Showing 18001 words to 21000 words out of 51618 words

Chapter 7 - Gudun Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete

top. Sosai kayan suka zauna mata a jikinta wanda yake a murje tsaf.....zallar hutu da kwanciyar hankali sun bayyana muraran a tattare da ita,ko ina nata ya soma cikowa alamun da hasken gaske dai girma ne yake cuso kai cikin qananun shekarunta da duka duka basu haura sha biyu ba.

Duk yadda yaso ya daure don kada sanya baki akan lamuranta su yawaita amma ya kasa,saboda shiga ce da ya haramtata baki daya cikij gidan,ba kuma yanzun abun ya faro ba,tun zamanin da nafissa kawai ke rayuwa cikin gidan a matsayin diya mace,har kawo yanzun da diyoyi matan cikin gidan suka sake yawaita.

Sake quluwa tayi ta cika fam sanda taji yana qwala mata kira sunan

"Ke!" Sunan da duk duniya tafi tsanar ka kirata dashi.

Bai umarci tazo ba,da kansa yake takowa inda take tsayen. Sai ta samu zuciyarta da bugawa cikin tsananin tsoron wanne laifin kuma tayi?,saidai kuma taurin kanta da zuciyar nan tata maras tsoro na sake qarfafar dukka gabbanta akan bata aikata masa laifin komai ba.

"Sau nawa zan gaya miki na hanaku irin wannan shigar?,ina atamfofin da AMA ta raba muku?" Yayi mata tambayar yana tsareta da lion eyes dinsa da a yau suke cike da fushi.

Baki takeso murguda masa ko ta maida masa amsa me ciwo,don dai ita zuwa yanzu tuni ta cireshi daga sahun mutanen da take jin nauyinsu take kuma ganin kima martaba da darajarsu

"Ni ban iya sakasu ba,kuma ma zafi garesu"

"Kalleni nan" ya fada cikin zallar tsare gida. Kasa duban idanun nasa tayi,duk kuwa da yadda takejin a yanzun bawai kallon idanunsa ba,har zagi tanajin zai iya fita a bakinta a yadda takejin ya matse rayuwarta haka da yawa.
"duk ranar da na sake ganinki da wadannan kayan ki tabbatar saikin raina kanki,abu na biyu muddin na sake ganin qafafun wadannan cikin gidan nan a tare dake......basai na gaya miki abinda zanyi ba,bacemin a gun" ya fada a kausashe kuma a tsawace.

Wani irin fushi da tarin haushinsa takeji kamar tayi me?. Me zatayi masa ne ta huce wannan abun da yayi mata?,me zatayi masa ta rama?,kawai sai ta bude zazzaqar muryarta ta fara jera waqoqinta hankali kwance tana wucewa zuwa sashen bibi

_Bamu damu da kowa ba kar wanda ya damemu......baka bani ban baka to hushin na menene?,ashe zaman duniya iyawa ne_

Da mugun sassarfa ta soma tafiya me hade da gudu da kuma sauri,saboda ta tabbatar abinda tayi din babu wani makawa da zai hanata karbar hukunci mafi muni daga hannunsa.

Cikin kunnen nasa dukka baitocin waqoqinta suka sauka. Wani irin mamaki ne ya kasheshi,zuciyarsa tayi wani mugun yunquro masa,har a cikin ransa yakejin yau din dole ya ajjiye duk wani dubayya da yakeyi ya hukuntata yadda ya kamata.

Kusan lokaci guda suka isa parlor din bibi. Daidai lokacin da take zaune saman daya daga cikin qawatattun kujerun turkey da suka sake daga darajar parlor din har set biyu mabanbantan kaloli da suka dace da juna. Hannunta na dauke da tasbaha da bata rabo da ita tana ja,musamman lokutan da take ita daya irin wannan,yayin da rabin hankalinta yake kan tv france dake gudanar da wani shiri dake nuna ainihin zallar al'adun gargajiya na qasar nijer din. Lallausar rigar wani farin zaren ulu ne a jikinta,wanda yake da adon ja jefi jefi,budaddiyar rigar ta asalin saqar qabilar abzinawa. Tun daga yanayin jikinta zuwa suturarta zaka fahimci sukunin rayuwar da take ciki da kuma zallar kulawa da take samu.

Bata kawo shigowar kowa a cikinsu ba a lokacin,don haka a dan firgice ta daga idanunta tana saukesu daga bakin glass door din parlor din nata.

Tun kafin ta gama rarrabe tunaninta akan abinda ke faruwa sultana din ta fado,kafin takai ga dauke idanunta a kanta ko kwanyarta ta warware mata komai maina ya biyo bayanta.

Taku daya tak ya sakeyi ya cimmata,wanda duka duka tazararsa shi da ita da kuma bibi din baikai taku biyu ba.

"Kul maina!,menene haka?" Muryar bibi ta dakatar dashi daga saukewa sultana zaratan hannayensa da yayi niyyar yi saman farar fuskarta.

A hankali ta sauke kallonta daga kan dogayen yatsun mainan ta maida kan fuskarsa

"Zauna maina" Ta fada cikin wani irin mode dake nuna tsoro da fargabar da suka cika zuciyarta.

Ji yayi sam bazai iya zama din ba,sai ya sauke hannayensa ya xubesu zuwa cikin aljihunsa,ranshi a mugun bace yana jin yadda jijiyoyin jikinsa ke harbawa saboda tsananin bacin rai.

Bibin ta sani,koda ta tambayeshi ba'asi a yadda fushinsa ya hau zuwa matakin da tasan ya kusa kaiwa qarshe,koda zata dige tana tambayar nasa ba zaya ce komai ba,don haka ta waiwaya ga sultana data dade da yin garkuwa da bayanta,ta dunqule ta kuma cure a bayan nata,manyan idanunta na runtse gam,abinda ke bayyana ainihin asalin tsoronta

"Me kikayi kuma sultana?" Tambayar da bibi ta jefo mata ya bata tabbacin ta samu tsira daga hukuncin ya maina din,wannan din ya sassauta tsoratarta da kuma fargabarta,ta zame ta zauna sosai tana kallon bibi kamar ba itace ke boye a bayanta da razananniyar fuska ba

"Nima bansan abinda nayi masa ba bibi,hakanan kawai ya biyoni zai bigeni" kyawawan idanunsa ya hada ya lumshesu guri daya yana furzar da iska daga bakinsa. Wani baci ransa yake sakeyi,bayan zallar rashin kunya harda qarya?,abar da yafi tsana kayi masa?

Yana daya daga cikin abinda yasa wasu ke masa kallon tsatstsaura,saboda shi din yana cikin jerin sahun mutanen da kwata kwata basu iya qarya ba. Kome dacin abu,komai girman abu idan zasu fada zasu fadi maka ne kansu tsaye kuma iyakacin qarshen gaskiyarsu,ko tayi maka dadi ko batayi maka ba. Daya daga cikin abubuwan dake tunzura fushinsa shine qarya,kusan duka yaran gidan sun sani,samun sassaucinka idan kayi masa laifi ka amsa kayi,wannan kawai na iya sanyawa ka wanke dukka laifinka a wajensa
[4/18, 10:43 PM] C.E.O HUGUMA CLOSET: *_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

PAGE 11


"banason zancan banza,ki hidi mini me kikayi?" Mursisi tayi ta mutstsuke idanunta

"Nifa bibi nace ban sani ba,gashinan ki tambayeshi,ni bansan me nayi masa ba" waiwayowa bibi din tayi cikin mamaki ta maida dubanta ga maina,suna hada idanu ya janye idanunsa sannan ya juya a nutse yana barin wajen. Tabbas tsaiwarsa a wajen zata iya sanyawa ya dauki hukuncin da bazai yiwa kowa dadi ba,zuciyarsa ta kawo masa iya wuya,yarinyar ta fitini kowa cikin gidan,ZAKKA takeson zamewa ahalinsu ko kuwa?.

Tunda ya fita a gidan tun yammacin gab da la'asar din bai sake dawowa cikin gidan ba,har dare ya fara shiga,lamarin da ya dagi hankalin bibi. Wani irin qaunarsa Allah ya dora mata kaf cikin jikokinta,hakan kuma baya rasa nasaba da yadda shima maina din yake ta tata,yake kaf kaf da ita,yana gaba gaba wajen bata kulawa da kiyaye duk abinda ya shafeta. A yadda yakeyi matan zaka dauka ba kaka take a wajensa ba mahaifiya ce.

Sanda ya shigo gidan yana shirin wucewa sassansa sukayi kacibus da najma,taja baya cikin girmamawa da wannan tsoron da kowanne yaro cikin gidan yake miki tace

"Bibi ce ta sake aikoni naga wai idan ka dawo,tace idan ka dawo ka shigo ciki" key din dake jikin qofar sassansa ya murza ba tare da ya dubi yarinyar ba,karon farko da yakejin zafin bibi na yadda take tare duk wani laifi na yarinyar,take kuma hana a hukuntata hukuncin da ya dace da laifinta

"Ki gaya mata na dawo,amma zan kwanta sai gobe zan fito" yana gama fadi ya tura qofar a nutse ya sanya qafafunsa ciki.

Wani irin qawataccen falo ne madaidaici,wanda aka yiwa wani qawataccen tsari da kayan gado 'yan italia masu tsari da rashin hayaniya.

Idan ka dauke tafkeken agogon bango dake hade da ayatulkursiyyu babu komai a jikin bangon dake malale da wani irin wallpaper sai qananun frames masu kyau da suke dauke da hotunan wata kyakkyawar baby girl.

Dukka mutum daya ce cikin frames dun hotunan,saidai kuma kowanne hoto an yishi ne cikin mabanbantan shekaru. Cikin wani irin tsari aka jera hotunan,tun daga haihuwarta zuwa koyon zama fara tafiya har zuwa sanda ta zama soma zama mutum sosai.

Gaban hotunan ya isa a hankali kamar wani abu yaja hankalinsa. SULTANA ce a jiki,saidai ba sultanar da ya sani bace,ba sultanar da ya raina bace,ba sultanar da ya zame mata uwa kuma uba bace. Dukka wasu halaye da bayaso ya kuma tsana daga yaran rainon qasar France,cikin al'adunsu da basu da kyawu ta fuskar addini da kuma cikin wasu al'adun,yayi namijin qoqarin cisge fiye da rabinsu daga jikin dukkan wani ahali na gidan,amma sannu a hankali sai kuma lamarin ke qoqarin juyewa zuwa kan sultana?.......sultanar da ya aza dukkan burinsa nason ganin rayuwarta tafi ta kowa cikin zuri'ar mayak'i zamewa madubi kuma abar sha'awa?,sultanar da ya daukarwa kansa alqawarin dukkan wani muradi da burikan nafessa da qasa ta rufesu zai rayasu cikin gangar jikin sultanar?,sultanar da yake jin kaf fadin duniya tun bayan gushewar uwa da ubanta shine next person dake da alhakin da yake ganin ya rataya a wuyansa?.

Iska me zafi ya furzar daga bakinsa. Soyayyar su bibi gareta itace BABBAN RAUNI raunin da yake neman zama cikas ga dukkan wata shimfida da ya yiwa rayuwarta.

Hannu ya nutsa cikin sassalkar sumarsa dake qara fidda zallar quruciya da kuma kwarjinin dake kwance saman fuskarsa,sai ya juya a nutse ya soma fidda kayan jikinsa ya maye gurbinsu da lallausan black towel dinsa na wanka ya wuce toilet dinsa.

Kiran wayar FU'AD cikakken aboki cikin abokai biyun rak da yake dasu tun zamanin quruciya shi ya dauke hanakalinsa,ya kuma dan cinye masa lokaci,ya daga kiran ya dora saman dressing table dinsa ya sakata a speaker yana amsa wayar tashi.

Duk yana masa magana ne akan makaranta,shi dinma cikin lissafinsa yaso komawa niamy ne a jibi,amma hakanan yakejin bai kamata ya koma a wannan tsukin da yake qoqarin saita al'amura ba,yana buqatar qarin wasu kwanaki tunda ba wani abu da idan ya subuce masa a makarantar a wadannan kwanakin da zai zama matsala cikin karatunsa.
Kamar kowacce safiyar litinin,farfajiyar makeken qawataccen mansion house din mallakin zuri'ar SIDI MUHAMAT MAYAK'I cikin tsafta take da tsari. Rukuni rukuni na motocin alfarmar da suke mallaki ne na mazauna gidan,wanda yawancinsu sun kasance mallakin MUHAMMAT MUHAMAT MAYAK'I wato ABA da fitacciyar 'yar kasuwa HAMDIYYA ABDU ME KANO.

Cikin sassanyan safiyar yake tsaye cikin madaidaiciyar balcony dinsa,kaman yadda yake a dabi'arsa,yana da son shan sassanyan iskar nan ta safiyar kowacce rana gabanin rana ta fito ta zafafa sararin subhana,duk da cewa an fara fuskantar yanayin sanyi amma bai fasa hakan ba,don komi sanyi yakanji iskar wannan lokuttan daban take a hunhu zuciya dama qwaqalwaraa,tana bashi wani irin nutsuwa sosai.

Kamar ko wacce safiya,yau dinma bisa rakiyar tanja take takowa inda school bus tare da sauran yaran gidan ke dakon isowarta. Kyakkyawar fuskarnan a tsuke take kuma a dinke take tsaf,hakanan duk taku daya da zatayi tana yinsa ne da tunanin yadda zata kubcewa zuwa makaranta a yau din. Idan akwai abinda ta tsana duk duniya baya ga takura cikin sha'aninta to makaranta ce zata biyo baya. Yau din suna da jarabawar lissaf wato math, subject din da take tunanin tunda Allah ya tsirota ya yanka mata zuwa makaranta cikin qaddararta bata taba fuskantar me ake fada a cikinsa. Bata taba bata abun rubutunta ta gwada yin note na math ba,dukkan wani laifi da tasan dalibi yana yi don a koreshi daga aji nata tafi qirqirarsa a sanda professeur ya shigo da nufin bada darasin mathématiques(mathematics).

"je le déteste(naqi jininsa)" ta fada tana jan qaramin tsaki. Abu daya zai hanata tayar da bori kanta tsaye kaman yadda ta saba,sanin da tayi aba yana a cikin gidan,kuma tabbas akwai mutane da yawa da sukeson ya gano ko yaga laifinta irinsu oncle maina,wannan ya sanya ya dake kawai.

Har ta saka qafafunta a step din farko na motar tanja na ajjiye mata lunch bag dinta sai ta janye da baya a hankali tana sake hada ranta,wani kyakkyawan tunani da kuma kyakkyawar dabara sukazo mata

"Fiddomin lunch bag dina tanja ba zan hau motar nan ba yau" baki a dan sake tanja ke dubanta,yau kuma da abinda suka tashi kenan?

"Eh cewa nayi bazan shiga wannan motar ba,daga yau na daina hada mota da kowa" tayi maganar tana sabule jakar bayanta,ta koma ta zauna saman kujerar plastic dage warwatse a gurin.

Kallon kallo su najma suka farayi a tsakaninsu,kowanne takaici ne fal zuciyarsa,amma kuma wanda zai fara furtawa a tsakaninsu ya gagara. Badon komai ba sai don sanin da sukayi mata. Idan bata kasa da kai ba kada ka sake kace zata dauka,bata barin kota kwana kamar yadda bakinta baiyin shuru,bata cuta amma iya wuya ba zata bari a cuceta ba,koda kafi qarfinta saita nema haqqinta.

Lamira da dukka ta fisu zafi zafi ce taja tsaki tana ninke takardun jarabawarta

"Kada Allah yasa ki shigo,daurin gindi kika samu shine zakina rainawa mutane hankali" akan gaba lamiran tayi maganar,saboda daman me tankata take jira,sai ta miqe zumbur ta zubda jakar tana dosar window din da lamira ke a zaune

"Dake nake?,ko nayi magana dake?" Ta fada cikin masifa tana kaiwa lamira hannu ta window da dogayen yatsunta dake lullube da lallausar farar fata,sai wani siririn zoben gold guda daya me masifar sheqi da daukar idanu dake a yatsan tsakiyar hannun nata. A ido idan ka kalleta sai ka zaci lausasan hannayen nata ba zasu iya duka ba,amma a zahiri ta naqalci fada da kafiya akan fada idan ta fara shi.

A nutse ya dire cup din da ya gama shan ruwan dumi da shi yana dan tattare girarshi saboda hayaniyar da ya fara jin a farfajiyar gidan.

A hankali ya miqe ta cikin balcony din nasa,ya qara gaba kadan yana qarewa wajen kallo.

Ta riqe window din motar da kyau,tanja da modu suna qoqarin hanata fadan amma taqi yarda. Kowannensu cikin takatsantsan yakeson janyeta amma ta maqale window din.

Sakin qarfen balcony din yayi yana maida slippers dinsa sanann ya juya yana nufar qofar da zata sadashi da farfajiyar gidan. Yana sake kusantar wajen yana kuma sake jin tashin muryarta cikin zaqalqalewa da masifa cikin siririyar muryarta. Ya hadiye wani abu me tauri ransa yana baci. Ita daya amma kowa na gurin qoqarin kawo qarshen fadan yake amma saboda tanason jan rigimar fadan yaqi rabuwa.

Dukkansu basu lura da isowarss wajen ba,sai ambatar sunanta da yayi wani da wani kakkausan sauti,abinda ya sakata tsaiwa cak
[4/18, 10:43 PM] C.E.O HUGUMA CLOSET: *_GUDUN ƘADDARA_*

*H U G U M A*

PAGE 12


,zuciyarta ta tsinke da tsoro amma wannan tarin kafiyar tata gami da taurin zuciya ya sanya batayi ko gezau ba a fili bare ta nuna hakan.

A nutse ya qaraso wajen yana dubansu a nutse

"Ku saketa" ya fadi a nutse. Sakin nata sukayi hakan ya sanya fa silalo daga jikin motar ta tsaya da qafafunta. Baibi ta kanta ba ya waiwaya ga tanja yana neman ba'asin abinda yake faruwa,inda inda tanja din ta soma yi masa,wannan ya sanya ya maida tambayar tasa ga lamira dake dab da window din.

Cikin nutsuwa da takatsantsan tayi masa bayani da harshen da zai fahimci komai. Sanda ta kammala maganar watsawa sultana wani kallo yayi yana hadiye bacin rai. Kullum sake lalacewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login