Showing 33001 words to 36000 words out of 66328 words

Chapter 12 - Kurman Baki Hausa Novel Complete

fahimcetan to ba fahimtarta zatayi ba,zata batawa kanta baki ne,don haka tace

"Gaskiya ne,hakane,amma akwai gaskiya daya da zan gaya miki,don Allah ki dinga qoqarin amfani da turare,sannan kodon zirga zirgar da kake wuni kanayi wankanki ki maidashi sau biyu"

"Ke hajiyayye kin ganni nan,saleem bai taba cewa wani abu ba,turare kuwa mu ko munsa ko bamu saka ba mun wanku fes daga gurin kakanninmu,jikinmu baya komai in gaya miki,ki qyaleni na huta"

"Hakka" tace da ita kawai tana tura kujerarta baya,ta dauki wayarta ta soma chart abinda.(hajiyayyen bazawara ce, mijinta ne ya rasu ya barta bata taba haihuwa ba,shekarunta kuma duka duka basu wuce arba'in da biyu ba).

Idanunta ta rufe saidai maimakon tayi nazarin maganganun hajiyayye a'ah,asarar da zata tafka ta maganinta take qiyastawa indai shegen likitan nan ya riqeta bai sallameta ba a gobe

"Aikuwa koda tsiya koda tsiya tsiya dai an sallameni gobe" ta fada tana muskutawa hadi da gyara kwanciyarta.

"Me kika ce?" Hajiyayye ta daga kanta tana tambayarta

"Ba dake nake ba" ta amsa mata don bata taba zaton zancan zucin da takeyi ya fito fili ba. Itama bata sake tambayarta ba ta maida kanta ga abinda takeyi.

********Dogon tsaki taja tana gallawa wayar ta data dauki ruri a karo na babu adadi harara

"Kinsan fa ni banason irin wannan abun,waye yake kiranki da baki daga ba bare ki kawo masa uzuri?" Umma dake zaune a gefanta tana cin tuwon dare ta fada

"Isma'il ne umma"

"To ki daga mana?"

"Haba umma,dame zanji don Allah?,da takaicin shegen yaron nan da na aika ya siyomin indomie yaje ya zauna koda nacin kiran wayarsa?" Side hannunta data gama cin tuwon umma ta farayi tana cewa

"Duk dai ke kika jawowa kanki,inda tuwonki kikaci da ba yanzu bakinki alaikum ba,ba wanda yaji bare ya gani"

"Allah ya sawwaqe,tuwon masara aisaidai a bawa gawata" ta fada tana kyabe baki tare da gyara zamanta tana ci gaba da hada sabbin syrup da supplements din gyaran jiki dana qiba data siyo jiya. Gefe kuma ga mayukan saka hasken fata suma data yiwa roba guda.

Dai dai nan yaron ya kwado sallama ya shigo hannunsa da baqar leda

"Kaci uwarka surajo,inda kasan dadewa zakayi uban me yasa ka karbarmin aike?"

"Banason lamarin zagin iyaye na gaya miki malama" umma ta fada tana kwada mata harara

"Layine a wajne wallahi da qyar akazo kaina"

"To kinji ma" umman ta fada ta yunqura tana miqewa da kwanonta ta nufi kitchen.

Jakar umma ta jawo ta zuge,daga can umman ta jiyo qarar zuge jakar

"A'ah fa,ni ba zaki talautani a daren nan ba,na baki kudin indomie me kuma kike nema?"

"Pepsi zai siyomin don Allah,sai kuma ashirin din dana masa alqawari,zan biyaki bashi na ansa" ta fada tana ciro kudin da sauri ta miqawa surajo din tana masa inkiyar yayi sauri ya fita.
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 16


*_RUK'AYYAT GRAPHICS_*

*_Ina mata ma'abota sana'o'in online dama na cikin gidaje?_*

*_kamfanoni da ma'aikatu da masu office office?_*

*_kuna buqatar qayataccen kuma unique design masu kyan gaske na_*

LOGO
INVITATION CARDS
BANK STICKERS
BUSINESS LOGO
SAVE THE DATE
P.O.S BANNERS
BIRTHDAY CARD
BOOK COVER
DATA FLAYER
BIRTHDAY VIDEOS
VIDEO INVITATION
AI PICTURES

_KAI DAMA SAURAN DUKKANIN GRAPHICS DESIGNS_

*_INA MASU SON KOYON SHI KANSA GRAPHICS DIN DUNGURUM GUM GABA DAYA DON DOGARO DA KAI KUMA BUQATAR KANKI?_*

*RUKAYYAT GRAPHICS* itace amsarku

_KU GARZAYA MAZA KU TUNTUBETA,KU DANNA WANNAN BLUE DIN RUBUTAN DON YIN MAGANA DA ITA KANKU TSAYE_

https://wa.me/+2347084515410

_ZAKU SAMU KOMAI DAI DAI DA ALJIHUNKU BISA FARASHIN RANGWAME_πŸ‘ŒπŸ½πŸ‘ŒπŸ½πŸ‘ŒπŸ½πŸ‘ŒπŸ½
_____________________________


Da gudu surajo ya cilla ya fice daga gidan,saboda yasan indai umman ta fito ta karbi kudinta to ya shiga uku gurin wasila. Hakanan 'yar naira ashirin dinsa shima ta shiga rububi.

Umma na daga kitchen tana mitar halin wasilan na zabe zaben abinci

"To wai umma idan bakiyimin ba waye zaimin?,kuma ai ansan banason tuwon aka tashi akayi mana,kinga kuwa bazan kwana da yunwa ba". Suna tsaka da wannan taqaddamar Surajon ya dawo. Tasa hannu ta karba tana cewa

"Surajo me abun arziqi da na tsiya,yanzu dai sai gaka sharp sharp,to ga kudinka" ta miqa masa ashrin din. Hannu yasa ya karba yana cewa

"Ana sallama ma sake a waje" fuska tadan bata

"Waye?"

"Isma'il ne" ya bata amsa dai dai sanda umma ke fitowa daga kitchen

"Bawan Allah dan albarka,je kace tana zuwa kaji" juyawa yayi ya fice abinsa,yayin da fuskar wasila ta canza ta jawo ledarta tana budewa. Kallonta umma tayi

"Nayi tsammanin zakije ki fara saurararsa kada abar mutum haka a tsaye?"

"Ni yunwa nakeji wallahi umma,sai naci abinci tukunna,idan bazai iya jira ba ya tafi"

"A'ah,kedai kiyi da jiki ki gama" umman ta fada tana kade gefan tabarmar da suke kai din ta sanya hijabinta ta tayar da sallar isha'i.

Da gayya ta dinga laqai laqai harta gama,siririn mayafi kawai ta yafa saman doguwar rigar jikinta tadan sake shafa turare tayi hanyar soron. Haushin isma'il takeji,wannan shige matan da yakeyi,sai taga kamar yana nesanta ta ne da irin mazan da take sa muradi,yaqi ya gane yaqiyin zuciya kuma ya barta.

Kansa a qasa yana danne danne a wayarsa,jin takunta ya sanyashi daga kai daga abinda yakeyi yana dubanta,sai ya saki qaramin murmushi yana fadin

"Barkanki da fitowa ranki ya dade"

"Yauwa,barka" ta fadi kadaran kadaham. Ita kanta tasan isma'il bashi da wata matsala ko makusa,amma an riga an gaya mata ba shine alkhairi a tattare da ita ba,kuma itama ta gamsu da hakan,tunda baikai arziqin da takeson mijinta ace yana da shi ba,yadda take da tarin magauta din nan,tanason ta auri mijin da idan ta shiga gidansa za'a san yes!,ta auri me arziqi,mijin da first night dinta zai bata kyautar mota,mijin da zata dinga zuwa umra da aikin hajji har sai ta gaji,mijin da zai dinga sauya mata kalar motocin da zata ji dadin takota ta shigo unguwarsu tana fankama da hura hanci,ta bule maqiya da mahassada da qura,ana kiran hajiya wasila tana kyautar sabbin kudi,dukka tasan isma'il bazai iya affording wannan ba,duk kuwa da tasan ci sha sutura da wirin zama duk ba zata raza ba,don bai rasa komai din ba,hasalima Lagos yake zuwa yayi sari na shagonsa me yawa. Ya siya fili kuma gini yakeyi me kyau,amma yace mata idan bai samu kammalawa ba har lokacin aurensu zai kama musu haya kafin ya kammala daga bisani sai su tare.

Itakam babban abun kunya ne a gareta ace wai yau ita wasila.......wasila guda tana a gidan haya,me yafi wannan abun kunya?,duk wadanda duka sanya ido suga ya zaka qare suyi maka dariya suyi shewa son ransu kenan,Allah sitru buqui inji kishiyar me doro.

Shi ya karba daddumar da ta fito da ita ya shimfida sannan suka zauna akai.

Kusan fiye da rabin hirar shi yakeyi,har zuwa wani lokaci da yaga ta fara hamma da lumshe idanu duk kuwa da cewa duka duka baifi minti arba'in da zuwa ba

"Yadai?" Ya tambayeta cikin kulawa. Fuska ta yatsina ta danja tsaki

"Bacci nakeji,kuma ma dai yunwa ma nakeji,haka kawai umma tayi mana tuwo yau"

"Subhanallahi" ya fada cikin dan gajeran nazari. Bayan dan shuru da ya biyo baya na sakanni sai kuma yace

"Ai bai kamata ki kwana da yunwa ba seela ta" ya fada yana fiddo wayarsa a aljihu. Bugu biyu aka daga suka gaisa

"Ina layin nan dake kallon gurinku........eh takeaway nakeso a hadamin me kyau.......yauwa komai da komao,ya miqo layin sosai sai yazo gaban wani gida me farin fenti ina daga ciki...... alright na gode" daga haka ya cire wayar a kunnensa ya maida aljihunsa

"Ai da ka barshi wallahi" Ta fada kawai don jin baki

"A'ah,ba za'a yi haka ba ai,so kike nima na kasa bacci?" Murmushi ta saki tana jin dadi a ranta

"Yauwa ni da albishir mafa nazo miki,ga yunwa kuma kina ji,anya albishir din nan zai fadu?" Wata zaquwa ce ta kamata, zuciyarta na hasaso mata waya zai sauya mata

"Fadi kanka tsaye yallabai,ai dukka kunnuwana suna tare da kai"

"To shikenan yallabiya" ya furta cikin dan salon tsokana,yaza hannu ya tura hularsa baya sannan yace

"Zuwa yanzu wasila ina gani lokaci yayi da zamu maida alaqarmu ta ainihin gaske,tunda iya fahimtar juna mun yishi tsahon shekarun da muke tare,ina so ki shaidawa umma,ta yiwa su kawu magana in sha Allah qarshen watan nan zan aiko da kudin aurenmu hade da kudin sa rana,kuma banason duka a wuce wata hudu in sha Allah ba'a yi bikin ba" tunda ya fara zancan ta zuba masa ido gabanta yana faduwa. Bata shirya auren isma'il ba bata kuma son ta rasashi tun yanzu,tafison koda zai tafi sai idan FAISAL ko wani kaman faisal din ya kawo mata kudin aurenta tasan ta kama dahir

"Kudin aure kuma isma'il ka gama ginin ne?" Ta fada tana dubansa. Dan nazarinta yayi kadan

"A'ah,yanzu ba magana ake ta gama gini ba,gini na yana da buqatar a zuba masa kudade da yawa,inason nayi abu me kyau me tsari,wanda duk wanda ya kalla zai san na mori nemana" Fuska tadan bata tana girgiza kai

"Gaskiya nidai nafi buqatar ka kammala tukunna"

"Wasila" ya kira sunanta kai tsaye a maimakon seela da yakan kirata da shi,abinda yasa itama tayi hanzarin daga kai tana dubansa

"Ni na shirya aure magana ta gaskiya,sanann hajiya kanta kullum maganarta kenan nayi aure taga 'ya'yana kafin ta Allah ta kasance a kanta tunda ban rasa komai ba,hankalina nima yanzu ya karkata ga hakan,in sha Allah bazan wuce wannan lokacin ba tare da nayi aure ba,idan kin shirya nima na shirya"

"Idan ban shirya ba fa?" Ta fadi a qasan ranta tana dan satar kallonsa gabanta yana sake tsananta faduwa. Isma'il shine saurayi kusan na biyar da haka ta taba faruwa a tsakaninsu. Abdullahi,abubakar,nasir da sagir ga kuma isma'il. Dukkansu sun tafi ne saboda samun masu kudin da take muradi a irin wannan lokacin,kamar hadin baki dukkansu sai zance ya fara nisa a tsakaninsu sai masu kudin da take buri su bayyana saisu rushe gwamnatinsu,sai bayan ta sallamesu ne saboda ganin wadan nan sai suma daga baya su fece su barta ba wan ba qanin. Tayi qunan rai a sannan ba dan kadan ba,tun daga lokacin ta yanke hukuncin ta daina sallamar standby din har sai ta tabbatar ta kama wadancan din,yanxu gashi ana neman kwatawa
(Yan mata!,yan mata!,wallahi wallahi wallahi kuyi hankali,ku yiwa kanku karatun ta nutsu,a irin wannan yanayin da ake ciki babban arziqi ne ma ki samu wanda zaice yau so nake muyi aure,da yawansu ba aure bane a ransu,saidai suzo su hole da ke kamar uwa su ta haifa musu ke,da yawan 'yammata ba mijin aure suka rasa ba, a'ah.......MIJIN BURI MIJIN MAFARKI suke jira ko ince suke nema,kibar wahalar da kanki kina namena lallai saikin auri me kudi,wallahi wannan din da kika raina qila shine me kudin da kike burin amma kika wulaqantashi,Allah ya rubuta sai ya aureki zakuyi arziqin tare amma kika bijire saboda idanunki sun kulle, ba'a ce ki auri namijin da bazai iya kula dake ba,namijin d a baikai ajinki ba,tunda ko a musulunci akwai KAFAA'A wato dacewa da juna,amma ta yaya a gidanku ana kulawa dake da kwatankwacin kudin da sukakai dubu dari kice ke wanda zai kula dake da million d'ari kike nema?wanne irin buri ne wannan?. A qa'ida dai ba'a son ana kula dake a dubu dari ki auri wanda saidai ya kula dake da dubu goma,ko ina anason aga mace gidan mijinta yafi gidansu ci gaba,AMMA FAπŸ‘‚πŸΌπŸ‘‚πŸΌπŸ‘‚πŸΌ ba tarin dukiya ba. Albishirinku!!!!,akwai tarin dimbin matan da zaki gani cikin leshi na kece alfarma,motar hawa ta isa da qasaita,gold kowanne corners na jikinta bodyguard da sauransu,amma billahillazi la'ilaha illa huwa da zata bude miki cikinta saikin kwana kina sallah kina godewa Allah da ya barki a inda kike,shi aure bawai mutum me DUKIYA kadai ake nema ba,Inaaaaaa........'yar uwa nemi MAI ZUCIYA wanda ko matar da take Jin mijinta wani ne idan kuka jera da ita zatasan lallai kinfi qarfin raini,nemi mijin dake KISHINKI wanda bai yarda matarsa ta rasa komai ba,wanda bai yarda a raina matarsa ba,wanda zai maidake SHALELE kifi qarfin rainin kowacce mace,mijin da zai kula da lafiyarki sai inda qarfinsa ya qare,wanda ya damu da damuwarki me tsare miki mutuncinki da dukkan qarfi da iyawarsa,wanda zai dauki iyayenki tamkar nasa ya basu girma na musamman.ba mai tarin dukiyar da baki da tabbas din zaki cita cikin kwanciyar hankali ma kuwa?. Da yawan 'yammata basu shiga gidan aure sunsan meye ainihin ma'anar miji ME DUKIYA ba dame ZUCIYA wannan shike rudarsu. Akwai wani jin dadin da duk girmansa kome miji yake baki koda kullum million hamsin ce wallahil azeem idan yana miki wasu halayen ba zaki taba jin dandanonsu ba,saikin gwammace naira dubu goma yake baki yake mua"amalantarki cikin nuna qauna tausayi da girmamawa,don Allah qannena yayyena da sa'annina YAMMATA ku farka,KU FARKA,KU DAINA KORE MAZAJEN AURENKU SABODA HANGE DA NEMAN WANDA YA FISHI,Allah ya shiga lamuran rayuwarmu gaba daya πŸ‘πŸ½πŸ‘πŸ½

*HUGUMA*πŸ‘‘
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 17



Tana tsaka da wannan nazarin akayi sallama qofar soron,isma'il ya miqe a nutse ya karbo saqon ya dawo ya zauna yana ajjiyewa gabanta

"Kada ki damu,amma kije kiyi nazari,saidai am sorry to say....koda baki shirya aure ba in sha Allah zanyi aure a wannan lokacin,don haka kiyi tunani a hankali kina da sati daya cif,duk abinda kikaji zuciyarki bata kwanta da shi ba kada ki yanke shi,ki zabi abinda kikaji kinfi aminta dashi,zaman aure zamuyi wanda muke saka ran mutu ka raba,bawai aje a dawo ba" da wadan nan maganganun yayi mata sallama ta dauki ledar takeaway dinta ta wuce gida.

Da farko jikinta yayi sanyi sosai,har ma ta dinga juya lamarin,wata salihar zuciya daga qirjinta tana gaya mata

"Me zaki jira?,kin cika shekara talatin fa kenan wasila,ki yarda da isma'il kiyi aurenki ki huta,tunda bazai barki da yunwa ko a wulaqance ba" zuciyar dake da gamayya da shedan na tuna mata

"Shi kuma faisal ya zakiyi dashi?,idan kika amincewa isma'il shi kuma faisal yana da niyyar aikowa kinga kin yiwa kanki asara,yanasonki Faisal yanason kuyi aure,akwai jifan da ake miki ne ansan da arziqi a jikinsa ba'a so ki shiga gidan hutu shi yasa,amma da tuni kin jima da zama matarsa" kai ta jinjina tafi yarda da shawara ta biyu. Su masu jifan nata qila an duba musu sunga wahala zatasha a gidan isma'il shi yasa basu maida hankali su rabasu ba,sun hango arziqi jikin faisal wannan dalilinne yasa sukafi maida hankali a kansa.

"Bari kiga" ta fada ita kadai tana janyo wayarta,wata number dake dauke da sunan MALAM ta lalubo ta dannan masa kira.

Sai data kusa katsewa ya daga,suka gaisa da kakkaurar muryarsa sannan ta fara masa bayani

"Isma'il ya matsa malam,yanzu haka zancen turowa yakeyi,ni kuma tun kafin ma ka shaidamin babu alkhairi tsakanina da shi nafison faisal gaskiya,don Allah malam a taimaka asa faisal ya turo ko yayi maganar kafin isma'il ya dawo" kai ya jinjina,yanzun haka a buqace yake da kudi

"To ai shi kansa faisal din ba maganar aure a ransa kwata kwata,saidai zamu bullo masa ta bayan gida,bazai wuce wata guda ba tare da ya aiko din ba"

"To na gode sosai malam Allah ya saka maka da alkhairi"

"Ameen........yanzuuuu ......akwai turare da zamu siya,daga Syria ake kawo wannan turaren,sai wasu duwatsu daga misra a cikin ruwa ake samo ire irensu"

"Kamar nawa kenan ane buqata malam?" Dan shuru yayi sannan yace

"To,ai wasila ke abar tausayi ce,dole me imani ya tausaya miki saboda irin jifa dake jikinki Allah yayi yawa dashi,ki bayar da dubu ashirin,abinda bai cika ba na cika miki cikin aljihu na" Taji dadi sosai,godiya ta dinga yi masa kamar ta durqusa,sukayi sallama ta kashe wayar.

Ranta fes ta soma cin takeaway dinta,a yanzu tunaninta inda zata hada kudinne kawai,don ba komai takeson gayawa umma ba,wani abun sai ta doje akai,tafison kome zatayi tayi abinta kai tsaye ba'a kawo mata cikas ba.

Wayarta ta jawo sai tayi tunanin tayi kiran faisal(sau tari dama wasu 'yammatan suna qarewa ne da kiransu,kafin ya kirasu sau daya sun kira biyar). Duka yau basuyi waya da shi ba,amma takan bashi uzurin cewa harkokinsa ne sukayi masa yawa.

Har ta katse bai daga ba,sai data qara kira bugu biyu ya dauka. Ranta fes ta shagwabe masa,shima ya biye mata suka bata kusan awa biyu suna waya,don leqowar umma biyu amma bata gama wayar ba.

Suna tsaka da wayar dai dai lokacin da tasan yafison hira da ita ta katse wayar,sai bayan minti kusan biyu ta kunna ta kirashi

"Nayita trying kuma naji a kashe"

"Uhmmm wallahi,qawata ce ta shigo,bikinta ya kusa,ta kawomin anko amma nikam gaskiya na gaji da yin ankonnan,nima burina yanzu ace yau nice na fitar da nawa ankon kamar kowa?"

"Nawa ne kudin ankon?" Ya fada yana share maganarta ta biyu

"Dawainiya baby?"

"No,kada ki damu abinda kakeso kake wahaltawa ai ko"

"Gaskiya ne" ta fada da wata siriryar shu'umar muryarta cikin son sake shigar da kanta zuciyarsa

"Lace ne 20k,sai atamfa 10k"

"Alright,to ba damuwa,zan saka miki 40k harda kudin dinki"

"Wow.....Allah ya biya, godiya nake" a cikin ranta tana jin ta samu kudin da zata biya malam harda riba.

Wannan abun da ya faru a ranta sai ta sake jin me zatayi da isma'il?,mutumin da qarshen kyautar bajintar da zaiyi mata itace 10k,itama sai bisa abu me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login