Showing 39001 words to 42000 words out of 51618 words
Chapter 14 - Gudun Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete
Tamkar gilmawar walqiya,tamkar kuma gizo sultanar taga saukar mari kan fuskar maina. Tayi muguwar razanar da har sai data miqe daga saman kujerar da take zaune a kai
"Koma ki zauna,ai tunda kike nan tu es en sécurité,bai isa yayi miki komai ba,mara gaskiya kawai,ba daka mata tsawa da hanata tona maka asiri zakayi ba,défendre kanka zakayi kaima indai kai me gaskiya ne,ka gaya mana a ina ka santa?" Koda yana da nufin masa bayani bayajin zai iya buda bakinsa a yanzu,domin wata irin wuta ce kai kawo tsakanin qirjinsa zuwa bakinsa,wani irin kallo yake jifan DPO din dashi da idanunsa da sukayi jazur kaman an masa kwalli da borkono.
"Wannan bashi da gaskiya,ku sakamin shi a bayan kanta" ya fada cikin bada umarni. Bai hanasu yi kasa komai ba don yasan kowanne motsi zaiyi a wannan lokacin to tabbas zai iya daukan mummunan hukunci akansu gaba daya saidai duk abinda zaya faru ya faru. Takalminsa suka karba agogonsa da wayoyinsa dukka suka kashe. Yana tsaye daga dakin yana kallon yadda suka rufe sultana suna mata sannu hade da sake dubata
"Ki rakata gida aicha" DPO din ya fada
"A'ah zan iya tafiya" ta fada da sauri tana satar kallon inda suka rufe maina
"Idan aka ganni da ku kowa ma zaisan me ya faru,banason mamana ta sani hankalinta zai tashi"
"Shikenan,ku kaita bakin layi" ya fadi yana sanya hularsa gami da miqewa.
A hanya sam batajin me suke cewa sai tunanin abinda ya faru a station din. Ranta ya danyi mata rashin dadi da kulleshin da sukayi,so tayi ace tunda Allah yasa sun rama mata mare maren da tasha a hannunsa su sakeshi hakanma kadai ya isa.
A bakin layin nasu suka ajeta ta taka har zuwa gida da qafarta. Tana shiga farfajiya ta biyu ta sami su lamira. Dukkansu sukayo kanta
"Su zinnira sukace wai yayankine ya tafi dake,sunce kaman yaa maina,amma shi kuma baya nan,ina kikaje har akayi aka gama baki wajen anata cigiyarki?" Kusan a jejjere suka dinga jefa mata tambayar
"Yaaya Samaila na raka wajen budurwarsa(wani dan aminin oncle bashar ne" itace amsar data basu kenan tana wucewa sashen bibi ba tare data tsaya jiran labaran da suka qullo zasu bata ba,don babu abinda labaransu zasu qara mata ta sani sai zallar bacin rai,tunda dai maina din da basusan da zuwansa ba ya bata mata ranar gaba daya.
"Allah ya sakamin" kawai take fadi duk sanda ta tuno burin da taci akan ranar amma ya wargaza komai
"Allah yasa ya sake musu taurin kanshi su sake lallasashi yadda ko ya dawo gida zai barmu mu sarara" ta kuma fadi sanda ta tube kayanta ta shiga wanka.
Wankanta tayi abinta ta shirya tsaf kamar ba abinda ya faru taci gaba da sabgoginta. Duk sanda ta tuna ya maina din yana kulle a station sai taji dariya tazo mata,musamman idan ta tuna zafin kansa tsananin tsaftarsa da qyanqyaminsa,yau ya zaiyi dasu?.
Ba wanda ta gayawa sai lamira yasmine da aminata
"Kuma wallahi wallahi naji zancan a bakin wani ko?,ni kadai nasan me zanyiwa mutum" ta fada tana zare fararen idanunta
"To waye ma zai fada?,can tsakaninku,amma ki sani wallahi duk ranar da yaa maina ya dawo taki ta sameki kin shiga uku,don wallahi bazai qyaleki ba" cewar aminata.
Duk da maganar aminata tasan gaskiya ne ta kuma ratsata amma saita murje idanunta. Dare ya fara yi tana jin bibi ta fara cigiyarsa amma tayi kunnen uwar shegu,sai ma ta nade abinta cikin blanket din da tasa tanja ta kwaso mata daga daki.
Kasa jurewa bibi tayi ta soma neman wayarsa tana fadin
"Yau kuma ina Aliyyu ya tsaya,shi da bame yawon dare ba,ba kuma wani tarin abokai gareshi ba bare nace su suka riqeshi?" Tabe baki sultana tayi tana sake cusa kanta cikin blanket
"Yau dai shalelen naku dan baqar zuciya sai kwanan magarqama" ta fada qasan zuciyarta tana lumshe idanunta hankalinta a kwance.
Tana nan a kwance ama ta aiko itama nemansa,bibi tace bata ganshi ba tunda ya fita itama nemansa take,ga dukka wayoyinsa a kashe, ba'a rufa mintuna arba'in ba ama din ta kasa daurewa ganin dare yana yin nisa ta shigo da kanta,don itama ta gaza samunsa,ta kuma tambayi su goumar ba wanda yasan ina yake.
[4/18, 10:43 PM] C.E.O HUGUMA CLOSET: *_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
Page 23
W A S H E G A R I*
Idan ka hango yadda ta takure a quryar bango ta kuma cukuikuye cinyoyin Bibi saika dauka mala'ikan daukan rai ne daura da ita. Idanunta sunyi tsilli tsilli sanda maina ke maimaita yadda komai ya faru da wata iriyar saryayyar murya. Dukkansu suna wajen banda aba da tafiya ta kamashi niamy da sassafen. Idanunshi basu kan kowa saboda suna cike ne da wasu al'amura da shi kansa baisan iyakarsu da nauyinsu ba. A karon farko da yaji yarinyar ta fice masa fit daga kanshi gaba daya.
Yana gama kaiwa qarshe shuru ya ratsa dakin,sai bibi dake sallalami tana qoqarin ture sultana daga jikinta
"Ashe fitinarki har takai haka sultana?,ki daure dan uwanki kiyi masa mummunan qazafi irin wannan?,sultana?,babanki maina yake fa?,shine yaci kashinki yaci fitsarinki fa sultana?,anya?" Bibi ta furta cikin wani fushi da bata taba kwatantashi ga sultanar ba.
Oncle umar kuwa waya ya ciro yayi kanta,saida oncle bashar ya tsaidashi da qyar
"Ka banni yau jikinta ya gaya mata,ta dauka duk cikin gidan ba'a iya dukanta ne?"
"Kada ku daketa" muryar maina da wani irin sauti ta cika falon. Waiwayawa sukayi suka dubeshi,har ya miqe tsaye ma abinsa
"Ba fyade tace zanyi mata ba?,to tabbas ta rubuta ta ajjiye NI MAINA SAI NA YI MATA FYADEN,zatasan me ake nufi da ainihin fyade"
"La'ilaha illa anta.......na shiga uku ni kubra" bibi ta fada da mugun qarfi tana zaro dukka manya idanunta waje,muryarta tana rawa
"Aliyyu,maina.....me kake fada!,maina!!" Ta qwala kiran sunansa sanda yake dab da ficewa daga falon. Bai dakata ba bare yaji me take cewa ya sanya kansa yana ficewa,ba daga falon ba daga gidanma gaba daya.
"Na shiga uku na lalace ni kubra,me yake shirin faruwa da iyalina?" Bibi ta sake fadi cikin rudewa da tashin hankali.
"Kinga bibi,kada ki wani dagi hankalinki fa"
"Kasan maina ne?,kasan duk furucin da zai furta yana nufin abinda ya fada din,kasan halinsa kaifi daya ne,kasan baya fada ya canza ko?"
"Ai bashi ya haifi kansa ba bibi" ama da sai a sannan ta samu fusgo tata nutsuwar ta fadi tana matsawa kusa da bibi din don ta taya su oncle bashar rarrashinta.
Duk yadda sukaso kwantarwa da bibi hankali ta qiya,hasalima kuka takeyi
"Ina tsoron halin maina na kafiya akan magana da cika magana idan ya fadeta,ina tsoron kada da gaske din ya lalata rayuwar marainiyar Allah"
"Ba zata faru ba bibi don Allah ki kwantar da hankalinki" ama ta sake fadi cikin nata tashin hankalin da rudanin.
Sun dauki dogon lokaci kafin su samu bibi ta tsagaita kukan,tace amma su nemo mata maina tayi magana dashi. Sam ranar maina din qin zama a gidan yayi,kamar yadda ya kama wayoyinsa duka ya kashe,bai kuma shigo gidan ba sai qarfe sha biyu saura na dare.
Yana shiga ama tana sanya qafafunta,tamkar dama tana biye dashi. A mamakance ya waiwayo yana dubanta
"Ama,bakiyi bacci ba?" Dubansa take da fuskarta a dinke tsaf
"Ta yaya kake tunanin mahaifiyar da d'anta yayi irin wannan mummunan furucin a gabanta zata iya kwanciya ta runtsa?" Tayi masa tambayar da salon da ya sanyaya masa jiki
"Zauna" ta bashi umarni kai tsaye. Bai musa ba ya koma a hankali ya zauna yana kallonta
"Aliyyu,ina dukka hankalinka da tunaninka suka tafi?,ina iliminka?,kasan illa da munin iqirarin da kayi?,ta yaya zaka dauki wuqa da kanka ka dabawa cikinka?" Ta dakata tana maida numfashi
"A gaban kowa kayi iqirari irin wannan?,inda kana da qanwa uwarku daya ubanka daya da ita wani ya fadi haka a kanta zakaji dadi?" Idanunsa ya runtse yana jin ciwon dukka kalaman a karan kansa
"Inaso ka janye wannan iqirarin,ka kuma baiwa bibi haquri,don banason ma zancan yakai kunnen mahaifinka,bana so kuma hakan ta sake faruwa ko da wasa"
"In sha Allah,kiyi haquri ama" ya fada a tausashe.
"Ya wuce,zan turo saddi da abincinka" ta fadi tana fita a dakin.
Ya jima zaune a wajen yana juya lafazin nasa,har zuwa sanda saddi ya riskeshi da karagar abincinsa cikin warmers na alfarma masu tsananin kyau kamar yadda yake kusan hakan al'adar ama ce,komai nata me kyau da tsada ne.
Ko kusa ko alama bata taba daukar kalmar SAI NA MIKI FYADE da ya maina ya furta din zata zame mata wani abun damuwa ko barazana ba,abinda kawai yafi mata dadi da bai taba lafiyarta ba ya juya kuma yabar gidan. Ga tarin mamakinta sai gashi a sanda dare ya fara yi kalmar tana dawo mata,ta rufe idanunta ta rungume nini da kyau ta kuma nutse a blanket dinta amma sai taji maganar tana dawo mata.
A hankali labarai akan fyade suka soma dawo mata cikin kwanya. Labaran da bata taba basu muhimmanci ba cikin rayuwarta,wasu ma ta mantasu sai gasu suna dawo mata daya bayan daya. Sannu a hankali tsoro taji ya fara shigarta. Tunda take bata tabajin tsoron kwana cikin dakin ba sai a yau,tanaso ta miqe ta fice ta tafi dakin bibi amma tsoron ya hanata motsi. Qarar rufe kitchen da tanja tayi tayi mugun kada mata ciki,sai zuciyarta kawai ta bata yaa maina ne yazo zaiyi abinda yace din,abinda ya qarasa firgitata ta saki qaramin ihu hade da hawaye
"Wayyo bibi,ki taimakeni" muryarta tanja dake niyyar wucewa taji,abinda ya dawo da ita kenan,ta murza qofar dakin ta bude,sai kawai sultanan ta sake rikicewa tana boye kanta qasan pillow.
Kallo daya tanja tayi mata ta lura a tsorace take
"Sultana,tanja ce" ta fada tana kamo kafadarta. Jin muryar tanja din ya sanyata watsar da nini din ta miqe da hanzari tana riqe tanjar
"Ki kaini wajen bibi" ta fadi hawaye yana kwance mata saman fuskarta.
Sosai abun ya bawa tanja mamaki,me ya sanya sultana kuka da razani haka?. Hannu ta saka ta daga sultanar
"Muje na kaiki" ta fadi ba tare data tsaya tambayarta abinda ya faru ba.
Bugu biyu sukaji muryar bibi din tana cewa su shigo. Tanja ta tura qofar ta saka sultana a gaba suka shiga.
Bibi din tana zaune saman abun sallah,da alama ta jima da idarwa ta zauna ne kawai qilan tana wani tunani na daban.
Da kallo ta bisu har sultana din ta qaraso,gaban bibi ta zauna tana kwantar da kanta saman cinyarta tana hawaye. Kanta bibi ta fara shafawa a hankali
"Nazo wucewa ne naji ihunta" mummunar faduwa gaban bibi yayi, zuciyarta ta harba tana fargabar jin statement din tanja na gaba
"Da na shiga sai naga kaman a tsorace take ta qudundune a blanket shine tace na kawota gurinki"
"Shikenan jeki tanja sai da safe"
"Allah ya bamu alkhairan" ta fadi tana juyawa ta fita a dakin ta basu waje.
Shuru ne ya biyo baya na wasu mintuna a dakin,har yanzu sultana tana kwance saman cinyar bibi. Zuciyar bibi din kuma tayi nisa wajen saqe saqen abubuwa da dama na dogon zango,sai daga bisani ta sauke ajiyar ta kuma kira sunan sultana din
"Me ya baki tsoro?" Tayi mata tambayar tanason tabbatar da abinda zuciyarta ke saqa mata.
"Ba komai" ta fada a sanyaye tana sake narkewa kan cinyarta,don ko maganar ma sai taji kamar tana qara mata razani ne. Bata qara tambayarta ba itama bibi din,sai data gama addu'o'inta sannan tace
"Tashi ki hau gado ki kwanta" zare jikinta tayi ta haura gadon bibi ta rakata da kallo tana kallon laushin da jikinta yayi.
[4/18, 10:43 PM] C.E.O HUGUMA CLOSET: *_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
PAGE 22
A hankali dare ya fara nisa ba maina ba dalilinsa,sun gwada wayarsa fiye da sau shurin masaki amma ba wani respond. Tun sunayi iya su yasu har aka saka mazan gidan iyayensa. Allah yasa aba yana gari.
Abun ya dagi hanakalin kowa saboda ba halinsa bane yin nesa da gida haka,musamman idan yana gari baya wuce sallar isha'i a waje. Sai gashi yau din har ana tunkarar biyun dare ba maina ba wayarsa ba kuma motsinsa.
Tuni sultana tayi nisa a duniyar bacci abinta,hankalinta kwance tamkar ma bata da masaniyar komai akan lamarin,koda wasa bata nuna tasan komai ba,kamar yadda su aminata suka zuba idanu suga qarshen abun. Sunsan dai qila lokacin yankewa sultana mummunan hukunci ne yazo cikin gidan.
Dukkaninsu kwanan zaune sukayi a falon bibi cikin tashin hankali. Har safiyar lahadin ba wani motsinsa ko labari,abinda ya sake tashin hankulansu
"Zaman nan bazaiyiwu ba yaaya,inaga ya kamata muyi report policestation daga can mukai cigiya gidajen radio da television,wannan shirun ba na lafiya bane" oncle umar ya fada yana miqewa
"Hakan shine zaifi dacewa,zamanmu a nan ba abinda zai maganta" oncle bashar shima ya fada
"Amma sanda ya fita bibi,baice muku zaije wani gurin ba bayan karbo dinkin?" Aba ya fadi yana duban bibi
"Nace masa dai inason nama wajen yahaya"
"Bayan can fa?bakiyi saqo ko ina ba?,don mun duba yahaya din yace yaje amma bai samu naman ba ko fita a motar baiyi ba ya juya"
"Indai haka ne to wajen yahuza nasan zaice zaije ya samomin" bibi ta fada da sauri hankalinta yana kawowa
"Shikenan,bari mu bincika can din,daga nan idan bamu samu komai ba akai saimu qarasa policestation din mu bada cigiya". Da wannan shawarar oncle bashar da oncle umar suka fice,yayin da sukaci gaba da zaman dakon jiran abinda zai faru cikin gidan. Sultana nacan kwance tana sheqa baccin safiya hankali kwance,tana jin kamar ta fidda qaya daga gidan.
Suna isa yahuza yana qoqarin wanke gurin sana'ar tasa. Duk da bai sansu ba amma yana ganinsu yasan cewa manyan mutane. Cikin rawar jiki yayi musu iso zuwa cikin ainihin rumfar tasa
"Akwai yaro Aliyyu dake zuwa wajenka siyan nama"
"Aliyyu?" Ya fada da dan tambaya
"Eh,maina ba" oncle bashar ya maimaita mishi
"Oh to....naji naji,jikan bibi.....aiko jiya ma yazo gurin nan siyan mata nama"
"Yauwa,madalla,abinda mukeson ji kenan dama,yaushe yabar wajen?,don tun jiya bai koma gida ba" zaro ido yahuza yayi cikin tsoro
"Bai jima ba na sallameshi,ya matsa kusa da policestation dincan yace zai dauki abun hawansa,duk da naga jama'a da dama a wajen,da alama wani case din aka kawo ko wata rigimar akeyi,don naji mutane na zancan an kama me fyade da satar mutane" yahuza ya zarce da bada bayanin da ba'a tambayeshi ba
"Akwai policestation kenan anan kusa?" Oncle umar ya tambaya. Jinjina kai yahuza yayi
"Gata can" ya furta yana musu nuni da ita". Waiwayawa sukayi dukkansu suka kalleta. Oncle umar ya fara miqewa
"To ai ta kwana gidan sauqi,inaga saimu qarasa mu bada report tunda dai bincike ya nuna daga nan guraren aka rasa kuma ina yayi"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,Allah ya bayyana,Allah ya bayyanashi" yahuza ya furta cikin madaukakin jimami,duk da yanaji a jikinsa bawai bata maina din yayi ba,yafi kyautata zaton kawai ya tafi shan iskarsa ne,tunda ta yaya sankacecen matashi majiyin qarfi irin maina din za'a iya saceshi kamar wani kaya?.
Tare suka gangara a qasa har zuwa cikin policestation din suna tattauna yadda zata kasance. Sanda suka isa gurin 'yan sanda hudu suka taras saman kanta suna hira abinsu.
"Cigiya mukazo bayarwa na yaronmu da ya bata jiya" oncle bashar ya fada yana kallon dan sandan
"To bismillah,ku zauna yallabai" ya fadi cikin girmamawa saboda kwarjinin da sukayi masa,uwa uba kuma dukka alamu sun nuna cewa su din wasu manya ne cikin nijer din.
"Kai......sanda.....zo ka taho mini da abun rubutu,oga yace wannan yaron idan aka kai azahar baice komai ba a fara tuhumarsa,don ya fuskanci girman kai aggareshi me yawa,sai an sauke mishi shi" dan sandan da ya bawa su aba masauki ya fada da qatuwar muryarsa me kauri da cika kunnuwa.
"Ya lamarin ya kasance yallabai?,inajin da kaina zan shiga na daki yaronnan yadda yakewa mutane gani gani tun jiya,yaqi bada tarho din kowa bare a nemi yan uwansa,da alama dai da gasken bashi da gaskiya"
"Ku dinga bi a hankali