Showing 36001 words to 39000 words out of 66328 words
Chapter 13 - Kurman Baki Hausa Novel Complete
amfani tare kuma da qwaqwqwaran dalili. Tun a daren ta yankewa kanta shawarar sallamar isma'il,indai aikin malam yayi kyau Faisal yana magana zatace a saka wata biyu ma,tasan daga umma har yayunta duk a shirye suke mijin dama kawai ake jira.
********Tun da tayi sallar asuba bata koma ba ta wuce kitchen don hada abincin yara da nasu da wanda za'a kaiwa zainab asibiti.
Shima saleem din da ya dawo daga masallaci zama yayi saman abun sallah yayi lazumi da karatu kamar yadda ya saba,bayan ya kammala bacci yadan daukeshi.
Koda zai farka ta kusa gama sallamarsu,don uniform kawai suke sakawa,ya shiga dakin ya iskesu kowa yana saka uniform dinsa. Alhassan ya gama iftee yake sakawa socks. Su alhassan suka fara gaidashi,ganin haka kuma sun hada ido da haneefa sai itama ta matso tana gaidashi.
Gefe ya koma yana karantar kowa. Tare ya canza musu uniform da komai na makaranta,amma idan kaga nasu haneefan zakayi tunanin sai da suka shekara biyu sannan aka dinka nasu alhassan,a haka ma kuma wai a wanke suke. Yana daya daga cikin abinda yasa daraja da martabar ruqayya ke qaruwa a idanunsa,sau tari idan zai canza musu abu takance yabar nasu alhassan din tunda nasu baiyi komai ba, musamman idan ta fuskanci baya da kudi sosai a hannunsa. Saidai karamcinta yakan sanya bayan wani lokaci itama yayi mata kyautar wani abun da yake kaman madadi na wannan sadaukarwar da tayi (hakan yana da kyau,bawai kice don an yiwa kishiyarki ba koda miji yadan shiga yanayi kema ko a mutu ko ayi rai sai an miki ba ke ba ruwanki,a'ah.....zuciya fa tanason me kyautata mata,sannan duk abinda ke faruwa namiji yana ankare,saidai ba kowane zai nuna ba amma a qasan zuciyarsa yasan da hakan. Bugu da qari ke kanki idanma ba zaki iya haqura ba,akwai hanyar da hankali kwance zaki fanshe kudin ba tare daya ankara ba,kema kuma baki rasa wannan darajar ba cikin wayo hikima da dabara).
Da dukka lunch box dinsu ta shigi,tuni haneefa ta biyewa khalil suka dinga doka tsalle bayan sun bude sunga meye a ciki. Rabon da suje da sabon girki har sun manta,sannan koda zasuje da shi dinma ina yaga dadi da haduwar wannan. Dubansa ya maida kanta ta duqa kadan daga tsaye tana gyarawa iftee hijabinta. Yadan lumshe ido,ko yaushe abinda zai sanya yaga kyanta cikin idanunsa takeyi. Rigar baccin jikinta me wani irin taushi da sulbi sabuwa ce, gray color me wani irin daukan idanu,tabi tattausar chocolate color din skin dinta ta kwanta sosai. Baya taba gajiya da kasancewa tare da ita,koda komai bazai hadasu ba ta jingina da jikinsa kadai yana shaqar daddadan qamshinta yana shafar soft skin nata kadai yana sakashi nishadi. Hular kanta tadan zame bata,gashinta duk da baikai tsahon na Zainab ba amma yafi na Zainab bashi sha'awa da qayatar dashi. Don kafin ta karba girki shekaran jiya taje aka wanke mata shi fes aka mata stretching don ba kasafai ta fiya ma sanya relaxer ba. Qamshin hair mist kawai yakeyi da hair oil.
"Zauna ki huta" ya fadi yana amsar agogon iftee da take shirin daura mata. Dagowa tayi sai suka hada ido,ta sakar masa murmushi ganin yadda yake faman qare mata kallo,har albarkatunta dake cikin riga idanunsa sai da sukakai kai
"Na gode" ta fada a tausashe taja baya tana zama. Dan murmushi ya saki,qamshin kanunfari na fita daga bakinta,sai zainab ta fado masa,ya tabbatar da itace tayi masa magana a irin wannan lokacin saidai ya kauda kai.
Da kansa ya kadasu farfajiyar gidan wajen driver,sai da ya tabbatar sun fice sannan ya dawo gidan da dan sassarfa,don ta riga data tsomoshi.
Tana qarasa gyaran falon ya sameta tsaye gaban tv. Ta bayanta ya tsaya ya rungumota jikinsa yana cewa
"Aiba wani aiki,aiki kuma ya qare,aji da dan hajiya malam saleem" qaramar dariya ta qwace mata,don ya tuna mata da tsohon sunan da ake kiransa shekarun baya
"Haba malam saleem,da safen nan?"
"To me zan jira?,bayan jiya qwalele kikayimin,wai ina isowa na tarar kinyi bacci ko tausayina ma bakiji" ya fadi yana shafa kafadarta har zuwa tsintsiyar hannunta. Tsigar jikinta ce ta zuba wannan ya sanyata noqe kafada
"Kuma kika saka wannan rigar don kawai daukan alhaki ko?" Ya sake fada yana juyo da ita tare da saka hannunsa ya fara balle bottom na rigar. Shigewa jikinsa tayi wannan ya bashi damar riqeta sosai suka wuce bedroom dinta dake a gyare fes don dama ba ciki suka kwana ba. Yanayin bedroom din ya sake qara masa shauqi qwarai da gaske,ya tsumu da turaren wuta qwarai,hakanan bata gajiya da yiwa bedsheets pillow case da blanket dinta kabbasa.
(Ko da magani sai da tsafta,ko da gyaran HQ saida gyaran tukunya,gyaran lafazin baki iya mu'amala da gyaran muhalli. Koda wadannan sai kina updating yanayin position na auratayyarku,ba ko yaushe ki shirgice ki jibge kaman kayan wanki ba,KINSAN AMFANIN DIRTY TALK?KINA MASA KO SAIDAI 'YAMMATA A WAJE SUYI MASA KINA ZAUNE?IDAN KIKA GA KUMA AN MASA KICE WANE YA ZAMA DAN ISKA MAZINACI?,BAYAN KEMA KIN TAKA RAWA?,TURQASHI.....nauyinku nakeji amma zan bincina muku kadan cikin littafin nan ta hanyar data kamata idan na samu chanceπ,ragowa kuma zai shige a littafin GUDUN ΖADDARA 2024 in sha in sha Allah.
*HUGUMA*π
*_KURMAN BAΖI_*β«β«β«
*HUGUMA*
PAGE 18
________________________________
https://chat.whatsapp.com/KHGP5vnV6yg6X9CpkQcf39
*_Assalamualaikum warahmatullah_*
*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*
*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*
____________________________
Ita ta fara ankara bayan komai ya kammala,ta tureshi tana sauka a gaggauce daga gadon
"Lokaci yana wucewa fa, za'a kaiwa maman haneefa breakfast" da kallo ya bita yana dan bata rai cikin sigar zolaya
"Shine kuma zaki tureni?"
"Yi haquri,kai dinne....."ta fadi tana qyalqyale masa da dariya sannan ta tura toilet din ta shige. Har ga Allah batasan abinda yasa yake sake maqale mata ba duk kwanan duniya,abu guda daya ta sani,duk da maganin gyara ingantattu da take hadawa kanta ko da ta siya gurin amintattun da tasan su waye?,zuciyarsu kuma a tsarkake take......bayan wadannan ta naqalci abubuwa masu yawa dake tafi da zuciyar saleem din. Ba ruwanta da abinda ke tafi da zukatan maza,ABINDA KE TAFIYAR DA ZUCIYAR SALEEM ne kawai a gabanta (maza sun banbanta,me yiwuwa abinda ke burge wancan ba shine abinda yake burge mijinki ba,ki karanci mijinki a karan kansa,saiki tsara yadda zaki tafi dashi).
Yana lalace a gurin yana tuna yadda ruqayyan ke bashi gamsuwa ta kowanne bangare tare da hasaso matsayin Zainab a duk lokaci irin wannan. Zai iya rantsuwa koda ya samu zainab din a matse,amma baya samun nutsuwa da gamsuwar da ruqayya ke bashi. Ruqayya kawai yake kaiwa ziyara ya samu hanyarta ba wani tarkace da zai dinga kawo masa tsaiko,ba dattu da qananun abubuwa bisa hanyar. Ruqayya kadai tasan salon kalaman dake sanyashi yaji ana tsinka masa tunani,kalaman da koda baiyi niyyar kasancewa da ita ba ya dawo babu shiri,kalaman da koda cikin kasuwa yake ta furta masa su zaiji bashi da sauran burin da ya wuce ya dawo gida ya kasance da ita,kalaman da zaijishi tamkar an daukeshi daga duniyar da yake ciki zuwa wata ta daban (sune dirty talk,a hausance ana kiransu da kalaman batsa,Yake budurwa?,kina yiwa saurayinki su koda shi zaki aura?,ββββ,hakan babban kuskure ne,MIJI shi kadai ake gayawa maganganu na batsa,zaki samu tarin lada me dinmbin yawa,nasan zakice kai?,a batsar za'a samu lada?. Eh tabbas!!!,muddin ga mijin da yake da igiyoyin aurenki ne guda uku,BANCE SAURAYI BA!β. BANCE WANDA KUKA KUSA KUYI AURE BA!!!βββ. Su wadannan yin wannan maganganun dasu ba abinda yake gadarwa face zallar zunubi da tarun fushin Allah,UWAYEN GIDA DA AMARE KU BIYONIππ½ππ½ππ½ππ½ππ½)
(Kowacce zuciya meson bin rudin shaidan ce da kuma son jin gard'in sabon Allah,dukkanmu abinda ke mana waigi ahine tairon Allah tare da tsoron haduwa da fushinsa a ranar gobe. Duk mace ko nakijij da kika basa sabon Allah,bawai don basa so bane,ko don ba zasu iya aikatawa ba,aah.....zallar tairon Allah ne yasa akewa zukata waigi daga aikata hakan. To a wannan zamanin wata fitina ta samemu,Allah S W T ya kawomu wani lalataccen zamanin da wai DIYA MACE BUDURWA DA AKA SANTA DA TSANANIN KUNYA DA KAMEWA, KUNYAR DA HAR AKE SUFFANTA KUNYAR MA'AIKI DA MISALIN KUNYAR BUDURWA saboda sanin tsananin kunya da kamun kai da duk wata 'ya mace budurwa ke da ita. Amma anzo zamanin da yarinya zata iya baje jikinta me tarin daraja tayi hoton tsiraicinta ta turawa wani,anzo zamanin da diya macen da magana ke mata wuya gaban d'a namijin da yake ba muharraminta ba amma yanzu zata iya baje baki suyi magana akan abubuwan da wata matar auren ko zaki saka kanta gabas ba zata iya fadinsu ga mijinta ba!!!. Idan kika ga chart dinsu da ita saikin kisa sumewa. Toke ladingo kina aikin me?,ke baki b'aro zantuka ba ga ladidi can tana ware miki tufka?,me take gaya masa da ke ba zaki murje kunyarki ki gaya masa ba,BAKI AKA FIKI?,KO IYA GAYAWA MIJI BATSA AKA FIKI?.
Ita zuciya tana da so da kwadayin sabon Allah duk kamewarta,saidai tuna girman Allah da girman azabarsa zai sanya ka dinga tanqwarata kana hanata abinda takeso,ME ZAI SA BA ZAKI TAIMKAKESHI BA?. Idan ma irin wamnan charts din ke burgeshi kuna zaune a falo kowa da wayarsa amma irin charts din kukeyi ke dashi. A bedroom(kuyi haqiri ta kama na gaya muku ne,saboda akwai mata da yawa da idan kikayi magana dasu akan wannan zasuce miki wallahi basusan ma anayi ba,su kunya sukeji da sauransu) irin wadannan kalaman batsan da zaki dinga fitowa baro baro kina gaya masa yana bala'in qarawa musu karsashi da kuzari me azabar yawa,sau da yawa wasu guraren cikin littafi(nawa bansan na wasu ba) zakuji nace ya rada mata wasu kalamai a kunnenta da suka bata kunya/ko ta qunshe kanta/kota gagara tsaiwa/ko ta rada masa wasu kalamai da suka sanyashi sakin murmushi/ko ya qanqameta da sauransu,dukka irin wadan nan kalamanne da bazaiyiwu ka fito ka rubutasu baro baro ba sabanin yadda wasu marubutan ke rubutasun gayansu(muna musu fata da addu'ar Allah ya ganar dasu gudun kada rubutunsu yayi waiwaye bayan dogon zamani ya tadda yara da jikokinsu ya zame musu qaiqayi koma kan masheqiya ya ruguza ginin tarbiyyar da suke gani sun bayar). Kunyar me zakiji ke da suke halal a bakinki tsakaninki da mijinki?,KIN GWAMMACE WATA TAYI MIKI SHUKAR DA BA TATA BA?. Gwara ki tare ko ina,ki tare komai. Da masu farautar sun fara gaya masa zaiga meye sabo a ciki?,ai wance tana gaya min su(kuma bayan kin gama gayan masan kin kunna abinki ga magani a gefe zaki saukeshi,wadancan kuwa idan abun yazo da sauqi basu da abinda zasu saukeshi dashi ta hanyar data dace kaman ke) zaiga meye sabo a ciki?(idan ke zazzafa ce ma kin fisu iya tsara kalaman masu tayar da hankali zaiga bashi da sauran lokacinsu). Mu cire kunya game da mazajenmu ta wannan fannin don Allah,tako wacce siga mu dinga updating muna daidaita kanmu da zamani,KOWANNE NAMIJI DAN DUNIYA NEπ(ba ina nufin duka 'yan iska bane a'ah,amma kowanne namiji yanason rayuwa yana son holewa duk taurin kansa duk miskilancinsa) kada kiga mijinki ustaz ne ko shuru shuru kice ai wane ba ruwansa wallahi KI GWADA KI GANI ZAKISHA MAMAKI MUSAMMAN A OTHER ROOM sanda al'amura suka fara tafiya(DON ALLAH KARKICE KIN TSUFA,KO MISKILI NE wallahi za'a yi babu ke,namiji baya tsufa shikam wallahil azeem,me yasa idan sun auro sa'annin jikokinsu sai kiga sun zama tabararru kuyita zaginsa?π,tana masa abinda ke kike ganin tsufa yazo ba zaki masa ba,bayan cikin bedroom dinnan daga ke saishi,ba'a taron assembly kuke ba....ku yafemin mommiesππ½ππ½π). Wanda bakinsu haya shuru kuma bance ki bawa kowa labari ba bayan kin gwada,kiyita blushing abinki idan assignment dinki ya samu nasaraπ,ki sake fidda wasu hanyoyin kuma a kanki,sai shawara da zaki iya baiwa ga kowacce mace ta tsaftataccen harshe ba tare da kin bankadawa kanki asiri ba. Allah ya dawwamar damu da mazajenmu,wadanda basu da aure ya basu ikon kame kansu ya hadasu da mazaje salihai nagartattu.ππ½ππ½
*Ruwan wanka me kyau ta hada ta fara wanka farko. Ta sake hada wani zata sakeyi,har ta dauko sabulunta yau kadai taji qamshinsa baiyi mata ba,ya tsaya mata a hanci da qirji,saita maida ta buda shower gel dinta ta matsa ta fara wanke jikinta. Ita dinma hakanan taji kamar wari wari takeyi mata,amma sai ta kauda kai cikin hanzari taci gaba da wankan tana Allah Allah ta gama.
*********Tana zaune saman gadon asibitin bayanta jingine da bango. Tun a daren jiya kawo yau idanunta da hanakalinta yana kan matar da suka kasance su biyu ne a dakin. Matar da qyar take takawa cikin takatsantsan duk sanda zata shiga bandaki,amma jikinta da bakinta sun nuna ras take,hakanan babu wani me jinyarta koda mutum daya ne,sai wasu nurses guda biyu dake shigowa suyi hira su fice. Yadda suke magana da nurses din yasa ta fahimci kamar qawayenta ne,kuma cikin maganar tasu ta fuskanci kamar dinki aka yiwa matar,saidai kuma dinki wanne iri?,shine abinda hankalinta yafi karkata akai kenan taketa da kwadayin jin dinkin meye akayi mata?.
Bata tashi fahimta ba saida nurse din tazo duba dinkin. Mamaki sosai ya kamata,iya saninta masu haihuwa akewa dinki a wannan wajen,to amma ita wannan ai sam bataga alamun ciki ko haihuwa tattare da ita ba. Hasalima batayi mata kama da matan aure ba,tafi mata kama da irin matannan 'yan duniya.
Bata gushe ba tana ci gaba bin qwwqwafin matar,sai ta lura manyan wayoyi ne a hannunta,hakanan manyan kudade take fiddawa tana kashewa ko a jikinta.
Tuni zuciyarta tayi nisa gurin son sanin wace matar?,wanne sirrine a tattare da ita?,tayita Allah Allah hajiyayye ta fita,don ta shirya tunkarar matar qila ta samu wani haske daga gareta.
Cikin sa'a hajiyayye kuwa ta fita dubiya can ward na yara,da sauri ta sauka a gadon tana daura dankwalinta ta zura slippers dinta ta tunkari gadon.
Tana kashingide tana danna iphone14 dinta hankali kwance,sai ta daga kai tana amsa sallamar zainab din tana binta da wani kallo.
"Sannu ya jiki?"
"Da sauqi" ta amsa ciki ciki tana ci gaba danna wayarta
"Ni sunana zainab,kuma nice nake jinya a dakinnan" ta fada tana murmushi
"Ayyah sannu" ta sake fada ciki ciki
*_KURMAN BAΖI_*β«β«β«
*HUGUMA*
PAGE 19
https://chat.whatsapp.com/KHGP5vnV6yg6X9CpkQcf39
*_Assalamualaikum warahmatullah_*
*_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_*
*_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_*
____________________________
Ta amsa ciki ciki tana maida hankalinta akan wayarta.
"Tambaya ce dani idan bazaki damu ba"
"Inajinki" ta fada ba tare data sake kallonta ba
"Don Allah kiyimin taimako ki gayamin meye amfanin wannan dinkin da akayi miki bayan ba haihuwa kikayi ba?" Ta qarasa fada cikin d'ari d'ari tana dubanta.
Wani kallon tara saura ta watsa mata,don itakam tunda ta zauna a gurin hamamin jikinta ya addabeta,batasan uwar da tasa ta kwaso jiki tazo zata dameta ba. Ta buda baki zatayi magana daya daga cikin qawayenta nurses suka shigo
"Jimmy,ya dai?,baquwa kikayi?" Maida kallonta kan nurse din tayi
"Ni bansan me yake damun mutane da shiga sha'anin da bai shafesu ba....."
"Wallahi ba haka bane,ina cikin kaidin kishiya ne,mafita nake nema don Allah ki taimaka ki gayamin" ta fada gabanta yana faduwa,kada taqi mata bayani wannan damar ta subuce mata.
"Malama me kikeso?" Nurse din ta fada cikin sakewar fuska
"Dinkin da aka yiwa qawarki nakeso ayimin bayani" murmushi ta saka suka hada ido da jimmy din,sai ta jawo kujera ta zauna tana fuskantar zainab
"Wannan dinki shine kankat a fannin matsi,babu wani magani da zaiyi miki abinda kikeso sama dashi,yanansake tsuke gaban mace ya maidata tamkar budurwa 'yar sha hudu" . Tuni jikin zainab ya dauki rawa,gaba daya hanakalinta ya daga,yanzun duk wayewarta a fannin matsi akwai wani abu da yayi saura wanda batasan da shi ba?,ashe duk wayewarta bata kai ba?,koda yake dai dama shi ilimi ance kogi ne.
"Don Allah malama ki taimakeni,nima inason ayimin,wallahi akwai matsala,na rasa hanyar da zan mallaki hankalin mijina,duk wani abu da mace zata yiwa namiji don ta mallakeshi ta hanyar shimfida nayi amma a banza,komai kyan magani nayi amfani da shi bana ganewa,idan kinga ya nuna jin dadinsa to sanda ya fita hayyacinsa ne bazai iya mallakar kansa ba wajen nunan jin dadin. Ni nafiso koda ba ranar girkina bane hankalinsa ya zamana yana tare dani,yana d'okin dawomin,wasu matan naga har satar kwana akeyi a kansu,amma ni koda wasa bai taba yi ba,tunda muka cinye amarci shikenan. Mijina ya auroni yana sona,ya auroni kuma don ya samu 'ya'ya dani,ni na fara haifa masa yara,amma