Showing 63001 words to 66000 words out of 66328 words

Chapter 22 - Kurman Baki Hausa Novel Complete

HQ din da ya riga ya bude sosai tunda an sake yagashi an dinke kuma ba'a dinke dai dai ba" kaman ta sake dora hannu a kai ta zunduma ihu dajin bayanan nurse din,yanzu ita daje beman tsukewa saboda lalacewa saita bude budewar da tafi ta baya yawa da muni?. Bai sake cewa komai ba kaman yadda ruqayya ta buga tagumi jikinta a mugun sanyaye,tamkar itace cikin matsalar, zallar mamakin zainab ne yake sake mamayeta,yanzun ita saboda kishiya da miji harta aminta ta cutar da kanta har haka?,yanzun gashi cikin su uku waye a ciki?.

Duk zaman bin layi zuwa shiga wajen dr nur da sukayi saleem baice ta tafas ba,duk da irin ciwo da radadin da zuciyarsa ke masa wannan wanne irin tonon silili ne Zainab din ta jawo masa,har dinki taje akayi mata?,ta bankada al'aurarta ba tare da saninsa ba?,macece namiji ne waye yayi mata oho?.

Tun daga shigarsu tsantsami ya kama dr nur kasancewarta me tsananin tsafta,saidai salon iya aiki yasa ta jure illa facemask data saka.

Kai kawai take jinjinawa bayan ta gama gwaje gwajen da suka dauki lokuta sunayinsu

"Kin samu cutar CANCER ciwon daji na bakin mahaifa wato CERVICAL CANCER"

"CANCER kums likita?!" Zainab din ta fada a mugun gigice,gigicewar da ba ita kadai tayita ba hatta da ruqayya sakamakon ya girgizata,bare saleem da ya dasu a gurin bakinsa ya gaza furta komai.

Kuka da tumami Zainab din ta farayi cikin matuqar razani da firgita, duk yadda dr nur taso tasha kanta tayi shuru amma ta qiya,har saida bakin saleem ya budu ya daka mata tsawa.

"Ki tashi ki mata bayanin dame dame kika cusawa gurin ya zama haka?"

"Tana inserting wani abune?" Dr nur ta tambaya tana duban saleem cikin ranta tana hango banbanci qarara tsakaninsa da zainab din qasan ranta tana fadin

"Aure me hade hade" don ko kusa ko alama babu daidaituwar aji tsakaninsa da ita.

"Zakiji a bakinta,inajin har fitsarin jaki sawa takeyi" ya fada yana miqewa don ya tabbatar Allah ne kadai yasan me dame Zainab din tayi. Yasha ganinta yasha kuma hanata tare da gargadinta sau babu adadi amma bataji ba.

"Yallabai haquri zakayi ka zauna mu fuskanci matsalar nan a tare" Dr nur da itama ta fuskanci asalin fusata daga wajensa ta fada

"Na gama da matsalarta ni,na gama fuskantar matsalarta,yanzun matsalarta tatace,Allah ya bada mafita" galala zainab din tayi tana jin asalin tashin hankali yanzu yana ratsata. Kadadai ace iqirarin da yasha yi mata wanda ita bata daukeshi a bakin komai ba a sannan a yanzu ne wa'adinsa zai cika?.

"Don girman manzan Allah kayi haquri ka dawo ka zauna", ruqayya da tayi tsaye a bayansa ta fada a tausashe. Ta hadashi da babban bango kuma dan gatan Allah wanda bazai iya tsallakewa ya qetara sunansa ba,don haka ya dawo yana shirin zama,ita kuma tayi qofa zata fice don ta gaji da jin wannan tashin hankalin

"Ke kika dawo dani dole ki zauna kema" saleem din ya fada a kausashe. Juyowa tayi tana kallonsa

"Ita meye nata a ciki dama?,banda ma son a tozartaka ya za'a yi kishiya ta dinga jin sirrin ciwonka?" Zainab ta fada cikin muryar kuka. Wani kallon banza saleem ya watsa mata

"Ke kikaso,ita aji nata mana" . Kasa dawowa ta zauna ruqayya tayi,tana daga tsaye jingine a bango kanta a qasa cikin tashin hankali. Tiryan tiryan zainab ta rattabo bayani da bakinta,abinda ya tashi hankalin kowa a wajen,ruqayya tsigar jikinta ta dinga tashi sai ta bude qofar kawai ta qarasa ficewa ba tare data jira umarnin saleem ba.

Motarsa ta koma ta zauna tana maida numfashi,abu goma da ashirin,ga tashin hankali ga tashin zuciya,saita kwantar da kujera tayi kwance kawai tana maida numfashi.

Kusan awanni biyu cur sannan taji shigowar saleem din motar,har tayi bacci ta farka,ta miqe ta zauna tana duban fuskarsa da babu alamun walwala a tattare dashi. Kiran waya yakeyi don haka batace dashi komai ba har aka daga,sai a sannan ta fahimci yayan zainab yakewa magana yana shaida musu tana asibiti an bata gado,a taho dame kula da ita

"Subhanallahi me ya sameta"

"Zatayi muku bayani idan kukazo" abinda yace dashi kenan. Baice komai da ita ba bayan ya gama ya tashi motar ne kawai suka wuce gida. Itama sai taja bakinta tayi shuru.

Ranar gaba daya sukuku ya yita,damuwa ce fal ransa da bacin rai zallah,da akazo diban kayan zaman asibiti na zainab din ya sanya haneefa ta debo kayansu ita da khalil. Yarinyar nata murna ta debo din,saidai duk cikin kayan babu wani na arziqi,sai baya ruqayya tasa aka kaisu aka sake wankewasu fes.

Bata sake masa magana ba sai washegari da safe da zata shiga kitchen hada musu breakfast

"Yaushe zaka fita asibitin zan hada musu da abinci"

"Ba yanzu ba,idan kina da me zuwa ki bayar yakai" ta danyi mamaki don ba haka yakeyi ba duk sanda wata ta kwanta asibiti ita ko zainab din

"Ba damuwa,zan samu na kammala da wuri sai na fita nakai"

"Ban aikeki ba" ya fada, koda ta dakata tana neman ba'asi blanket yaja ya lullube kansa abinsa ya juya mata baya.

Kwana uku tayi tana aike musu da abinci,a rana ta ukun sai bayan qarfe goma na dare ya shigo gida. Tana zaune batayi bacci ba don ta kasa,saboda ba sabonsa bane yin dare a waje,ta kuma kikkirashi amma bata sameshi ba.

Tunda tayi masa sannu da zuwa ta tabbatar akwai matsala babba tattare dashi. Har zuwa sanda sukazo kwanciya ta dubeshi

"Gobe inaso naje na gano jikin zainab in sha Allah "

"Ba zaki ba" ya fada a taqaice yana gyara pillow dinsa. Ranta tadan bata kadan

"Me yasa kake haka ne?,ko yaran aika bari su ganta ko?"

"Ce miki akayi ana ganinta?,ko salon idan kinje kin dawo ki ishi mutane da koke koke?" Ya fada yana tuna yadda likitan dake kan dubata a yanzun yayi masa bayanin irin illar da ciwon yayiwa jikinta da sassan mahaifarta,ransa yana baci kuma idan ya tuna yadda sam bata rusuna ba saima zagin ruqayya da takeyi duk da alkhairinta gareta da yadda ta hana kanta zaune kullum cikin girkin safe rana da dare.

"Karki sakemin wannan maganar,hasalima mamanta ta nema mata saki tace sakacina yasa ta shiga halin data shiga din na kuma bata sakinta,na biya kudin abinci da jinyarta gaba daya,so ba wani abu da ya rage kuma" idanu sosai ruqayya ta fiddo gabanta yana tsananta faduwa

"Sakifa kace saleem,matar tana saman gadon jinya har zaka yanka mata takardar saki?" Ta qarasa fada muryarta na rawa,cike da tsoron zargin da mutane zasuyi a kanta

"Ji nan ruqayya" shima ya kama sunanta kai tsaye sannan ya zauna yana dubanta sosai

"Me daki shi yasan inda yake masa yoyo,duk da ke matatace kuma gida daya muke akwai abinda bai kamata ki sani ba ba kuma zaki sani ba,kuma koda mamanta bata nema mata saki ba dama xamana da ita ya qare. Kinsan sau nawa mukayi case din magunguna da ita?,a gaban mamanta a gaban mamana?,mamanta ita ke goya mata bayan cewa dole ne tayi gyara saboda ke!,maganata ta qarshe tsakanina da ita kafin na tafi saudiyya akan maganin ne,ni da ita mukayi yarjejeniya duk randa na sake ganin wani abun daya danganci wannan tarkacen nata ko meye ya biyo baya kada tayi kuka da kowa sai kanta,ke ina hanaki gyara!,ban taba hanaki ba,saboda me?,saboda nasan duk abinda zaki sanyawa cikinki ko ki sakawa qasanki bazai taba lafiyarki ba,bazai taba tawa lafiyar ba,kinsan sau nawa tarkacen maganin da zainab takeyin amfani da shi ya cutar dani?,kinsan banda ina da sauran numfashi a gaba da tuni zuciyata ta samu matsala?,da tuni na mutu ba zancena akeyi ba saboda abubuwan da take sakamin a abinci da cikin abun shana?,wani abun yakanyi sati yana tabani,kina lura da wasu lokutan sai girkinki yazo ya fita ban nemi komai daga wajenki ba?,kinsan dalili?,ta sakamin wani abu a abincina ko a jikinta da nima ya tabani kuma banason na shafa miki wani matsalar da idan nayi hakan tamkar zalunci ne a wajenki,shekara nawa ana haka?,sauran dabi'unta ke zaki bawa wani labari,duk abinda ya kamata nayi don samun daidaito nayi amma ya tashi a banza,banaso banaso ki sake cewa wani abu akan wannan"

"Bazan sake cewa din ba,amma kuma idan bera nada sata daddawa ma da warinta" ta fadi masa kai tsaye tana dubansa

"Nace karki sake cewa komai,saikin sake fada din?" Yayi mata maganar ta sigar tambaya. Akwai maganganu da yawa a ranta da kuma rashin dacewar da take gani na sakin zainab tana asibiti,amma bacin ran da ta gani da kuma tsoron shigar shidan al'amarin saita janye qafafunta ta sauka qasa kawai.

*_ZAFAFAN DAI_*🫑🫑πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*πŸ₯΅β€β€πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯


*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*

πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯


_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_

*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*

*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*

*TSUTSAR NAMA Billynabdul*

*GUDUN K'ADDARA Huguma*

*AMEENATU Mamuhghee*


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYARπŸ’–πŸ’―πŸ’–... ZAFAFA BIYAR NAKU NEπŸ’ƒ_

*_KURMAN BAK'I_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 31


*_YOU ARE ALL INVITED TO MY BUSINESS GROUP_*

*MASU SARI DA MASU SIYAN D'AI D'AI DUK KUZO MU JONE,SIYAYYA CIKIN AMINCI DA KWANCIYAR RAI*

https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz



Idanunta cike fal da wasu irin qwalla masu zafi take juya takardar sakin dake hannunta. Wani irin zafi radadi da bacin rai ne ke kai kawo a ranta a duk sanda ta kalli takardar,duk da kuwa mamanta ta bata yaqinin cewa ita ta qarfafa ya saketan

"Wa ya gaya miki kana zafafawa akan miji tare da nuna masa sai dashi zaka rayu?,gwara ki qwaci 'yancinki yasan cewa ba dole sai dashi ba"

"Tabbas na yadda da maganar bahaushe da yake cewa namiji dan kunama,namiji buhun qaya,namiji TABARMAR QASHI" ta fadi maganar a sarari.

Gyara zama raliya da tazo dubata take kuma zaune a gefanta tayi,jiki da gwiwarta dukka a sage,ciwon da ya sarqafi zainab din ba qaramin ciwo bane,kamar yadda ba da wasa yake gigita rayuwarta da lafiyarta ba,tayi wani irin bushewa ta qanjame,saboda lamarin cutar cancer ba qaramin ciwo bane me qanqanin illa

"Ko meye zaki fada akan namiji bazan musa miki ba,tunda gashi qiri qiri zahiri mun gani ni dake,banda butulci irin na da namiji?,kome kikayi kuma ko me kika zama ai ta silarshi ce,ta dalilinsa ne,inda baki aurensa ai da ba zaki saka komai a jikinki ba,komai don ki burgeshi kikayi ko" raliya ta fada cikin tsananin jin zafi itama kafin ta sake dorawa

"Ni wallahi na sare da lamarin namiji,na daina wahalar da kaina sabodashi,tunda duk fadi tashin maganina wai bai hana bawan Allahn nan hango wata macen ba,har yana shirin miqa sadaki ban sani ba......".

Sallamar safeena ita ta saka sauran maganar katsewa,kusan taji duk abinda suke cewa saboda ta tsaya daga famfon tsakar gidan daura alwala.

"Kuyi haquri ba labe nayi muku ba,na tsaya daura alwala naji duk abinda kuke fada" waiwayawa tayi ga raliya

"Daina gyara ai bai ganki ba anty raliya,keda za'a kawowa wata dole kiyi gyara ai,amma gyara na hankali,wanda duk ko meye zaki ci ko kisha ko kiyi seat bath kinsan ingancinsa ba gamje gamje ba......anty Zainab kiyi haquri,saki yana da ciwo akan kowacce mace,amma kusan fiye da rabin matsalolinki kece kika assasu, idan silar dirkar magani baji ba gani yaa saleem ya sakeki,to tabbas ba shine babban jigon faruwar hakan ba,akwai wani dalili behind it" idanu zainab ta zubawa safeena

"Kin dade kina wannan maganar safeena amma yau Ina da sha'awar saurarenki" kujera taja ta zauna gaban zainab

"Na taba gaya miki amma a sannan gani kike gaibu ne,maganin mata wani ciko ne da kwaskwarima a wajenmu kamar yadda ake mana bitar zaman aure duk wata a islamiyya,amma ba shine jigo ba,sam sam bashi zama jigo,zaki iya fin kishiyarki da shansa amma ta fiki a wajen miji saboda ta fiki tsafta,ta fiki iya tarairayar miji,ta fiki iya girki,ta fiki lafazi,ta fiki iya tarbar baqi,ta fiki kula da miji a daki......duk gayyar wannan abubuwan kina tunanin maganin mata kadai ya isa ya qunshesu?,sannan koda kin hada dukka wadannan abubuwan kina nufin har abada miji bazai bata miki rai ba?,ba zaku samu sabani ba?" Tambayar ta sanyayar da jikin zainab da raliya,kunya ta kamasu na yadda yarinyar qanwar bayansu ta fisu hangen nesa.

**********Da tsohon cikinta wanda ya shiga watannin haihuwa take takowa zuwa gaban wasila dake zaune a gefan gadon dakin. Sanye cikin laffayar amarci data lullube jikinta tsaf,sai fuskarta dake kallon ruqayyan har zuwa sanda ta miqa mata cup din data tsiyaya wani abu a gora

"Karbi ki shanye" ba musu tasa hannu ta karba. Sanda takai bakinta zaqin mazarqwaila da sauran tarkacen saiwoyin dahuwar tsumi masu dadin qamshi suka ziyarci hancinta.

Tsaf ta shanye ta miqa mata cup din tana cewa

"Wai dama kina amfani da irin kayayyakin nan?" Murmushi ruqayya ta saki tana ajjiye cup din

"Indai kinga bana amfani dasu to ina cikin irin wannan yanayin na samuwar juna biyu"

"Amma nayi mamaki" wasila ya fada tana dubanta. Wani murmushin ruqayya ta kuma saki

"Kema kina cikin sahun wadanda suke min kallon bana shan komai bana amfani da komai sai fruit?" Dariya tadan saki

"To ai iya abinda nake gani kenan"

"Daga yau na wanke miki tunaninki,har maganin mata ina siya,amma ba kowanne magani ba maganin da ya amsa sunansa,gumba,daka, tsumi zuma duka,amma kinsan a hannun wa?" Kai ta girgiza

"AMINTATTUN MATA wadanda nayi imanin sunsan kansu,sunsan me zasu bamu musha......sannu abu na biyu basai kin fito kina cika baki kina kurin ke kina Shan maganin mata ba,duk inda ake zancan maganin mata kina kan gaba,duk inda aka zauna saikin nunawa duniya ke ayuce,babu kalar maganin da baki sani ba,ba kuma wanda baki taba gwadawa ba,kai har na bature......kinsan duk matar dake amfani da magungunan mata na bature tausayi take bani?" Ruqayya ta qarshe fada a sanyaye

"Kaman yaya?"

"Har sai na tsaya miki bayani ma wasila?,zainab bata isheki izina ba,babu tabbacin ranar da zata koma mace kamar kowacce mace,ki gayamin da cushe cushe da shaye shaye me ya amfana mata?,shi kansa na gargajiyan ba'a ce ki dawwama a kansa ba,baci ba sha me kyau sai azabar kwankwadar magani......dukkan magani yana tasiri cikin jiki ne idan anacin abinci ana qoshi,ana tsafta ana kula da kai,wata matar ko shaving bai dameta ba amma tasan kowanne kalar magani,ta yaya zaki tara dakarun qazanta,mafakar infection sannan kice kinaso magani ya miki aiki?,ta yaya baki iya salo salo na kasancewa da miji a turaka ba,baki iya aika 'yan aike ba,baki da tsafta baki da kalami kuma kice maganin da kikai amfani zai yiwa miji tasiri?,qaryarki tasha qarya,ki gwada ki gani,ko ranar da bakisha magani ba muddin kinsan salo salo na faranta ran maigida,da kalolin auratayya zaki gigita miji fiye da gigitawar da magani zaiyi masa"

"Amma ke muguwa ce,wai duk wannan abun kike amfani dasu amma kikabar mutane na miki wani kallo na daban?" Murmushi ruqayya ta saki

"Meye amfanin macen da bata da aji wasila?,aiki zama me aji ko cikin 'yanuwanki mata bare gaban miji,uwa uba kuma ace kina da abokiyar zama hauka ba naki bane,dole ki kame kanki,sannan duk dadinki da miji karki fasa addu'ar zaman lafiya me dorewa a tsakaninku" dukka hannun ruqayya wasila takama ta riqe

"Alhamdulillah,nidai na rabauta da malama kuma 'yaruwa,lallai na yarda mukewa kanmu asarar tagomashin alkhairin ubangiji,bazan taba mantawa dake ba ruqayya,kinban shawara na riqe addu'a,gashi cikin wata shida Allah ya juyan lamarina,ya bani miji wanda yafi su zaid da faisal,lokaci daya Allah ya sakan soyayya da nutsuwa a raina,ya mantar dani komai,koda na samu Ahmad nayi baccin nutsuwa irin wanda ban taba yin irinsa ba,tunda a baya da na samu saurayi nice zaryar gurin malamai,a duban da alkhairi?,a duban me hali ne.....kinsan me?" Kai ruqayya ta girgiza tana dubanta,har cikin ranta tana jin dadi yana ratsata,ba ranar data fi mata wannan farinciki yau wasila ta saitu ta sanadinta

"Wallahi ban taba zuwa da buqatata sunce komai lafiya ba,kullum sai sun qirqiri abinda zasu gayan da zai daga min hankali,ya kuma sanyani gobe na dawo,ko na nemo kudi na bayar koda ban shirya haka ba,koda bani da komai,ke idan sukaji kwana biyu shuru ma wasu sukan kirani suce sunga taurarina suna canzawa,akwai alamun matsala,ashe qarya ne,ashe matsalata tsakanina da ubangiji na ne, ashe da gaske qananun laifukan da bawa yake rainawa suna iya zama silar nesantashi da cikar burikansa,ashe suna babbar matsalata,na hada Allah da wani wajen neman biyan buqatata" ta fada cikin rauni,raunin da ya sanya ruqayya dafa kanta

"Kici gaba da godewa Allah kici gaba da istigfari kuma......" Sallamar haneefa ta katsesu

"Shigo" ruwayya ta bata umarni tana jin dadin yadda ta soma canza yaran,duk yadda take tunanin zata sha wahala da dabi'unsu bata sha din ba,kuma ba komai bane tayi imanin addu'a data dinga yi tana neman taimakon Allah yayi riqo da hannayenta akan sha'anin yaran,sai gashi Alla ya mallaka mata su cikin watanni shida kacal komai yana zuwa mata a sauqi

"Gwaggwo ce tace idan kun gama ku fito ku ake jira"

"Gamu nan" ta bata amsa saita juya ta fice a nutse yarinyar kamar ba ita ba

"To amarya yau sai kwanan gidan Ahmad"

"Ina fatan na sameshi mafi alkhairin namiji fiye da yadda nake zato" ta fada da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login