Showing 51001 words to 51618 words out of 51618 words

Chapter 18 - Gudun Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete



"Sultana!" Ya kirayi sunanta da wata razananniyar murya. Dukka hannunsan ya sanya ya dagota yana duban fuskarta.

Kowacce halitta dake fuskarta ta sauya kamar yadda gangar jikinta ya saki gaba daya. Ba wani abu dake motsi a jikinta,saima sandarewa da yaga tayi. Hancinsa da ma bakinsa yakai ga fuskarta,ba numfashi ba alamarsa,sai sanyi da fuskartata da kuma tafukan hannayenta sukayi.

"Ta mutu!" Ya fada a gigice bayan ya sanya yatsunsa biyu a jijiyar daya tabbatar a karatunsu muddin bata harbawa to batun rayuwa a tare da mutum

"Sultana!" Ya sake kiran sunanta wanda ya taho hade da gunjin kuka.

Kansa ya kifa saman tata fuskar ya saki kuka me qarfi,kukan da tsahon rayuwarsa bai taba yin irinsa,ya kashe musu sultana,da wanne ido xai kalli bibi?,da wanne ido zai kalli aba?,uwa uba da wanne ido zai kalli nafessa?. Ya kashe sultanar da ya raineta da hannunsa?,ya kashe sultanar da yaci kashi da fitsarinta?,da wanne ido zai kalli sauran mutane?.

D'il yaji harbawar jijiyar sau daya,abinda ya sanyashi daga kansa da sauri yana dubanta,ya kuma tattara dukka hanakalinsa da nutsuwarsa ko zai sakejin ta harba din amma bata harba ba. Hannunsa ya sanya ya dafe saitin zuciyarsa da qarfi wani kuka me ciwo yana sake qwace masa. Da sauri ya sauka daga gadon ya gyara mata kwanciyarta.

Cikin mintuna goma ya bata dukkan wani tallafi da zai iya sanyawa ta rayu,saidai bata dai bada wani reaction ba har ya gama. Amma kuma yana da cikakken hope akan taimakon da ya baiwa numfashinta da zuciyarta,Sai ya tattara komai nasa ya sake matsawa gabanta ya shafa sumarta yana jin kamar zuciyarsa zata fado.

Bazai iya tsaiwa yayi ido hudu da Bibi ba

Bazai iya fuskantar aba ba

Me zai cewa ama?. Sai ya sauke hannunsa da sauri ya juya yana fita daga dakin,wanda daga nan bai zarce ko ina ba sai dakinsa.

Ko minti biyar bai rufa ba a dakin ya fito,babu komai a hannunsa sai qaramar takarda daya soketa jikin qofar dakin nasa,sai wata qaramar jaka dake riqe a daya hannun nasa. Ya fara takawa yana barin ainihin ginin gidan yana dosar qofar fita a gidan. Zuciyarsa na wani irin fusgarsa,wata izuwa dawowa cikin gidan,wata kuma zuwa fita daga gidan,fita kuma da zata kawo nisan tazara me yawa,har sai ya tanadi amsoshin da zai baiwa ahalin MAYAK'I. walau SULTANA ta rayu ko kuma TA RASA RANTA,Ya tabbatar dole wataran ya fuskancesu,dole ya fuskanci abinda ya aikata a yanzun,saidai kuma a yanzunne bai shirya fuskantarsu ba.


*_ina Aliyyu maina ya tafi?_*

*_shin ya tafi kenan?_*


*_ya bibi ama da aba zasu kalli maina a yanzu?_*


*_meye zai biyo bayan rayuwar SULTANA da MAINA?_*

*_FAREWELL BUT A NEW CHAPTERS UNFOLD_*

*_YANZU MUKA KAMMALA SHIMFIDAR LABARIN,AINIHIN LABARIN SAI BAYAN SALLAH IDAN ME DUKA YA KAIMU_*

*_INA MUKU FATAN ALKHAIRI,TARE DA FATAN YIN IBADAR WATAN AZUMIN RAMADANA LAFIYA_*

*_INA ROQA MUKU ALKHAIRIN UBANGIJI TARE DA FATAN ZAMU SHIGA CIKIN RAHAMARSA YA SAKAMU CIKIN 'YANTATTUN BAYINSA ALFARMAR WANNAN WATAN_*

*KADA KI SAKE 'YAR UWA,KIYI IBADA DA KYAU,TA YIWU WANNAN SHINE RAMADAN DINKI NA QARSHE A RAYUWA*

*MATATTU DA DAMA DAKE QARQASHIN QASA A YANZU HAKA SUNACAN CIKE DA BURIN INAMA ACE SUNA CIKIN WADANDA SUKA SAMU DAMAR HALARTA WANNAN LOKACIN CIKIN GIDAN DUNIYA,SABODA SUNSAN YADDA AIKIN LADA KEDA MATUQAR TSADA DA DARAJA A BARZAHU*

_SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIKA,ASH HADU AN LA'ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA'ATUBU ILAIKA_

_MA'ASSALAM_👑👑

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login