Showing 54001 words to 57000 words out of 66328 words
Chapter 19 - Kurman Baki Hausa Novel Complete
mata laifi. Dankwalinta da ya cire ta jawo tana daure kan nata dashi sannan ta fara saukowa daga saman gadon da nufin shiga bandaki
"Tsaya ni wucewa zanyi don n gama shiryawa,sufyanu yana waje yana jirana zamu dauko hajiya"
"Allah ya kiyaye sai ka dawo" ta fada har yanzu fuskarta ba walwala tanason ya gane cewa lallai yayi laifi
"Ki kula da yara ki kula da gida,banda fita barkatai don Allah,ko meye ya taso ga waya nan a shaidamin"
"To" ta fada bayan ta tura baki gaba. Har ya juya ya dakata
"Kinsan dai har yanzu akwai case dinki kan tarkacen magungunan nan........kuma baki manta da sharudan da na aza miki ba?........ kiyi qoqari ki kiyaye,ki zauna a hakanki ni bana buqatar wani gyara indai na magani ne,akwai gyararraki da yawa da ya kamata ayi amma ba wannan ba" ranta ya sake baci,tana matuqar jin haushin taji yace basai tayi amfani da komai ba hakan da take ya gamsar da shi,yo ita din goyon mahaukaciya ce da zata biyewa dadin bakin namiji?,tana da kishiyar irin ruqayya ai bataga ta bacci ba,zama bai ganta ba
"Sai na dawo" ya sake fada yana saka kanshi waje
"To" tace masa a cunkushe tana tura bandaki ta wuce ciki tana abunda tafi qwarewa akai wato qunaquni. Baiga alamun yaran sun tashi ba suma,yasha mata fadan tashinsu sallar asuba amma a banza,yo itana bata tashi ba sai anyi fama ina ga yaran.
Tashinsu yayi yasa sukayi alwala suka watstsake sannan yayi musu sallama ya fito.
A farfajiyar gidan ya samu ruqayya ita dasu alhassan,har iftee ma na maqale a gefe, dukansu sanye da jallabiyyar da ya siya musu ne saboda sallar asuba. Kusan tare yaran suka gaidashi,ya tsugunna gabansu yana amsawa hadi da jawo iftee dake maqale da qaramin hijabin dake nuna tare akayi sallar asubar da ita ya rungumeta yayi kissing nata yana amsawa hadu da tambayarsu yadda suka tashi. Duka suka rankaya har bakin gate din,ya hanasu fita saboda yayi sassafe da yawa,dukansu suka hada baki wajen masa addu'a har ana rige rige tsakaninsu da umman tasu,hatta da iftee, addu'ar da basu daina ba har zuwa sanda motarsa tabar qofar gidan ta dauki hanyar ficewa a layin.
Sosai tafiyar saleem ta bawa zainab daman yin al'amuranta a tsanake,komai nata sai ya ninka fiye da na baya,qazanta sai abinda yayi gaba,don kuwa tana iya shafe kwanakinta biyu cur bata duqa tayi shara ba,kamar yadda wanka ya tafi hutu a tattare da ita. Abinci kuwa ba ita ba hatta yaran za'a iya cewa horon yunwa take musu,don saidai su shiga sassan ruqayya suci,wasila tayita mita don takaicin zainab takeji kamar kamar me amma hakanan ruqayya ke cewa ta basu ba komai bane,lada zasu samu. Da wannan damar zainab tayi amfani ta riqe 'yan kudadenta ta siya magunguna ta adana wanda zatayi amfani dasu bayan anyi mata aikin,sauran 'yan canji ta duba ma haneefa atamfofi a 'yan pieces ta siyawa khalil gumama da pieces na shadda aka dinka masa duka a zuwan kayan sallarsu. Ba wani takalmin arziqi bare jaka mayafi da sarqoqi da ubansu duka ya fidda kudinsu,nata kayan kam ba tasu take ba,don ta tsara gaya masa cewa an sace a wajen tailor dinta,shikenan hankali kwance.
Tuni sun tsara da nurse din satin farko da aka kama azumi za'a yi mata dinkin,a lissafinsu kafin ya dawo ta warke sumul muddin zata kula da wajen tana tsaftaceshi da shiga ruwan zafi. Wannan ya sanya ta tura neman me zama da ita,bata samu ba sai safina ta samo 'yar wan babansu. Ba yarinyar taso ba,saboda basu cika jituwa can can ba saboda banbancin halaye dake garesu.
"Ni umma yarinyar ta fiya tsaurin ido,ga shegiyar kafiya da taurin kai"
"Eh amma ita kadai zata iya da aikin gidanki,don bata da son jiki ko kasala,da qyar fa nasha kanta ta yarda,kinsan abdurrahimu baya barinsu zuwa ko ina su kwana,sun riga suma da sun saba,yanzu ma a qila wa qala ake"
"Shikenan,ki lallabata tazo din,don azumin bana da alama zai bada kashi" a haka sukayi sallama da umman nasu.
********Ranar da aka sauke azumi na uku ne,bayan an gama shan ruwa kafin akai ga tayar da sallar asham ruqayya ta shiga dakin d wasila ta sauka.
Da sallama ta shiga ta sameta saman dadduma,dakin ya kaure da qamshin turare,sai wasu mayuka dake zube ta budesu tana hadasu guri guda.
Guri ta samu ta zauna suna yiwa juna sannu,don wasilan ba laifi idan taso akwai aiki.
"Nikam tunda aka fara azumin nan kamar baki da walwala sosai" dubanta wasila tayi kai tsaye sannan tace
"Bazan boye miki ba,wata jarrabawa ce ta shigo min rayuwa,kinsan zaid?"
"Zaid?,zaid?,wanne?"
"Abokin yaa bashir wanda ya tafi madina karatu satin da aka fara bikinki?"
"Oh.....ya zan manta da yaa zaid da ya kawo me lecture ranar wuni na"
"Exactly......ya dawo nigeria ruqayya,shi zuciya ta kuma ya jarabtu da so,nayi addu'a nayi addu'a amma ba abinda ya canza,naje wajen malam yacemin lamarin akwai rikitarwa,amma yace zaiyimin aiki a kansa cikin satin nan ya gani idan akwai alkhairi"
"A irin wannan watan wasila?" Ruqayya ta tambayeta cikin tsananin tashin hankali kwance a fuskarta,abinda ya Sanya jikin wasila yin sanyi ta bita da kallo.
Sassauta fuskarta tayi ruqayyan ta zamo ta zauna gaban wasila
"Wasila,wasila......babu wata addu'a da zakice ba zaki iya yiwa kanki da kanki ba sai wanine zaiyi miki,muddin kikaga kina addu'a kina ganin kaman bata karbuwa cikin daya biyu ne,kodai kin saka shakka a ranki game da addu'ar kin sawa ranki bata karbuwa,ko kuma kin saka gaggawa lokacinki yana tafe amma saboda gaggawa irin ta dan adam ya sanya kike ganin har yanzu shuru"
"Wasila"
"Na'am"
"Kinsan Allah da kansa yace yana kunyar bawansa ya daga hannu ya roqesh ya hanashi abinda ya roqa?,kinsan ko sau daya kikayi addu'a zuciyarki tayi rawa akan cewa wannan addu'ar bata karbu ba to tabbas kin jawowa addu'arki matsala,annabi S A w yace kuyi addu'a kunajin yaqinin ta amsu cikin ranku,koda bakaga haka a zahiri ba ka sanyawa ranka cewa ta karbu din" shuru wasila tayi tana jinjina kai
*_ZAFAFAN DAI_*π«‘π«‘π₯π₯π₯π₯
*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*π₯΅β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯π₯π₯π₯
*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_
*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*
*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*
*TSUTSAR NAMA Billynabdul*
*GUDUN K'ADDARA Huguma*
*AMEENATU Mamuhghee*
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYARππ―π... ZAFAFA BIYAR NAKU NEπ_
*_KURMAN BAΖI_*β«β«β«
*HUGUMA*
27
*_ZAFAFAN DAI_*π«‘π«‘π₯π₯π₯π₯
*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*π₯΅β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯π₯π₯π₯
*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_
*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*
*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*
*TSUTSAR NAMA Billynabdul*
*GUDUN K'ADDARA Huguma*
*AMEENATU Mamuhghee*
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYARππ―π... ZAFAFA BIYAR NAKU NEπ_
PAGE 27
"Ba wani wata dake cike da falala sama da wannan watan,dama ce a gareki ki tsaya ki roqi Allah,basu isa su sanya Allah dole ba,ba wanda ya isa ya sanya Allah ya baki abinda bai cikin rabonki ko qaddararki,indai suna da wannan power din me yasa su basu canza qaddarorinsu ba?,me yasa basu zama masu arziqin da zasufi qarfin zama a soro ko jeji suna saurarar buqatun mutane?,kinsan cewa duk matar data taka taje wajen boka ko dan duba,duk da yanzun an canza musu suna nason zuciya da son rai,ana kiransu da malamai ana kiran DUBA da ISTIHARA,muddin mutum zai gaya miki wani abu da yake a boye,kaza ne zai faru,kaza ne yake faruwa,kaza ne zai faru,siyo kaza siyo zakara siyo akuya rago ki yanka kiyi sadaka,daka borkono qona abu kaza binne abu kaza to SALLARKI TA KWANA ARBA'IN BLANK TAKE EMPTY TAKE cikin littafin ayyukanki,kuma kin sani na sani sallah itace abu na farko da ake fara dubawa cikin ayyukan bawa,idan tayi kyau sauran ayyukan sun karbu,idan ka samu matsala tun daga nan ba zaka wuce bama bare a tafi duba ragowar ayyukanka. Awannan lokacin a cikin mata akwai macen da bata rufa kwana arba'in bataje wajen wani malami akan wata matsala ba,kinga a qididdigar lissafin ayyukanta bata da sallah,ki gayan ran qiyama meye marabarta da ARNE?,tunda duka guraben sallarta sun xama empty silar zuwanta gidan malamai yan duba yan tsubbu da yan bori?"
"Wasila,duk abinda kikaje wajen malami yace miki zaki sameshi kuma kika sameshin,wallahi wallahi ba malaminne yayi sanadiyyar samun da kikayi ba,dama can Allah ya rubuta zaki sameshi,kuma da kinyi haquri bakije ba kina zaune a dakinki rabonki zai taddoki ta halastacciyar hanya ba tare da kin sabi mahaliccinki kinje wajen dan duba ba,wata ne wannan da ake ninka ladan ayyuka,ki zage kiyi addu'a kawai tsakaninki da mahaliccinki shine yafi".
Sosai jikin wasilan yayi sanyi,kamar dai hankalinta ya fara kaiwa wani wajen daban.
*********Yammacine lis lokacin da mata da yawa suka fara nisa wajen sauke abincin buda baki hadi da qoqarin kammala gurin da za'a yi buda bakin. A daidai sannan Zainab na cikin labor room na asibitin cikin matuqar farincikin matsalarta zata kawo qarshe.
"Kinyi inserting wani abu ne?"
"Ai kullum cikin matsi nake,waye zai zauna yaga zama?,mazan nan ka gyara ma amma baka tsira ba ina ga ace baka gyara ba?"
"Gaskiya ne,hakane" nurse din ta fada can qasan ranta tana dariya da mamakin Zainab din.
Har ta gama hada duk waji scissors da sauran tarkace Zainab din batayi ko gezau ba
"Ki shiga toilet ki wanke abinda kika saka din kizo mu fara"
"Toh nurse" ta fada da rawar jiki tana wucewa bandakin.
Bayan ta fito ta zare pant din ta ajjiye sannan ta haye gadon ta bubbuda qafafu kamar yadda nurse din ta umarceta sanda take qoqarin balla razor din da zata kankareta biyu
"Subhanallahi,meye haka don Allah?" Nurse din ta fada ganin irin cunkoson go slow din da gurin ya tara
"Me kenan?" Zainab din ta tambaya
"Tashi ki sauka kiyi aski,wannan ko inda zan dinke mikin ai bazan gani ba" ta fada tana jan tsaki qasan ranta tare da yin Allah wadai da son kudi itama irin nata.
A gaggauce ta saisaye ta dawo ba wani cikakken baiwa wajen kulawar tsafta yayin aski,nurse din itama ta kula da hakan amma ganin itama a gaggauce take da ayin sai kawai taja kujera ta saka face mask ta fara aikinta.
Sai da aka fara din ta gane Allah daya ne,don zata iya cewa batasan azabar stitches ba don bata taba qaruwa wajen haihuwa ba. Kafin a gama tayi wujiga wujiga,sauqinta daya ta taho da safina wadda batasan me za'a yi ba,tadai ga kawai Zainab din ta shige labor room.
Magashiyyan ta kwanta ta kasa motsawa,tana jiyowa ana kiran sallah musulman cikinsu suna tafiya buda baki,ita da azumin Allaha a bakinta amma ta kasa koda kurbar ruwa saboda wata irin azaba dake ratsata kamar ta cire dukka gwiwoyinta zuwa cibiyarta.
*_G I D A_*
Komai sun kammalashi kamar yadda suka saba kafin ayi kiran sallah alhassan da alhussain da sukakai zuminsu daidai da na kowa na zube na jiran kiran sallah wasila na musu dariya
Haneefa da khalil ne suka shigo daya yana biye da daya
"Kuzo nan" ruqayya da fitowarta kenan daga daura alwala ta kirasu
"Wasila zuba musu abinci banajin gidan nan Zainab ta wuni"
"Iyalan ci,tunda ba'a gaya miki za'a fita ba basai ki qyalesu ba"
"Ki bari mana wasila" ruqayyan ta fada tana dubanta. Bata sake cewa komai ba ta miqe ta nufi kitchen.
Gaba daya safina ta kasa tantance me yake faruwa har sai bayan shigarta dakin taji nurse din tana jaddadawa Zainab dokoki. Mamaki ya kamata,itadai tasan ba haihuwa tayi ba bare ace qaruwa tayi,hasalima ko ciki bata dashi,to amma meye hadinta dinki?. Gabanta yadan fadi data tuna wata hira da taji wasu mata sunayi,kenan itama tabi sahun matan dake zuwa a diddinkesu kawai saboda su bawa namiji wani abu ba tare da suna duba makomar lafiyarsu ba?.
Sanda duka isa gida tamkar 'yar shayi haka ta riqe zainab,takaici ya sake kamata sanda suka isa sassan Zainab din,komai ba bisa kan qa'ida ba,ta tabbatar kuma tsohuwar qazanta ce ba ta jiya ko yau ba. Tun tana aikin tana daurewa harta magantu
"Wai bakwa shara bakwa wanke wanke ne?,kun taba mopping sashen nan kuwa?" Harara Zainab dake fama da azabar radadi ta balla mata
"Ban sani ba,ku me yasa kuka fiya magana ne keda hajiyayye,hala gulmata kuka zama kuyi saboda kalamanku iri daya ne da nata"
"Ba wani gulmarki,inama muka hadu ni?,abunne ya bani mamaki,tunda dai da nazo na leqa sashen anty ruqayya mun gaisa naga ba haka nata sashen yake ba,hakanan farfajiyar gidan nan fes yake ko ina da ina,to sai naki sashen ne zai zama haka?"
"Zanci mutuncinki safina,ki wuce ki bani guri" ta fada a hasale. Baki safinan ta tabe tayi gaba,ba tun yau ba ta sani Sam zainab din bata qaunar a gaya mata gaskiya ko qanqani.
Sam ruqayya batasan abinda yake faruwa ba,tana can sashenta tana sabgar gabanta,babban abinda yafi damunta kada tasha azumi,kuma Allah ya taimaketa tana samu tana gwadawa wasu lokutan.
Tsananin son jiki da zallar qazanta ya sanya zainab bata iya shiga ruwa da kyau kamar yadda nurse din ta umarceta,tunda akayi dinkin tafi ganewa ta jabe a zaune a falo,ta lalace tsakanin kallon tv da chart kamar ba azumin ramadan akeyi ba. Tun safina ta murje idanunta,duk wanda yayi ba daidai ba tsakanin khalil da haneefa ubansu takeci,don tace ba zatayi wahalar banza ba,ta sha wahala kafin ta samu tadan kintsa sashen,duk da ba komai ya koma yadda ya dace ace ya kasance din ba,amma ba laifi sassan ya shiga saiti kaso sittin cikin dari,don wani abun idan ya baci baya gyaruwa.
Sau tari idan dinkin ya dameta da qaiqayi sosa abinta takeyi,ko tayita mutsu mutsu har sai ta sosheshi,idan kuma yana radadi bankada zaninta takeyi ta kunna qaramar fanka. Sannu a hankali gurin ya fara rurucewa yana sakin wani irin ruwa,amma sanda taga ruwan a pant dinta sai murna ta kamata
"Bayan matsi har ni'ima wannan dinkin yake saukarwa, Alhamdulillah" ta fadi farinciki yana kamata. Batayi wani yunqurin komawa asibiti ba,don nurse din ta gaya mata ta sallameta tunda ta gaya mata ruwan dumi zata dinga shiga,zaibi jikinta basai tazo dubawa ba. Tayi hakanne saboda dokar asibitinsu kora ce ga duk wanda yayi irin wannan,saboda hakan tamkar ya shiga a matsayin cin amana ne da zamba.
********Karfe sha biyun dare ta kammala salllolin darenta da basa wuceta a wanann watan,dukka tana yin addu'o'inta ne akan samun gamawa da duniya lafiya,zaman lafiya a gidanta da mijinta,da shiryuwar yaranta da yaran musulmai gaba daya.
Sau biyu takanci abinci,irin wannan lokacin da kuma lokacin sahur shine take samu abincin ya riqeta sosai,tana yawaita shan kankana duk suna cikin abinda ke sauqaqa mata azumi(ga mace me ciki dakeson yin azumi ba tare data wahala ba,ta yawaita shan kankana tana taimakawa sosai).
Har ta zuba abincin a dining saita dinga jin kamar sheshsheqar kuka a dakinsu iftee,ajjiye abincin tayi ta juya zuwa dakin.
Wasila ce saman abun sallah sanye da hijabi take kuka kariris. Girgiza kai ruqayya tayi ta qarasa shigowa
"Lafiyarki wasila?,da daren nan?"
"Na shiga uku na shiga jarabawar da bansan yaya zanyi da ita ba,ruqayya ki taimakeni,anya ina da sa'a a rayuwata?,anya ina da rabon yin aure?"
"Me ya faru?" Idanunta da sukayi jajur ta daga
"Dazu na biya ta gida muna magana da yaa bashir saiga yaa zaid yazo zasu fita,sai naji yana gayawa umma zasu bincike ne kan yarinyar da zaid din zai kaiwa kudi bayan sallah......na rasa yaa zaid shima ruqayya don Allah ya zanyi?"
"Malamin naki da kikaje gurinsa daxu ya gaza kenan?,ina tarin alqawuran da yayi miki?,ina mijin daya fasalta miki yace zaizo shi zaki aura?" Sak wasila tayi,don bata taba tunanin ruqayya ta ramfota ba
"Kin yadda yanzu sa zancena kan cewa dukkaninsu maqaryata ne?,kin yarda da maganata akan cewa ba zasu