Showing 24001 words to 27000 words out of 51618 words
Chapter 9 - Gudun Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete
dake cike da tsiwa ta isa ga kunnuwansu tana rera waqar ado isa gwanja
_Allah ka aika munafukinmu qarshen nesa,tafiyar qasa koda lafiya ko babu,kaishi garin da ko kuyanga babu,barshi a can da arziqi ko babu,ni nasha tabara nasha yasin,kuma nasha rigakafin alatsine_ . Sai ta juya zuwa waqar wani mawaqin qasarsu ta nijer
_Munafuki Alla kasheshi,koda safe koda rana ko ma dare ne_
Tana maganar ne kanta yana kallon lobby na dakunansu tana kuma nufar can,tamkar batasan da zaman mutane a wajen ba.
Mutuwar zaune bibi tayi,ana kukan targade ga karaya ta samu,ana neman gyara ga sabon ruwa ya ballo. Ko waye kai,komai girmanka muddin ba iyayensa ba baka isa ka ratsa waje bakayi masa sallama ba,kamar yadda duk yadda yake da buqatar shiga guri muddin ba'a amsa sallamarsa an kuma masa izini ba yana juyawa ne ya koma inda ya fito. Wannan ya samu asali ne daga cikakken karatu da tarbiyyar daya samu daga islamic school din da yayi masu kyau a Nigeria.
Har ta kusa shigewa ya kirayeta cikin tsawa,kaman ta wuce ciki sai narkakken tsoronsa dinnan da take qoqarin binnewa ya motsa mata. Tunga taja ta tsaya kana ta waiwayo tana dubansu ba tare data iso inda suke ba
"Koma ki yima mutane sallama" idanunta masu kama da digon zaiba ta dan juya tana bata fuskarta,ta motsa qaramin bakinta dake cike da tsiwa tace
"Nifa na riga nayi sallamata ehe" daga wannan ta juya tana shirin wucewa dakin tare da sake maimato waqoqinta a sarari sosai saboda saqon ya isa gareshi.
Wata baqar zuciya ce ta motsa masa,tabbas sultana dashi take,shi takewa wadannan waqoqin. Uwa uba yau shine zaiyi mata magana tasa qafa ta shure?,tama maidashi mahaukaci?.
Daga sultana har bibi babu wanda yasan lokacin da ya isa dakin. Dai dai sanda take wurgi da komai na makarantarta kamar yadda ta saba tana sake sakin waqoqinta cikin harshen faransanci,ranta fes tana jin ta fara samun nasarar rage haushinsa cikin ranta.
Cire hijabinta yayi daidai da dauketa da marin da yayi,babban dukansa shine marin,bai iya wani duka ba idan ransa ya baci bayan shi. Sanin darajar da fuska take da shi ya sanya bai cika yin dukan ba,zaiyi wuya kaga ya daki wani cikin qannensa,amma wajen iya bada horo su kansu sun tabbatar babu na biyunshi kaf cikin family.
Wata irin gigitacciyar qara ta saki tana dafe kuncinta da hannayenta bibbiyu ba tare data fuskanci meye ya sameta ba. Sautin muryarsa saman kanta kwanyarta tayi saurin ingizo mata me yake faruwa da ita,saidai kafin ta gama daidaita tunaninta ya sake aje mata wani Marin hade da qatotuwar tambayar da batasan da wanne zataji ba,marin ko amsa masa tambayarsa
"Saikin gayamin wanene munafukin cikin gidan nan" yayi maganar yana zare belt din dake jikinsa. Dukka jikinta rawa ya fara yi,saboda ganin fushi muraran saman fuskarsa,uwa uba tunda take bazatace ga ranar da aka sanya madoki aka daketa ba,shine ma mutum na farko kaf fadin rayuwarta da ya taba taba lafiyarta tunda tazo duniya,wannan ya sanya take matuqar razana duk sa'ilin da ya shimfide mata dogayen yatsunsa saman fuskarta
"Waye munafukin nace?!" Ya maimaita tambayarsa yana ware mata lion eyes dinsa da suka sake gigitata,sai ta ware dukka muryarta tana qwalawa bibi da tanja kira
"Wayyo Allah na bibi,zai kasheni,zai kasheni,wayyo na shiga uku"
Yatsansa ya dora saman lips dinsa yana sake fidda mata idanunsa dake danqare da bacin rai
"Kika sake buda bakinki a nan sai na miki dukan da ba zaki qara iya daga yatsarki ba,tais toi idiot(shut up idiot)!" Ya qarasa fadi a tsawace. Dole qanwar naqi ta sakaya ihunta,duk da tana jiyo bibi na bugun qofar hadi da kiran sunanshi da bashi umarnin ya bude,saidai kuma bata da ikon cewa komai.
Stool dinta ya jawo ya zauna a gabanta,ta qanqame jikinta guri daya tamkar me jin sanyi. Ba sanyi takeji ba,tsantsar tsoro ne ya sanya jikinta ke shivering,amma batason yaga hakan daga gareta,hawaye kwance saman fuskarta,ilahirin fuskar tata radadi take mata
"A frère dinki kika sanni ko?,to daga yau ki saka a ranki maina nake a wajenki kamar yadda nake a wajen kowa na gidan nan,zan fiddo miki ainihin kalata tunda na fuskanci kin zama graduate a fannin rashin kunya
[4/18, 10:43 PM] C.E.O HUGUMA CLOSET: *_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
PAGE 14
"Dago kanki ki kalleni!" Ya gaya mata da wata a tsawace
"Baki isa kifi qarfin kowa a gidan nan ba,idan ma kinfi qarfin nasu ne ni bakifi qarfina ba,zan iya tattakaki nayi miki dukan da ba'a taba yi miki irinsa ba kuma babu abinda zai faru,daga yau zan kafa miki dokokin da idan kika tsallake guda daya a cikinsu ki tabbatar da kin shiga uku" ya fada yana murza yatsunsa. Idanunta ta runtse tana jin sautin yatsun nasa,wani sabon hawayen ya balle mata,yau ita ya maina yake yiwa haka?,ita ya sanya a gaba yake yiwa wannaj tijarar?,ita ya yiwa irin wannan titsiyen da babu mahalukin da ya taba yi mata irinsa?.
Kimanin minti talatin yana gindaya mata sharudda da qa'idoji,sultana din tana zaune a gabansa ba tare data motsa ko ta furta komai ba. Duka maganganunsa basuyi tasirin komai a ranta ba face wani mugun qulli data yi masa,haushi da tsanarsa na ratsata.
"Kinji dukka abinda nace?" Ya tambayeta da kakkausar muryarsa. Kai ta gyada masa idanunta suna mata wani mugun radadi
"dis-le plus fort(ki daga murya ki fada)!" Ya fadi a kausashe
"Eh" ta amsa da dakusashiyar muryarta.
Da wani mummunan kallo tabi bayansa,tana jin kamar ta bishi tayi masa mugun duka, idanunta tamkar zasu fado har ya fice. Hannuwanta biyu ta saka tana shafar fuskarta. Maruka hudu cikin qanqanin lokaci?,bata taba sanin haka mari yake da tsananin zafi ba sai yanzu tunda baby wata halitta data taba dora mata hannunta saman jikinta da sunan duka sai shi.Dama haka mutumin da aka mara yakeji?,tambayar ta taho mata da tawagar hawaye suka zuwa saman fuskarta.
Daga tanja har bibi taqi kula kowa,juyin duniya amma funfurus taqi tace komai,sai hawaye da taketa yi babu qaqqautawa. Duk wani abu da bibi keyi mata ita ta yiwa kanta shi. A wannan yanayin lokacin tafiya islamiyya yana yi ta shirya. Yana daya daga cikin dokokin da ya kafa mata,bata jira kowa ba ta yiwa driver dinta magana yayi gaba da ita. Saidai ko da suka isa makarantar babu abinda ta tsinana sai kwanciya,har akayi karatun aka gama babu abinda ta maida hankali ta fahimta.
K'arfe takwas na dare tana nade cikin blanket saboda busawar sanyi da aka fara samu lamira ta shigo dakin. Dan kallonta tayi ranta yana mata sanyi da yadda yaa maina din ya sanya sultana din tayi laushi a yau
"Kije ya maina yana kiranki a parloir" sai data hadiye wani abu cikin wuyanta sannan ta bude dara daran fararen idanunta tana kallon lamira da kyau,tanason zazzage masa masifa da tsiwar data cika mata qirji tun safe to amma batason dogon magana a yadda take a fusacen.
Har lamira takai qofa sultana batace komai ba,sai lamira din ta dakata
"Yace ki taho da manuels et cahiers d'exercices naki" faduwa taji gabanta yayi a karon farko,sai ta kauda kai still dai babu abinda tace din har lamiran ta fice.
Kaman ba zata tashi ba sai kuma ta miqe. Jakar makarantarta ta jawo dukka biyun islamiyya da boko ta fara zazzage litattafan ciki gaba daya.
A sanyaye ta bisu da kallo daya bayan daya tamkar yau ta fara ganinsu. Akwai qura tabbas! Shine abinda zuciyarta ta raya mata.
*_DA ALAMA YAU AKWAI TONON SILILI_*😂
Cikin qwarin gwiwar nan da taurin rai da zuciyarta ke bata a ko yaushe ta miqe da littafan cikin kyakkyawar handbag dinta,wadda tsara ba cikin tsarabar da aba keyi mata duk sanda zaiyi tafiya kamar babu gobe.
Har ta kusa da bakin qofa ta tuna da kayan da suke jikinta. Kallon kanta tayi,shirt ne da wandon leggings da suka bi lafiyar jikinta,suka kuma yi mata matuqar kyau kamar baby doll. Tana da wata irin qirar kyakkyawan jiki da shape me kyau tun tana da qananun shekaru sosai. Tsaki taja kamar zata tsinke harshenta,tana jin kamar ta yita dukan maina a yau din nan,ta juya ta koma dakin tana qunaquni
"Haka kawai a wani dameka,tsabar rainin wayo,ko meye na tare masa oho" tayi maganar tana zuge closet dinta.
Lalube lalube ta shiga yi saboda batasan ainihin muhallin da kowanne kaya nata yake ba,tunda ko meye zata saka tanja ke ciro mata,hakanan idan aka kammala wanki da gugansu ita dince dai ke sake zaman shiryasu fes. Kafin wani lokaci ta gaji tubus,sai ta koma bakin gado ta zauna tana haki kamar zata fashe da kuka
"Tanja!" Ta bude siririyar muryarta tana kiranta,abinda ta kwana biyu batayi ba kenan,don tun wancan ranar takejin haushinsu,ta kebe kanta daban,a cewarta sunaji sanda maina din ya tsintstsinka mata mari,ya kuma sanyata a daki zai kasheta,amma ba wanda ya qwaceta har sai da yayi iya yinsa ya qare.
"Tanja....tanja.....tanja" ta sake jero sunayenta a jere.
"Na'am na'am uwaddaki" ta amsa tana shigowa da dan saurinta.
Closet sultana ta nuna mata da yatsa
"Ina jilbab dina suke?"
"Na'am?" Tanjan ta tambaya cikin mamaki,saboda ita dai iya tsahon zamanta da sultanar shine abinda bata taba tambaya cikin sutura ba,ko da mayafi ma yana iya qare zamaninsa a cikin kayanta bata waiwayeshi ba, za'a iya siyoshi ya gama zamansa yakai lokacin badawa a bayar dashi yana sabo
"Allah tanja kin jini sarai,ku dama kullum kunfison baqincikina" ta fada qwalla na cika shiny eyes dinta.
Tanja batace komai ba ta matsa ga closet din ta bude. Sai gata ta fiddo jilbab din sabo kar onion color ta miqa mata,sai tayi tsaye tana dubanta.
Kasa sakawa tayi saboda gaba daya ya dabaibayeta,ta yita juyashi cikin jikinta tana sakin tsaki,tanja na tsaye dariya tana kamata amma ta kanne.
Da gasken ta kasa sakawa,sai kawai ta yageshi ya wurgar tana sakin kuka gami da komawa ta zauna
"Allah sai Allah ya sakamin tsakanina da ya maina,duk shi ya jazamin wannan aikin,Allah ka sakamin" ta fada cikin rawar muryar kuka.
"Tashi ki gani kinji" tanja ta fada tana dauko hijabin. Kamar ba zata tashin ba to amma idan ta tuna qarawa kanta mintuna takeyi daga mintunan da yasa akayi kiranta sai ta miqe din.
Tsaf tanja ta saka mata ta kuma daure mata kan
"Ma sha Allah,fatabarakallahu ahsanul khaliqin" tanja ta fadi tana murmushi. Wani mugun kyau fuskarta tayi cikin hijabin,tanjan tana iya cewa bata taba ganin tayi mata kyau cikin sutura ba irin haka. Tamkar wata diyar larabawa,kyakkyawar fuskarnan dake dauke da quruciya da qarancin shekaru ta fita sosai tsakiyar hijabin.
"Uwaddaki,ya miki kyau wallahi tallahi" tanja ta fada tana dariya. Harara sultana ta jefa mata,sannan ta tura baki gaba tana kwasar litattafanta ta fice,a zuciyarta tana jin cewa tanja tana mata ba'a ce kawai zaginta takeyi,ina wani kyau a nan?.
[4/18, 10:43 PM] C.E.O HUGUMA CLOSET: *_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
PAGE 15
Tana riqe da litattafan da takeji kamar ta watsar da su tayi ta sanya kai falonsa. Da sauri ta koma da baya sannan tayi sallama tana jin ranta yana baci.
Kansa ya dago daga duba wani littafi dake riqe cikin hannunsa suka hada idanu. Gabanta ya fadi,nutsuwa da tsoron da batasan daga ina suke ba suka saukar mata.
"Wa'alaikummus salam" ya amsa mata yana maida kansa ga littafin. A nutse tattako ta qaraso ta nemi waje ta zauna,cikin sanda ta ajjiye litattafan tana satar kallonsa. Sai data kusa minti biyar a zaune sannan ya ajjiye littafin a gefe,ya miqa hannu ya jawo litattafan nata ya fara dubawa.
Tun da can yasan ba wani abun arziqi zai taras ba,amma abinda ya gani na yau din ya zarce na kullum muni
"Ba arabi ba boko?" Ya daga kai yana jefa mata tambayar da wani irin yanayi dake nuna bacin ransa da kuma mamaki
"Gaskiya mana,dole kije ki zauna kiq zuwa da wuri" ya sake maimaitawa yana jin kamar ya tashi ya zaneta da kyau.
Sake maida dubansa yayi yana sake nazartar littafan,assignment homework harma da classwork kowanne mark dinta zero ne. Littafin haddarta ta islamiyya ba komai akai sai tsalli tsallin ayoyi. Littafin assignment na islamiyya kam blank ne ma,ga question a rubuce amma babu digon amsa ko daya sai sararin gurin.
Wani bahagon tsaki yaja ya maidasu ya rufe,ya tabbatar idan yaci gaba da dubawar sanda zai tsinka mata mari ka bai sani ba,mafi alkhairi shine ya rufe din.
Tambayoyi ya fara jero mata daya bayan daya,saidai bata da amsar kowacce tambaya daga islamiyya har bokon,cikin tambaya ashirin da qyar take iya amsa daya
"Ya rahman" ya fada yana lumshe kyawawan zagayayyun idanunsa da suka soma kadawa. Gaba daya babu komai a kanta,duk wani gini da ya fara mata a baya babu shi. Ta zama bata gane komai a yanzun,lallai wani sabon aikinne a gabansa. Sai yaji gaba daya komawa niamy tanason ta sake barin jiki da ransa,saidai kuma shi kansa yasan hakan bame yiwa bane, karatunshi ya riga ya fara nisa,karatu me wahala da tsada,a gefe guda kuma daukar irin wannan mataki dai dai yake da shiga rigima da ama,gwara aba zai iya fuskantarsa ya bashi uzuri,amma baijin amma zata fahimta kwata kwata,musamman da zai zama batun akan sultana ne.
Zama yayi sosai ya bata lokacinsa ya zana musu jadawalin karatu,lokutta ya zaba na daban da yake available a gida,itama kuma bata komai a sannan. Sanda ya gama ya bata takardar karba tayi kawai ta kalla
"Kan bala'i" ta fada tana jinjina qoqarinsa. Ita zaiwa wannan tsarin karatun?,don ya hanata walwala ko meye?,itakam ba zata taba lamunta wai wani karatu ya shiga rayuwarta ba,akan meye?,bayan ba wani abu da karatun zai tsinana mata,haka ta miqe ta tattara littattafan nata da tarin assignment jingim da ya bata.
Ko takan litattafan bata sake bi ba ta shiga sabgoginta,a tsakanin juma'a zuwa asabar ya bata ayyukan,kuma ba zasu sake zama karatun ba sai litinin. Bata tashi tunawa ba sai ranar lahadi da daddare,a take idanu ya raina fata,ta dauko litattafan amma ta kasa gane komai,sai taja tsaki tana watsar da littafan ta koma ta kwanta,cikin ranta tana qissima yadda zata kaucewa zaman karatun a washegari.
Lallabawa tayi ta fice dab da magariba data fuskanci yaa maina din yana nan,kuma tayi imani sai anyi zaman karatun,wannan ya sanyata ta shirya abinta ta sulale ta fice ko bibi bata sani ba.
Gidansu muhsee ta wuce,daya daga cikin abokanta da gidansu ke bayan layinsu. Ranta fes ba wani fargaba ko tunanin girman laifin data aikata take wucewa kai tsaye zuwa gidan.
Kidan dake tashi a harabar gidan nasu shine ya baxu har wajen gidan. Ta saki murmushi tana jin dadi cikin ranta,ta kwana biyu batayi rawa ba yau zata motsa jikinta yadda ya kamata. Qafafunta har qaiqayi sukeyi mata. Yaune birthday din muhsee,sanda ya tura mata invitation bata taba tsammanin zata samu halarta ba saboda yadda yaa maina din ya matse komai,ya hanata sak ya hanata rawar gaban hantsi,daga islamiyya sai boko,sai kuma tarin assignment din da ya hadata dashi wanda ko yaya ya ganta zaune bata komai tambaya ce akan
"Shin kin gama duk ayyukanki da kika samu guri kika zauna kina raba ido?" Wannan kusan itace tambayarsa ga kowanne yaro ma gidan duk sanda ya ganshi a zaune,muddin yana daukan karatu