Showing 3001 words to 6000 words out of 66328 words
Chapter 2 - Kurman Baki Hausa Novel Complete
yafawa wajen,ta sake miqa hannu ta tara ta yafawa gurin ba tare da ta sanya hannu ta wanke ba,ta miqe tana qoqarin maida pant dinta da uban danshin dake maqale a sumar dake mararta damqam,wadda a qalla kusan watanni biyu kenan cikin ta uku ba tare da ta samu aski ba.
Sai a sannan ta lura da pant dinta da ya canza launi saboda kalolin magungunan matsi da taketa inserting tun yammacin jiya. Tsaki taja,ta fasa sakawa,sai ta zareshi ta jefa cikin bathtub dinta wanda ke dauke da kalolin pants da Braziers dinta da bata samu wankewa ba,ta tsartar da yawun bakinta dalilin rashin brush tana sakayo qofar toilet din cikin hanzari saboda kiran da taji ya shigo wayarta tana gudun kada ya tsinke bata daga ba.
LIKITAR AURE sunan da ya fito kenan baro baro,wani mahaukacin tsaki da yafi dukka na baya ta saki
"Ku******mar uba,aikin banza" ta fadi a fili takaicinta yana kasheta,sai tayi rejecting kiran ta shiga watsapp abinta.
Shamsiyya ta fara lalubawa cikin jerin chats din dake dashboard dinta
"Yauwa" ta fada da sauri tana gyara zamanta saman gadon ganin ta sameta a online cikin sa'a. Sallama ta danna mata,yana shiga yayi ticking blue
"Ina kika shiga likita tana ta kiranki?" Saqon shamsiyya ya shigo. Ji zainab tayi ba zata iya jurewa typing ba,sai ta fara yi mata voice note
"Yo me zanyi mata?,bayan asara tana dab da fadamin?,nayi amfani da komai da tace amma babu abinda ya faru tsakanina da saleem,hasalima tunda ya dawo daga kasuwa ya shiga dakinsa ya ajjiye jakarsa ya dawo parlor ya hau wasa da 'yan biyu,haka kawai naga kamar ya shigo ne da wani irin fushi,ana kiran sallahr magariba kuma tunda ya fita sallah bai dawo ba sai bayan isha'i,da na kawo abinci ma baici ba ya shige wanka abinsa,da ya fito kuma yace bayajin dadin jikinsa ne gaba daya,na juya yaqi cin komai,da na gaji nima sai na qyaleshi don ba wannan ne yafi damuna ba,kinsan wani rainin wayo?,na tafi naje na kwantar dasu hassana kafin na dawo sai zuwa nayi na tarar yayi bacci?,ya duqunqune a blanket,juyin duniya ya tashi ina da buqata wallahi ko juyowa baiyi ba". Zaman jiran shamsiyya ta gama ji ta bata amsa sai taga yayi mata tsaho,don haka ta fice daga inbox dinta ta fara duba charts.
Saqon wani group dinsu da take masifar so mai suna MATAN NI'IMA shi yafi kowanne shigowa, group din yana matuqar sakata nishadi don tana qaruwa dashi sosai ta fannin magungunan mata,musamamman na turawa,wanda ita kanta ta sissiya wasu tayi amfani dasu,hakanan a boye ta siyawa saleem ta sassaka masa abun sha ba tare da ya sani ba. Tayi hakanne saboda sanin da tayi masa,baya qaunar ire iren wadan nan magungunan sam,duk abinda za'a ce masa magani ne na irin wannan fannin to baya ciki,ita kuma yadda matan keta comment a kansa ya sakata sha'awar gwada amfani dashi.
Saqonnin ta fara bi a hankali,tun tana jin hirar na gundurarta kamar ta fice har ta soma daukan hankalinta
_Maman mahbuba ya daren?,ya kikaji aikin maganin?_
_a fito mata a bamu feedback mana_
_hmmma ai abun ba'a magana,wadda bata gwada ba gaskiya an sha da ita_
Ire iren maganganun da suka sanyata zaquwa kenan,ta soma bin saqonnin da sauri sauri har ta gano bakin zaren hirar.
Kai tsaye ta yiwa matar data fahimci a gurinta akaci kasuwar maganin magana ta private,sai taga ma jiranta ta karanta saqon bata lokaci ne,don haka ta sauka ta kirata direct call.
Tana dagawa taji ta ambaci sunanta,abinda ya dad'ad'awa zainab rai. Wato tayi shaharar da sunanta ya tambara a group din kenan har ake iya kama sunanta kai tsaye?.
Sama sama suka gaisa,zainab ta nema qari bayani akan magananin. Bayanin da matar tayi mata yasa taji ta gamsu d'ari bisa d'ari
"Nawa ne kudinsa?,idan na turo kuma zan samu a yau?"
"Eh akwai available,zaki samu,dubu ashirin da biyar,to amma tunda kece ansan saba da juna,ki tura ashirin,naki ne da na megidan duka zaku sha,na tabbatar saikin kawo wata ma". Nauyi taji kudin sunyi mata,saboda sosai tayi barnar kudin wajen likitar aure. Tun daga fallen zanin daurawa na magani data siya a wajenta da tarkacen kayan matsi a qalla ta barnatar da kusan dubu dari da talatin,abinda ya rage mata a hannun nata yanzun dubu ashirin ce,kuma zubin adashi takeso ta fara dashi,to amma hausawa sukace ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba,don haka tace
"Ba damuwa zan baki address,a kawomin sai na bada cash"
"Shikenan ba damuwa".
Ranta fes taji kamar an sauke mata wani nauyi da yahau saman zuciyarta. Sai ta koma ma ta kwanta tana sake bin feedback na matan da sukayi amfani da maganin.
Murmushi sosai ta dinga saki,tana jin cewa daren yau lallai zai zama na musamman,tana jin ma su hassana gurin ruqayya zata turasu,kuma ko taqi ko taso dole ta karbesu don ta samu ta sake sosai.
Wannan kwanciyar ta kaita har azahar bata sani ba tana group din ana maida yadda akayi tana biye dasu,har ji tayi ya qagu maganin ya iso. Bata ankara ba sai kiran sallar azahar din taji ana qwalawa. Ta rafka salati tana miqewa hadi da bin dakin da kallo.
Tun safe tana fama da qunci,ko brush batayi ba bare ta sakawa cikinta wani abu,bare kuma ayi batun gyara gidan da dakin saleem,ga yara suna kan hanya sun kusa tasowa a makaranta,bata dafa musu abincin da zasuci su wuce islamiyya ba.
A gaggauce ta sauko ta fara da kwashe tarkace kayan dake warwatse a qasan bedroom din,tana yi tana qiyasta rashin mutuncin da zata tsiyaya a yau idan maganin ta ya iso.
Bata jin zata dagawa ruqayya qafa ko diss,tabbas sai ta cusa mata kwatankwacin abinda take gani da ji a duk sanda take da saleem. Wani irin sabon riritawa kulawa tare da kuma tattali take gani a idanu da fuskarsa a duk sanda ya kwana sassan ruqayyan. Tayi imanin babu wani abu dake siyawa mace irin wannan soyayyar illa abu biyu. Kula da HQ da magungunan da zasu matseki gam ta yadda zai kiyayeki tare da dasawa zuciyarsa babu macen da zata kai darajarki ta wanann bangaren. Sai kuma hanya ta biyu da ba zata jurewa zirga zirgar wahalarta ba bayan ga wadda ta fita sauqi wato asiri. Imaninta yafi tafiya ga cewa asirinne,domin itadai bata taba ganun ruqayya ta siya wani abu waishi maganin mata ba,ko labari bata taba ji ba,to ta yaya macen dake zaune haka saket ba tare da kayan aiki ba zata samu irin wanann soyayya da kulawar indai ba ta hanyar tsubbu da asiri ba?.
Ko kafin ta gama gyara dakin ta gaji tubus,ta watsar da tsintsiyar ta zauna gefan gadon tana jan wani tsakin wanda bata gajiya da yinsa. Ba abinda ta tsana a duniya irin aiki,a yadda ta hasaso rayuwar aurenta ta kuma tsarata shine taci ta kwanta kawai,komai saidai a miqo mata. Saidai ga tarin rashin sa'a sai gashi tayi katari da mutumin da sam sam bashi da ra'ayin aje me aiki cikin gidansa.
"Duka duka ma me akayi?,yaran biyu rak?idan akwai buqatarta nan gaba sai a dauka din" wanann itace amsar da saleem ya bata lokacin da tazo masa da batun.
Cikin tarin qailula,zallar son jiki da rashin son morawa kai komai sai gashi takai gefin la'asar bata gama komai ba. A dai dai lokacin driver ya dawo da yara daga makaranta,suka shigo fici fici dasu kamar kullum cikin nau'in jigatuwar da duk dalibi yake tsintsar kansa.
*HUGUMA*👑
https://chat.whatsapp.com/HeRo2w8C8gdG0Et1lqafjk
*_KURMAN BAƘI_*
*H U G U M A*
Page 03
Yara biyu ne a gaba suka fara shigowa,mace da namiji wanda dukkansu ba zasu wuce shekara goma da hudu ba. Macen itace babba sai namijin. Farare ne sosai kamar yadda yanayin fatar mahaifiyarsu zainab take. Daga bayansu sauran yaran maza biyu suka shigo. 'Yan biyu ne identical masu kama da juna sosai. Rirriqe labulen sukeyi suna shigowa a hankali da alama babu sakewa sam a tattare dasu. Tunda sukaga qofar maman nasu a kulle hankalinsu ya gaza kwanciya,duk da qarancin shekarunsu amma dai dai da rana daya basa qaunar su shigo gidan su samu mahaifiyarsu bata nan.
Zainab daketa fadin tashin kintsa falon ta watsa musu harara
"Shegu masu shegen baqin hali,duka duka shekarunsu basu wuce a qirga da yatsu ba amma sun iya nunqufurci da shegen gulma da sanabe irin na uwarsu" ta fadi idanunta a kansu kamar zasu fado,har yanzu tana jin dacin haifar yaran a dai dai lokacin da take ganin cewa itace da gida,a sanda dukka lissafinta ya gama bata ta gama mallakar saleem mahaifiyarsa da kuma danginsa,ta haifa masa abinda ya jima yana mararin samu wato 'YA'YA,sai gashi a dare daya ruqayyan ta gigitata da wata irin ba zata da bata shirya mata ba.
"Don uwarku ku koma idan ba zaku shigo ba" ta fada cikin daka tsawa tana jan tsaki. Tsam al_hussain ya riqe hannun al_hassan yana mele baki alamun zagin data masa ya taba ransa. Yafi al_hassan zuciya sosai,sai kawai ya figi hannun dan uwansa suka fice zuwa babban parlor din da ya hade qofofin falukan da suka samarwa da kowaccensu sassanta.
"Kinga shegen yaro?" Zainab ta fada cikin mamaki tana binsu da kallo. Tun yanzun yaran suke da wani irin hankali da saurin fahimtar abu,tana tunanin gaba zaiyi wuya basu zame mata tarnaqi ko alaqaqai ba.
"Zakaci ubanka zanga ka dawominne" ta fada tana daga murya don ta tabbatar suna falon a zaune.
"Mama yunwa nakeji fa gaskiya" babbar diyarta haneefa ta fada tana yamutsa fuska
"Iyalan ci da baku da aiki sai cin abinci,yo nima banci ba tun safe,ki bude lunch box dinki ki cinye sauran abinda ke ciki kafin na gama kintsa gidan na dora" ta fada tana ci gaba da hidimar gabanta. Ita a yanzu ma bata abinci take ba,maganinta kawai take kasa kunne taji me delivery yace gashi ta afa ta tabbatar ya isa cikinta. Yunwa ba yau ta saba zama da ita ba.
"Mama dumamen abincin jiya ne fa dama kika zuba mana,kuma wallahi tun kafin azahar shinkafar ta jiqe,sai abincinsu alhassan muka ci"
"Kut" zainab din ta fadi tana dakatawa da abinda takeyi bayan ta waiwayo
"Uban waye yace kuci musu abinci?,ban hanaku ba?" Ta fada cikin fushi tana kaiwa yarinyar mari. Tun ranar da yaran suka taba yabon girkin ruqayya a gabanta saleem ya tayasu taji ta tsani duk wani abinci da zai fito daga gurinta,duk kuwa da cewa girkin dare hadawa sukeyi,hasalima tare sukeci a babban falon gidan.
Zagi ta shiga dura mata abinda ya sanya yarinyar sakin kuka ta miqe tana zubda jakar makarantar da flask din a wajen tayi dakinsu da gudu. Hakan bai hana Zainab ci gaba da masifa ba kamar zata ari baki,da da hali dukan tsiya zata yiwa haneefa din a yau,saidai ta tabbatar muddin ta taba lafiyarta kamar a kunnen mahaifinta,abinda kuma tasan bazai haifar mata da d'a me ido ba,tana son yau ta gyara wasanta ba zata bar wani abu na rashin jin dadi ya wargaza mata shirinta ba,dole yau tayi kaffa kaffa da komai.
Dan qara speed na motar tayi hankalinta yana kan lokaci. Tasan tabbas zuwa yanzu yaran sun dawo,bataso hakan ba amma uzurin da ya riqeta dole ta gama kafin ta taho.
Shigowar motar tata yaja hankalin yaran, suka watsar da abinda sukeyi suka rufo da gudu gurinta. Tana qoqarin bude murfin motar amma sun hanata saboda yadda sukayi tsaye a bakin qofar suna murnar ganinta. Murmushi ta saki tana dubansu zuciyarta na karyewa. 'yan awanni kadan tayi bata gidan,amma dukka hankalinsu ya tashi,ina ace yau mutuwa tayi ta barsu?. Cikin taqaitattun mintunan da ta qara bata nan yaran har sun fara fita a kamanninsu,sunyi wasa a farfajiyar gidan sun vodeyAllah,suit din uniform din tasu sun cikata da qasa da ruwa abinsu,kada ma kayan alhussain yaji labari.
"Yanzu don Allah ba zakuji kunya ba ifti ta ganku a haka?,ummm?" Ta fadi tana dan duban yarinyar tata dake daure cikin wata jaka da aka maqale a seat din motar. Jikkunansu suka kalla kafin su qyalqyale da dariya. Alhassan yace
"Momy ni jikina bai baci ba sosai,ni zan dauketa"
"Allah momy na rigashi zuwa" alhussain ya fada yana qoqarin tureshi.
"Duk ba wanda zan bawa 'yata,me yasa baku shiga gurin maman haneefa kun zauna ba?" Ruqayya tayi musu tambayar tana fidda jakarta tare da saka iftihal a kafadarta
"Ba zaginmu tayi ba ta kuma yi mana tsawa" alhussain ya fada yana tura baki gaba. Waiwayawa tayi ta kalli yaron,har cikin ranta taji ba dadi,hakan yana nufin ko babu ranta ba zata iya riqe yaran ba kenan,ta kuma san irin salon zaginta,bata iya qanqanin zagi ba,fadan kullum sai sunyishi da saleem kenan,domin yace bazai lamunci zagin da take kuntumawa ba,ba zata lalata masa yara ba.
"Aiki take kuka dameta,muje ciki ku cire uniform kuci abinci" sai ta saka yaran a gaba suka wuce cikin gidan tana biye dasu a baya da jakunkunansu.
Bata samu nutsuwa ba sam sai da maganin ya iso,ta zauna ta farkeshi ta duba sannan tayi amfani dashi kamar yadda matar ta gaya mata. Sakin wani murmushi tayi tana saka dukkan lurarta ga jikinta,ta fara lissafe lissafen irin canje canjen da akace ta sanya ran zata ji
"Hmmmm,yau da sabga,ruqayya yau zaki qunshi baqincikin da sai ya kusa ajalinki" ta fada a sarari tana dariya. Tabbas yau zata aiwatar da komai ne da gayya saboda ta qona ranta yadda ya kamata,ta fanshe tarin baqinciki da bacin ran da take qunsa mata kowacce safiya da irin baqin kinibibinta.
Duk yadda taso taga ta kammala komai ko don ta faranta ran saleem din yadda yasan yafison yazo ya sameta amma ta kasa,jiki dukka da zuciyarta a haka suke,ta riga data saba,zallar son jiki kasala da rashin son yin aiki sun zame mata jiki,sai data bata lokacin da girkin ma bata dorashi ba sai la'asar liqis.
Yadda ta kacame da aiki a kitchen din ya Sanya nylon din rigar baccin dake jikinta ta soma damunta,ga zafin kitchen din ga kuma rashin yin wanka. Gefe taja tana jan tsaki
"Ni shi yasa duk ababen nan basu dameni ba,me za'a wani yi da rigar bacci" zareta tayi ta azata jikin qofar kitchen din,ta ja zanin jikinta tayi daurin qirji dashi taci gaba da juya miyarta wadda keta kamawa saboda yadda ta raba hankalinta gida biyu,rabi yana ga girkin rabi kuma yana ga wayarta da taketa bin charts na group dinsu dake sake qara mata qwarin gwiwa tare da samun tabbacin yau din daren zai kasance na musamman ne.
A nutse ya isa da motarsa harabar da ya saba ajjiyeta,ya daidaita tsaiwarta sannan ya kashe motar yana furzar da iska daga bakinsa a mugun gajiye.
Yau tunda ya fita bai zauna ba,ya gaji liqis yadda ya kamata,sunata zirga zirga tsakanin warehouse dinsu da shagunansa,ko abinci bai samu yaci ba,yunwa ce a kwance a cikinsa.
Hannun rigarsa ya tattare yana duba lokaci,ana dab da kiran sallar magariba ne,duka duka bazai wuce mintuna goma sha biyar ba. Hannu ya sanya ya bude motar ya fito hannunsa dauke da ledoji,qarar rufe murfin motar yaja hankalin zainab dake kitchen,ta ajjiye ludayin miyarta da sassarfa ta fito daga kitchen din ta isa window din da yakw sadata da kowanne kallo da ya danganci harabar gidan.
Kamar zuciyarta zata fado sanda yake nufar sashen ruqayya,abinda tafi tsana kenan a rayuwarta,duk kuwa da cewa ita dinma hakan yake musu,baya taba shallake sashenta idan ya shigo sai ya fara dubata sanann ya wuce wajen ruqayyan yadda al'adarsa take kenan duk sanda ya kasance kece da girki. A nutse ta sauke idanunta ga ledar hannunsa,tanaso tasan meye a ciki?,saidai duk iya qwaqwarta ta kasa tantancewa saboda ledar baqace me duhu babba da qarama.
Sakin labulen tayi yana jan tsaki,ta waiwayo ga haneefa wadda suketa wasan guje guje,wasan guje gujen da ya qarasa hargitsa gyaran 'yar burum burum din da ta yiwa falon. Tsawa ta doka mata sannan ta narka mata ashar
"Ga babanku can yayi sashensu alhassan,bishi ki ga me ya shigo da shi a baqar ledar hannunsa" yarinyar kamar ba zataje ba,sai kuma ta zumbura baki tayi gaba
"Zakici ubanki da shegen rashin son aike"