Showing 6001 words to 9000 words out of 66328 words

Chapter 3 - Kurman Baki Hausa Novel Complete

ta sake binta da zagin idanunta kamar zasu fado saboda harara,sai kuma taja qwafa ta wuce bandaki a gurguje tanason watsa ruwa kafin yakai ga shigowa.

Wani sassanyan yanayi ne da parlor din wanda ko yaushe baya rabo da shi saboda tsaftar da ya kamashi. Komai na tsaftace ne akan tsari da sanin darajar muhalli.

Sassauqar doguwar riga ce a jikinta ta wani yadi maras nauyi ruwan madara me haske sosai,kusan duk shigarta tana yinta ne bisa tsari da favourite colours na saleem din. Alhassan da alhussain na zaune daga qasan carfet saman qananun duddumansu,kowanne jallabiyya ne a jikinsa farare da qananun hulunan tashi ka fiya naci. Kyau yaran sukayi kuma duk wanda ya kallesu dole su bashi sha'awa.

Sallamar uban ta sanyasu hankulansu yowa kansa,al_hussain shi ya fara yo gaba yana qoqarin karbar ledar hannunsa hadi da fadin

"Abba sannu da zuwa" wadda suka furtata kusan lokaci daya da al_hussain dake daukema abban nasu pillow daga saman kujerar don ya samu wajen zama.

A duk sanda ya sanya qafafunsa a sassanta yakan jishi tamkar cikin wani muhalli na daban yake ba'a cikin gidan ba. Sau tari yakan tambayi kansa da kansa

"Me yasa ya qaro aure?" Wani lokaci zuciyarsa da kwanyarsa kanyi hadin gwiwar bashi amsar

"Rabo". Kamar ko yaushe a yau ma amsar da ta bashi din kenan,wanda yayi dai dai da ajjiye kaskon turaren wutan dake hannunta,ta kuma sauko daga dining area din yana gyara zaman dankwalin kanta me sulbi tana fadin

"Barka da warhaka"

"Barka kadai" ya amsa mata yana bin su alhussain da kallo wadanda suka nade abun sallarsu suka wuce dakinsu.

Hannun 3sitter din da yake kai zaune ta zauna itama,idonsa ya dawo dashi kanta lokacin da ta miqa hannu ta jawo gorar ruwa me matsakaicin sanyi ta zuba glass cup tana miqa masa. Sai da ya saki murmushi sannan ya miqa hannu ya karba,ya shanye tas sannan ya miqa mata cup din

"Na rasa wacce irin baiwa ce dake da har kike gane yunwata da qishirwata ba tare da na furta ba" murmushin ta kuma sakar masa

"Da kallo guda daya tak da zanwa idanunka na gama samun amsar komai" kai ya gyada cikin gamsuwa tare da jin matsayinta yana sake zarcewa wani madaukakin muhalli a zuciyarsa. Kullum wayewar gari sai ya godewa Allah da bai bawa shaidan galaba a kansa a shekarun baya ya ingizashin da zai zama sanadiyyar rasa ruqayya ba,inda hakan ta faru?,yanzu da a wanne gurbi yake a rayuwa?.

"Amma,me yasa ba kowacce mace ke da wannan baiwar ba?" Idanunta ta dan janye daga kansa,jikinta ya bata inda maganarsa keson dosa,don haka tadan juya ido kadan

"Ya danganta da yadd kika zabi ki fuskanci mijinki ko ki mu'amalanceshi,hakanan ya danganta da iya adadin lokacinki da kuma kulawar da kika bashi".

"Sai yaushe zainab zata dinga fahimtar irin wadan nan abubuwan tayi koyi dake ta kuma canza?" Dauke kanta ta sakeyi a karo na biyu. Duk girman matsin da zaya shiga muddin akan zainab ne bata da sha'awar ta shiga lamarinsu,lamarin miji da mata sai Allah,duk yadda take gani a yanzun a wata ranar tana iya ganin sauyin hakan a tattare dashi,duk da cewa zuwa yanzu ta jima da mance wannan lamarin

"Ba'a sassa na kake ba,kada maman haneefa taga ka jima da yawa" ta fada tana miqewa, miqewar da taja hankalinsa har ya gaza dauke dubansa daga kanta

"Au korata ma kikeyi?" Ya jefa mata tambayar da kafin ta bashi amsa turo qofa da shigowar haneefa taja hankalinsu.

Rarraba ido ta fara yi tsakanin fuskar abban nasu da ruqayyan. Har cikin ranta ruqayyan tana jin babu dadi. Yadda yanayin tarbiyya haneefa take a gidan,akwai sakaci na bala'i daga wajen mahaifiyar da bata cancanci zama uwa ba. Duk da haneefa ta girmewa su alhussain nesa ba kusa ba,amma akwai nisan tazara me yawa a tsakaninsu,tun daga hankalinta zuwa nutsuwarta.

Tsuke fuska saleem yayi ransa na baci,a tsawace yayi mata magana

*HUGUMA*👑

https://chat.whatsapp.com/HeRo2w8C8gdG0Et1lqafjk



*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫

*HUGUMA*

PAGE 04


"Halan baki iya sallama ba bare gaisuwa haneefa?" Ta tsorata ainun,don duk yadda yake sakewa da iyalansa amma sun sani,muddin ya dauki zafi da kai ko fushi to zakaji babu dadi

"Sannu da zuwa abba,ina wuni?" Ta fada tana hade maganganun duka guri daya

"Koma kiyi sallama" ruqayya ta fada a sanyaye. Sakin labulen yarinyar tayi ta juya zuwa waje,haushin tsawar da akayi mata tana cikata,tana ji a ranta maamantata ce ta jawo mata.

Irin yadda taga su alhussain din sukayi haka tayi,ya amsa yana dauke kai,saidai cikin ransa yaci alwashi bazai dauki wannan sakarce sakarcen da yayi imanin laifin na Zainab ne,dole ya zauna da ita ya kafa mata sharudda da qa'idojin da zata yawaita tunawa kanta bazai dauki irin wanann ba.

Ledar hannunsa ya miqawa ruqayya babbar

"Ga mutanen naki" murmushi ta saki cikin jin dadi,kamar yasan a daren tana da buqatarsu,duk da al'adarsa ce tunda kayan suka zama abebadan shanta

"Na Gode qwarai qwarai,kaima Allah ya faranta maka ya qara budi da wadata"

"Ameen ya hayyu ya qayyumu, your prayers are my strength" ya fada yana dan lumshe ido. Idanunta ta kada masa tana murmushi,ya zare nasa idon da sauri yana yin gaba

"Inda zan zauna n qara awa daya tak zaki cikamin kunne da magiyar na tashi na tafi yanzun kuma kina yin abubuwan da sun saba doka da qa'ida irin ta yau" dariya ya bata sosai,sai ta rungume ledar ta juya zuwa cikin kitchen don ta wanke kayan ta kuma adanasu cikin fridge.

Shigowar haneefa ya sanyata dungure man data dauko zata shafa ta waiwayo tana bada hankalinta ga yarinyar. Tun kafin ya gama shigowa ta kasa jumurin jira

"Me ya shigar musu dashi?,ina ledar?" Baki haneefa din ta tura alamun dake nuna tsiwa ta zauna mata sosai a jikinta

"Ina zamana kin saka anyimin fada harda tsawa"

"Ba wannan na tambayeki ba leda nake tambaya" ta fadi tana zaro idanu cikin takaicinta tana duban haneefar

"Ya bata" ta amsa mata a a taqaice

"Ya bawa wa?" Zainab ta fada tana zaro idanu cikin jin bala'i da tashin hankali

"Mommyn alhassan"

"Lallai yau an taro fitina a gidan nan,wallahi bazan dauki irin wannan abun ba" ta fada tana jin kamar zata dora hannu a kai ta rusa kuka. Tako ina saleem cikin jawo abubuwan da zasu kawo rudani a zamansu yakeyi,rashin adalci tako ina yake gwadawa rayuwarta,duk qoqarin da ita din keyi na ganin sun zauna lafiya ita kuma ta faranta masa.

Tana tsayen da daurin qirjinta hannunta riqe a qugu ya tura qofar dakin hadi da sallama ya shigo.

Kamar me ciwon wuya haka ta waiwayo da qyar tana amsa sallamar,bakinta zaka dauka ya cusa lomar biredi ne data hanata yin magana da kyau.

Tuna fadan da ya gama yi mata yanzu yanzu ya sanya haneefa juyawa ta fice a dakin.

A nutse ya qara takowa ciki yana karantar yanayin dakin. Mutum ne shi me wani irin qaqqarfar halittar jiyo qamshi ko warin abu,don haka a yanzun ma kusan abinda hancinsa ke jiyo masa sam baiyi daidai da abinda zuciyarsa keso da muradi ji cikin gidan sa ba.

Mayar da dubansa yayi gareta,tana tsaye qerere tana binsa da kallon da baisan daga ina ta samoshi ba. Cikin daurin qirji,gashin kanta me tsaho da laushi ya samu guri ya cure abinsa saman kanta,wanda hakan ke nufin akwai dauda da rashin tajewa da ya zama silar wanzuwarsa a haka. Kauda idanunsa yayi,don idan da sabo za'a iya cewa ya riga ya saba. Cikin ranakun mako guda bakwai zaiyi wahala zainab din ta tsallake kwana biyu ba tare da ya ganta da daurin qirjin ba,walau da safe ko da dare kamar haka,ko yanzunma yasan qilan dashi ta wuni,bayan tasan babu abinda yafi tsana irinsa

_Note:Da yawan maza sun tsani wannan al'adar,domin bata da wani alfanu sai canzawa mace yanayi,musamman idan ta hadu da nau'i na qazanta irin ta zainab,akwai wasu lokuta da mace kanyi daurin qirjin don jan hankalin miji,in a stylish way,ta yadda zaki daure bakin zanin a tsakiyar qirjinki kamar kin qulle abu,ki koma sassauto da zanin zuwa rabin qirjinki wanda hakan zai bashi damar gano pant da wasu sashe na breast dinki,bawai daurin qirji irin wannan na gargajiya mara ma'ana ba da fallen zani me dauda_

"Sannu da zuwa" ta fada da qyar a hakanma tana tausar zuciyarta ne gudun kada daren yau din ta sake tafka asara kamar yadda tayi a jiya

"Yauwa,ya gidan ya yaran"

"Lafiya lau.....mu ina tamu ledar?" Ta tambayeshi kai tsaye tamkar ita ta aikeshi. Daga kai yayi ya dubeta yana maimaita tambayar da tayi masan,qasan ransa mamaki yana cin ran nasa. Ya akayi tasan ya shigo da leda?,har yanzu bata daina wannan dabi'ar tata ba kenan ta shegen sanya idanu a shige da ficen kowa na gidan?.

"Oh wadda kika aikeni da ita?" Dan sararawa tayi kadan,saboda amsarsa ta bata hasken inda ya dosa

"A'ah,ni ban aikeka ba,wai saboda naga yara sun ganka da leda ya kamata suma ace an basu ko tunda suma 'ya'ya ne kamar kowa" ta fada tana murmushin yaqe.

Takaici ya qumeshi sosai,wai ita a hakan fa ta qure dukkan iyawarta ta gaya masa magana me dadi kenan. Miqewa yayi daga dosana zaman da yayi saman stool dinta

"Abinda yake ciki ba cimarki bane,fruits ne,ke kuma nasan babu daya a ciki da kike ci,itace me ta'ammali dasu kullum shi yasa nakai mata na dibarwa su haneefa,duk da su dinma sun koya ba lallai su iya shanyewa" ya bata amsar yana nufar qofa.

Kallo ta bishi dashi tana tabe baki,a ranta tana jin kawai zallar mugunta ta sanya ruqayya ta sakashi siyo fruit din. Wannan shan fruit da cin ganyayyakin nata yana masifar qona mata rai,aikinta kenan kullum kamar wata raquma

"Ni bazan zauna ina fama da 'ya'yan itace ba,nafi qarfin gaban nan,mu saidai mu rungumi qwaryar qwayoyi musha muyi tatil mu gigita mutum" ta fada qasa qasa tana shafe fuskarta da mai,koda ta gama kuma bata nemi powder ba bare turare ta fara laluben kayan da zata saka.

A gajiye ya tura qofar dakin nasa da shirin fidda kayan jikinsa ya watsa ruwa ya wuce masallaci yayi aallar magariba. Cikin qasa sa second biyar dukkan wannan karsashin nasa da dokin ya fita a kansa gaba daya.

Yadda ya fita yabar dakin da safe haka ya sameshi,babu wani abu da ya sauya. Hatta da comb da ya taje kansa kafin ya fita yana zaune abinsa dungurgur saman madubin. Numfashi ya zuqa ya kuma fesar zuciyarsa na wani irin tafasa. Ya sha gaya mata,a duk sanda qazantarta ta motsa taje ta qarata,tunda yayi iya yinsa,to amma ta tabbatar qazantar bata shafi komai nasa ba.

Murfin qofar ya saki bayan ya jingine briefcase dinsa jikin bango ya koma da baya falo inda yabar yaran. Duban ledar da ya ajjiye musu yayi,sun gutsutstsura fruit din kawai sun barshi sai ma bata gurin da suka sakeyi. Daga khalil dake da shekara shida har haneefa din dake da shekara goma cikin ta sha daya rasa me hankali yayi a cikinsu. Alhassan da alhussain dake da shekaru takwas cikin ta tara ya tuna,a wadan nan shekarun nasu sun iya share guri suyi mopping fes,sun iya wanke wanke da wanke qananun undies dinsu na mamansu dana qanwarsu,a yawancin lokuta har fada yakan yiwa ruqayya,saidai ta langabar da kanta

"Ka bari sunyi mana daddynsu,idan basuyimin ba wa nake da da zaiyimin,sannan wataranma fa suma mazan auren wasu ne,idan suka iya ai kaga har matan da zasu aura sun huta suma,wataran sayi karba a aikin gidan,ko kuma wata lalurar idan ta samu matayen ko?" Hanci ya lakace mata

"A fakaice dai ni kike zagewa fa rukky" dariya ta saki tana riqe yatsunsa

"A'ah wallahi daddy,rainon inna ne fa kai?,kaima ai koda bata koya maka aikin gida ba aita koya maka abinda yafi wannan muhimmanci,iya kula da iyali,zuciyar soyayya da tausasawa da kuma kyautatawa" yadda kalaman suka fita a bakinta sun sake ninka kimarta a zuciyarsa,sun kuma sanyashi yana sake jin nauyinta da kuma rashin son tuna wasu abubuwa da suka wuce a baya.

"Kiramin mamarku" yace da khalil,bayan ya wuce ya kalli haneefa

"Haneefa"

"Daddy" ta amsa

"Ki tattare wannan abinda kukaci din ki sakasu a fridge,sauran ki saka a shara,duk abinda bakuci idan na kawo ku daina lalatashi irin haka,saboda qannenki zasu gani su koya ne"

"Tom" kawai tace tana miqewa cikin sakalci ta soma gyaran wajen,wanda kana gani kasan bata saba ba kwata kwata.

Kanshi ya girgiza kawai ya koma bedroom din nasa. Tsaho wasu mintuna bata iso ba,har ransa yaso ya soma baci,sai kawai ya miqe ya soma rage kayan jikinsa yana dorasu saman wadanda ya ciresu da safe.

Sai da ya kammala sannan yaji ta turo qofar,still da uban daurin qirjinta na dazu,ya rasa me takeyi tun shigarsa dakin da fitowarsa kawo yanzu da bata nema wani abun ta saka ba ta raba kanta da daurin qirjin nan

"Gani" ta fada tanason nemo dakiya a ranta,saboda tun shigowarta ta gama gano abinda ya farun. Shaf ta manta da wani batun gyaran dakinsa gaba daya,tunda ta zauna yau qoqarin neman maganin da zaiyi mata aiki sharp sharp shi da ita takeyi,kuma ko yanzun alhamdulillah ta fara jin alamun hakan cikin jikinta,saura shi.

Waiwayo yayi yana qoqarin hadiye bacin ransa ya dubeta,sai ya hangi khalil kusa da ita

"Wuce falo wajen haneefa" yace da yaron,bacin ransa yana sake tasiri. Kwata kwata basu da tsarin shiga guri daga shi har 'yar uwarsa,ko ina ma suna iya bin iyayen ko su shiga ba tare da rarrabe dacewa ko rashin dacewar hakan ba,yau ya kawo qarshe kuma dole ya sanyata ta gyara ginin data bata,bazai bari suci gaba da girma akan haka ba.

"Haka ya kamata dakina ya zama?" Ya fada yana tsareta da kallon tuhuma bayan ficewar khalil din. Hannu ta saka ta sosa kanta

"Wallahi na sha'afa ne inata aiki tun safe"

"Eh naga alama a gidan ai" ya amsa yana juyawa abinda ya shige bandakin.

Bai iya wanka a ciki ba saboda Allah ya zuba masa tsantsami,sai daya zazzaga garin klien hypo da ruwan izal ya wanke toilet din fes da kansa sannan ya hada ruwan wanka. A gurguje yayi wankan saboda gudun qwacewar lokaci,saidai duk yadda yaso ya fita akan karin sai da lokacin ya kusa qwace masa,abu na biyu daya tsana ya rasa jam'i,yana fitowa ya zura jallabiyya kawai a gaggauce ya fice.

Bazai iya tuna randa yayi missing sallahr magariba ba duk sanda yake sashen ruqayya,saboda komai da tasan yanaso tana tanadar masa kafin yazo ga buqatarsa. Akwai banbancin da tazara me dinmbin yawa tsakaninta da ita,yana dukka iyakar qoqarinsa ne kawai wajen kamanta adalci da boye hakan a mu'amalarsa da su gwargwadon iyawarsa,amma ko sau daya zainab din idanunta basa gani.

A kullum zancanta daya ne zuwa biyu,ruqayya ta mallakeshi shi yasa sai abinda takeso ake gani,baya kamanta adalci a tsakaninsu duk da qoqarin kyautata masa da takeyi. Ya rasa wanne adalci take bida bayan wannan?,me takeso yayi mata?,da wannan tunanin ya isa masallacin ya zare takalmin qafarsa ya shiga.

Bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha'i,don gaba daya bashi da wani karsashi da dokin zama a gidan gaba daya.

Kallon takaici kawai yabi dakin dashi,ya kada kai yana wucewa ciki ya ajjiye abun sallarsa. Sanda ya dawo falon da niyyar zama ba komai dake kai kawo sai qaurin abinci,ya kalli kitchen din kaman zaiyi magana sai kuma ya sake dauke idonsa. Wannan na daya daga cikin dalilan da ya sanya kullum ta Allah muddin zai zagaya backyard na kitchen dinta sai ya taras da uban lalataccen qanzo,qudaje da sauran qananun qwari suna parade akai iya son ransu. Duk yadda zaiyi wajen kwatanta mata ta daina amma hakan ya gagara,a taqaice ma abicin store dinta shine yake fara qarewa cikin gidan. Bama abincin ba,zai iya cewa kusan komai ma.

Kamar ko yaushe a nutse ta shirya cikin wani sassauqan riga da wando na pakistan masi taushi da hasken launi,dan qaramin mayafin da kayan yazo dashi mai qarancin kaurin da kana iya hangen gashinta dake gyare a matse cikin band ta lullubawa kanta,ta lakaci oil perfume dinta ta shafe jikinta da shi sannan ta soma nufar qofar dakin.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login