da fad'in tayi barci.

Shine kuma xaka xo da sultan, ai tace baxata iya kwanciya acan ba.

Umma ga sultan, afiya tana buqatar ta huta dole wani xai tsaya a kusa da ita amma ba sultan ba.

Tace taci abinci kuwa cos yau duk bata ci komai ba.

???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Ta sha tea har da magani ma, gud night umma.

Tace aa yarima baxaa bar afiya ta kwana ita kad'ai ba saboda yanayi na ciwo, bari na kira aje a tayata barci yanxu.

No need, ya katse ta tare da juyawa ya bar d'akin.

Tsaye yayi akanta yana kallon ta sai rawar sanyi take da alama sanyin AC ya soma damun ta, ya kashe yana kallon ta bai san ta inda xai soma cire doguwar rigar dake sanye a jikinta xuwa na barci ba, abu ne da bai taba yi ba, yaje ya duba cikin kayan ta ya d'auko rigar barci, sanda ya tallabo ta bud'e idanuwan ta tayi a hankali tana kallon sa.

Sanyi... ta fad'a bakin ta na rawa, ya kai hannun sa wuyanta har lokacin xafi rau, ta sha magani amma me ya hana xaxxabin sauka haka, ya xuge zip d'in rigar yana qoqarin cire wa, ta riqe hannun tana kallon sa da idanun ta jawur tace Sanyi.

Cikin muryar da bai san yana da irin ta ba ya kwantar da kai yana fad'in sorry dear, wannan xata yi maki nauyi wurin kwanciya idan an sauya da rigar barci.

Ta lumshe idanun ta, tana ji har lokacin da ya gama sauya mata kayan, har lokacin bata daina rawar sanyi ba, abin ya bashi mamaki sosai, lemme see your tongue afiya, idanun ta a rufe ta turo harshen ta, ya saka hannu ya bud'e idanun, ya janyo tamin hannun ta yana murzawa a hankali tare da observing akan ta, rigar barcin dake jikin ta ya qara cire wa shima ya cire ta jikinsa, ya shiga duvet tare da janyota xuwa jikinsa.

Bata da xabi a Wannan lokacin daya wuce ta taimaki kanta itama, ta qara shigewa jikinsa yana goga jikinsa acikin na ta,? sunyi gogayyar jiki sosai (body contact )duk ilahirin jikinsu sai da ya hade tun daga kan fuska har qafafuwansu, dumin jikinsa yayi matuqar taimakama ta, ta dawo hayyacinta ta daina rawar sanyi kafin kace me har ta fara xufa kamar farko, da kyar ya kai hannun sa ya lalabo remote ya qara kunna ac d'in, ya soma daddanna mata jikinta har barci mai nauyi Ya dauketa, shi ma ya raba ta gefenta ya kwanta yana kallon kyakkyawar fuskarta , bai jima ba barci Ya daukesa.

Dukkansu basu farka ba sai da gari yayi haske, Aiman Ya fara bude idanuwansa Ya ganta kwance a jikinsa gashin kanta ya rufe mata fuska, ta dora hannuwanta a jikinsa ta rungumeshi sosai, yasa hannu Ya Yaye gashin ya xuba mata idanu lokaci daya Ya saki murmushi Ya qara shigewa jikinta hade da kaimata sumbata a lips dinta, bai san lokacin da suka qara hadewa hakan ba, bayan barci ya d'auke su, ya jima baiyi barci mai dad'i cike da nutsuwa irin wannan ba, ashe basu yi sallah ba sam sun makara ya janye ta daga jikin sa da sauri ya fad'a toilet.

Ta bud'e idanun ta da kyar kafin ta tashi dafe da kanta wanda har lokacin bai daina mata ciwo ba, fitowar aiman toilet ya saka ta d'aga kanta tana kallon sa, shima kallon ta yayi kafin ya juya ya bar wurin, toilet ta nufa itama.

Ranka shi dad'e saqo ne daga nabila tana son ganin ka, jakadiya ta fad'a kanta a sunkuye cikin tsoro.

Afiya ta dube ta kafin ta maida kallon ta ga yarima da ya daure fuska kamar ba shi ba.

Alama yayi wa jakadiya da ta tashi kana ya cigaba da breakfast d'in sa, afiya kuwa tuni komai ya fice mata a rai sai juya tea take cike da tunani iri iri, wace nabila kuma daga ina take son ganin sa dama tana gidan ne.

Wace nabila ake magana, ta tambaya tana kallon sa.

Kamar baxai yi magana ba yace akwai wata nabila da kika sani bayan wace kika gujewa kika bar mata miji na tsawon shekara hud'u.

Hankalin ta ya qara tashi, itama auren ta kake yi, ta tashi dafe da kanta sai kuma ta dube sa taya kake tunanin xan iya xama da kai da mace biyu a gidan nan.

Akwai ta uku ma tana xuwa nan bada jimawa ba, ya bata amsa batare daya dube ta ba.

Me kake nufi? Ya d'ago yana kallon ta tare da fad'in me kike so?

Baxan xauna da wata a gidan nan ka saki ilham da nabila idan ba haka ba ni xaka sake ni.

Yace baxan saki ilham ba, itama tana da matsayi mai girma a xuciya ta kamar yanda na gaya miki a jiya.

Kenan kana son ilham.

Duk abinda kike tunani haka ne ya tashi fuska a d'aure, cikin bacin rai tasa hannu tana watsi da kayan dake dining batare da ta damu da wad'anda suke fashewa ko kuma abincin da take xubarwa ba, I hate you wallahi sai ka sake ni bana son ka saif nake so shi xan au.... tayi shiru sakamakon saukar mari da taji a kuncin ta, ya fisgota da qarfi cikin bacin rai, baxan taba rabuwa da ilham ba kamar yanda kema baxaki taba samun saif ba, idan kika kuskura kika qaramin maganar saif a gabana wallahi you will regret, dan kinga ina rarrashin ki ko kuma dan kin ga na damu dake, ya sake ta tare da tura ta da qarfi kan sofa cikin tsananin fushi ya dafe kansa, taya ma na damu dake, meyasa na bari xuciya ta take tunanin ki wannan ne dalilin daya saka na kasa son kowacce mace a duniyar nan amma meyasa na damu da xuciyar da ke begen wani a waje, nima na tsane ki I don't want to see you again, ya juya ya fice ta fashe da kuka mai tsanani.

Kai tsaye sashen ilham ya nufa Karo na farko tun xaman ta a gidan daya taka qafar sa xuwa sashen ta, ba qaramin mamaki tayi da ganin sa duk da a yanxu ta rage jin sonsa a ranta tun daga wulaqancin da yake mata, ganin saifullah ya dawo mata da komai na xamantakewar su take tunanin idan saif ta aura tabbas baxai taba wulaqanta ta haka ba, itace ta jawa kanta na qin karban soyayyar saif a lokacin.

Kallo d'aya tayi masa tasan akwai tashin hankali a tattare da idanuwan sa, taji tsoron yanayin sa bata taba ganin sa a irin wannan yanayin ba, babu xato babu tsammani taji ya janyota xuwa ga jikinsa ya rungumeta tsam sosai, lokaci d'aya suka sauke ajiyar xuciya tayi lamo tana shaqar qamshin jikinsa kamar su tabbata a hakan.

Am so sorry for everything ilham, ya fad'a a hankali kamar mai rad'a ya tallabo fuskarta ya had'a da tashi tare da lumshe idanuwan sa, wani yanayi take ji a tattare da ita, ta sumbaci bakin sa a hankali, ya bud'e idanuwan sa yana kallon ta itama shi take kallo, akwai soyayyar sa mai tsanani da yake gani a idanuwan ta tabbas ilham ta soshi kuma tayi haquri da shi babu abinda xai iya saka mata dashi a rayuwar nan, wani qaramin gold na xobe ya ciro daga jikinsa da niyar ya baiwa afiya, ya janyo hannun ta ya saka mata a yatsanta, cikin tsananin farin ciki ta ware idanu sosai tana kallonsa yaja dogon hancin ta yana murmushi, my beautiful wife are you happy?

Ta gyad'a kai da sauri cikin mamakin wannan sauyi na aiman da take gani a yanxu.

Yace haka nake son ganin ki cikin farin ciki ko yaushe ilham, kisa a ranki kina da matsayi a xuciyar aiman.

Tayi shiru tana kallon xoben tana kallon sa, shima kallon xoben yayi kafin ya dube ta yace kina son saif a yanxu sama da aiman.

Cikin tsananin tashin hankali ta maida kallon ta gare sa, yace saifullah yana son ilham fiye da afiya, aiman kuma ya damu da afiya fiye da kowacce mace a duniyar nan, tsananin kishi da bacin rai ya hana afiya ta gane soyayyar aiman a xuciyar ta take ganin saif is the best for her bayan saif ya fi cancanta da xama da ilham, ya janyo yatsanta dake sanye da xoben ya sumbata a hankali.

Mun xauna da saifullah munyi magana ya gayamin komai dangane da soyayyar ku haka ya sanar dani xaman sa da afiya, saif deserves everything from me, ya kula da matata da d'ana ni kuma na kasa kula masa da abinda yake so ilham, me xanyi na biyasa alkhairi da yayi min, nayi tunani bani da abinda xan bashi da ya wuce ilham.

Ta rumtse idanun ta tana hawaye sosai, ya saka yatsansa yana xagayawa da shi a fuskar ta, da wannan dalili a yanxu ni aiman na yanke igiyar aure na d'aya akan ki, ya janye hannun sa.

Ta fashe da kuka gwani ban tausayi, yayi jim yana kallon ta xuciyar sa ba dad'i, yace bana son kukan ilham nayi tunanin hakan da nayi xan faranta maki ne kamar yanda kike qoqarin faranta min, innocent ilham bata cancanci xama da iri na ba, you hide my secrets baki taba fad'awa kowa matsalar da kike ciki ba a gurin iyaye na ko iyayen ki tabbas kin cancanci xama mace ta gari,? ni kaina nasan ina da matsala ilham amma ban san taya xan gyara kaina ba, kimin addu'a a duk san da kika tuna da ni anjima kad'an saif xai xo ya d'auke ki, ki soma shiri ki kuma je inda umma har ya juya xai fice tayi saurin tsaida shi,

Wane irin matsayi nake da shi a xuciyar ka ta tambaya, yayi jim kamar baxai yi magana ba yace kina da matsayi irin na rumaisa yanxu a xuciya ta ki d'auke ni matsayin yayan ki, duk wata matsala ko damuwa ki sanar dani kafin ki sanar da gida.

Tayi murmushi mai bayyane da fararen haqoran ta shima murmushin yayi tare da fad'in akwai tsaraba da xaki je dasu gida xan saka a xo maki dasu yanxu.

Ta jinjina kanta a hankali tana kallon sa har ya fice, she is happy xata sami saif amma deeply she is hurting na rabuwa da miji irin aiman tabbas tayi rashi amma she pray hakan ya xamo alkhairi a rayuwar ta.

Ta lumshe idanunta cikin tunanin aiman, his touch was like heroin in my veins and I was grateful addict, the contrast between pleasure and pain he always delivered to me I couldn't get enough.

Aiman yana barin sashen ta ya nufi inda sarki cikin fargabar yanda xai sanar dashi rabuwar sa da ilham.
[2/22, 5:29 PM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Nesa kad'an da sarki ya xauna tare da sunkuyar da kansa kasa, bayan ya shiga falon sarki.

Akwai damuwa ne yarima? Sarki ya tambaya yana kallon sa.

Ina neman afuwa idan nayi ba dai dai ba daddy, na yanke hukunci batare da shawarar ku ko sanar da ku ba, kayi haquri daddy.

Menene sarki ya qara tambaya Karo na biyu.

Na yanke igiyar aure na d'aya da ilham, kayi min afuwa.

Sarki ya sauya fuska sosai xuwa bacin rai yayi shiru ya rasa me xaice ma saboda baqin ciki daya ke ji, kallo d'aya aiman yayi masa ya maida kansa ya sunkuyar cikin tashin hankali da ganin yanayin sarki.

Nan take ya soma yi masa bayanin komai da yanda suka yi da Saif har had'uwar afiya da saif kamar yanda ya bashi lbr da taimakon da yayi masu da alaqar sa da ilham, ya qara da fad'in na sake ta ne saboda tana da wanda take so yake son ta daddy, ban d'ora mata iddah ba har tsawon wannan lokacin, baxan iya kasancewa da kowa ba bayan afiya daddy dan Allah ka fahimce ni ya fada tare da riqo hannun sarki yana roqon sa.

Sarki ya dafa kansa, wannan hukuncin bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login