Showing 12001 words to 15000 words out of 41393 words

Chapter 5 - Mulki Ko Sarauta Book 1 Complete Hausa Novel

Nawarty   

01 Oct 2025

392

darajar dan adam mutum ne dake matuqar girmama mace da kare mutuncin ta ko da babu wata alaqa ta jini tsakanin su ballantana ace macen da yake aure, saboda nabila ta xauna gidan ka kayi mata ciki kake tunanin kowa ma irin ka ne, Saif ba irin ka bane idan kana xargina dashi ka bani takarda ta a yau yarima, I just want to be with saif only saif ta fad'a tana share wasu hawaye da suka xubo mata.

Kalamanta babu ta inda basa sukar sa a xuciya da gangar jiki, tana son takardar sakin ta saboda ta xauna da wani namiji ba shi ba, taya afiya xata so wani namijin ba shi ba, jikinsa ya d'auki rawa ta xuba masa idanu tana kallon yanayin sa ga mamakin ta sai taga ya kwantar da kai kamar ba shi ba abinda bai taba yi mata ba a rayuwa wai aiman ya rarrashe ta ko kwantar da kai kamar yanda yayi yanxu.

I have changed, can't you see, I always care for you, ya dafe goshin sa kad'an kamar baxai yi magana ba sai kuma ya jawo ta ya had'a ta da jikinsa sosai tare da fad'in you change me afiya ko da bana son ki you mean the world to me, kada ki barni ki cigaba da sona batare da kin had'a soyayyata da wancan guy d'in ba I promise to make you happy, ya fad'a tare da kai dogon hancin sa kan wuyanta yana shaqar qamshin jikinta dake neman tada masa tsumin daya jima yana begen samun sa, ta lumshe idanun ta tana sauke numfashi a hankali, idan tace bata son aiman ta qaryata xuciyar ta am... tunanin ta ya katse lokacin da taji aiman na qoqarin janye rigar barcin dake jikinta da qarfi ta ture sa daga jikinta, yayi kamar xai fad'i saboda jikinsa da ba kwari a lokacin, cikin bacin rai ta dube sa tana fad'in how dare you, taya kake tunanin samun afiya a sauqaqe haka a daren ranar da nadawo gidan ka a bisa tilastamin da akayi, meyasa kake tunanin xan iya qara yarda na had'a jikin da waccan qaxamar macen tayi mu'amala dashi, ina hankalin ka yaje da ka kasa gane wannan afiyar dake gaban ka a yanxu daban take da waccan afiyar ta baya, na mallaka maka kaina da jikina a baya saboda soyayyar da nake yi maka, yanxu kuma ba xaka mallaki xuciya da gangar jikina ba har sai lokacin da ka furta kana son a???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?fiya har cikin ranka tare da tabbatarwa kowa cewa xuciyar aiman ta afiya ce idan ba haka ba baxaka taba samun soyayya ta ba.

Batare da yayi magana ba ya juya ya fice daga sashen gabaki d'aya cike da kunya, wannan wane irin toxarci ne afiya tayi masa batare da ta duba girma da matsayin sa ba xata saka hannu ta ture sa daga gare ta, ta gama raina sa a yanxu da taga cewa ya soma damuwa da ita, taya xai furta mata so bayan bai ji hakan a xuciyar sa ba, shi ba gwanin qarya bane da xai mata qarya da so, idan dole sai ya furta mata so ne to tabbas xasu tabbata a hakan dan baxai yi qarya akan abinda baya ji a xuciyar sa ba.

Ilham da kusan tafi awa d'aya bakin window tsaye tana jiran fitowar aiman tun lokacin da taga shigar sa sashen afiya, tana kallon sanda ya fito ya nufi nasa sashen, xuciyarta banda xafi babu abinda take mata, aiman bai taba taka qafafun sa ko hanyar sashen ta ba balle ta saka ran xuwan sa kamar yanda taga yau da kansa yaje sashen afiya kuma ya jima aciki, wane irin matsayi afiya take da shi haka a gurin yarima, ita tana son sa kuwa kamar yanda yake son ta idan haka ne baxata xauna ba dole xata d'auki mataki babba a game da wannan afiyar bata yarda yarima ya so wata mace ba bayan ita, xata je yanxu ta same sa duk yanda xaa yi tana so ya bata haqqin ta.

Afiya ma alokacin tana tsaye bakin window ta xubawa taurari idanuwa cike da tunani iri iri duk akan yarima, ta maido kanta a hankali xuwa farfajiyar gidan tana kallon yanda masu tsaron gidan ke kai da kawo wa a gidan, ta jinjina kanta lallai har yanxu al'adar gidan nan bata canxa to me ma xai saka ta canxa bayan gidan sarauta ne, yau sultan bai neme ta ba tayi tsammanin baxai yarda da kowa a gidan ba xai dawo ya kwanta gurin ta ne, ta maida hannuwan ta duka biyu ta rungume a jikinta tare da kallon sashen yarima dai dai lokacin taga wata mace da bata ga fuskar ta ba sanye da alkyabba tana qoqarin shiga sashen sa, ta xuba mata idanu har lokacin da ta shiga, wacece wannan me kuma xata je yi sashen aiman ta tambayi kanta tare da kallon agogon dake manne a bangon d'akin sha biyu da rabi na dare, ta maida kanta a sashen yarima cikin mamaki, ko nabila ce har yanxu suna tare aka barsu a gida, qila ya aure ta taji gabanta yayi mummunan fad'uwa kamar ta sauka qasa taje ta ganarwa idon ta, idan taje tace me taxo yi bayan da kanta ta korasa yanxu.

Taja qaramin tsaki inda ta ajiye wayar ta ta nufa tare da dialing number saif, kamar wanda ke jira bugu d'aya ta shiga,

Cikin dariya yace mutanen Nigeria kamar na kira kuma ina tsoro ina sultan d'ina? Murmushi tayi a hankali tare da fad'in sultan yana gun umma.

Duk yanda yaso ya rumtsa ya kasa sai juye juye yake a makeken gadon sa da bai taba ganin fad'i da girman sa ba sai yau kad'ai daya saka rai xai kasance da afiya, ya rasa dalilin sa na damuwa da afiya haka da har barci ke neman gagarar sa a yau.

Sallamar ta ya saka shi juyawa a hankali yana kallon qofar batare daya amsa ba, yana ganin ta yaji kamar taxo ta d'ora masa damuwa ne akan wadda yake ciki a yanxu, ganin bai kula ta ba sai tayi qoqarin kwanciya gefen sa tare da matsawa ta shige sosai jikinsa kamar xai maida ta ciki.

Na kasa barci prince, all I want is you, ina son ka da yawa dan Allah ka soni ko kad'an ne ta fad'a tare da kai hannun ta a faffadan qirjinsa tana shafa a hankali.

Nan take duk wata tsika ta jikinsa ta soma tashi daga yanayin yanda take tafiyar da hannunta a jikin sa, ya sauke numfashi a hankali tare da janye hannun ta daga cikin sa, bata ji haushi ba cikin wani salo na daban ta d'ora yatsanta tana yawo dashi a wuyan sa xuwa qirjinsa, yayi lamo yana sauraren ta tamkar baya jin abin har cikin jinin jikinsa sosai ta shagaltar dashi duk da bai nuna ba sai ya matse ta sosai a jikinsa, ta saki murmushi kad'an mai tattare da nasara akan sa ba bata lokaci ta soma qoqarin had'a bakin ta da nashi, ya janye kansa tare da kai bakin sa dai dai kunnen ta a hankali yace ina so na kasance da afiya a hakan, shekara hud'u ban qara jin dumin jikin ta ba amma ta kasa gane hakan har take kora ta daga gare ta, taya xan nunawa afiya so har ta yarda dani kamar yanda kike min a yanxu I want to be with her forever in my life than any woman in this world ?

Nan take jikinta ya mutu murus, komai nata ya daina aiki taji d'akin gabaki d'aya yana juya mata tamkar an soka mata kibiya a xuciya, a hankali ta soma raba jikinta daga nashi tana hawaye masu xafi da rad'ad'i a xuciya.

Tana fita a d'akin ya saki murmushi tare da gyara kwanciyar sa, wannan yarinya xata yi jarabar tsiya, ko dai tasan namiji a waje ne take liqe masa haka? ya tabe bakin sa miye damuwa ta.

Ta jima tsaye bakin window bayan gama wayar da saif tana kallon sashen yarima cikin tunani iri iri game da wacce taga ta shiga kuma har yanxu bata fito ba, kome suke yi, bata san meyasa ta damu ba tana tsaye a wurin taga fitowar ilham d'in wannan karon da sauri take tafiya ba kamar d'axu da take tafiya a hankali da xata je ba, duk yanda taso taga fuskar ta bata gani ba saboda alkyabbar ta rufe fuskar ta, ta tsurawa sashen da taga ta shiga ido, can kuma ina ne, wacece take xaune acan.

Washe garin ranar yana saukowa ya sami jakadiya tana had'a breakfast a dining,

Barka da saukowa ranka shi dad'e.

Batare da ya amsa ba yace ina afiya, tayi Jim kad'an kafin tace yanxu nake so naje na duba ta.

Yace kenan abinda kuka girka batare da ixinin ta bane, idan bata son girkin fa.

Tuba nake yallabai wannan naka ne, afiya yanxu xaa girka mata kowane irin abinci take so.

Ya xauna tare da fad'in kixo da afiya yanxu idan bata son wannan abincin nima baxan ci ba sai a sake girka irin wanda take so.

An gama ranka shi dad'e, ta fice da sauri cikin mamakin yarima a yau xuwa sashen afiya.

Yana xaune jakadiya ta dawo jiki a sanyaye ta russuna tare da fad'in,

Ranka shi dad'e ban sami afiya a sashen ta ba har kayan da taxo dasu duka babu an kwashe.

Cikin wata irin raxana ya dubi jakadiya sai kuma ya tashi cikin tsananin rud'ewa kada afiya ta qara gudu ne ya fita xuwa sashen afiya, tabbas babu afiya kuma babu kayan ta, hankalin sa ya tashi sosai da sauri ya nufi sashen umma yanda bayi ke xubewa suna gaida sa bai kula kowa ba yana qoqarin shiga d'akin umma yaji tana fad'in,

Shine kuma tun da sassafe sai ki d'auko kaya kixo min da su, bakya jin magana ko.

Tace aa umma, na yarda na kwana jiya a gidan ne saboda Abba ya rantse amma baxan iya xama acan ba dan Allah umma kada kice aa ki barni na xauna anan.

Wata ajiyar xuciya ya saki tare da jinginawa a bango, bai san halin da xai shiga ba idan afiya ta sake gudu a yanxu ya shafi sumar kansa a hankali ya juya xai bar falon sai a lokacin ya lura ashe da kayan barci ya fito harabar gidan cikin bayi da maaikatan kuma babu takalmi a qafafun sa, taya ma xai iya sake fita a hakan?
[2/13, 7:55 PM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Baya jin xai iya fita a haka, Allah yasa sanda ya fito babu wanda ya ganshi ma, bai jima da xama ba umma ta fito tana ganin sa xaune a falon tayi mamaki musamman da kayan barci.

Lafiya yarima? Ya d'ago yana kallon ta a hankali duk kuma sai yaji kunya da nauyin ta sun kama shi abinda bai taba yi ba a rayuwa jin kunyar mahaifiyar sa ta ganshi xaune da sassafe a falon ta kuma da kayan barci, ya bud'e baki da kyar yace morning umma.

Tace an tashi lfy, ya tashi tsaye yana shafar gefen fuskar sa, bai iya qarya ba baisan yanda xai yi qarya akan gsky ba ko da kuwa xata janyo masa matsala ne haka yake tun yana qarami, nan yayi mata bayanin xuwan sa da kuma dalilin rashin fitar sa har taxo ta same sa a gurin.

Bata san sanda murmushi ya subulce mata ba, idan afiya ta gudu ta bar gidan sai me, ko ka manta, meyasa ma xaka damu har ka rud'e haka bayan ko a farko da ta gudu ko a jikin ka baka damu ba.

Yace umma na canxa yanxu don't you see?

Yes aiman ya canxa sosai akan farko I pray ka cigaba da canxawa, yanxu ai sai ka tafi tun da kaji ba guduwa tayi ba.

Shima murmushin yayi, umma ba takalmi kuma da wannan kayan barcin?

Aa to me yasa tun farko baka tantance yanda ka fito ba, a hakan xaka fita favour d'aya xanyi Ma na baka takalmi ka saka.

Ok ma, ya fad'a yana dariya umma ta juya ta koma cike da mamakin wannan farin ciki dake fuskar aiman duk na menene, yau babu shan qamshi da daure dauren fuskar da yake yi chab.

*

Mami yaushe xamu je gidan mu? Ta shafa kansa a hankali tare da jan kumatun sa tana dariya, babu wani gida da yafi maka wannan my dear, nan ne gidan mu sultan.

Ya soma buga qafafun sa tare da make kafada, bana son wannan garin lets go back, babu dad'i anan mami ni bana so take me back home sai ya fashe da kuka.

Duk yanda ta so rarrashin sa yaqi yarda sai kuka yake sosai iya qarfin sa yana jan hannun ta akan ta tashi su tafi, tana xaune tana kallon rigimar tashi tana murmushi, a hakan umma ta shigo ta same su itama duk yanda taso ga rarrashin sa yaqi yarda shi baya son gidan mutane sun yi yawa suna bashi tsoro baya son ganin su, basa sa kaya masu kyau kamar irin na qasar su, abincin su ba dad'i dai dai lokacin aiman ya shigo a bayan sa kuwa ilham ce, kukan sultan ya saka aiman xuwa.

Kallo d'aya afiya ta yiwa ilham ta d'auke duban ta gare ta, wannan kuma wacece ko itace nagani jiya, menene tsakanin su da yarima, oh wannan itace na gansu a jirgi tare.

Ilham kuwa ta kasa d'auke idon ta akan afiya saboda kyau da kwarjini da tayi mata duk yanda take tunanin afiya ta xarce tunanin ta ashe shiyasa aiman yake rawar kai akan ta shiyasa aiman ya kasa kula kowacce mace saboda yasan irin wadda ya ajiye, nan da nan taji wani tsana da kishi na afiya ya taso ya tokare xuciyar ta.

Kukan da sultan ke yi ya saka aiman d'aukar sa ya rungume a jikinsa, yaron akwai rigima ya fad'a yana kissing goshin sultan, sultan ya saka hannu yana ture fuskar aiman tare da fad'in bana so, leave me ni bana son gidan ku.

Kallon sa ilham tayi tun jiya da ta soma ganin yaron taji bata son sa saboda tsananin kama da yake da yarima taso ace itace ta haifa masa wannan yaron duk da haka bata cire rai ga samun wanda yafi sa ma dan tana da tabbacin yan biyu xata haifa nan gaba.

Aiman yayi dariya ya riqe hannun sa, bana son kukan if not babu inda xaka je mami kawai xan bari taje ta barka, nan take yayi shiru kuwa yana ajiyar xuciya, aiman ya kwantar dashi kafadar sa relax my Prince kake wahalar da kanka haka akan abinda baxai taba yiwuwa ba, sultan bai fahimce sa ba ya soma lumshe idanun sa kad'an kad'an saboda barcin dake son d'aukar sa.

Umma tayi Jim ta rasa yanda xata bullowa afiya game da ilham sai da taja numfashi kad'an ta dubi ilham ganin basu gaisa ba tace ilham baki ga afiya bane, idan ita bata san ki ba inaji ke kinsan kowacece ita da matsayin ta a gidan tunda an sha fad'a maki kuma ko ba komai ita babbace a gurin ki meyasa da kuka shigo kika gaidani baki gaidata ba.

Ilham ta sunkuyar da kanta qasa kad'an tace tuba nake ranki shi dad'e ayi min afuwa kafin ta dubi afiya da har lokacin kanta ke qasa ta gaida ta, kamar baxata amsa ba sai daga baya can qasan maqoshin ta wanda da kyar suka ji tace lafiya tana yatsina fuska kamar wacce aka yiwa dole.

Umma ta dubi afiya tana fad'in qanwar kice afiya itama matar yarima ce, dum taji saukar wani abu a qahon xuciyar ta har lokacin bata d'aga kai ba sai dai komai nata ya tsaya cak, aiman ya lura da haka ya ajiye sultan da ya jima da yin barci a saman gado kafin ya dawo kusa da afiya ya xauna jikinsa har rawa yake.

Ilham kuwa murmushin jin dad'i tayi ganin an gayawa afiya matsayin ta a gidan.

Umma ta cigaba da fad'in sai kiyi haquri komai da kike gani rubutacce ne a gurin ubangiji, bayan tafiyar ki da shekara biyu alhaji Ahmad ya matsa da yiwa aiman aure, yau shekarar su biyu da aure, ki d'auke ta matsayin qanwa yar uwa kamar yanda itama ilham tuni na gama sanar da ita matsayin ki a gidan kinji afiyata.

Har lokacin afiya bata amsa ba kuma bata d'ago ba, ita kad'ai tasan halin da take ciki game da abinda take ji a yanxu, aiman yayi aure, umma ta tashi ta fice da wayar ta a hannu tana kiran number ammi ni baxan iya da fitinar afiya ba ku da kuka matsa ayi auren sai kuxo kusan yanda xakuyi da ita ta fada a xuciyar ta tana barin d'akin.

Itama ilham d'in barin d'akin tayi xuciyar ta fes dan ta lura afiya bata ji dad'i ba kuma haka take so, Allah yasa tayi xuciya ta bar mata mijin Ma.

Umma ta manta bata gayamiki ba itama bana son ta, ya tsinci kansa da yin maganar batare da ya shirya ba, tsakanin jiya da yau ya rasa meke damun sa da baya iya controlling kansa akan afiya musamman idan tayi fushi.

Ta d'ago tana kallon sa duk da idanun ta sun canxa kala hakan bai hana mata boye damuwar ta ba ta saki murmushin da iya kar sa bakin ta, tace congrats aiman for having this beautiful lady as your wife, ina taya ka murna.

Yace kin fimin ita afiya, bana ganin kyawun ta sai naki kawai, abinda na sani dole aka min a auren ta bana son ta.

Tace amma ni kana sona? ta tambaya tana kafe sa da manyan idanunta.

Ya girgixa kansa da sauri tare da fad'in no but I care for you.

Taja numfashi kad'an xuciyar ta na mata xafi da gaske yake har yanxu aiman baya son ta, sai yaushe xai so ta? ta girgixa kanta tana kallon sa dan Allah ka barni na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login