Showing 21001 words to 24000 words out of 51618 words

Chapter 8 - Gudun Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete

takeyi abun nata kuma yana qara gaba ne. Bayason ya fiddo mata da ainihin kalarsa gaba daya,saboda yayi imanin hakan bazaiwa kowa dadi ba a gidan. Yana da wani irin fushi zuciya da kafiyar da shi kansa yasan girmanta,wannan ya sanya yake yawan kaucewa dukkan abinda zai bata ransa

"Kada na bude idanuna na sake ganinki a tsaye a nan wajen stupide(shashasha)" yadda yayi mata maganar da kuma yadda kowa ya zuba mata idanu yana kallon fadan da yake zazzaga mata sai taji abun baiyi mata ba,kaman ya tozartata ne,abinda yasa taji zuciyarta ta wani quntace guri daya,sai kawai ta saki kuka iyakar qarfinta tana rufe fuskarta da hannuwanta.

Sake baci sosai ransa yayi,saboda shikam baiga uwar da akayi mata ba,uwa uba ma hukuncin da zaiyi matan baiyi mata shi ba. Wannan ya tunzurashi ya taka a zafafe ya finciko hannunta yana tambayarta cikin tsawa kan abinda akayi matan.

Wani ihu ta qwala kai kace ya karyata ne gida biyu. Ihun nata da yaja hankalin aba dake tattaki ta bayan gidan.

"Lafiya?,ke sultana meye?" Ya kuma jefa mata tambayar yana isa gareta hadi da kamo hannunta. Kai kawai maina ya kawar yana hadiyar wani abu me cikin wuyansa,iya yadda take kukan kawai yana sake bata masa rai da tunzurashi.

"Don nace bazan hau bus scoloire ba shine yakemin fada zai dakeni,ya kamamin hannu inajin ma ya karyani" ta fada tana miqawa aba hannun nata.

Hannun ya kama yana dubawa da kyau hadi da jujjjuyashi,sai ta saki 'yar qaramar qara

"Wayyo Allah na" ta fada hawaye shabe shabe saman fuskartata,kai kace da gaske karyata din yayi

"Sannu sultana,ya isa,sannu" aba din ya fada fuskarsa na nuna alamun abun ya tabashi

"Ina modu" aba ya fada yana duban sararin gurin

"Gani ranka ya dade"

"Jasu ku tafi makarantar,kai hassane......"

"Yallabai" ya fada yana matsowa cikin girmamawa

"Ka fiddo wancan motar,a wanketa a duba lafiyarta,daga yau ta zama ta daukan sultana" a dan hanzarce maina ya daga kansa ya dubi aba din,ransa yana motsuwa. Da gaske dukkan abinda takeso sukeyi mata kenan?,ya daga tayi hukunci irin nata sai a biye mata. Idanunsa suka hada da aba din,sai ya jefa masa harara abinda ya sanya maina sake kauda kansa kenan. Akan sultana babu abinda ba zasu iya yi ba kenan?.

Ransa a matuqar bace ya soma barin wajen. Yayin da sultanan ta bishi da kallo dariya can fal qasan ranta,tana fatan inama zai waiwayo ta samu damar yi masa gwalo,ko ba komai yau ya gane matsayinta a wajensu aba din.

Ya jima zaune cikin sofa din falonsa yana jujjuya abubuwa. Yayi dukka iya lissafinsa amma ya kasa bashi dai dai,ba haka yakeson rayuwar sultana ta tashi ba,to amma ta yaya zatayi saiti kamar yadda yakeso?,bayan wadanda yake da buqatar dafawarsu dukka su dinma idanunsu a rufe yake. Idonsa ya lumshe yana fidda iska daga bakinsa,yana qoqarin kawar da zuciyarsa daga yunqurin fara jin haushin yarinyar. Makaranta yakeson komawa,amma tunanin abinda zai bari idan ya tafin shike taka masa burki.

Knocking yaji anayi,amma har aka kwashe wasu sakanni ya gaza bada umarnin a shigo din. Sai bayan da ya tabbatar ba za'a daina masa knocking din ba sannan ya motsa bakinsa yana tambayar waye

"Goumar ne" ya amsa masa daga wajen

"Entrez(shigo)" ya amsa shi yana sauke qafafunsa qasa tare da qoqarin saita yanayinsa.

A nutse ya murda qofar yana shigowa,goumar baqin buzu kamar yadda sultana ke kiransa kai tsaye,sunan kuma ya soma bin bakunan wasu 'yan gidan. Shine d'a na farko ga Oncle bashar qani ga aba wanda shike binsa.

Kusan shine wanda yabi maina sawu da sawu,ya dauki dabi'unsa da yawa bawai ta siffar kwaikwayo ya siffantu da dabi'ar haka kawai ba,a'ah bibiyace ta jini kamar yadda ake iya samu daga kowa cikin kowacce zuri'a.

"Ama tana kiranka,tace votre petit déjeuner est prêt(abincin safenka ya kammalu)" qafafunsa dake saman dan table din mulmulallen katakon ya sauke yana dan sake ciki da idanunsa tamkar bayason budesu gaba daya

"Zauna goumar" maina ya buqaci haka daga gareshi. A nutse ya samu seat ya zauna,sosai mainan ya gyara zamansa yana kallonsa

"dites-moi(ka gayamin)iya lalacewan da sultana tayi" a dan rude kadan goumar ya daga kansa yana duban maina din

"Frère(haka yake kiransa wasu lokutan) lalacewa kaman yaya?" Qaramar Ajiyar zuciya ya sauke idanunshi akan goumar

"Eh,na fara tsorata da tarin halayenta,ina tsoron kada ya zama maza sun hure mata kunne......" Kai goumar ke girgizawa

"Ban taba ganin abu mai kama da wannan ba frère,banajin kuma haka" gyara zama maina yayi yana dan jin nutsuwa kadan

"Amma ka gayamin,wanne kallo za'a yima mace me irin halaye da dabi'un sultana?,idan a nan qasar ba aibu bane a sauran wasu qasashe fa?" Shuru goumar yayi ba tare da yace komai ba. Halayen sultana suna bashi mamaki ta yadda sukayi matuqar shan banban da na sauran yaran gidan,to amma kuma fadin hakan ga maina kamar qarawa fetur wuta ne.

Shurun goumar ya sanyashi miqewa kawai. Sai da ya biya ta bedroom dinsa ya zare takalman qafarsa ya maida gurbinsu da slippers sannan ya fito.

Har kullum sassan Ama din nasa daban yake da sassan sauran matan gidan ba,bawai don tana mahaifiyarsa ba a'ah,zai iya cewa kaf duniyarsa,a kuma 'yar taqaitacciyar rayuwarsa bai taba katari da macen da tayi tsananin sanin ciwon kanta irin ama din ba.

Masu aikinta ne qwara hudu rak da bata tana sauyasu ko ragesu ba keta kai kawo suna sake gyara tsarin dining din. Kai tsaye za'a iya kiran ama din da ruwa biyu,'inda ana tsotsar boko to tabbas za'a iya cewa ita kam ta tsotsi boko daga jinin mahaifinta. Ta wani kuma idan kace bafaransiya ce shima bakayi kuskurenba,saboda yadda abubuwa da yawa na qasar haihuwar mahaifiyarta ya kama jikinta ya kuma zame mata jiki.

Kamar kowanne lokaci yau ma tana saman qawatattun kujerun da aka kewaye falon da su har rukuni uku. Hankalinta ya tafi sosai kan system dake kan cinyarta,ya kuma tabbatar abinda ya shafi business dinta ne.

Fararen idanunta ta daga tana amsa sallamarsa gami da dan binsa da kallo,har cikin ranta tana jin wani abu mara dadi yana motsa ranta. Damuwarsa bata taba boyuwa a wajenta koda kuwa yayi qoqarin yin hakan. Duk abinda ya faru dazun saman idanunta akayishi,ta kuma tabbatar yana daya daga cikin abinda ke damun ransa yanzu hakan.

"bonjour ama(barka da safiya ama)"

"matin" ta amsashi a taqaice tana gyara zaman eye glasses dinta. Sai da ya zauna sosai sannan ta dauki qaramar wayar dake gefanta tayi kira zuwa kitchen,magana tayi na mintuna qalilan sannan ta ajjiye wayar. Sake maida dubanta tayi a kansa

"petit-déjeuner(breakfast)naka wa ka barwa?" Bai amsa mata ba sai shafa lallausar sumarshi kawai da yayi da daya hannun nasa yana jin damuwa cikin qirjinsa

"Ba kowa ama" dan shiru ya ratsa tana danne dannenta a laptop kafin ta sake magana

"Yaushe zaka koma bakin karatunka?" Tayi masa tambayar tana zube masa idanunta. Qaramin murmushi ne ya subuce masa,ya gyara zamansa yana cewa

"Yau kuma ama?" Kai ta gyada cikin basarwa

"Oui(eh)......" Ta fada kai tsaye

"pourquoi?(me yasa?) Ama,ko kin gaji da nine?" Yayi tambayar cikin salon tsokanar da ba kasafai ya fiya yinta ba a tsakaninsu,duk kuwa sa cewa akwai sakewa qaunar juna da kuma fahimta,amma halinsa na miskilanci ya sanya ba komai yake iya yi ba

"Eh......na gaji da ganinka a haka kana ragaita tsakanin abinda ba zaka iya gyarawa ba......ba sultana ce ba?, itace ta tsaidaka ko?" Tayi masa tambayar idanunta tsakiyar nasa.

Zare idanunsan yayi sannan ya motsa labbansa a hankalin cikin son kare sultanar,kada ta sake baqi cikin idanu da zuciyar ama din

"Non ama(a'ah ama)"

"To menene?.....sultana ce haka sukeson su ganta,haka suka tsara mata ta taso ta kuma rayuwa,to kai a suwa?. Don kawai kana yaya ga mahaifiyarta?,duka duka shekarunka nawa maina?,tu as beaucoup à faire dans ta vie(kana da abubuwan yi da yawa cikin rayuwarka) ka fuskancesa ka barta tayi rayuwa yadda suka tsara mata,ne perds pas ton temps(karka bata lokacinka)" ta qarashe fada cikin zafi zafi.

Shuru yayi yana sauraren sautin muryarta,zuciyarsa na sake motsawa,gaba kura baya sayaki,ta yaya zai iya bari sultana ta taso a haka?,duk kuwa da cewa abune da da yawa daga cikin al'umarsu suka taso suna ganinsa,kusan ya zame musu ruwan dare,ba kuma komai bane,amma kuma shi cikin jininsa ya tsani wannan tarbiyyar tasu sam,yana qyamatarta qwarai da gaske,da kuma gasken turawan France sun musu illa qwarai,sun shiga tarbiyya al'ada da kuma dabi'unsu

"suis désolé(am sorry)" ya fada kawai a taqaice don bashi da wata kalma da zai iya furtawa bayan wannan a yadda yaga ran aman ya baci.

Wannan duka ya hadu ya dinga damunsa cikin rai. Duka duka abincin bai iya ci me yawa ba ya tashi,abinda ya sake bata ran ama kenan. Tana ganin duka ya tattara damuwar sultana ne a ransa,wanda koda shine ya haifeta iya abinda zaya nuna kenan. Yayin da shi nasa damuwar tafi karkata ga yadda soyayya da zallar gata da su bibi ke nunawa sultana keson zamewa tarnaqi cikin samuwarta da maidata cikakkiyar mace wadda yakeson ya raina. Cikakkiyar macen da duk mijin da Allah ya bata zaiyi alfahari da zamowarta matarsa. Mace daya tamkar da dubu da tarbiyyarta zata fita daban da sauran mata cikin al'ummarsu.

**********

A nutse bibi ta shafa addu'arta kan fuskarta da dukkan tafukan hannayenta guda biyu. Can qasan ranta abun yana ci gaba da tsinkular ranta,fargabarta tana sake qaruwa kan sha'anin sultana da maina. Ta gaza fahimtar ina ainihin matsalar take?,sai ya dafa qasa da dukka hannuwanta tana tashi daga saman lallausar farar dardumarta.

Babban falonta ta fito cikin nutsuwa da kamalar data cika fuskarta. Akwai dattako sosai akan fuskarta da kuma cikar dattijantaka. Hakanan tsarin halittarta yake,tana da nutsuwa qwarai cikin komai nata,SULTANA CE kadai rauninsu.

Tanja kadai ta samu zaune cikin falon tana kallo. Lokaci ne na hutu ga dukka ma'aikatan gidan,bata kuma tsawwalawa ga kowanne ma'aikaci dake qarqashin sashenta,suna walwalarsu tamkar kowanne mutum cikin gidan. Kusan ma'aikatan sashenta ma sunfi na kowanne sashe samun 'yanci.

"Sannu da fitowa" tanja ta fada tana lanqwasa qafafunta

"Yauwa tanja,ko zakiyimin kiran maina don Allah?"

"Maina kaman ya fita shi da alhossain"

"Indai tun dazunne na tabbatar zuwa yanzu ya dawo" bibi ta fada tana zama saman daya daga cikin kujerun hadi da ambatar sunan Allah

"To" tanja ta amsawa bibi tana miqewa ta gyara dankwalinta sannan ta nufi waje.

*HUGUMA*👑👑👑
[4/18, 10:43 PM] C.E.O HUGUMA CLOSET: *_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

PAGE 13

Waya ta sameshi yana yi. Dogon wando ne fari qal a jikinsa da singlet fara itama,sai ya ajjiye wayar yana duban tanja data tsaya nesa da falon

"Mainasara bibi ce take kira"

"d'accord" ya amsa can qasa da muryarsa me sanyi.

Ko daya baiyi niyyan shiga sassan bibi din ba,ya sanyama ransa ma sai tayi cigiyarsa kafin ta sake ganinsa,saboda yana ganin cewa suna da tagomashi wajen lalacewar ginin da ya fara yiwa rayuwar sultana. Saidai kuma bibi din ta wuce ta kirashi yaqi zuwa,don haka ya sauke qafafunshi dake saman table qasa yana ajjiye wayarsa saman kujerar ya wuce zuwa bedroom dinsa.

Kaftan abaya budaddiya ya zura navy blue,kalar data fidda sigar kyawunsa matuqa,haskensa ya fito sosai,ainihin zallar hasken cikakken ba'abzine.

Kamar yadda yake dabi'arsa hannayensa zube a aljihun kaftan abaya din yana qissima abubuwa da dama cikin ranshi. Iskar bayan azahar tana kadawa kadan kadan me cakude da sanyi maras tasiri. Ire iren wannan yanayin suna masa dadi sosai kasancewarsa mutum ras son zafi ko kadan. Hatta da sutura ba kowacce yake sanyawa ba saboda baison abinda zai takura jikinsa.

Da nutsatstiyar sallamarsa ya shiga parlor din bibi. Ta amsa masa tana karantar nazarinsa sanda yake basarwa ba tare daya kalli fuskarta ba,daya daga cikin alamun fushinsa kenan.

"Samu waje ka zauna" bibi ta bashi umarni kai tsaye,ita dinma yau fuskarta ba'a sake take kamar yadda ta saba ba.

Kaman bazai zauna din ba sai kuma ya matsa sofa din gefanta ya zauna a kai bayan dukka wadanda ke zirga zirga a falon sun kau,don basu waje.

"Aliyyu" bibi ta kirashi da sunansa na asali kai tsaye. Sexy eyes dinsa ya daga ya kalli Bibi sannan ya motsa bakinsa

"Kada kace komai maina,mamaki kurum yanzu kake bani" ta fadi tana qare masa kallo tamkar tanason hange meye abinda ya canza a tattare dashi da ya sauya launin mu'amalarsa da sultanan tashi

"Gaba daya ka canza maina,kamar ba kai ba,ka tashi daga mainan sultana ka koma aliyyu haidar,ka tashi daga frèren sulty ka koma wani abu na daban,kana neman zamewa yarinya kamar wani dodo,kamar ba kaine ka raineta da hannunka ba?,kamar ba kaine kaci kashi da fitsarinta ba?,kamar ba kaine kake hana idanunka bacci saboda sultana na kuka ko tana rigima ko bata da lafiya ba,dukka ina wannan kulawar?,tsakaninka da ita yanzu sai kyara sai hantara sai tsangwama,sama da tsangwamar da kakewa kowa cikin gidan nan" bibi ta qarashe fada tana sauke maganganun nata hade da fitar sirrin numfashi,da alama daga qasan zuciyarta maganganun suke fita


"Me yasa bibi?" Ya jefa mata tambayar,idanunta kadan ta qanqance tana dubansa alamun neman ba'asin tambayar da yayi matan

"Me yasa bibi zaku barta ta sangarce bayan kowa cikin gidan nan tarbiyya bai daya ake musu,waye tafi cikin yaran gidan nan bibi?,sai abinda sultana ke so?,sai abinda ya kwanta mata a rai yayi kuma dai dai da raayinta?,bibi wannan ba soyayya bace sam ba qauna bace,ita din diya macace,gidan wani zataje,baki tsoron ta tashi a haka taje masa da dabi'ar da bazai iya ba a dawo muku gida da ita?,wala'alla ni din bana kusa da ku,kune zaku fini jin ciwon hakan,kuma kafin ni na gani ku zaku fara gani kune zaku fara karbar sakamakon"

"Auzubillah......haidar me kake cewa haka?" Bibi ta fada fuskarta na nuna girman da zancan yayi mata. Ba komai saman fuskarsa kaman ma baisan me dame ya cewa bibin ba ya dage dukka girarshi biyu

"Oui(yes)"

"Dukka maza ne zasu iya daukan halin banzanta?"

"Subhanallahi,da gaske ka sauya maina,ka canza,na tabbatar frèren sultana bazai taba fadin haka a kanta ba......to bari kaji,kai din yaro ne da har yanzu bai wuce shekara ashirin da biyar zuwa da shida ba,a dukka matakan tarbiyya banjin kasan wani abu me yawa,bata haka ake yiwa yaro tarbiyya ba,tsanani da matsi basa kintsa yaro ko kadan,ka sanyawa sultana zafi da yawa,kana amfani da irin zafinka na halitta,ita diya mace kwata kwata bata buqatar zafafawar namiji,bare kuma yaran mata da yanzun suke tasawa tarbiyyarsu nada matuqar sulbi da santsi,don Allah maina.....banajin dadin canzawarka kwata kwata,ka koma frère din sultanansa na baya".

Idanunsa ya lumshe sannan kuma ya budesu, muryarsa a lanqwashe yace

"Bibi na fiki jin rashin dadin dabi'un sultana,na kuma taras da ku ba masu goyon baya na ba wajen maidata hanya,bazan canza ba indai sultana ba zata canza ba,dole ta koma kamar kowanne yaro dake gidan nan" kai bibi ta gyada,tun ba yau ba tasan irin nasa halin. Yana da tarin kafiya da taurin kai akan dukkan abinda ya sanya a gaba ko ya furta zai aikata. Fadin zaiyi abu yana da wuyar ji daga bakinsa,amma muddin ya furta din to babu sauyi,komai dadi komai wuya.

Sake gyara goyon school bag dinta tayi dake bayanta,tana jin kamar ta fada dakin ta rufe yaa maina da duka,ai ita batasan haka yayi nisa wajen qinta ba,batasan haka zuciyarsa tayi zurfi wajen son quntata mata ba,lallai Allah baya bacci da har kunnuwanta suka jiye mata komai. Indai yana tunanin iya tsare gidansa,daci da baqin ransa,fada da hararraminsa zai bashi abinda yakeson yaga ta koma din to tabbas zata tabbatar masa ita din ba tsoronsa takeyi ba,kuma bai isa tabuka komai ba

"Sultana kibi a hankali,kinfi kowa sanin waye frère" wani sashe na zuciyarta ya gaya mata sanda take qissima da irin salon da zata shiga falon

"Idan garwashi ne shi ni wuta ce" ta baiwa kanta da kanta dama zuciyar dake gargadinta amsa,bata kuma sake tsayawa sauraron kowacce shawara daga zuciyarta ba ta sanya kai falon da waqar data zame mata madadin sallama.

Idanunta saman fuskarsa tana nazarin furucinsa daya bayan daya,dai dai sanda siririyar muryarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login