Showing 15001 words to 18000 words out of 51618 words
Chapter 6 - Gudun Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete
Duk yadda yaso ya zabge bacin da ranshi da zuciyarsa tayi amma hakan ya gagara. Yayi zaune a falon ama yana games bisa wayarsa,duk da hakan ba dabi'arsa bace. Cikin masu aikin ama din daya ta ajjiye masa madarar nonon raqumi me kyau da gardi,kasancewar tana daya daga cikin abubuwan da yakeso tun daga quruciya,dayar kuma ta aje masa ruwa. Duk da miskilanci cikin jininsa yake amma sunyi mamakin yadda ya dauki tsahon lokaci bai taba komai a ciki ba. Ama tana sama batasan da zamansa ba don bai qarasa can ba. Bata sauko ba har sai da habee ta shaida mata an kammala komai tazo ta duba kaman yadda aka saba.
Zabgegiyar buzuwa kuma ba'abzinar cikin shadda 'yar mali dinkin boubou take saukowa daga stairs din,daga wuyanta zuwa hannunta dauke suke da warwaraye da sarqa da suka qara mata kyau cikar ado da kuma zati.
Ita dinma bata lura da shi ba sai data kammala saukowa. Shi din shine d'a na fari a wajenta,yana da wani irin kaso me yawa na soyayyar 'ya'yanta qwalli uku dake zuciyarta.
Kallon farko tayi masa tasan ranshi a bace yake. Bacin ransa bashi da dadi sam,tasan wannan,ba kuma kasafai yake nunawa ko bayyanawa ba. Muddin dai kuma cikin gidan aka bata masa rai tasan baya rasa nasaba da bangaren bibi,indai daga sashen bibi ne kuwa ba shakka sultana ce.
Har zatayi magana idanunta ya sauka kan briefcase din mijinta da kyakkyawar luggage dinsa,abinda yasa ta fasa magana akan wancan yanayin nasa
"Aba dinku ya dawo ne?" Ta jefa masa tambayar tana tsareshi da kallo. Gyara zamansa yayi cikin kujerar yana zama sosai,saidai bai kalleta ba don yasan idanunsa kadai zasu gaya mata ranshi a bace yake,indai ta fahimci hakan kuma yasan zaiyi wuya bata fahimci meye silar bacin ransa ba
"Ya dawo,ya shiga wajen bibi su gaisa"
"Shine zaka zube masa kaya a nan?"
"Na shigo ban sameki ba" ya fada shortly
"Me ya hana kasa ayimin magana ko ka haura da kanka?"
"Am sorry" ya fada da harshen turanci.
Idanunta ta dauke daga kansa tana tabe baki. Itakam abun yana mata dadi ta yadda yake fahimtar yadda yarinyar ke neman zama gagarau cikin gidan,kaf yaran gidan babu wanda ake fama da case dinsa irin sultana,ba wanda take shakka cikin gidan bare kuma na waje. Zamanka lafiya kada ka shiga lamarinta,saidai kuma duk da hakan zata iya bugar qirji tace tana cikin jerin sahun mutanen gidan da ko kada idanu da zummar rashin kunya bata iyayi mata bare wani abu na daban. Batasan me yasa ba,amma tafi alaqanta hakan da rashin janta a jiki da kuma rashin shiga shirginta da batayi.
Takawa tayi zuwa kitchen din tanason tabbatar da komai ya kammalu yadda takeso,wanda tana shiga din aba yana shigowa,abinda ya sanya maina din miqewa
"A fito lafiya aba" ya fada cikin rissinar da kai cikin nuna girmamawa.
Da kallo aba ya bishi har ya fice,cikin gidan a qannensa guda biyu baisan zuciyar waye aliyyu ya dauko ba,ama cire ta marigayi shi ba'a maganar sa sam.
Muryar ama ce ta dawo dashi daga nazarin da ya fada. Macace me saurin karantar abubuwa da kuma gane inda abubuwa suka dosa
"Daga dawowa sai kuma ka fara tunane tunane aba?" A nutse ya maida dubansa gareta
"Bazan taba hutawa da tunani ba akan dukkan wani al'amari da ya shafi yaa hameedu ba" taku biyu tayi gaba kadan,ta saka hannu ta dauki briefcase dinsa ba tare da tace dashi komai ba,tamkar ma kuma bataji furucin nasa ba.
Batason me yasa tsahon shekaru goma amma ya gaza barin kunnuwanta da zuciyarta su huta da tuna mata al'marinnan ba tare da nanata mata abinda ya riga da ya shude,ya kuma wuce wucewa ta har abada. Tayi GUDUN K'ADDARA iya gudu,tana kuma fatan ba zata taba cimmata ba.
*_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
PAGE 09
Yana shiryawa bayan ya fito daga wanka tana taimaka masa amma yana karance tsaf da ita. Walwalarta ta ragu ainun,kuma dukkan alamu sun nuna shaguben da yayi mata dazun ya taba zuciyarta kamar kullum.
Tsaf ya gama shirinsa sannan ya samu gurin saman sofa bed ya zauna yana dubanta
"Nu'aima" yayi kiranta da sunanta na ainihi. Dara dara kuma farare sol din idanun nan nata da ya santa dasu. Tun daga quruciya har kawo girma suna nan basu canza ba su ta dago tana dubansa
"Why?,me yasa kowanne hali naki a bayyane yake amma kin kasa canza halinki akan duk wani abu da ya shafi nafissa,me tayi miki ne?" Sosai tambayar tayi mata tauri a ranta,ta gaza gane me ya sanya suka kasa fahimtar ta ne?,me yasa kowa ke mata bahagon kallo da kuma bahaguwar fahimta?,bayan sunfi kowa sanin wacece ita?.
Sai data gyara zamanta sosai sannan ta dubeshi,sai kuma ta kauda kanta gefe
"Har yanzu kun gaza fahimta na ne aba,nidai na sani iya iyawata,nayi abinda ya dace ne kawai da rayuwarmu gaba daya wanda nayi imanin inda an samu akasin hakan a yanzun ba wanda yake da guarantee na halin da duka ahalinmu ke ciki" nannauyar ajiyar zuciya aba ya saki,sannan ya saki wani siririn murmushi
"Amma kinsani bawa baya taba GUDUN K'ADDARARSA?" Tambayar tasa tazo mata wani iri,kamar ma zata iya cewa bata fahimci ainihin saqon da yakeson isar mata ba
"Kamar yaya kenan?"
"Kamar yadda ya faru" ya sake dilmiyar da ita ta hanyar bata amsar da ba ita take da buqata ba a sannan.
Iska me sanyi ta furzar a bakinta,sannan ta sake juya kanta gefe
"Na fada xan kuma sake maimaitawa,bana qin nafissa da tuni ta jima da gushewa cikin duniya,kamar yadda sultana batayimin komai ba da zan qita,inda ina qinta ne,da babu yadda za'a yi na bari maina yayi ruwa da tsaki cikin lamuranta......abu daya zan gaya muku,ku ajjiye komai ku dora rayuwarta bisa siradi da turbar da ya dace".
Tsam ta miqe ta fara hada kayayyakin da ya gama amfani dasu. Murmushi ya saki qarami,wannan kusan itace amsarta ta qarshe a duk sanda magana irin wannan ta hadasu,bata taba canzawa ba. Ya jima baiga tsayayyar mace me kamar maza irin nu'aima din ba,ba gudu ba ja da baya,bata kuma tsoron duk abinda ta tunkara.
Cikin qawataccen parlor din mallakin hamshaqiyar 'yar kasuwar HAMDIYYA ABDU ME KANO su biyu ne rak zaune a cikinsa. Sassanyar la'asar ce maras hayaniya dake busa sanyi kadan kadan maras shiga jiki sosai. Saidai duk da hakan hakan bai hana matashin ba'abzinen Aliyyu maina sanya wata lallausar baqar zipper hoodie sweater ba wadda ta fidda ainihin sassanyan kyawun fuskarsa,siriri kuma dogon hancinsa ya fita dodar saman miskilar fuskarsa dake a yanayi na babu yabo babu fallasa,dukka a hakan saboda yana tare da AMA dinsa.
Cikin takardu suke kaca kaca shi da ita,kyawawan zagayayyun idanunsa suna saman takardar hannunsa,ya tsareta dasu tsaf tamkar meson banbance ainihin launin dake jiki.
Baya yaja a hankali ya zauna yana miqe dogayen qafafunsa dake taka muhimmiyar rawa wajen zamtowarsu dogo kuma tsayayyen namiji,ya furzar da iska kadan daga bakinsa yana lumshe kyawawan zagayayyun idanunsa. Furzar da iskar da yayi ita taja hankalin hajiya hajja hamdiyya. Ta daga idanunta a nutse tana ajjiye kyakkyawan abun rubutun hannunta idanunta a kansa
"Yaya dai?,idan ka gaji a kawo maka haleeb mana" kansa ya girgiza a hankali ba tare da yace komai ba. Shurun itama tayi tana ci gaba da dubansa,ya motsa kadan ya ajjiye takardun hannunsa gefe
"Kina tara lissafi da yawa ama,wannan duka kafin wannan satin ya kamata ace kin fidda komai" qafarta tadan kada kadan tana dubansa
"Ka manta bani da mataimaki?" Ta jefa masa tambayar kai tsaye cikin salon son titsiyeshi.
Kansa yadan kawar,don yasan ya dauko maganar da zata janyo masa tarin qorafi dake wajenta
"J'ai besoin d'aide(ina buqatar matemaki)" ta fada da harshen faransanci,wanda ya kama bakinta da kyau fiye da zato,ba zaka taba tsammanin akwai wani yare saman harshenta ba bayan wannan. Cikin shi da ita din ba wanda ya sake cewa komai,sai ta jawo wayar dake saman wani qawataccen table na glass dake daura da ita ta fara danna numbers din da zata sadata da sashen kitchen dinta.
A taqaice ta bada umarnin abubuwan da take da buqata ta maida wayar ta ajjiye tana duban maina din. Tana da tarin tsaruka masu yawa a kansa,kasancewarsa dan fari a gareta da take masa hangaen kyakkyawar makoma. A dukka tsarinta da burinta maina din daga secondry school ya gama duk wani karatu a duniya,burinta shine ya fuskanci dukiyarta,tunda tarin dukiyar da mahaifinsa ya mallaka yana da tarin amintattu dake kula masa da kowanne sashe nata. Duk da hakan taso ace ya kasance shine shugaba a garesu gaba daya. Burinta akan rayuwar yaran nata qwalli biyu kacal me zurfi ne,tanaso ta basu gata da rayuwa me kyau fiye da wadda suka samu daga wajen nasu mahaifan ita da 'yaruwarta nuwaira.
"Me da me ka samu hadawa?" Ta sake tambayarsa tana kallon wayarta dake haske da idanunta ba tare data kai ga dauka ba,da alama bata shirya dauka din ba. Cikin nutsuwa da melodic voice dinsa ya dara fidda mata bayani dalla dalla.
A nutse take gyada kanta tana saurarensa,ba shakka ba qaramin alfahari take da maina din ba,yana da wata irin sharp brain,lissafinsa har tsoro yake bata,ba shine ke juya mata dukiya ba,ba kuma shike mata business din ba,amma kusan kaman ya fita sanin yadda kudadenta ke gudana tare da jujjuyawa,asara faduwa inda za'a samu riba da inda aka tafka kuskure.
A hankali tare kuma da wani irin qaqqarfan sound qarar kida ya ratsa muryar maina,lokaci guda kuma ya ragewa muryarsa kaifi da karsashi.
A nutse ya daga kansa yana duban Ama cike da mamaki,yana daha daga cikin nau'in mutanen da basa qaunar hayaniya kwata kwata. Itama ama din shi take kallo,tsaf ta karanci qwayar idanunsa da kuma tarin tambayoyin data karanta a cikinsu.
"Waye da wannan aikin Ama?" Yayi tambayar a nutse yana ajjiye document din hannunsa.
Bakinta ta mele kadan sannan ta amsa masa tana hade yatsunta guri guda
"Waye a cikin gidannan ya isa yayi wannan abun idan ba sultana ba?"
"Sultana?" Ya tambaya fuskarsa da sautin muryarsa cike fal da alamu na mamaki. Bata sake amsa masa ba sai jawo takardar data ajjiye dazun da tayi taci gaba da dubawa.
Kansa a qasa yana murza hannunsa cike da bacin rai,yana tunanin zai iya jure tashin sautin kidan har zuwa lokacin da wani cikin gidan zai tsawatar ya dakatar da kidan amma sai ya gaza jurewa. Saboda cikin qwarewa da wani irin salo yake tsinto muryar sultana din tana biye da waqoqin turawan qasar faransa din,tamkar tare da mawaqan suka rubuta waqar,abinda ya bayyana masa zallar tadda take saurarr tare da biyar waqiqinsu kenan sau da qafa.
Sake ture documents din yayi ya miqe fushi na soma cin zuciyarsa har ya soma tasiri saman fuskarsa.
"Ina zuwa ama" ya fada yana ficewa daga falon.
Baki ta sake tabewa tana girgiza kai. Yana daya daga cikin abubuwan da sukayi mata tsaye a rayuwa yadda mainan yayi tsaye cikin rayuwar yarinyar. Yarinyar da kaf gidan babu wani yaro da yayi miqewar qafar da tayi. Ko meye ne zatayi ba wani laifi nata fitacce da ake iya gani,ko yaushe tana da immunity,maina din kadai ne yake iya keta wannan immunity din. To amma me yasa shi din bazai sanya idanu kamar yadda kowa ya sanya ba?.
"Saboda nafissa" wata zuciyar ta bata amsa,sai ta saki siririn tsaki ta ajjiye takardar ta dauki wayarta.
Idan daga nesa kake ka kalli wajen zakayi tunanin wani gagarumin dinner party akeyi a wajen.
Dukka kusan tsararrakinta ne a wajen,wadanda sukayi shekaru dai dai da nata,sai kuma wadanda suka dara shekarunta da kadan. Abun ban mamakin da kuma daure kan shine,kusan dukkansu maza ne tsararrkin nata,sai mace qwaya daya a cikinsu.
Bayan tsananin baci da ranshi yayi harda tashi da hankalinsa yayi. Ba sau daya ba ba sau biyu ba indai idanunsa dai dai suke ganin yana ganin yaran kusan duk yammaci a farfajiyar gidan,saidai bai taba kawowa wai suna taruwa cikin gidan bane da zummar sunzo wajen sultana. Gaba daya tunaninsa na bashi gurinsu almu saddi da su atta suke zuwa. Yanzun kenan duk taron yarannan maza suna abota ne da sultana?.
Tambayar data sake tunzura bacin ransa,ya qara sassarfar tafiyarsa,fatansa kadai ya isa ga gungunsu da basusan ma da tahowar tasa ba. Yayin da shugabar tawagar sultana tayi nisa cikin wata irin rawa data sake bashi mamaki.
Yadda take lanqwasa jikinta zakayi tsammanin babu qashi ko daya cikin jikinta. Yadda kuma take rawar cikin karsashi kadai zai tabbatar maka hakan yana mata nishadi qwarai.
Tsaiwarsa guda daya ta dakatar da tarin hayaniyar da sukeyi a wajen. Kaf dinsu ba wanda hantar cikinsa bata kada ba. Sanda yasa hannu ya yiwa mp din nata wani wawan duka ta dauke dif saida kowa cikinsu yaji kamar yayi layar zana ya bace.
"Ku fice!" Ya fada da gigitacciyar fusatacciyar muryarsa.
Babu shiri har wani na ture wani suka soma laluben babbar katafariyar qofar data iyakance harabar farko ta gidan da haraba da biyu,inda ainihin ginin gidan yake da kuma muhallin da suke a zaune din.
[4/18, 10:43 PM] C.E.O HUGUMA CLOSET: *_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
Page 10
Yadda ya rakasu da kallo haka sultana ma. Saidai kuma abinda ke zukatan kowa tsakanin shi da ita ya banbanta da na danuwansa.
Zallar fushi da bacin ran yadda ya wargaza mata dabarta data saba hada musu dukka qarshen sati ita da abokai da qawayenta. Suci su sha su kuma cashe ba tare da kowa ya matsa musu ko ya adabba musu ba. Sai gashi yau rana guda daya tak,daga fara zuwar musu hutun tsakiyar karatu yana neman ruguje mata abinda ya kusan zame mata al'ada,akan meye?,ba wanda ya taba yi mata hakan a gidan sai shi?.
Ta gefan maina kuwa nashi fushin yasha banban da nata. Wani bahagon kallo yake jifanta da shi cike da zallar bacin rai dake cin zuciyarsa ainun. Abubuwa iri daban daban zuciyarsa ke qiyasta masa ya aikata mata da zai zama makwafi na daukan mataki ko kuma hukuntawa a gareta. Saidai kuma ta wani fannin ta qarfin tuwo yake danne zuciyar tasa,tare da sake gayawa kansa wacece sultana a garesa,sultanan nafissa ce,sultanan kamar d'iya take a wajensa.
"Wuce cikin gida tun ban tattakaki a wajen nan ba" ya fada a mugun tsawace. Har tsakiyar kwanyarta taji sautin qaqqarfar husky voice din nasa dake cakude da fushi,fushin da zuwa yanzu ta shiga sahun jerin mutanen da suka sakan qarfinsa da kuma illarsa.
A nutse kuma a hankali ta juya zuciyarta na wani irin raurawa. Kuka takesonyi na yadda ya bada ita gaban friends dinta,amma dakakkiyar zuciyarta na gaya mata
"Akul kada ki fara,kada ki yarda yaga lagonki kamar yadda yaga lagon su lamira"
Da idanu ya rakata daga nan inda yake tsaye yana hadiyar bacin ranta,tabbas inda yasan tafiyarsa da kuma yin nesansa da gida haka zata sake tabarbara al'amuran sultana.......haka zata sake maida sultana......haka komai zai sauya da ya haqura da tafiyar,da ya nemi afuwa daga wajen aba,yaci gaba da roqarsa ya barshi yaci gaba da lallaba karatunshi a haka.
Sai data fara nisa sannan ya ankare da shigar dake jikinta,shigar qananun kaya trouser da shirt inner da