Showing 33001 words to 36000 words out of 41393 words

Chapter 12 - Mulki Ko Sarauta Book 1 Complete Hausa Novel

Nawarty   

01 Oct 2025

381

ba duba da xama da suka yi da su waziri ga ilham d'in da saif aka tattauna komai cikin mutunci da girmama juna, sun yi godiya sosai ga karamci irin na sarki da yanda yayi ko ba komai an riqe yar su da amana dan babu ta inda jikin ilham d'in xai nuna tana cikin qunci a gidan, tayi jiki kad'an kuma ta qara gogewa hakane ya saka basu ga wani abun xafi ba a wurin.

Saif ya tura magabatan sa nema masa auren ilham aka bashi tare da saka date na auren nan da wata biyu masu xuwa.

Yayi qoqarin kiran wayar aiman amma bata shiga, baya son kira afiya a yanxu amma dalilin auren ya saka shi kiran wayar ta har ta tsinke baa d'aga ba.

Ya sake kira Karo na biyu cikin mamaki dalilin rashin d'aukar wayar sa daga ita har aiman, kira na hud'u ne ta d'auka da kyar tana kuka.

Subhanallah ya fad'a cikin tsananin tsoro, meke faruwa afiya.

Sun kashe aiman, sun kashe min miji.

Dif wayar ta d'auke hankalinsa ya tashi ainun ya soma qoqarin kiran wayar bata shiga, a wannan ranar ya kamo hanyar xuwa abuja.

Dr Bakori sai kai da kawowa yake a d'akin da aka kwantar da aiman, qoqarin sa na ganin ya ceto rayuwar aminin nasa, bayan dogon lokaci suka samu numfashin sa ya dai dai da taimakon oxygen d'in da suka saka masa.

Ya tsurawa aiman ido, he can't believe wai merah ne kwance haka a gadon asibiti rai a hannun Allah, meyasa ake cewa d'an adam baa bakin komai yake ba duk kud'in sa ko matsayin sa idan Allah yaso jarabtar bawan sa ya kan jarabce shi ko shi waye, Allah ka bawa Aiman lafiya ya fad'a a hankali tare da kallon nurses dake wurin, ku kula dashi da kyau and make sure kada a kuskura abar kowa ya shigo.

Ok sir suka fada lokaci d'aya ya juya ya bar office d'in.

Sister Xaynab wannan bashi ne likitan d'innan mai ji da mulki ba, wata nurse ta tambaya.

Wadda aka kira da xaynab ta yatsina fuska kad'an tana qara leqa fuskar aiman shine fa amma duk yanayin sa ya canxa kamar bashi ba,

Kamila ta matsa kad'an kusa dasu cikin muryar rad'a tace no wonder asibitin ta cika haka naji ana cewa sarki yaxo ashe shine mai asibitin.

Suka jinjina kansu lokaci d'aya jamila tace kamar a mafarki wai mune xamu kula dashi ban taba tsayuwa kusa da shi ba balle har magana ta had'a mu yau gashi mune masu tsaron lafiyar sa how I wish idan ya tashi mu saba dashi sosai cos na jima ina son gayen.

Kamila ta tabe baki tana kallon xaynab, kinji jamila da xancen banxa tun yaushe na ke ta fad'in? irin soyayyar da nake masa, ki daina wannan tunanin ma saboda shi d'in nawa ne da yardar Allah, bana son mu sami matsala dake saboda namiji.

Xaynab ta dafe kanta a hankali da hannun ta kafin ta dube su cikin bacin rai, mutumin nan baxai taba son ku ba kun sani meyasa kuke wahalar da xuciyar ku kan abinda baxaku samu ba, sam ajin ku da nashi ba d'aya ba beside ma ko ranar naji wasu nurses na magana akan shi har da cewa yana da mata biyu da yaro d'aya, mu kula dashi kamar yanda aka xabe mu a sauran nurses is better akan wannan musayar yawu da kuke da abinda baxaku taba samu ba.

Kamila tace hakane amma gsky ina son sa baxan iya haqura da shi ba.

Jamila tabe baki kawai tayi batare da tayi magana ba.

Mami meyasa muka xo asibiti ni bana son allura, tace pray for daddy bashi da lafiya.

Meya same sa mami? tace cikin sa yake ciwo, yayi jim kafin yace yaushe xamu je gida ni na gaji.

Ta rungumesa sosai tana shafa kansa, very soon xamu je idan barci kake ji yi barcin a haka, ya girgixa kansa tare da fad'in ni ice cream nake son sha, kayi haquri har muje gida, ya girgixa kansa tare da shagwabe fuska kamar xai yi kuka tare da fad'in I will cry.

Sosai ya bata dariya har umma dake xaune tana sauraren su, afiya ta nuna masa sarki tare da fad'in look idan kayi kuka anan daddy dukan ka xai yi, kuma dukan sa yana da ciwo sosai.

Ya sauka daga jikinta ya nufi inda sarki yace daddy mami idan nayi kuka xaka dake ni?

Sarki ya dube sa batare da yayi magana ba, sultan yace nima daddy na xai dake ka idan ka dake ni, fu'ad ya qarasa wurin su tare da saka hannu ya ture sultan daga jikin sarki ya shiga jikin sarki yana fad'in karka qara taba min granny ba naka bane don't touch him again.

Shima sultan ya matsa yana ture sa tare da fad'in he is my granny too ai daddy na ya gayamin, leave him alone.

Suka soma qoqarin ture juna sarki ya riqo su yana kallon su, banda fad'a, sultan qanin ka ne don't you know, kai kuma fu'ad yayan ka ne, dukkan ku ni kakan kune grandfather.

Fu'ad ya rungume sarki ta baya yana kuka ban yarda ba ban dashi kai babana ne, sultan Ma ya fada jikinsa yana qoqarin kuka ni bana son shi.

Rumaisa ta d'auki fu'ad tana fad'in ka dad'e tare da granny, sultan is new with him ka barshi mana, ya soma kuka yana qoqarin saukowa tare da miqawa sarki hannu alamar ya karbe sa shima sultan ya shige jikinsa ya kwanta sosai yana kallon fu'ad.

Afiya tace dan Allah ki barsu bana son kukan nan wlhy, umma tace sauke shi menene damuwar ki da rigimar yara, tana sauke shi ya nufi sarki, domin a xauna lafiya ya d'ora sultan a qafa d'aya fu'ad a qafa d'aya.

Aiman ya farfado bakori ya fada lokacin da ya qaraso inda suke, yana son ganin ka.

Sarki yaji dad'i sosai, shi ya fara shiga har lokacin aiman na kwance sam bai iya magana idanun sa ne kawai a bud'e, ya tsurawa sarki idanu shima sarki shi yake kallo duk yarima ya canxa kamar bashi ba, ya sunkuya tare da riqo hannun sa yana so yayi wa sarki bayanin afiya ta bashi guba amma baxai iya magana ba.

Rarrashi da addu'a sarki yayi masa kafin ya fito umma ta shiga, tana ganin sa ta fashe da kuka tace nabila ta cuce mu yarima Allah ya tada kafad'un ka.

Ya xuba mata idanu cikin mamaki, kenan nabila ce tayi yunqurin kashe sa ya lumshe idanun sa, ta sumbaci goshin sa tana shafa kansa a hankali, Allah ya baka lafiya amma komai yaxo qarshe yanxu yarima, matsalar mu ta kau insha Allah.

Rumaisa da afiya suka shigo, afiya na labe bayan rumaisa cikin tsoro da fargabar yi masa magana, rumaisa tayi masa ya jiki ya amsa da idanu yana qoqarin had'a ido da afiya dake labe a bayanta, fu'ad da sultan suka nufe sa da gudu daddy..

Lokaci d'aya suka yi qoqarin hawan gadon da yake kwance akai, rumaisa tayi saurin riqo su, sultan ya soma qoqarin kwace hannun sa yana fad'in he is my daddy leave me, fu'ad ma haka yake fad'a daddy sa ne.

Tace tam duk ku tsaya daddy bashi da lafiya baku ganshi a kwance ba kada kuyi qoqarin hawan gadon kunji.

Sorry daddy fu'ad ya fad'a yana kallon aiman, shima sultan ya kwaikwayi fu'ad d'in tare da qoqarin janye hannun fu'ad a jikin aiman alamar ya daina taba masa daddy.

Aiman kallon su kawai yake, rumaisa taja hannun su tana fad'in kuxo muje gida musha ice cream kafin daddy ya tashi ta fada cikin wayo da dabara aikuwa suka bi bayan ta da gudu suna jin dad'i.

Shiru d'akin yayi na tsawon wani lokaci, tana tsoron yi masa magana idan tayi duba da xargin da yake mata na qoqarin kashe shi, aiman kuwa lumshe idanun sa kawai yayi, ta qarasa gurin sa a hankali tare da riqo hannun sa.

Ya bud'e idanun sa kanta a sunkuye tana hawaye sosai, hannun sa daya saka yana share hawayen fuskar ta ya saka ta saurin d'agowa tana kallon sa, sai yayi mata murmushi ta fad'a jikinsa sosai tana kuka.

I can't kill you, you mean everything to me, my life my soul and I love you so much....

I love you Afiya taji muryar kamar a mafarki, cikin tsananin mamaki ta d'ago daga qirjin sa tana kallon sa idanun ta shar da hawaye, bakin ta na rawa tace me kake cewa, shima kallon mamaki yake mata batare da ya san me ya fad'a ba jin kalaman kawai yayi a bakin sa tamkar an fisge su da qarfi....
[2/29, 8:25 AM] Nawarty: Littafina na kud'i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980.

Ya tsura mata ido, tace please just say it again.

Menene wai? Abinda kace yanxu, yace komai ban ce ba, tayi murmushi tare da maida kanta jikinsa shiru yayi yana mamakin kansa menene ya fad'a da gaske shine ya fad'i hakan.

Jin an bud'e qofar ya saka afiya tashi da sauri daga jikin sa, Dr bakori ya shigo tare da kamila a bayan sa, ya jiki tayi saurin fada tana qoqarin had'a ido da aiman da tun da yaji ya farfado ta matsa sai taxo ta ganshi.

Aiman bai amsa ba idanun sa na kan bakori.

Madam can you excuse us pls, kinxo kin maqale mana patient haka.

Afiya taji wani nauyi ashe ya ganta ta sunkuyar da kanta qasa tana qoqarin tafiya aiman ya riqa hannunta tare da girgixa kansa.

Kamila kuwa tun da taji ance madam ta maida hankalin ta gun afiya sai taji ta raina kanta sosai bata ga laifin aiman ba dan yaqi kula wasu matan a waje saboda yasan irin macen da ya ajiye a gida, haushi da kishin afiya taji lokaci daya musamman yanda taga aiman d'in ya riqa hannun afiya alamar baya son ta fita.

Dr bakori yayi murmushi yana fad'in is ok our prince, ya duba shi afiya da kamila na tsaye, you are so lucky aiman gubar bata riga ta gama shiga jikin ka ba kuma bada yawa kaci ba, da yanxu fa sai dai mu haqura da kai.

Aiman murmushi kawai yayi, kamila kuwa ta matsu yayi magana taji muryar sa, ta matsa kad'an tare da russunawa, ya jiki Allah ya qara lafiya.

Gyad'a kai kawai yayi har lokacin yaqi kallon ta, afiya ta kafe kamilar da idanu cikin son gasgasta xargin yarinyar yanda take rawar jiki haka da aiman.

Dr bakori ya juya ya fice kamila tabi bayan sa, aiman ya dubi afiya tare da fad'in call umma pls, ta juya ta bar d'akin.

Umma wai kixo, tace meya faru.
Afiya tace nima ban sani ba yace a kira ki.

Umma ta tashi tana fad'in yanxu Ma nake son tafiya gida tunda jiki alhamdulillah, sarki tun d'axu ya tafi saboda gawar makirar can dake gidan.

Waye ya mutu kuma? Afiya ta tambaya cikin mamaki.

Umma ta dubi rumaisa ki sanar da ita halin da ake ciki kana ta fita batare da ta qara sauraren su ba.

Umma kin fara magana d'axu kika yi shiru ban fahimce ki ba game da nabila.

Umma tace ai damuwa da kukan da kaga jakadiya tana yi a baya har muka yi maganar da kai duka nabila ce ta sanyata a wannan halin tare da mahaifiyar ta.

Yayi jim yana sauraren ta, ta cigaba da fad'in jiya sai suka tursasa mata saka guba a abincin ka dana sarki da taqi shine ita nabilar ta karba ta saka da kanta, ni ban aika jakadiya kiran ka cin abinci xuwa sashen afiya ba wannan duk shirin nabila ne, jakadiya ta sanar da sarki abinda k faruwa kafin ya ankara ashe kai har kaci abincin ma, an maido min abinci cewa baxaka ci ba sai na aikawa nabila, banyi tunanin akwai wani abu aciki ba da itama baxan aika mata ba xan sa a xubar, bayan taci ne itama sai ta mutu, a bayanin da jakadiya tayi wa sarki mahaifin nabila ne ya saka a kashe ka ranar da xaku je kano sai tsautsayi ya fad'awa Bilal, itama nabila d'in ce ta sanar da ita lokacin da take ikirarin ko ta aikata abinda suka saka ta ko kuma su kashe ta da yan uwan ta gabaki d'aya, ko da aka kira gidan su nabila d'in a sanar ake gayamana mutuwar mahaifin ya kashe kansa saboda mutuwar y'ar sa nabila, yanxu sarki yaje gida tun d'axu bansan yanda xasu yi da gawar ba yanxu.

Aiman ya lumshe idanun sa Karo na biyu ya soma hawaye sosai, umma ta riqo hannun sa tare da fad'in mu godewa Allah daya tsare mana kai ga duka tarkon nabila musamman Ma wannan, kukan na menene yarima.

Yace umma ina kuka saboda aminina Bilal, ina kuka saboda ban d'auki fansa da hannu na kamar yanda na d'auki alqawarin duk wanda keda sa hannu a mutuwar sa ba amma 60% na damuwa ta ya kau yanxu tun da mahaifiya ta cika min wannan alqawarin nawa.

Umma ta xare ido tana kallon sa tace ni bani na kashe ta ba yarima, bansan da guba a abincin ba kuma ban bata abincin da wani nufi ba bayan girmama umarnin sarki daya ce a kula da ita shine har na bata abinci yarima taci.

Murmushi aiman yayi ganin ta tsorata, itama hannun ta saka tana share hawayen fuskar sa.

A ranar saif yaxo ya jinjina abinda ya faru, aiman yaji dad'in xuwan saif d'in har suka yi waya da ilham Ma ta gaida shi da jiki washe garin ranar ya bar garin.

Bayan kwana biyu sosai aiman ya sami lafiya majinyatan sa kamila da jamila sai nan nan suke dashi afiya kaf ta gane su bata taba nuna masu komai ko kishi akan yaran ba tasan babu yanda aiman xai kula su balle ya so su, a maimakon jinyar aiman da suke sai ta maida su tamkar yan aikin ta a asibitin, d'auko wannan wanke wannan yi wancan kira wannan duk sune ko da basa nan ne xata aika xaynab ta kira su domin ta lura duk ta fisu hankali acikin su, sai ya xamana bayi da aka kawo su kula da su afiya duk ta sa aka maida su gida komai su kamila ke yi, hankalin su bai taba basu afiya nayi masu hakan ne saboda ta gano su ba suna kallon hakan a matsayin tana qara kusan ta su da aiman d'in ne.

Aiman ma sarai ya gane take taken yaran lokacin daya fahimci abinda afiya ke yi kansu murmushi yayi, yanxu da ilham ce yasan kafin abar asibitin sai anyi masifa sosai amma ji yanda afiya ke tafiyar da su tana wahalar da su batare da sun ankara ba, metron nafee tun da tayi toxali da afiya bata qara xuwa duba aiman ba cos tasan baxai taba son ta ba har abada yana da irin wannan matar.

Ranar da xasu koma gida afiya ta saka su kamila kwashe kayan su kaf xuwa motocin su, da xasu tafi ta d'auki kud'i masu yawa ta basu tana murmushi.

Ladar jinya da kuka yiwa mijina, muna godiya sosai, and I pray Allah ya baku maxaje nagari.

Suka yi shiru suna kallon ta afiya ta bar d'akin da sauri sanin aiman ya dad'e da fita daga d'akin.

Kud'in hannun su suka kalla, wai dama duk wannan wahala da dawainiya da muka yi bata fahimci me muke nufi ba sai ta d'auki kud'i ta bamu cewar jamila.

Kamila tace to kodai ta fahimce mune shiyasa take ta wahalar damu ki duba fa shi kamar bai san muna yi ba bai taba kula my ba.

Xaynab ta karbi kud'in hannun jamila tana fad'in idan kun gama jimamin ku same ni a ward mu raba kud'in mts ta fice abinta.

*

Tun da jakadiya tayi ido biyu da yarima sai ta xube gabansa tana kuka sosai na neman afuwa akan laifin da tayi, ko kad'an aiman bai damu ba damuwar xuciyar sa duk yana kan mutuwar nabila da bai d'auki fansa sosai akan ta ba.

Kwanan sa biyu ya murmure ya sami lafiya sosai kamar ba shi ba, tafiya yake a hankali sultan na bayansa da gudu sai surutu yake masa wani ya amsa mishi wani kuma yayi murmushi kawai har suka iso fadar sarki.

Sultan ya nufi sarki yana tsalle, daddy yace yau xamu je shopping.

Mai martaba yayi murmushi kawai yana kallon sa, aiman ya xauna tare da sunkuyar da kansa qasa kad'an ganin har lokacin sarki bai bar fushi da shi ba tun sakin ilham ya sa ya kasa sakin jiki da shi kamar ko yaushe.

Daddy am so sorry ya fad'a yana kallon mahaifin nasa a sanyaye.

For what? ya tambaya cikin halin ko in kula d'innan.

Aiman yayi jim kafin yace for divorcing ilham, nayi kuskure kayi haquri daddy.

Sorry granny sultan ya fad'a yana kallon sa, daddy yace kayi haquri.

Wannan karon murmushi aiman da mai martaba suka yi, kafin su soma hira sama sama ba kamar kullum ba, sanda aiman xai tafi sultan yace sai ya d'auke shi baxai tafi da qafafun sa ba, haka aiman ya d'auke shi suka fito.

Wani bawa dake raqube yana jiran fitowar yarima ya nufe sa da sauri jikinsa na rawa.

Ranka shi dad'e dan Allah ka taimake ni na siyawa mahaifiya magani bata da lafiya sosai.

Aiman yayi shiru kafin yace tun yaushe bata da lafiya.

Bawan yace an kwana biyu yanxu.

Shine sai yanxu xaka nema mata kud'in magani, ina kud'in da ake biyan ka.

Cikin kuka mutumin yace na siye abinci sauran na kai yara makaranta dama ban saka su ba, ayi haquri yallabai.

Aiman ya bashi kud'i tare da fad'in xuwa gobe idan jikin ta bai yi sauqi ba ka kaimin ita asibiti.

Nagode ranka shi dad'e Allah shi albarka ya qara tsawon rai da arxiki.

Aiman ya fice sultan ya dube sa, daddy menene ka bashi he looks happy.

Aiman yace kud'i, yace menene kud'i me ake yi dasu, aiman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login