Showing 6001 words to 9000 words out of 51618 words

Chapter 3 - Gudun Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete

min télécommande(remote)" cikin girmamawa ta rusuna ta juya ta isa ma'ajiyarsa ta dauko ta miqa masa.

Channel ya canza gaba daya,zuciyarsa na wani irin quna da zafi,babu abinda yafi tsana a duniya a yanzu irin kalmar FYAƊE. A duk lokacin da aka haska wani mutum dauke da laifin fyaɗe,yakanji inama za'a bashi damar hukuntashi,tabbas idan har ace zaya samu irin wannan damar,zaiyi masa hukunci ne mafi tsanani,wanda ko mace akace masa gata zai yanka da gudu ne ya gusa daga wajen,sakamakon azabar da shi daya yasan yadda take da zai ɗanɗana a hannunsa. Harshensa har ɗaci yakeyi sanda ya buɗe baki yana magana da bibi

"majorité ire iren wadan nan abubuwan akwai sakacinmu dake haifar dasu"

"ƙwarai kuwa,wasu abubuwan kuma ƙaddarar bawa ce daga sarkin mabuwayi" gama maganar bibi yayi dai dai da fitowar sultana. Da ido bibi ta bita tana kallon yadda fuskarta tayi jazur,sai kawai ta miqe a hankali tana sauka daga gurin dining din,abinda ya sanya sultana tsaiwa cak tana kallon bibi din,don ita ba zata yarda ta barsu a wajen daga ita saishi ba,ya sake taba lafiyarta ba gaira ba dalili

"Ina kuma zaki tafi bibi?" Ta tambayeta tana karya wuya,hawaye nason taruwa cikin idanunta

"Qaraso ki zauna" maina da idanunsa yake kanta ya fadi,fuskarsa a matuqar hade,abinda zai alamta maka babu wasa ko misqala zarratin a tattare da shi. Duban cikin idanunsa tayi,niyyarta tace ba zata zauna din ba,to amma kuma sai kalmar ta maqale mata saman harshenta. Kamar ba zata qaraso din ba,amma yadda kaifaffun idanunsa suka ritsata ya sanya ta sauya akalarta zuwa inda yake mata umarnin,zuciyarta kamar zata fashe,duk wani qaunar da take masa taji ta fara raguwa sosai cikin ranta,sai wani haushinsa da takeji. Tana matuqar qaunar lafiyarta,hakanan bata qaunar duk abinda zai taba mata lafiyar. Karo na uku kenan ana sauya mata makaranta saboda attempting din dukanta da aka taba yi sau daya a kowacce makaranta.

Tsaki yaja dai dai sanda ta zauna saman kujerar,ta dafe hannunta tana saman kujerar tana gyara zamanta sosai saboda qafafunta ba zasu kai qasa ba,duk da tana cikin sahun yara masu tsaho. Tsakinsa ya sake qular da ita tare da bata haushi sosai,sai ta juyar da kanta gefe tana murguda bakinta tare da sakin qananun surutai qasa qasa.

"Duba nan" ya fada yana tattara dubansa a kanta. Tilas tabar kallon hagunta ta dawo da kallonta zuwa gareshi

"Wannan kayan.......ban hanaku sakasu ba?,kun dauka a french muke?" Ya tambayeta a kausashe,har cikin ransa yana jin haushi da takaici. Zuwa lokacin alamomin girma sun fara bayyana a jikinta,tana da girman jiki wanda yake da saurin bayyanar da girman d'iya mace,hakan kuma yasan yana da alaqa da rayuwar jin dadi da tsantsar kula da jikinta ke samu na dukkan wani abu da zai inganta lafiyar jiki data fata ya kuma tabbatar da girma na dan adam a lokaci qanqani. Ya sani kusan da madara aka raineta,har ya tafi akan shan madara ya barta,duk da bashi da tabbacin har yanzu tana sha?,yana ji a jikinsa ma lokaci yayi da zata ajjiye duk wasu dabi'u na quruciya,ta fuskanci girma wanda yake dab da iso mata.

"Last zuwan ama Nigeria na qarshe ta kawowa kowaccenku wadatattun atamfofi da zata dinka,sannan dukkaninku kuna da abaya wadatacciya,wannan shine gargadi na farko kuma na qarshe,kada na sake ganinki da irin wadan nan kayan a jikinki" ya fada yana kallon idanuwanta.



*ZAFAFA BIYAR FAMILY*🫂🫂🫂🫂🫂

🔥 *me kike jira ne da har yanzu baki shige ahalin zafafa ba*

*_ZAFAFA BIYAR_*❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥


❤‍🔥 *_SABUWAR SHEKARA_*

❤‍🔥 *_SABON TSARI_*

❤‍🔥 *_SABBIN LABARAI_*


❤‍🔥 *_TSUMAMMIYAR SOYAYYA_*

❤‍🔥 *_CAKWAKIYA_*

❤‍🔥 *_LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DAKE TAFE DA WANI IRIN SALO_*

❤‍🔥 *_SALON DAKE DAUKE DA ZALLAR GOGEWA DA QWAREWA WAJEN SARRAFA ALQALUMA_*

❤‍🔥 *LABARANSU NA MUSAMMAN NE DAKE DAUKE DA WANI IRIN SALO ME RATSA JIKI_*

*_KWANTAR DA ZUCIYA_*

*_CIRE DAMUWA DA SABUNTA SOYAYYAR MASOYA_*

*QAWATATTU KUMA TSARARRUN LABARAN 2024 DIN SUNE KAMAR HAKA*


*KWANKWASON JIMINA* _ME WUYAR TABAWA_ (miss xoxo)

*TSUTSAR NAMA* _ITAMA NAMA CE_ (Billynabdul)

*AMEENATU* (Mamuhghee)

*GUDUN K'ADDARA* _GUZURIN TARAS DA ITA_ (Huguma)


*_KOWANNE LABARI NA DAUKE DA SUNA ME HARSHEN DAMO,KAMAR YADDA GUNDARIN LABARIN KE DAUKE DA SALON DA ALQALUMAN ZAFAFA BIYAR NE KADAI ZAI WARWARE MUKU SHI_*

*_Biya naki ta wadannan lambobin domin ki zamo cikin ZAFAFA FAMILY HOUSE_*

*TSARIN SHINE KAMAR HAKA*


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*THANKS FOR CHOOSING US*🫂🫂🫂🫂
*_GUDUN KADDARA_*


*HUGUMA*

Page 04


https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr


Haushi kamar zai kasheta,wai shikam yaa maina yana kallonta ne har yanzu a little sultana da ya bari shekara hudu baya?,itafa ba zata dauki ire iren wadan nan abubuwan ba bayan tana kallon yadda sauran qawayenta na makaranta ke rayuwarsu cikin 'yanci. Kaf cikinsu ma bataga me saka wata aba wai atamfa ba,meye hadinsu ma da ita?,sai ita zai bullowa da sabon tsarin doka?.

"Ni ban iya daura zane ba" ta amsa masa tana turo baki manyan fararen idanunta na kallon shinfidadden gilashin dining din,ji takeyi kaman ta mangareshi,har yanzu tana jin radadin marinsa akan fuskarta.

'Dan dukan table din yayi da tafin hannunsa

"regarder(look),ki iya ko baki iya ba duka zaki koya ne,muddin kinaso kiga ainihin mainassara kici gaba da yimin musu da kuma dan banzan kafiya da taurin kan da kika koyo"

"Kai kuma shegiyar masifa da bala'i da baqinciki da bacin rai kamar tsohon kuturu" ta fada cikin ranta. Baiji abinda tace ba,amma yaga sanda jajayen lips dinta suke motsawa

"Me kika ce?" Ya jefa mata tambayar data kusa sakata fadowa daga kan kujerar da take zaune akai din. Da sauri ta daga fararen idanunta ta kalleshi dasu tana motsa baki

'"ni?,ni bance komai ba" idanunsa ya lumshe kadan ya budesu. Ya tabbatar tayi magana,akwai abinda tace,amma cikin sabon halin da ya fuskanci ta sake kota koya harda iya fadin qarya kanta tsaye. Bayajin zaiyi wuya ya sake tafiya niamy haka ya zauna,gwara duk sati ya dinga tahowa maradi yana hutun qarshen makonsa a nan.

"Dauki abinci kici" ya fada yana nuna mata tsadaddun warmers din dake jere saman dining din

"Mari!,mari!!" Ta fara qwala kiran sunan kamar zata saki kuka. Da kallo ya bita yadda ta narke kamar me ciwo tana kiran sunan mai aiki,tana nufin ita zata zuba mata kenan,zubawar ma bata iyawa?.

"Ya isa haka karki kashemin dodon kunne" ya fada yana wurga mata wata iriyar harara wadda bata taba ganin ya mata irinta ba. Da kallo ta bishi ranta yana baci,sai taji idanunta na marmarin juyewa itama ta mayar masa da hararar da yayi mata din,to amma yana kallonta ta dauke kanta gefe,zuciyarta tana sakeyin zafi,haushinsa na sake cikata

"Nidai wallah ba zai takuramin ba,mutum ba ubanka ba ba komi ba" ta fada qasan ranta.

Plate din ya tura mata maimakon ya jawoshi gabansa ya dinga bata a baki har sai tace ta qoshi kamar yadda ya sabar mata a shekarun baya. Cikin ransa da zuciyarsa yakejin dole ya janye ya kuma rage dukkan wata kulawa da damuwa da yake nuna mata,domin ya fahimci aiki ne jajur a gabansa wajen maido sultana din kan hanya. Don girma ta fara girma,jikinta ma ya nuna hakan,a wannan gabar idan bai tsaya mata sa zafi zafinsa ba a haka zataci gaba da girma a sangarce,bayan kuma gidan wani za'a kaita,ya yiwa nafissa adalci idan hakan ta faru?.

"Oya bismillah" ya fada yana sake turbune fuska,idanunsa akan wayarsa dake ringing. Zai daga ta katse,sai kuma sautin sallama daga can bakin qofa.

Matashin saurayine wanda shekarunsa ba zasu haura sha biyar ba,dogo ne fari,kansa dauke da nannadaddiyar sumar nan ta abzinawa. A fusge yake kama da maina,saidai kuma idan ka kalleshi da kyau zaka fahimci akwai banbacin kamannin.

"Ya maina,ama tana kira" ya fada idanunsa akan fuskar sultana wadda ke kallon abincin gabanta kamar taga wani abun tsoro,fuskar nan a dagule da bacin rai

"D'accord,allons-y(alright, let's go)" miqewa yayi yana gyara shirt dinsa data tattare yana kuma sauke hannun rigarsa da yayi rolling up zuwa gwiwar hannunsa

"Kada na dawo na samu komai a ciki" ya qarashe maganar yana sauke mata kallonsa sai kuma ya dauke kai yana sauka daga dining area din ya nufi qofa.

Da idanu yaron ya bishi,kamar shima jiran fitarsa yakeyi ya dawo da dubansa kan sultana,ya saki dariya yana tattakowa da hanzari zuwa wajenta. Kafin ya iso ta miqe tsaye ma tana shirin barin wajen ba tare da ta sakawa abincin koda yatsarta ba


"Albishirinki,examens lundi(exams monday)" ya fadi yana dariya saboda sanayyar da yayi mata da tsantsar gabar da takewa makaranta.

Harara ta watsa masa kamar zata fiddo fararen idanunta waje

"Kada ka sakemin maganar examens,bazanyi ba,bazanje école(school)din ba munafuki" ta qarasa fada tana murguda masa baki. Dariya ya sheqe da ita sosai,SADDI mutumin sultana ne qwarai,saidai kuma zaman nasu ayi fada ayi dadi. Yasan duk abinda takeso shi yasa suke shiri,hakanan yana da tarin tsokana da calikanci wanda shike hadasu fada da sultana,saboda ita ba kasafai takeson tsokana ba,saidai akwai dan banzan surutu kamar yadda saddi yake da shi,shi yasa tasu tazo daya da ita sosai.

Waqe ya fara yi mata na gobe ranar makaranta ce cikin harshen farasanci,bata waiwayo ta dubeshi ba bare ta kulashi,saboda bacin ran maina kawai yau ya isheta takaici.

Dakinta ta shige ta kulle abinta tayi kwanciyarta,ko madararta data zame mata qa'idar sha duk dare bata nema ba a yau,don batason ma yazo ya isketa ya sake shiga rayuwarta ya bata ranta.

Tana jin tanja me kula da ita ta musamman da aka ware mata na buga qofa tayi banza da ita. A qalla ta kusa minti talatin tana bugu akan ta bude mata zata shigo ta shirya mata uniform da sauran tarkacen kayan tafiyarta makaranta kamar yadda ta saba duk ranar Sunday war haka amma tayi kunnen uwar shegu da ita har ta gaji tace

"Idan ma bakison zuwa makarantar ne to ki tashi ga láit(madara)dinki,ki kuma yi wanka ki canza kayan kwanciya" hararar qofar tayi ta sake juyawa abinta tana riqe game dinta da kyau tare da sake shiga next level na game din.

Game ce da tayi mugun shiga rayuwarta,muddin kanason ganin nutsuwarta da walwalarta to idan tana yin game dinne,tana bata lokaci da nutsuwarta irin wadda karatunta bai samu koda rabin rabinta ba. Ganin da gaske ba zata bude ko ta magantu ba ya sanya tanja ta haqura. A hanya sukaci karo da bibi

"Ta kwamta ne mutunniyar?" Bibi dake fitowa a kitchen ita da ammara ta fadi tana duban tanja

"Wallahi bibi ta qiya ta bude koda qofar ma,ni zato ma nakeyi fa tayi bacci,da maina zan kira ko zata bude idan ta jishi"

"A'ah,barshi tanja,dama yau sun hau sama sun fado da ita" ido tanja ta zaro,ba ita bama hatta da ammara sai data zare idon itama,kowanne mamaki yana ratsashi.

"Dama akwai ranar da yaa maina zai sab'a da sultana?" Ammara ta riga tanja tambayar bibi. Kai bibi ta kada tana yin gaba,ita kanta ta jinjina al'amarin,koda fada bata zaci maina zai iya daukewa a yiwa sultana a gabansa ba,sai gashi har shine da sanya yatsunsa guda biyar saman fuskarta,abinda ba'a taba yiwa sultana din ba.

Yadda bibi tayi gaba bata amsa musu ba yasa suka kalli juna

"Tabdijan" ammara ta fada,sai ta soma takawa tabi bayan bibi riqe da plate din appale din da aka wanke aka dora siririyar wuqa a kai. Dole tanja taja qafafunta cikin tsananin mamaki itama tana bullewa zuwa babban boys quaters din da ya kasance muhallin 'yan aikin gidan.


*ZAFAFA BIYAR FAMILY*🫂🫂🫂🫂🫂

🔥 *me kike jira ne da har yanzu baki shige ahalin zafafa ba*

*_ZAFAFA BIYAR_*❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥


❤‍🔥 *_SABUWAR SHEKARA_*

❤‍🔥 *_SABON TSARI_*

❤‍🔥 *_SABBIN LABARAI_*


❤‍🔥 *_TSUMAMMIYAR SOYAYYA_*

❤‍🔥 *_CAKWAKIYA_*

❤‍🔥 *_LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DAKE TAFE DA WANI IRIN SALO_*

❤‍🔥 *_SALON DAKE DAUKE DA ZALLAR GOGEWA DA QWAREWA WAJEN SARRAFA ALQALUMA_*

❤‍🔥 *LABARANSU NA MUSAMMAN NE DAKE DAUKE DA WANI IRIN SALO ME RATSA JIKI_*

*_KWANTAR DA ZUCIYA_*

*_CIRE DAMUWA DA SABUNTA SOYAYYAR MASOYA_*

*QAWATATTU KUMA TSARARRUN LABARAN 2024 DIN SUNE KAMAR HAKA*


*KWANKWASON JIMINA* _ME WUYAR TABAWA_ (miss xoxo)

*TSUTSAR NAMA* _ITAMA NAMA CE_ (Billynabdul)

*AMEENATU* (Mamuhghee)

*GUDUN K'ADDARA* _GUZURIN TARAS DA ITA_ (Huguma)


*_KOWANNE LABARI NA DAUKE DA SUNA ME HARSHEN DAMO,KAMAR YADDA GUNDARIN LABARIN KE DAUKE DA SALON DA ALQALUMAN ZAFAFA BIYAR NE KADAI ZAI WARWARE MUKU SHI_*

*_Biya naki ta wadannan lambobin domin ki zamo cikin ZAFAFA FAMILY HOUSE_*

*TSARIN SHINE KAMAR HAKA*


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*THANKS FOR CHOOSING US*🫂🫂🫂🫂
*_GUDUN ƘADDARA_*🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️

*H U G U M A*

PAGE 05


*_MONDAY_*


Cikin katafariyar harabar qawataccen gidan fara sol din school bus din yaran gidance me tsaho,wadda ke dauke da rukunin mazaunai a cikinta har kashi hudu banda mazaunin driver. Lausasan gurin zama shimfidar lallausan carfet daga qasan motar gami da wasu qananun curtains a kowanne window dake cikin motar,wanda shine zai bayyana maka ainihin nauyin kudaden da aka narka domin mallakar motar da kuma sadaukar da ita domin jigilar karatun yaran gidan.

Daga waje kuma a rubuce baro baro hannun hahu da dama na motar rubutu ne da manyan baqi kamar haka MAYAK’i BUS SCOLOIRE.

Daya daga cikin dabi’unsu a kowacce safiya,hayaniya ce zaka sameta fal cikin motar,fadace fadace da juna da kuma sauran rigingimu da baa raba yara da shi,har zuwa sanda za’a sauke kowannensu. Amma a yau din akasin wanann dabi’ar itace ta maye gurbin waccan. Shuru motar take,kowa ya kama mazauninsa cikin nutsuwa da kamala,wasu daga cikinsu ma litattafansu ne a hannunsu suka sake dubawa saboda exams da zasu fara a yau din. Duk kuwa da cewa kowa bakinsa cike yake da magana da kuma qorafi amma ba wanda ya iya tankawa saboda gudun daga murya.

Dukka hakan yana da nasaba da wanzuwar Aliyyu maina a wajen. Qasan daya daga cikin bishiyun da suka zamewa harabar gidan ado. Saman wata kujera ta itacen bamboo da aka qawatata da cushion masu laushi don samun dadin zama.

Sanye yake da wasu baqaqen pyjamas da suka fidda samartaka da kuma tashen quruciyar dake tattare dashi. Sassanyan kyawun da quruciya da kuma tashen girma ke sake haskashi. Hannunsa riqe yake da wani qaramin littafi da ba lallai ka iya tantance na meye ba yana dubawa. Kusan wannan din dabi'arsa ce a duk sanda ya dawo daga motsa jikinsa daya zamar masa al'ada kowacce safiyar duniya. Sadai a yau din da biyu yayi zaman nasa,ya karbi key na school bus dinne zaya kaisu makarantar da kansa,yanaso a qalla ya zaga gari ya samu kyakkyawar iskar da safiyar litinin din ke fesarwa.

Kaman yadda tarin abokai basa cikin tsari da dabi'arsa,hakanan yawa ba dabi'a tasa bace,wannan ya sanya lokaci lokaci yakanyi sha'awar zagaye garin na maradi bisa rad'in kansa.

Najma ce mutum ta farko data fara sauke qaramin curtains din jikin motar tana sauke ajiyar zuciya

"Gaskiya muna gab da makara fa,babu wanda zai gayawa yaa maina zamu makara ne?,kuma sultana ma bata fito ba?"

"Waye yake da jarumtar tararsa ya gaya masan?,ko ke zaki iya wannan shahadar?" Aminata dake seat din gaba ta gada tana waiwayowa hadi da jifan ammara da tambayar.

"Ke ba zakije ba sai ni?,na rasa kuma qarar waye zankai sai ta sultana?,qarar sultana a wajen yaa maina saboda ganganci?" Najma ta furta tana nuna kanta,akwai alamun girmamawa maganar daga harshenta zuwa baki.

"Kuna tunanin yaa maina da sultanan da ne?,kunsan jiya jiya naji bibi na masifan yaa maina din ya mari sultanan?" .

Waiwayo sukayi kowa ya zuba mata ido,wasuu baki bude suna kallon yasmine,maganar na shiha kunnuwansu tamkar labarin qanzon kurege.

"Ah lallai na yarda,bibi ta fara rikicin tsufa,ya maina dinne zai mari sultana,sultana fa?,bibi anzo gangara......." Maganar kaltoum kenan ta fada cikin jinjina maganar,abinda ya sanyasu sakin dariya gaba daya,dariyar kuma data dauke dif lokaci guda sanda aminata dake a gaba gaba tayi musu alama na tahowar maina,sai dukkansu suka shiga nutsuwarsu.

"as tu fini?(kun gama?' ya jefa musu tambayar cikin tataccen faransancin nan dake saman harshensa,wanda yayi mugun gwanancewa kai kace yaren uwa da uba ne yake yarawa

"Sultana ce kawai......" Yasmine tayi namijin qoqari hadi da qarfin halin furtawa. Saidai ita dinma kasa qarasawa tayi sanda ya watso mata idanunsa.

Duk da ta kasa qarasawar amma tuni ya hasaso me takeson fada. Sakin murfin motar yayi yaja baya a hankali

"vous êtes très stupide,saboda baku kishin kanku ba kuma damu da karatun ba shi yasa kuka kasa sanarmin" Ba wanda ya iya tanka masa a cikinsu,shi dinma ba jiran amsarsu yakeyi ba,sai kawai ya zube hannuwansa ga aljihun wandonsa ya fara takawa zuwa cikin gidan a nutse.

Bisa hanya yake sarrafa abun cikin ransa. Daga zuwansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login