Showing 27001 words to 30000 words out of 51618 words

Chapter 10 - Gudun Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete

a hannunsa.

Tana shiga gurin ya barke da ihun murna,dukka qawayensu ne maza da mata cike a gurin. Sosai kanta ya fasu da yadda suka nuna murnar zuwa gurin,tuni ta ware a cikinsu aka shiga hidima da sabgogi ba tare da tana duba lokaci ko tuna cewa laifi zata aikata dingimeme ba.

Tun kafin lokacin karatunshi da ita ya cika ya kammala komai ya sallami su najma da yakewa lesson kaman yadda ya saba duk sanda yake nan,musamman subjects din da yafi qwarewa akai su kuma suke basu wahala.

Tun yana duba lokaci har ya sauke qafafunsa qasa yana jawo wayarsa. Momma ya kira matar oncle bashar yace ta turo saddi yayi masa kiran sultana. Minti uku kacal saddi din ya nemi izinin shigowa sashen nasa ta hanyar yin knocking

"Entrez(shigo) ya fada yana gyara zamanshi. A nutsen ya shigo yana duban maina.

"yaa maina....bata nan" idanunsa akan fuskarsa saddi

"Bata nan?,da darennan a lokacin karatu?,ita da wa suka fita bayan time ne na karatu?" Kai ya girgiza

"Ba'a sani ba,bibi dinma batasan bata nan ba" idanu ya qanqance yana jin zancen banbarakwai

"comment ça se fait?(garin yaya ya faru?)"

"je ne sais pas(ban sani ba)" ya fada a ladabce. Wani iri yaji maganar tayi masa,kaman yaya za'a ce ba'a ga sultanar ba?,kuma ba'a san ina take ba?,duk girma da fadin gidan da yawan security din dake cikin gidan?,idan bata nan ina taje da daren nan?,lokacin da kowa ke cikin gidan.

"Jeka" ya fada yana miqewa daga zaman da yayi,ya lalubi wayarsa ya saka a aljihunsa ya zura baqaqen slippers dinsa yana ficewa a sashen nasa.
[4/18, 10:43 PM] C.E.O HUGUMA CLOSET: *_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

Page 16


Carko carko ya samu bibi da tanja da sauran masu aikin sashen bibi din,harma da su momma dake sassansu. A nutse ya qaraso falon yana duban fuskokinsu,kanshi tsaye ya tura tambayar ga bibi

"Garin yaya aka rasata?"

"Bana ce ba maina,don taci abinci da yamma bayan sun taso a makaranta,ta shiga daki tace zata kwanta kafin ayi sallar magariba,tanja ta shiga tada ta saboda ta samu sallar ta tarar ba kowa a ciki" Shuru ya biyo bayan bayanin bibi,yayin da maina ke nazari kadan kadan cikin kwanyarsa

"Inaga koda oncle umar a kirayeshi a shaida masa,dare yana yi kada ta fada wani hannun" mommy matar oncle umar din ta fada fuskarta na bayyanar da tashin hankalin da take ciki

"Non(a'ah),basai kun kira kowa daga cikinsu ba,zaku daga musu hankaline tunda har yanzu babu tabbacin wani abune ya sameta"

"Wani abune mana maina?, yarinyar na cikin dakinta a nemeta a rasa?" A nutse ya zubewa bibi kallonsa,bayason yayi doguwar magana ne cikin mutane,amma cikin jikinshi yakejin bawai wani abu bane ya sameta ba

"se détendre(relax)elle est en sécurité in sha Allah(lafiya qalau take in sha Allah" ya fada yana daga mata hannunsa

"Ina goumar?" Yayi tambayar yana wuwwulga idanunsa cikin falon.

Babu shi a wajen,don haka ya aika saddi yayi masa kiransa. Ba jimawa suka shigo tare don shi din bame yawo bane,mayen karatu ne,duk inda zashi baya wuce farfajiyar gidan ko garden na gidan,yayi nisa shine ka sameshi qarshen layinsu cikin wata qaramar majalisa da sukanyi duk yammaci,ita dinma ba kullum yake fita ba

"Karbo key din mota wajen bibi ka fito muje" ya fadi yana fita a parlor din ya barsu a nan a tsaye.

Goumar din Bai tambayi komai ba har ya tada motar suka fice a gidan. A nutse motar ke ratsa layin nasu har suka kai qarshensa. Yana qoqarin hawa kwalta sai ya canza shawarar yabi ta layuka,wannan ta sanya ya dan rage gudun yabi ta layin bayansu

"Ka sakamin ido kawai akan hanya goumar"

"Toh ya maina" ya amsa masa yana gyara zamansa cikin motar.

A slow motar ke tafiya,zaka tsammaci gurin tsaiwa take nema,dukka fitilunta ya kunna ya bada full light yadda zasu samu damar ganin abinda ke bayansu da gefen da gefansu da kuma nesa da su,daga shi har goumar babu me iya cewa komai. Kowa yaja bakinsa ya tsuke,amma kuma kowa da tunanin dake cikin zuciyarsa.

Tun daga farkon layin kidan ke tashi kadan kadan,kana natsowa ta wajen gidan yana sake qarfi a kunnuwanka. A tare suka kalli juna shi da goumar,sai kowa ya dauke dubansa ba tare da yace komai ba.

Sake rage saurin motar yayi. Dai dai sanda yazo qofar gidan sai yayi kaman zai tsaya amma sai ya fasa

"Gidansu waye wannan?"

"Gidansu sultee,gidan alhaji mamman bashar" kai mainasara ya gyada,sai ya fara neman gurin tsaiwa daga qarshen katangar gidan. Haka kawai yaji yana buqatar tsaiwa a wajen hakanan kuma haka kawai din yaji kaman sultana din zata iya kasancewa cikin gidan.

Ya kammala parking ya kashe motar,ya fara kwantar da kujerar,sai a sannan goumar ya kalleshi

"Yaa mainasara......ya muka tsaya?, ba tafiya zamuyi bane dare yana sake yi"

"Ka kula da me shiga da kuma wanda zai fita" maina ya fadi masa yana kwantar da jikinsa a kujerar gami da lumshe fararen idanunsa. Da mamaki goumar ya maida dubansa a kansa

"Amma......kana tunanin zamu samu sultana a nan wajen ne?"

"peut être(wataqila)" ya amsawa goumar tare da maida idanunsa ya lumshe kamar wanda ke shirin yin bacci

"Banda abin yaa maina mu da muka fito neman yarinyar da ta bace sai ka kawomu nan?,sannan kuma har ka kwanta kace zakayi bacci" goumar ya fada cikin ransa. Duk da haka sai ya maida kansa ga window din motar don yin abinda ya sanyashi.

Tana tsaka da rawarta hankali kwance,bata ma wani tuna yadda zata koma gida da kuma irin qurar da ka iya tashi sai taji kaman fitan wani abu daga jikinta. Gabanta yayi mummunan faduwa,a hankali ta sauke hannunta dake sama tana jujjuyashi zuciyarta na bugawa. Kada dai ace wannan abun da tanja tace mata zai dinga dawowa duk kowanne wata ne ya sake dawo matan.

"Na shiga uku" ta fada qasa qasa. Daga yadda taji dumi yana ratsata tabbas shine,babu komai a jikinta banda pant da dogon wandon dake jikinta,ta yaya zata fita a wajen ba tare da sun tsaidata har jikinta yakai ga baci ba?. Akwai qawayenta wajen,hasalima cikin gidan nasu akwai qawarta,to amma ta yaya zatace musu ga abinda takeyi?,bayan kuma babu wadda ta taba ce mata tana menstruation?.

Cikin dabara ta fara zame jikinta daga wajen a hankali a hankali. Bata tsaya ba sai data tabbatar ta zamewa ganinsu sannan ta doshi qofa. Ranta a jagule yake sosai,ita harga Allah batason wannan abun da tanja tace mata kowacce mace data gani tana yinsa,ita inda za'a bata magani ta daina yinsa kwata kwata da tafison haka,gani ma takeyi 'yan iska ne suke yinsa,kwata kwata ma shekararta nawa da zai dinga zuwa yana takurata?.

Cak ta tsaya sanda ta isa bakin gate din gidan,sai a sannan tunaninta ya dawo mata dai dai. Ta yaya zata koma cikin gidan ba tare da kowa ya ganta ba?,tasan zuwa yanzu zaiyi wuya idan ba'a fara nemanta kusfa kusfa cikin gidan ba.

"Ki basar kawai kiyi shigewarki,ko 'yan guards kada ki kalla" wata zuciyar ta bata shawara

"Ya maina fa?" Wani sashe na zuciyarta ya tambayetan iya tambayar kawai sai data sanyawa gabanta faduwa,sai ta cije lips dinta ta furzar da Iska tana qanqance idanu.

"Idan kika shiga dakinki kika kulle kikaqi budewa ai dole ya haqura" wata zuciyar ta sake gaya mata. Kai ta jinjina cikin gamsuwa da wannan shawarar,sai ta soma takawa tana fita daga gidan tare da baiwa kanta qwarin gwiwa,ta wani gefen kuma tana takatsantsan da takunta gudun kada jikinta ya baci.

"SULTANA MAYAK'I" aka ambaci sunanta daga cikin motar dake sako kai layin. Kanta ta daga tana duban motar da aka sauke glass dinta. Yarane matasa su biyu,wanda dukkansu ba zasu haura shekaru sha hudu zuwa sha biyar ba. Kowannensu kansa dauke yake da sassalkan gashi irin na ainihin buzaye,farare qal suna diban kamanni da juna. Koda ba'a gaya maka ba zakasan cewa yaran gata ne kamar yadda sultana take 'yar gata kuma sangartacciya. Akwai alamun hutu me yawa a tattare dasu.

"Tsaya a nan zamuyi magana da wancan babe din,saura kuma ka matsa daga inda kake,ko parking wallahi bamuce ka gyara ba" daya daga cikin yaran dake cikin wani lafiyayye kuma tsadajjen trouser da shirt ya fada,sanann yayi tsalle yana saukowa daga cikin motar dayan ma ya biyo bayansa.

Tana tsayen tana kallonsu har suka iso inda take tsayen. Da wani banzan kallo take kallonsa,batasan ma sun gayyaceshi ba da duk yadda take da son zuwa irin wadannan wuraren ba zata zo ba. Duk da rawar kai tsiwa da tarin surutunta,amma ita din mutum ce da ba da kowa takeson mu'amala ba,hakanan komai sonka da jama'a sukeyi idan bakayi mata ba sam ba zata taba shiga shirginka ba.

"ma petite amie(budurwata)" daya daga cikinsu wanda yayi warning driver dinsu ya fada yana murmushi

"ma petite amie?" Sultana ta fada cikin tsantsar mamaki tana masa wani kallon banza haushinsa yana cikata. Ya maidata 'yar iska da har zai kirata budurwarsa?.

"Kaga fa bata gane ba,yau dai ga dama ta samu kawai ka gaya mata" kai ya jinjina alamun gamsuwa,har yanxu yana murmushin yace mata

"Sultana Je vous aime(sultana ina sonki)" idanu ta zaro dukka waje saboda ba wanda ya taba cewa wai yana sonta din sai abdul din, hasalima ko hira me kama da wannan ita da qawayenta basu taba yi ba,iyakarsu hirar waqoqin da sukayi dadi da sababbi,wace zatayi birthday ko ta hada musu picnic,yaushe zasuje shan iska da sauransu

"je quoi ??" Ta tambayeshi galala tana masa duban sakarai zuciyarta tana quna

"Je vous......" Bata barshi ya qarasa maimaitawa ba ta daga hannu ta shareshi da mari tana huci

"Ashe mahaukaci ne kai?,dan iska kawai dalla matsa ka bani waje na wuce,banza" shafa gurin yakeyi marin da zagin nata suna hasalashi,sai ya miqa hannu gareta daidai sanda maina yayi wata zabura ya miqe ya zauna sosai,bai kuma bata lokaci ba ya kama murfin motar ya balle ya fice da wani mugun zafin nama.

A tsorace goumar ya bishi da kallo,ashe duk abinda ke wakana yana kallo kenan?,tun daga fitowarta har xuwa yanzu,a yadda ya jishi shuru idanunsa kuma kaman a rufe bai taba kawowa yana kallon komai ba,sai shima ya bude murfin motar ya mara masa baya.

Baya taja a zafafe cikin hasala ta fara auna ma abdul din zagi

"Ka sake ka tabani ka gani,banza dan iska,kana sona?,to ni ba 'yar iska bace ma nemi irinka 'yar iska kuyi soyayya,soyayyar banza soyayyar wofi,to idan baka sani ba bari na gaya maka soyayya iskanci ce,ni kuma ba 'yar iska bac........" Maqale mata maganar tayi a maqoshi saboda ganin yaa maina din da tayi a gabansu. Duk wani dakiya da taurin zuciyarta sai ya gagara ko ina na jikinta ya dauki rawa,ta soma ja da baya da baya qafafunta suna shaking.

Kallo daya ya yiwa su abdul suka arta zuwa motarsu har suna gware da juna. A idanunta suka kai ga motar tasu,sai ta juya da wani bahagon sauri tana lalubar hanyar gida.

Fincikarta taji anyi,kafin kuma ta gama gane abinda yake faruwa har ya soma janta ya watsata cikin mota. Seat din driver ya koma ya tayar da motar ya figeta yana fita a layin.

Tsamo tsamo tayi cikin motar jikinta yana rawa,goumar ne keta surfa masifa kamar zai ari baki. Idan yayi da.hausa ya koma France sai ya koma yarensu na buzaye har suka isa gida.

Qaton hon ya dinga danna musu babu qaqqautawa har sai da ya taso dukka security na gidan. Suka bude qofar ya shiga da motar ya tsaidata tsakiyar harabar gidan ba tare da ya isar da ita parking lot ba

"Dukkanku baku da amfani,meye amfanin ku da bazaku tsare shiga da fitar kowa ciki da wajen gidan nan ba,duk yawanku kuna meye da har yarinya qarama zata iya ficewa akan idanunku ba tare da kun sani ba!" Ya qarasa fada maqogwaronsa kamar zai fashe saboda fushi da bacin rai. Duk wata jijiyar kansa ta tashi rada rada. Waiwayawa yayi ga motar ya bude ya saka hannu ya finciko sultana,cakewa tayi tsaf tana riqe hannun motar cikin nuna kafiyar shiga cikin gidan.

"Ka sakeni zan shiga da kaina" ta fadi cikin ranta tana tabbatarwa yau asirinta ya gama tonuwa,kuma lallai yau sai kowa yasan tana menstruation,don a yadda takeji a jikinta ta riga da tayi stain(tache) wannan ya sanya ta sake kafewa taqi motsawa gudun tonuwar abun boye da zai iya sanyata ta kunyata.
[4/18, 10:43 PM] C.E.O HUGUMA CLOSET: *_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

PAGE 17




Taurin kai da zallar kafiya kawai ya hango cikin idanunta,wannan ya sake zafafarshi ya daga hannu zai wanke fuskarta da mari,abu daya da yake sanyawa ya samu sasaauci akanta. Har ta runtse idanunta tana jiran jin saukar marin,zuciyarta na ayyana mata muddin ya sauke tafukan hannunta saman fuskarta babu makawa sai ta haifar masa da dana sani,wannan wani alqawari ne data daukarwa ranta. A duk ranar da yayi kuskuren sake taba lafiyar fuskarta ya maretato a ranar sai ta sakashi yayi nadamar aikata hakan,wannan alqawarinta ne,muddin tana numfashi.

"A'ah,ya haka maina?,kul......" Muryar bibi ta dakatar da shi tana takowa gurin tana daga qafarta da qyar saboda ciwon qafa da yake dan damunta lokaci lokaci. Hannu ta sanya tana karbarta daga hannunsa

"A ina kuka samota?" Bibi ta fada tana riqeta da kyau tashin hankalin kan fuskarta yana bayyana qarara

"Bibi bansan na fita ba nima,ciwon mara na dinga yi ni kadai cikin dakin,sai na dinga jin bazan iya zama ba shine na fita nasha iska" qaryar data sambado tayi daidai da sauka da idanunsa sukayi kan dogon wandon jikinta ruwan toka wanda da kadan top din jikinta ta rufe mazaunanta dake da wani irin shape da yake fita yanzu da kadan kadan saboda girma da ya fara zuwa.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kawai ya fada yana kauda kansa. Ranar da nafessa ta fara menstruation ya tuna. Tana kwance a dakin bob cikin sutura da rufin asiri,kaf gidan babu wanda yasan da hakan ma,shi ta fara gayawa kuma shine ya fara mata tunin karatunsa da akayi musu a islamiyya. Har tayi nisa da farawa bibi ko (mamma/mahaifiyarta) basu sani ba. Yau ga diyar nafessa nata ya sameta tana gantali bisa kwalta,ya rabbb...... sultana kuwa idan akace zakka ce za'a ce anyi kuskure ko an fadi ba dai dai ba.

Kasa jurewar tsaiwarsu a wajen yayi ga masu aiki,idan yanzun shi kadai ya gani waye da waye next da zasu iya gani?,wannan tunanin ya sanya ya warceta daga hannun bibi yayi gaba da ita,bai ko tsaya sauraren bibin dake faman qwala masa kira tana son tsaidashi ba.

Tsoro ya sanyata kukan da bata shirya ba,tasan yau din ta shiga uku ta lalace. Abinda ya bata mamaki,duk yadda tayi zaton dokuwa zatayi ba haka bane,don dakinta ya wurgata ya juya yana barin sassan nasu.


********Karfe goma harda kusan mintuna ashirin da bakwai ta isa qofar dakin nasa. Sanye take da wani material me azabar tsada da daukar idanu,kamar yadda yake sunnarta ce sanya suturu masu tsada da daraja,ba kuma wai don alfahari ko fariya ba, a'ah ta isa ne ta kuma kai ta sanyasun. Tun asali da kuma tushenta ta fito ne daga gidan arziqi da kuma wadata,wadatar da taso ta zama sanadiyyar rushe aurenta da ABA. Karin maganar MATAR MUTUM KABARINSA itace tayi tasiri,ta kuma yi ruwa tayi tsaki wajej tabbatuwar aurensu,yau gashi harda zuri'ar samari uku a tsakaninsu. Kalar yadin ruwan sararin samaniya ne da aka yiwa ado da gold color,wannan ya sanya ta yane gashinta me santsi da golden mayafi. Kyawunta da ajinta ya fita sosai,hakanan adonta ya sake boye shekarunta.

Sau biyu kawai tayi knocking qofar ya taso ya iso bakin qofar yana budewa,don qamshinta kawai ya isar masa da wacece

"bonjour(barka da safiya)" maina ya fada yana fitowa zuwa falon nasa

"Ka tashi lafiya?" Ta amsa masa tana takawa zuwa falon itama

"Me yake damunka maina?,jiya bakaci abincin dare ba,yau lokaci yana neman gotawa baka fito ba" ta tambayeshi tana kallon idonsa.

Hannu yasa ya murza goshinsa yana jin bacin ran dake ransa tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login