Showing 30001 words to 33000 words out of 66328 words

Chapter 11 - Kurman Baki Hausa Novel Complete

tsantsar bacin rai. Daga zaunen saleem ya daga kai ya bita da kallo. Tsaiwarta a gurin kawai ya canza atmosphere na wajen. Daurin qirjin nan ne dai na gado sai armless shirt daga ciki,qafafunta tsage tsage a waje kamar sunyi d'ai d'ai

"Da akayi me?" Ya jefa mata tambayar. Cikinta ne ya juya abinda ya Sanya yawu taruwa a bakinta kenan,sai ta juya gefan hagunta ta fesar da yawun tasa bayan hannunta ta goge ragowar da ya bata mata baki. Da sauri ruqayya ta kawar da kanta gefe tana a'uziyya zuciyarta na tashi saboda tsantsami.

Juyowa Zainab din tayi tana duban saleem

"Ta yaya zakayi shawara da ita ita kadai,bayan ba ita kadaice matarka ba?,ba ita kadaice take da haqqi a kanka ba,sai nayi magana kuma aga na cika qorafi bayan adalcinne sam ba'a yishi ba?"

"Ni kika tsayawa akai kina gayan ban miki adalci ba?" Yadda yayi mata tambayar ta bugar mata da gwiwa,amma rashin son gaskiya da jin tafi qarfin ayi mata fada sunyi mata katutu saita kauda kanta gefe ta fara halin nata wato gunaguni

"Eh ai azzaluma ka tambaya gashi tana batun ni da ita duka mu rasa ku tafi kai da hajiya saboda tsabar muguntar kowama ya rasa,bayan ko hajiyarma ta taba zuwa ai,nice ba inda na taba leqawa a qa'ida......" Ta fada hannunta a qugunta ba tare data dubeshi ba.

"Idan baki matsamin akai ba sai ranki yayi mummunan baci,sakara mara wayo" maganar ta girmi kunnenta don bai taba gwada fadin hakan ba

"Um um daddynsu,ya isa don Allah" ruqayya ta fadi qasa qasa tana tausarsa saboda ta hangi fushin da ya fara tasiri a idanunsa

"Ki qyaleni na fadi mata,naji ta fara sako batun hajiya ne,ta dauka yanzun daa ne da zan dauki iskancinta akan uwata,wanda kikayi a baya ma na kasa tsawatar miki istigfari nakeyi har yanzu" can qasan zuciyar ruqayya cewa kawai tayi uhmmmm. Zuwan Zainab gidan tana amarya ba ita ba,hatta hajiyan ta shuka mata iskanci kala kala,ba zaka taba zaton akwai wata alaqa ta jini tsakaninta da hajiyan ba,a lokacin bai cewa komai,shi yasa ruqayyan tayi qoqari ta kama mutunci sosai a lokacin (kira ga uwayen gidaje,ina qara gaya muku sau tari ku kike siyawa kanku daraja da mutunci a farkon zuwan abokan zamanku,kuma kuke basu fuska da qofar rainaku tun farko,ki watsar da ita da me gidan gaba daya ki basu space ki maida kanki busy a lokacin da suke ganiyar cin amarcinsu,hakan shine zaifi zame miki alkhairi akan sanya idanu akan duk wani motsi nasu,ranki zaiyita baci ne kina ganin abubuwan da babu lallai suyi miki dadi,ke kuma babu tabbas din zuciyarki zata iya jurewa).

Wannan kame kan shine abinda ya jawo har yau duk iya iskancin Zainab da ganin ruqayyan ta tare mata gaba ta tare mata baya ba komai take iya tunkararta da shi ba.

"To ai saika dauki mataki yanzu ma bata baci ba" ta fadi a zafafe,saidai gama fadin keda wuya wani zazzafan amai ya biyo baya.

Dan janye jiki ruqayya tayi cikin mamaki,zubewar da taga zainab din tayi a wajen ya sanyata miqewa tana fadin

"Subhanallahi lafiya?" Qarasowa tayi dab da ita tana qoqarin riqota,saidai wani yanayi dake tashi a jikinta ya sanyata matsawa gefe ta tsugunna tana mata sannu.

Mugun galabaita ta fara yi,ita da saleem din suna tsaye a kanta. Wannan abun ya sake bawa zainab dama ta sake ragwabewa sosai ta narke kamar matacciya

"Dauko mata hijabi mu tafi asibiti" tsam ta miqe tana juya yadda Zainab din ta sake gaba daga yin amai?. Eh tayi wani irin amai mai yawa a gurin amma baici ace ta sassake haka ba.

Sau biyu tana sallama yaran basuji ba saboda sun qure qarar tv sunata kuma damben fada akan abun wasa,harda haneefa da ya kamata ace a shekarunta ba wannan abun yakeyi ba,ita ke kula ma da khaleel.

Sanda suka farga da kallo suka bita baki sake saboda ba zasu iya cewa ga ranar qarshe data tako sashen nasu ba. Tunda ta shiga falon yanayin falon taji sam baiyi mata ba,haka ta dinga takawa cikin tsantsani don ko ina datti ne,bata tunanin jiya ya samu kyakkyawar shara,yau kuwa dama tunda tana sauri biki ya samu tayi imanin inda zata leqa kitchen dinta ko wanke wanke batayi ba.

Kusan ginin nasu iri daya ne,wannan ya sanya bata sha wahalar gane inda bedroom dinta yake ba

"Karki shigarwa ummanmu daki fa" haneefa ta fada tana kallon ruqayya. Sosai abun ya bawa ruqayya mamaki,ta juyo tana duban yarinyar. Har tasan wani kishiya kada ta shigarwa kishiya daki?, komai ma wai zama zainab takeyi da yaran ta gaya musu?.

Hannu ruqayya ta saka ta yafitota tana murmushi

"Zoki nunan kayan ummanki zan dauko mata zani da hijab,asibiti daddynku zai kaita" tsalle tayo ta sauko daga saman kujerar da sun jima da cin ubanta ta nufo ruqayyan ba tare da ta maida hankali ga batun zuwa asibiti ba

"Zakisha wahala,dauko kayan ummanmu akwai wahala,don itama kullum saidai ta gaji ta dauko wanda ta gani ta mayar da sauran" bata cewa yarinyar komai ba tabi bayanta.

Kusan idan ka ganta cikin dakin Zainab haihuwa tayi,rabonta da bedroom dinta tun haihuwar khalil. Tayi mamaki har fiye da zato na yadda ta zamu dakin nata a hargitse,hatta da shimfidar gadon a harmutse take,harda qasa qasa a kai,panties nata Brazier da cup harda spoon ma. Qasan dakin kuwa baja baja yake da karikice da bazata ma iya tsaiwa tantancesu ba. Dakin ba abinda yakeyi sai wani irin hamami hamami kamar warin dauda cakude da warin hammata. Bata sani ba amma qila tsabar tashi da jiki da hammatar Zainab din keyi da annakiyar da dakin yake da ita ne ya sanya a madadin qamshin turare... Nata turaren ya zama wadannan warika ne gud biyu. Bandaki shima na buso tashi gudunmawar qarni da zarnin ta qoofar bandakin dake a wangale.

Gaba daya kayane jibge a rataye tun daga murfin sif din zuwa kan qofar bandakin,zannuwanta ne panties da riguna.

Haneefa ce ta bude sif din hankalin ruqayya nakan wani tsadajjen turarensu data gani yashe a qasa an tattara kwalbar an shareta acan matse matsi mudubi,ta yiwu dazun da tana saurin zata fice ne ya fashe garin ta saka,ita kuma ba zata iya tsaiwa ba ta tattareshi gefe da zummar saita dawo,data dawo din kuma bata da lokacin bi ta kansa sai ranar da Allah yakai tsintsiyar shararta gurin.

Zubowar kaya kawai ruqayya taji yiiiiiiffffff kamar an saki buhu. Gefe ta matsa da sauri adan tsorace,haneefa ta sheqe da dariya

"Haka ummanmu takeyi kullum idan zata saka kaya,ki zabar mata saiki barsu a gurin saikin dawo,ko natayaki mu mayar" yarinyar ta fada hankalinta kwance cikin nishadi kamar me bada labarin abun arziqi.

Tsaf ruqayya ta qarewa kayan kallo,tama kasa tantance meye da meye,don basu da maraba kwashen dilar kayan gwanjo

"Ke da nace kaya aiba wanki za'a kai ba,ba kayan dauda ba wankakku asibiti zataje" baki ta saki tana kallon ruqayya

"Ai sune wadannan,idan aka kawosu daga wanki watsasu mukeyi,idan muka cire kuma indai laundry basket dinmu ya cika sai mu ajjiye ciki idan an tashi kai wanki a kwaso,rannan ma daddy yace duka kayan ciki tsami sukeyi" ta fadi tana toshe hanci cikin son gwada yadda yayin a ranar tana dariya abinta don maganar har yau dariya take bata

"Ya isa,ina hanaki fadin abu ko an tambayeki bare ba'a tambayeki ba,mu kwashe kayan mu mayar" tace da haneefan.

Tana tilar kayan tana dauke numfashi da kau da kanta,haka ta dunga diba tana cusasu yadda ta gansu haneefa na tayata. Kafin su gama cikinta ya gama gurbata,da qyar ta iya gano zani da hijabi ta fito dasu a hannunta amma zuciyarta fal qyanqyami.

A nan ta samesu,ta ajjiyewa zainab din kayan amma sai tayi talau alamun ba zata iya sakawa ba. Saleem dinne ya karba ya fara saka mata. Da ya gama saka matan ya riqeta suka fita farfajiyar gidan Zainab din tana layi kaman zata fadi.

Kwanukan abincinta ta fara tattarawa tana daukesu a wajen kafin suma su fita a kanta.
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 15

https://chat.whatsapp.com/KHGP5vnV6yg6X9CpkQcf39


*_Assalamualaikum warahmatullah_*

*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*

*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*
____________________________



Tana kitchen taji ya sake shigowa

"Ki dauko mayafi muje mu kaita" waiwayowa tayi ta kalleshi,sai kuma ta kauda kai. Wani abune ke mata yawo a zuciya,ba zata taba manta wannan ranar ba,ranar da banda kiyayewar Allah babu abinda zai hana ta rasa ranta a abinda Zainab din tayi mata,bayan ta rasa ranta harma ta rasa ran abinda yake cikinta

"Kuje kawai saikun dawo,zan zauna da yaran tunda dai ba za'a barsu haka gida ba kowa ba" ido ya zuba mata na wasu sakanni,har zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juya ya fice.

Koda ta gama kintsa kitchen din alhassan ta aika ya kirayi su haneefa suka dawo sashenta,sannan ta saka alhassan din ya kulle sashen zainab din,don yafi haneefa nutsuwa da hankali,sau tari banda tsaho da ta fishi zaka dauka shine babban.

Falon ta dawo ta zauna lokaci lokaci tana duba wayarta,yaran suna kallon carton,saidai bari bari da su haneefa din keta sanyata,ba'a samu sauqin abun ba sai da khalil yayi bacci.

Dole ta saka ya qure ac dinsa saboda yanayin da jikinta ke bayarwa da ya soma dumame motar. Yawun takaici kawai yake hadiyewa,ya rasa me Zainab ke buqata a rayuwa da zai sanya ta canza halinta. Wasu lokuta yakanji kunyar ace ita din matarsa ce,abinda bai taba ji ba dangane da ruqayya duk da sunfi dadewa da ita nesa ba kusa ba akan zainab din.

Wani kuka take kwazara mishi babu dadin amo bare dadin sauraro,ita a haka dole kukan da zai taba ransa yaja hankalinsa,abinda bata sani ba zallar takaici ne ya qumeshi.

"Wallahi na sake yarda da gaske asiri yana tasiri a kanka,na rantse da Allah ko kaffara bazanyi ba inda ruqayya ke wannan kukan da tuni ka rasa inda zaka tsoma ranka,amma ba komai akwai Allah"

"Ba zaki rusuna ba kenan ki saita kanki ba"

"Me nayin da har zan rusuna?,saboda kawai idan ba'a sonka idan ka fada ruwa ma sai ace ka tayar da qura?,kuma ko meye ya sameni ai ta sanadinka ne,duk inayine don na gyara kaina na samawarwa kaina 'yanci kamar yadda ruqayya ke dashi,don bana son kaucewa hanya nabi malamai".

"Anzo gurin" ya fada a ransa,cikin zuciyarsa yana fatan ace shiriyarta ce tazo,sai ya sassauta tuqinsa yana duban titi

"Ai baki kama hanya ba sam zainab,ke din ba makauniya bace amma ta wani fannin kinfi makaho makanta,ta yaya kike tunanin zaki kamo ruqayya a haka?,bayan kinfi kowa sanin abubuwan da takeyi wadanda suka kaita matsayin da kike hange?,duk da ina iyakacin bakin qoqari na na yin adalci a tsakaninku?" Kamar ta banka masa ashariya haka taji,ita da yayi mata misali ko kwatance da ruqayya gwara ya sakata a daki ya lallasata tayi dumamen jikinta

"Wanne abu takeyi banda zallar kissa da munafunci da bin malaman tsubbu duk don ta mallakeka?,idanunka ya rufe ka kasa ganin gaskiya?,ni da kullum nake fadi tashin gyara maka shimfidarka amma qoqarina a banza yake kullum". Kai ya girgiza

"Zaki bawa Allah tabbaci ranar qiyama akan qazafin bin malamai zainab,ki kiyaye harshenki daga fadar abinda baki da yaqini akai" kuka ta fashe masa dashi

"Ehnnn,an tabo shalelenka ba?,muddin kana irin wannan akan ruqayya wallahi zaman lafiya tsakanina da ita har abada" ko ya waiwaya ya kalleta bai sakeyi ba,ya sani Zainab tayi nisan da bazata taba jin kira ba sai wani ikon Allahn.

Sun samu sunga likita,amma yawan gudawar da takeyi yasa likitan yace zata kwana anan a saka mata drip,gudun kada suje gida cikin dare abun yayi worsening.

Sosai ta sharbe masa tana ci gaba da koke kokenta da babu abinda suke qarawa saleem sai takaici. Don tuni likita ya gaya masa ya dinga sakata tana kiyaye shan magani barkatai

"Magungunan nan basu da wata qa'ida ko doka,duk maganin da za'a shashi ba bisa qa'ida ba dole yayi illa" tuni saleem din ya fahimci maganin meye,ba zata daina halinta ba kenan duk da tarin gargadin da yayi mata?.

Bai iso dakin da suka batan ba sai daya kira hajiyayye qanwar mahaifiyarta akan tazo ta kwana da ita sannan ya wuce dakin. Tanajin sallamarsa ta sharbe magashiyyan. Baibi ta kanta ba tsabar takaici,yaja kujera ya zauna kawai yana danna wayarshi.

Ba dadewa hajiyayye ta iso,ya miqe yana bata gurin zama

"Da kayi zamanka abinka" hajiyayye tace

"Ah dama ke nake jira,tafiya zanyi ni" ido zainab din ta bude da sauri,taci alwashin yau kwanan asibitin zaiyi,shine abinda zatayi kawai wanda zai quntata ran ruqayya. Yunqurin amai ta fara yi na qarya,shi da hajiyayyen dukka suka qaraso,saidai babu wani abu data fitar don tuni aman gasken ya fidda komai daga cikinta

"Idan na fita zan tsaya na yiwa nurses din magana,ko alluran tsaida amai din suzo suyi mata" ya fadi yana matsawa gurin saman kanta

"Sai da safe zan sake shigowa,banajima zamu kai azahar bamu koma gida ba,Allah ya sawwaqe " ya fada yana fiddo kudi daga aljihunsa ya ajjiye gefan kanta cikin qoqarin danne bacin ransa kada duniya ta fahimci halin da suke ciki

"Yanzu ko tausayin halin da nake ciki bakayi tafiya zakayi?" Ta fada da qarfi don hajiyayye taji harda matso hawaye

"Banda abinki zamansa a nan ai bazaiyiwu ba,kuma me zaiyi miki shi da bashi ke cire ciwo ba?,jeka abinka gida,Allah ya bamu alkhairi"

"Sai da safe" ya fadi yana ficewa.

Kaman jira takeyi ya fitan ta miqe ta zauna sosai har cannula din hannunta na qoqarin gocewa

"Banso kikayi magana ba, wallahi hajiyayye na fara gajiya da rashin adalcinsa,qiri qiri mutumin nan kiga abinda yakeyi,na rantse miki da Allah yau inda ruqayya ce zatayi kwanan asibiti bazai iya tafiya ya barta ba" kai kawai hajiyayye dake cire hijabinta ta daga ta kalli Zainab. Duk da tasan wasu abubuwan amma sai tayi kaman bata sani ba ta hanyar tambayarta

"Saboda me?"

"Saboda wani irin mahaukacin kula da yakeyi da ita da wani kulawa da na tabbatar ba ta domin Allah bace"

"Ke ya akayi kikasan bata Allah bace zainab?" Hajiyayye ta fada tana jawo kujera dab da gadon Zainab din saboda su biyu ne a dakin,donma daya patient din tayi bacci abinta tuntuni,kuma abun mamakin ita kadaice babu dan jinya. Sake jan kujerar tayi baya kadan saboda yanayin da jikin zainab din ke bayarwa taci gaba da kallonta daga nesa nesa

"Yo hajiyayye aiba irin wannan soyayyar a yanzu a wajen mazan wannan zamanin,kana gyara ma ya ka cika dasu bare baka gyara,nifa kullum cikin fuskantar matsala nakeyi da saleem,kyara gwasalewa,komai nayi banyi dai dai ba,komai nayi baya nuna wani jib dadi ko kuma wai na burgeshi,ni kuma a iya sanina macen da bata gyara HQ dinta ita ke fuskantar wannan matsalar,macen dake gyara take kulawa baji ba gani ai tafi qarfin ayi mata irin wannan tijarar,to ita ba wani gyara da takeyi matar nan,idan kuwa ba asiri ba banga ta yadda zata mallaki saleem ba"

"A tunaninki?" Hajiyayye data gama sauraron soki burutsun zainab ta fadi tana dubanta

"Hakane mana" zainab ta amsa mata kai tsaye

"Sam sam" ta sake maida mata tana zama sosai idanunta cikin nata

"Mun sani mafi rinjayen abinda ake kira da aure wannan abunne,to amma shi kansa baya tasiri baya kuma qayatarwa gami da jan hankalin d'a namiji saikin mallaki wasu abubuwan,tsafta,ladabi biyayya iya magana tattalin miji da tarairaya duka ina kika barosu?,ina kika baro iya girki?,ado da gayu?"

"Duk basukai wannan muhimmanci ba hajiyayye,indai sune ke riqe maka miji me yasa saleem ya auroni idan ka cire matsalar haihuwa?,ita kanta haihuwar ba damun wani namijin tayi ba indai zai samu wannan gurin da kyau" ta fada tana qoqarin maida kanta ta kwanta,don kwata kwata maganganun hajiyayye basu samu matsugunni a ranta ba.

Ta dade da sanin Zainab da kafiya da kafirin taurin kai,musu kuwa ba abinda yafi mata shi sauqi,tunda har bata da intention na ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login