Showing 60001 words to 63000 words out of 66328 words
Chapter 21 - Kurman Baki Hausa Novel Complete
ba 'yar iska bace,zama da mata masu hankali yasa nayi karatun da banzo wajen ba kuma alhamdulillah yana amfanata"
"Inaaa,saidai idan barbada kika fara safina" zainab tafada tana mirgina kai hadi da jin takaicin maganganun safinar data daukesu basu da maraba da zagi
"Indai tsafta ce karuwanci to na fara karuwancin......' safina ta fada don ranta ya fara baci,ya daga bada shawara zainab din zata jefeta da mummunar kalma irin haka?
"yasin matar nan na tabbatar wallahi pant dinta yafi brush dinki tsafta,don haka idan zaki qwaci mijinki da tsafta iya girki iya kalami.ladabi da biyayya tamkar ki kwanta ya takaki to...... don nidai banga ta inda mijinku ya rageku ba bare ace bai cancani a bishi ba"
"To ko aurensa zakiyi ki shigo mu goga kafada?" Zainab din ta fada tana miqewa cikin nuna kishi. Dariya safina ta bushe dashi
"Bazan iya goga kishi da mommyn alhassan ba,don nasan kamota da zama kamarta sai mace tayi da gaske" ta bata amsa da magana me harshen damo tana wucewa dakinsu
"Fito ki koma gidanku tatacciyar mara mutunci"
"Ko baki fada ba,aini na gama zama,ladan dana samu ma Allah ya amfanashi haka". A haka suka rabu da safina walle walle,tayita surfa ashar tana zagi bayan tafiyar safinan,don sai daga qarshe ta zauna ta faffasa maganganunta sannan ta fahimci zaginta ma ashe tayi a fakaice.
Duk da ta sauke azumi saboda jinin da taketa zubarwa wanda a nata tunanin period ne amma taji jiki kafin ta gama ayyukan da safinan keyi,daga qarshe dai ranar ungulu komawa tayi gidanta na tsamiya,don bata iya gama aikin ba tayi jiqa jiqa yadda ta saba ta samu waje ta kwanta saboda wani irin weak da jikinta yayi duk a sanadin jinin da take zubdawa me yawa.
*****Qarfe takwas na daren jajibirin sallah jirginsu saleem ya sauka. Dai dai lokacin da ruqayya ke kai kawo tsakanin falo da dakunan baccinsu don ganin ta wadata gurin da turaren wuta. Idan ka kalleta saita burgeka,saboda tayi kyau cikin dinkin wata lallausar atamfa da aka zuba mata doguwar riga. Daurin kanta ya zauna das,lallen dake hannu da qafafunta sun yiwa hannuwanta da suka qara taushi da haske kyau saboda cikin dake jikinta wanda ya fara turowa gaba. Duka yaran suna wajen wasila a daki anata faman fidda kayan da za'a saka a gobe idi. Yaran shadda tayi musu fara qal harda babbar riga iri daya da saleem data sanya aka zuba masa shima aiki a babbar rigar zatayi masa ba zata da ita a matsayin gift dinta na dawowarsa.
Suna jin qarar tsauwar motar suka diba da gudu kowa na rige rigen isa farfajiyar gidan,dama kuma kunnuwansu dama suna farfajiyar gidan tunda sukaji an tafi dauko baban nasu. Garin wannan saurin suka yarda iftee,ta tsala kuka kuwa abinda ya dakatar dasu ya kuma ja hankalin ruqayya ta iso wajen.
Harara daya tayi musu kaman yadda ta saba kowannensu ya shiga taitayinsa
"Ku koma ku zauna" ta fada a dake,tilas kowa ya koma saman kujera ya zauna idanunsa a bakin qofa suna daukin ganin abban nasu.
Godiya yayi ga Allah sanda ya shaqi iskar gidan,saidai kuma ya cika da mamakin abinda ya hana yaran fitowa musamman su iftee da ba kasafai koda yana gari suke missing zuwa tarbarsa ba.
Kayansa ya bawa yahaya qaninsa yace ya wuce dasu sashen ruqayya shi kuma ya saka kai sashen zainab tunda yasan a sashen ruqayya zai sauka,abinda ke dada faranta ransa kenan tun a jidda kafin su taso,yasan zai sauke dukka wata gajiya tasa,zai kuma huta da kyau qwarai fiye da yadda yakeso.
Yana sallama Khalil da haneefa suka yo kansa da gudu ya hadasu ya rungume yana amsa oyoyo dinsu. A sanyaye zainab dake zaune dafaan a wajen saboda jinin da ya fara bata zaninta bata samu ta tashi ba saboda wayar da sukeyi da raliya akan maganin da za'a amso mata na tsaida jinin data laqabawa suna jinin jifa,ta sauke wayar gabanta yana faduwa,saboda duka a lissafinta sai washegarin sallah zai dawo,kafin sannan suka ta samu ta saita komai,don taci alwashin ko na minti daya ba zata barwa ruqayya shi ba wai don tana cikin jini,sam ba zata bari ba,idan ma tayi ne don ta shawo kanta ita daya,kuma idan kwana biyun nan taci bulus,wani girkin da zata karba zata fara shine ta kuma qareshi cikin ciwo da tashin hankali hadi da jinin bari in sha Allahu,don ta qwaqule duk abinda yayi mata saura ta bayar ayi mata aiki akan ruqayyan.
"Lafiya kike?ko azuminne?" Ya tambayeta yana kallonta saboda yadda ta koma wata iri gaba daya.
Yaqe tadan sake masa kadan tanason kauda hankalinsa daga kanta
"Azuminne na bana ya bada wahala"
"To ya za'a yi?,ita dama aljanna ai ba'a samunta da sauqi kana daga kwance" ya fada yana zama saman kujerar yana mamakin yadda yaga qazantar sashen tadan ragu, cikin ransa yana fatan koyi takeyi da ruqayya tana rage wasu abubuwan.
Ya danyi mintuna dasu yana basu alawoyin daya riqo kafin ya miqe
"Inajin basusan na shigo ba,bari na qarasa ciki na huta" kai ta kawar tana jin zafi har cikin ranta yadda ya dawo dinnan a wajenta ya kamata ace ya huce dukka gajiyarsa,idan da hali ma kada ya tuna da wata ruqayya.
Har yaran sun bishi ta kirasu,ta danqara musu ashar tace su zauna a nan. Hakanan suka dawo suka zauna gwiwa a salube,shikam baima sani ba tunda already ya fita. Haneefa ce data gaji da mutsu mutsu tace
"Wannan zama kaman a birsin" tayi maganar kuwa akan gaba,don tana sauke maganar ta ta kai mata kyakkyawan duka a baki harda fuska,ta tsanyara ihu kuwa yarinyar tana dafe da fuskar
"Don ****** ni zan dinga fada kinamin musu?,to zakisha wahala don wallahi mugun duka zan dinga miki daga yanzu" miqewa tayi tana kururuwa hadi da banka kuka har ta shige dakinsu.
Kallon takaici zainab ta bita dashi har sai data shige dakin,taja qwafa tana maida hankalinta kan waya. Ci gaba da satar kallonta khalil yayi,don shima sashen nasu sam baya masa dadi,kamar gobe ba sallah ba,amma daxun da ya shiga wajensu alhassan sai yaji lallai da gaske gobe sallah. Gajiya yayi da zama ya miqe shima yabi bayan haneefa yana cewa
"Ni wallahi dama momynsu alhassan ce ta haifeni,mu ko kayan sallar namu ma tsofaffi ne inajin" ya fada yana fadawa dakin da sauri don kada ta samu nasarar dukansa. Baki bude tabi qofar da kallo,anya ruqayyan bata fara taba mata yara ba?,anya sharrin nata bai gangaro mata kayan yaranta ba?,koma meye anzo qarshen maganar ai ba zata qyale ba sam.
Kallo daya ya yiwa ruqayyan wata qaqqarfar ajiyar zuciya yaji ta subuce masa,tayi masa kyau iya kyau,gold Julius Holland din jikinta kamar saboda ita akayi wannan design din,yaran na lullube da shi amma hankalinsa yana kanta. Koda suka kebe bata gajiyar jikinsa yake ba,so yake kawai ya samu kaiwa ga kyakkyawan jikin da ya samu kyakkyawar kulawa da gayu me cike da nutsuwa da kuma cikakkiyar tsafta.
Duk da gajiyar da ya sauke mata amma hakan bai hanata qoqarin ganin komai na abincin idin gobe ya kammala ba,daga qarshe tun farko farkon dare ya tsareta a daki yace tazo ta tayashi baccin gajiya,tana cikin jikinsa yana zuqar daddadan qamshinta har bacci yayi awon gaba dashi,wannan damar ta samu ta zare jikinta ta rufeshi da kyau ta fita suka qarasa komai ita da wasila sauran suka barwa washegari.
*_WASHEGARI_*
Sunyi fes abinsu shida alhassan da alhussain harda iftee da itama akayi dinkin shaddar da ita. Idan ka ganshi zaka dauka sabon angone,duk da a wajensa ya furta mata haka yake jinsa kamar sabon angon,duk sanda ya kalli kayan jikinsa tun daga sanda ya sanyasu kawo yanzu tun daga harshe har zuciya bai daina saka mata albarka ba. Yasan nawa ne price na shaddar data siya masa har yadi kusan goma,ya kuma san tsadar aikin data bayar akayi masa don kawai ta faranta masa.
Duka kan iyalinsa ya hada suka wuce sallar idin saboda falalar dake cikinta,harda ruqayya wdda dama bata fashi duk shekara,indai bataje ba saidai idan bata da lafiya.
Kusan sau uku yana aike kan zainab ta fito amma tace bata zuwa,tuni ta hangosu ta labule,kuma shigarsu kadai ta cusa mata tarin takaici da baqinciki. Shin idan tace zataje dinma me zata sanya ita?. Har suka fice idanunta suna kan haneefa da khalil wanda shigarsu ta banbanta data yaran,ta lura da yadda saleem din ya tsaya yana kallonsu hadi da jefa musu tambaya,yayi kaman zai shigo sai kuma taga ya fasa,ta sauke ajiyar zuciya,don ta tabbatar zaibi ba'asin kayan jikinsu ne.
Sanda suka fice gidan sai ya zamana saura ita kadai,yau sallah don haka tayi niyyar itama tayi kwalliyar kece raini,saboda gobe tun da safe iwar haka zata matsa kambunta ta karbi miji. A duk sanda ta tuna haka ta Kuma tuna ta shiryawa hakan don wajen da ake abun dominshi nata a matse yake gam sai taji farinciki ya kamata,saidai kuma yadda jinin daketa zuba yaqi daga qafa abun yake sake daure mata kai,amma tana d hope don raliya ta gaya mata yau din bayan idi zata aiko mata da rubuta da.magunguna,kuma an bata tabbacin muddin dai asiri ne akayi mata awa hudu kacal zataga ya dauke.
A gurguje tadan gyara falonta da bedroom dinta don tanason kafin su shigo tayi adon da zai cusawa ruqayya haushi don basu da nisa da masallacin idin.
Hankali kwance ta soma cire kayanta don yin wanka a gurguje duk da tsummokaran jinin data jiqa wanda bata samu tsaiwa ta wankesu ba. Qunzugun ta zaro wanda ya jiqe sosai da jini,zarowar tasa yayi dai dai da fitar wani mummunan wari da ya sanyata kauda kai.
*_ZAFAFAN DAI_*π«‘π«‘π₯π₯π₯π₯
*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*π₯΅β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯π₯π₯π₯
*_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_
*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*
*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*
*TSUTSAR NAMA Billynabdul*
*GUDUN K'ADDARA Huguma*
*AMEENATU Mamuhghee*
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYARππ―π... ZAFAFA BIYAR NAKU NEπ_
*_KURMAN BAΖI_*β«β«β«
*HUGUMA*
PAGE 30
*_RUK'AYYAT GRAPHICS_*
*_Ina mata ma'abota sana'o'in online dama na cikin gidaje?_*
*_kamfanoni da ma'aikatu da masu office office?_*
*_kuna buqatar qayataccen kuma unique design masu kyan gaske na_*
LOGO
INVITATION CARDS
BANK STICKERS
BUSINESS LOGO
SAVE THE DATE
P.O.S BANNERS
BIRTHDAY CARD
BOOK COVER
DATA FLAYER
BIRTHDAY VIDEOS
VIDEO INVITATION
AI PICTURES
_KAI DAMA SAURAN DUKKANIN GRAPHICS DESIGNS_
*_INA MASU SON KOYON SHI KANSA GRAPHICS DIN DUNGURUM GUM GABA DAYA DON DOGARO DA KAI KUMA BUQATAR KANKI?_*
*RUKAYYAT GRAPHICS* itace amsarku
_KU GARZAYA MAZA KU TUNTUBETA,KU DANNA WANNAN BLUE DIN RUBUTAN DON YIN MAGANA DA ITA KANKU TSAYE_
https://wa.me/+2347084515410
_ZAKU SAMU KOMAI DAI DAI DA ALJIHUNKU BISA FARASHIN RANGWAME_ππ½ππ½ππ½ππ½
Daga ita har saleem babu wanda yake da tabbacin meye ya sameta,illa dai ta taimaka masa ya canza mata zani da riga,sannan yasa qarfi ya ciccibeta yana me dauke numfashinsa saboda abinda yakeji ya isa mota da ita.
Zataso taje ta canza kaya ta kuma jefa wani abun a bakinta saboda azabar yadda zuciyarta take tashi,to amma yanayin da Zainab din ke ciki bazai bata dana ba,don haka tana a tsaye a nan tasa alhassan ya amso mata slippers da hijabi ta zura tabi saleem motar.
Har suka isa asibitin Zainab matagugu take na matsanancin ciwon mara,dukkansu sannu suke binta da shi,saboda sunyi tambayar duniya bata cewa da kowa komai ba,dama ita ruqayya bata zurfafa a tambayar ba gudun jin abinda zai tayar mata da hankali ko maganar da zata bata mata rai.
Duk da cewa ranar sallah ne amma asibitin a cike yake,akwai tarin masu ziyara da kuma tarin marasa lafiyar da Allah ys jarabta da ciwuwwuka.
Sashen emergency na asibitin ne suka amsheta da gaggawa,saboda duk da kasancewarsa private amma babba ne,suna da tarin kayan aiki qwarai da qwararrun ma'aikata.
Koda suka shiga da ita dakin marasa lafiya ita da saleem din zaune sukayi suna dako. Tana ankare da saleem din da ya kasa zama,sai dan tattaki da yakeyi kadan kadan daga hauni zuwa dama.
Ba jimawa ya qaraso inda take ya zauna dab da ita,ta daga kai ta kalleshi suka hada idanu
"Kina da masaniyar wani abu akan ciwon nan na zainab?" Ya yiwa ruqayyan tambaya muryarsa a raunane. Yau din sai taji ba zata iya bagarar dashi ba kaman yadda ta saba a duk sanda ya sako mata zancan zainab
"Bansani ba,bansan komai ba,yadda ka ganta yanzun haka na ganta" shuru ya danyi,sannan yaja iska ya fesar
"Jikina yana bani koma meye yana da alaqa da ta'ammali da gurbatattun magungunan matan da batasan ingancinsu ba anyhow" dubansa ruqayya tayi da sauri sai kuma ta sauke kai batace komai ba.
"Ina wadanda suka kawo Zainab!,kuna ina!,bawan Allah kune?,ku taso maza maza!" Nurse din data leqo cikin daga murya da alamu na kiran gaggawa ta daga musu hannu tana fada.
Ruqayya bata motsa ba saboda tana ganin ba huruminta bane ta shiga din,amma sai saleem ya kalleta
"Taso muje" zata musanta ya saka hannunsa ya jawota sukayi ciki.
Kukan Zainab suka fara cin karo dashi wadda ke maqure saman gado tana gunza kuka,sai nurses guda biyu a gefe da suketa magana cikin bacin rai da metron daya. Hankalinta yayi mugun tashi da taga tare suka shigo da ruqayya,sai taji kamar ta bankawa wajen wuta a tashi ba tare da anyi maganar komai ba
"Malam ya akayi kabar matarka ta rube don girman Allah?,a haka kuma kake iya mu'amalar aure da ita?" Daya daga cikin nurses din ta fada bacin rai yana bayyana qarara saman fuskarta. Wani kallo ya watsawa matar saboda rainin hankalin da yaji qarara cikin tambayarta,shi zai riqa yawo ne da zainab duk inda zashi yana kula da gabanta?.
Metron din data fuskanci kamar ranshi ya tabu da maganar saita dagawa nurse din hannu sannan ta dubi su saleem
"Bismillah ku zauna"
"Harda kishiyar tawa?" Ta zabura tana fadi.duk da radadin da take ciki. Dukkansu suka zuba mata ido,nurse din nan dai wadda da alama zafi gareta tace
"Bakison kishiyar taki tasan me kike ciki kikayi wasa da gabanki?"
"Ya isa hadiza" metron din ta sake fada.
Zama sukayi gaba dayansu,metron ta kallesu
"Alhaji a gaskiya duk da mu ma'aikatan lafiya ne,muna kuma ganin abubuwa kala kala amma case din matarka ya tashi hankalinmu,al'aurar matarka idan bai rube ba to yayi lalacewar da bashi da maraba da rubewa,akwai dinki a jikinta wanda bai samu kulawa ba,an barshi sasakai har ya gama farkewa gaba daya"
"Na shiga uku dinkina!" Zainab ta fada tana dora hannu saman kai kaman ma ta manta a inda take.
Idanun saleem da ya juyo ya watsa mata su wanda zuwa yanzu sun sauya launi sune suka ankarar da ita,ta kuma tuna ta yiwa kanta barna zata tonawa kanta da kanta asiri. Wannan abun kawai da tayi ya tabbatarwa da saleem ta aikata din,ta kuma yi komai ne tana sane,don haka ya maida dubansa ga metron
"Bayan ya farke kuma da alamu infection sunbi sun shiga ciki yadda sukaga dama saboda rashin tsaftar gurin,sannan da alamu akwai abubuwan da ake yabawa wajen da basu cancanci zama a wajen ba,jinin kuma dake zuba a jikinta wannan gaskiya zan turaku zuwa ga doctor nur,tana nan a hawa na farko,amma dai ina addu'a abinda nake hasashe Allah yasa ba shine ya sameta ba"
"idan ma shine ticket din data yankawa kanta kenan" ya fada qasa qasa muryarsa dauke da maqurar bacin rai.
"Idan kun gama ganin Dr nur din zatayi magana damu tabbas,amma dai yanzun na tabbatar ba wanda zai iya ganinta a haka sai an fara maganin d'iwa da jinin dake fita a jikinta,idan sun tsaya ma sannan a fuskanci ainihin ciwon da yake jikinta da farkakken