Showing 3001 words to 6000 words out of 51618 words
Chapter 2 - Gudun Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete
a yashe a qasa. Tasa hannu ta kwashesu ta juya tana barin dakin.
Tsaye tayi gaban mudubin bandakin nata tana kallon fuskarta,sosai fuskar takeyi mata radadi,tasha ji a bakin su lamira cewa yaa maina din yana da zafin hannu,amma bata taba tantancewa ba sai yau,tunda bai taba kai hannunsa fuskarta ba. Hannu ta sanya ta sake shafar kuncin nata da yayi jajur,abinka da farar fata
"Dama haka zafin mari yake?" Ta tambayi kanta da kanta can qasa,saboda iya rayuwarta da kuma wayonta ba zata iya tuna lokacin da aka daketa bama bare a mareta
"Allah ya isa na" ta fada qasa qasa wasu sabbin hawayen suna zubo mata. Da baya da baya ta koma,tayi zamanta saman toilet seat tana ci gaba da fitar da sheshsheqar kuka. A iya marin da yayi mata yau kawai sai takejin wani mugun haushinsa irin wanda bata taba ji ba. Yaa maina din,shalelenta itama shalelensa,ba wanda ke tabuwa a wajen dan uwansa,amma yau sai taji ko fuskarsa bata son kalla.
Da zazzafan ruwa sosai yayi wanka bayan ya gama dukka uzururrukansa na ranar,da dan wuri yaso shigowa gida saboda yanayin sanyi da ya fara busawa,amma kuma daukan karatun da ya tsaya yi a zawiyya yasa lokacin shigowarsa gidan ya dan ja. Yana shiryawa yana bin tsarin dakin nasa da kallo,yaja tsaki lokacin da ya bude wardrobe dinsa yana bin shirin kayan da kallo.
Hannu ya saka ya zaro wata turtle neck sweatshirt me dogon hannu baqa,wadda ta fidda zallar hasken fatarsa da kuma narkakken kyau da yake shimfide a fuskarsa,wanda ke cakude da qyalli da sheqin samartaka.
A nutse ya shirya,idanunsa saman agogon dakin nasa ya dauki wayarsa yana shirin ya fita. Kamar jira wayar keyi ta dauki tsuwwa,sai ya dakata ya maida hankalinsa kanta.
'BIBI NA' shine sunan dake yawo saman screen dinsa. Daga wayar yayi yana ci gaba da shirin fitar.
Muryar Dijama ce, cikin d'ari d'ari da takatsantsan take gaya masa saqon bibi
"Okay" kawai ya fadi a taqaice yana katse kiran. Iska me zafi ya furzar daga bakinsa
"Me ya faru ne bayan tafiya ta?" Ya yiwa kansa da kansa tambayar da shima neman amsarta yakeyi. Gaba daya sauyin halayya da dabi'u yake gani daga yarinyar. Yarinyar da ya bata dukkan wani minti da awa dake cikin rayuwarsa wajen ganin ya raineta rayuwa me kyau,ya bata tarbiyya da tasha banban da ta kowa,ya kuma killaceta fiye da yadda ake killace kowacce diya mace dake jahar maradi,sai gashi tafiyarsa da waiwayo gida da yayi komai ya kwabe ya canza.
Iskar ya sake fesarwa,sai ya soma fita a dakin a gaggauce,can qasan ransa cike da tunani tare da son gano ina matsalar take?.
Zaune ya sameta cikin parlor din nasu,sanye da sassauqar doguwar riga me gajeran hannu,kantan nan yasha gyara qwarai,hannayenta dake sanye da wasu siraran warwaraye riqe da jarida tana dubawa. Farar ba'abziniya,wadda ke tafe da tsaho da qiba dai dai gwargwado. Tana da wani kyau na musamman wanda shekarunta basu kai ga boye shi ba.
Sallamarsa ya sanyata daga kanta ta dubeshi,sai ta sauke qafafunta da suke a harde a dazun ta gyara zamanta sosai tana amsa masa sallamar.
A gefe ta ajjiye jaridar tana dubansa har ya qaraso. Cikin girmamawa ya zame ya tsugunna a gabanta
"Barka da wuni"
"Barkanka,tun dazu nake maka aike ka fito kaci abinci amma hakan ya gagara" agogo ya sake kalla,tabbas yana toilet yaji shigowar almu har sau biyu
"Wanke nakeyi,ina kammala shiryawa kuma na fito"
"Saika qarasa kaci abincin ko?" Ta fada tana miqa hannunta da nufin daukar jaridarta.
"Zanje sashen bibi,yanzu zan dawo sai na zauna gaba daya" tsaiwa tayi da abinda takeyi,ta kalleshi yanayin fuskarta yana canzawa
"Me kuma zakayi a sashen bibi bayan na tabbatar tun safe bakaci komai ba?" Cikin lanqwasa murya da salon lallashi irin wanda ita daya yakewa duk duniya yace
"Yanzun zan dawo AMA,zanyi magana ne da sultana"
"Sultana?......kai dawo ka zauna" ama din ta fada tana sake sauke qafafunta qasa.
Yadda ta buqata haka ya koma ya zauna sosai yana lanqwashe qafafunsa,zama tayi sosai ta zuba masa idanu tana jin wani zafi yana ratsa zuciyarta,ME YASA TAKETA GUDU AMMA KAMAR K'ADDARA NA BIBIYE DA ITA?.
"Wai sai yaushe zaka san cewa ba ahalin su NAFEESA na haifawa kai ba?,sai yaushe zaka daina bautawa abinda ya shafi nafeesa da rayuwarta gaba daya?" Maganar ta sauka a wani muhalli me girma na zuciyarsa,ta kuma taba masa wani gurbi da bayason ta taba masa din har sai da ya dan lumshe idanunsa kadan ya bude,wanda yayi dai dai da sake magantuwar ama
"Tunda na haifoka ruhinka ke walagigi a hannunsu,tun kana da shekara sha biyar ka fara fuskantar qalubale duk don saboda su,da jajircewata da tsaiwata akan rayuwarka na kawo qarshen komai,a yanzun bayan komai ya shude da shekara kusan goma shine kakeson dorawa daga wata bautar da wahalar?" Tayi masa tambayar data sanyashi sake lumshe idanunsa kawai. Cikin tsakiyar zuciyarsa yake bawa kansa qwarain gwiwa,ya saisaita kansa zuwa harshensa sannan cikin tarin nutsuwar da tun yana qanqaninsa ta sanshi da ita
"Ni da nafeesa da sultana duka abu guda ne yayi mu,idan ba jinin nafeesa a jikina ama akwai jinin sultana,ita din qanwata ce halak malak,uwa daya ce kawai bata haifemu ba,amma uba daya muke ni da........"
"Aliyyu!" Ta kirayeshi da ainihin sunansa
"Banason kaci gaba da gayamin wannan labarin qanzon kuregen......". Yankewa maganar tata tayi sakamakon shigowar kira wayarta.
BIBI ta gani,sai ta dauke dubanta daga kan wayar ta maida akan maina,sanann ta sake kallon wayar a karo na biyu kafin ta daga
"Okay" kawai ta fada a taqaice,sai ta sauke wayar sannan ta maidata gefe ta ajjiye
"Maina" ta kuma kiransa,ba tare da ya amsa ba yayi qas da kansa
"Duka duka shekarunka ashirin da hudu ko da biyar a duniya,karatu nakeso kayi,ka zama mutum kamar kowa,banaso ka harmutsa rayuwarka cikin matsalolin da ba naka bane,bakai bane tilashinsu,kabar masu matsala suji da matsalarsu,so nake kayi karatu,ka zama wani,domin kaine madubin qannenka,kuma kaine gobe na" Yadda tayi maganar kadai zai fahimtar dakai zallar qauna da soyayyar da zuciyarta ke gwada masa. Ya sani,ama tana masa wata soyayya ta daban,wadda tasha banban data qannensa ma,bai sani ba,shin ko soyayyar ɗan fari daban take da a zukatan iyayensu?.
Wani qaunar ama ne ya sake saukar masa,tabbas duk abinda takeyi yasan tana yine saboda soyayya da qauna irin ta ɗa da uwa,to amma shi ɗin ta yaya zaya zuba ido ya bari tarbiyyar sultana ta samu rauni?,yarinyar da tunda sanarwar haihuwarta ya shiga kunnuwansa yakeji a jikinsa kamar shine mahaifinta?,kamar rayuwarta da haƙƙin kula da ita ya hau kansa kacokam.
"In sha Allah zan kula iya bakin ƙoƙari na,ba zaki sameni da wani abu da bakiso ba"
"kaje bibin tana kiranka" ta faɗa da sautin da zai nuna maka akwai hushi danƙare cikin ranta.
*ZAFAFA BIYAR FAMILY*🫂🫂🫂🫂🫂
🔥 *me kike jira ne da har yanzu baki shige ahalin zafafa ba*
*_ZAFAFA BIYAR_*❤🔥🔥❤🔥🔥❤🔥🔥
❤🔥 *_SABUWAR SHEKARA_*
❤🔥 *_SABON TSARI_*
❤🔥 *_SABBIN LABARAI_*
❤🔥 *_TSUMAMMIYAR SOYAYYA_*
❤🔥 *_CAKWAKIYA_*
❤🔥 *_LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DAKE TAFE DA WANI IRIN SALO_*
❤🔥 *_SALON DAKE DAUKE DA ZALLAR GOGEWA DA QWAREWA WAJEN SARRAFA ALQALUMA_*
❤🔥 *LABARANSU NA MUSAMMAN NE DAKE DAUKE DA WANI IRIN SALO ME RATSA JIKI_*
*_KWANTAR DA ZUCIYA_*
*_CIRE DAMUWA DA SABUNTA SOYAYYAR MASOYA_*
*QAWATATTU KUMA TSARARRUN LABARAN 2024 DIN SUNE KAMAR HAKA*
*KWANKWASON JIMINA* _ME WUYAR TABAWA_ (miss xoxo)
*TSUTSAR NAMA* _ITAMA NAMA CE_ (Billynabdul)
*AMEENATU* (Mamuhghee)
*GUDUN K'ADDARA* _GUZURIN TARAS DA ITA_ (Huguma)
*_KOWANNE LABARI NA DAUKE DA SUNA ME HARSHEN DAMO,KAMAR YADDA GUNDARIN LABARIN KE DAUKE DA SALON DA ALQALUMAN ZAFAFA BIYAR NE KADAI ZAI WARWARE MUKU SHI_*
*_Biya naki ta wadannan lambobin domin ki zamo cikin ZAFAFA FAMILY HOUSE_*
*TSARIN SHINE KAMAR HAKA*
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*THANKS FOR CHOOSING US*🫂🫂🫂🫂
*_GUDUN KADDARA_* 🏃🏽♀️
*HUGUMA*
PAGE 03
https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz
Har ya kusa fita ya dakata,ya waiwayo yana dubanta. Kallon jaridar kawai takeyi amma da alama bata iya ci gaba da karanta komai ba
"Don Allah ama almu ko atta,wani yayimin kiran najma ta dawo ta sake gyara dakin nan baiyi ba" fararen idanunta ta daga ta kalleshi dasu
"Ba d'iyar wadda zan kira ballantane ayimin gorin rashin diyoyi mata,ko wannan gyaran ma atta na saka yayi maka,suma a hakan zasu koya,tunda ko yanzun ma wasu abubuwan sukeyi min,banga abinda diya mace zatayi wanda zai gagari namiji yayishi ba" Dan qaramin miskilin murmushin nan nasa da yafi kama da motsa baki yayi. Abu guda daya tal da yasan ya jima yana ciwa ama tuwo a qwarya shine rashin haihuwar 'YA MACE,shi kuma ya jima da ciwa kansa wani alwashi game da hakan,alwashin da ita kanta bai sanar mata ba har yanzun
"Kiyi haquri zan saka a turota tazo ta gyara" kai tsaye ta sake dubansa
"Ka wuce ka tafi,kafin ka dawo zan shiga na gyara maka da kaina" kansa ya girgiza da sauri
"Karkiyi wahala,zan sake gyaran"
"Nidai iya abinda nace maka kenan" ta bashi amsa a taqaice tana maida kanta ga jaridarta.
Har ya isa sashen bibi zuciyarsa bata huta da tarin tunani da son gano laifin da nafeesa ta yiwa ama ba wanda har yake shafar SULTANA a wajenta,nafeesar da har tabar duniya bata da abokin fada,nafeesar da har ta gama rayuwarta badai kaji ance an kawo qararta ba,nafeesar da har tabar duniya ko musu bata iya ba bare sa'insa da wani. Laifin nafeesa daya ne LALURARTA indai har lalura da ciwo suna iya zama laifin dan adam......indai har suna iya zama kuskuren mutum da har Allah ya zabi ya dora masa ciwon,banda wannan shikam bazai iya adar da komai ba.
Kaf tunaninsa ya yanke lokacin da ya isa dakin sultana din,ya samu masu aikin gidan da su lamira sun cika dakin suna mata magiyar ta fito. Ransa ya baci lokacin da yaga bibi zaune a gefe,itama tayi magiyar tayi magiyar har ta gaji. Shigowarsa kadai ta sanya muryoyinsu daukewa,kowa ya shiga taitayi da nutsuwar sa. Shurun kuma shi ya isarwa da sultana cewa tabbas maina dinne ya shigo,shi daya ke da wannan fitinanniyar kwarjinin dake karya lagon kowa.
"Ni wallahi bazanji tsoronka ba" ta fada qasa qasa tana jan qwafa hadi da hararar qofar bandakin tamkar shine tsaye a wajen
"Duk ku fita" ya basu umarni yana takawa zuwa bakin bandakin.
"Anyi magiyar anyi lallashin amma taqi ta bude,tunda ta shiga take zaune a ciki,kamar wadda ta samu dakin gyatumarta" bibi ta fada hankalinta adan dage tana kallon maina da ya sanya wani dan scissors yana qoqarin warware lock din qofar. Kanzil bai ce da bibi ba. Sultanan na zaune daga ciki,amma tana iya jin kusur kusur dinsa jikin qofar. Sake hararar qofar tayi,don ta tabbatar bai isa yace zai bude qofar ba muddin idan ba itace tayi ra'ayi ta bude ba.
Kadawa hantar cikinta tayi sanda taga ya tura qofar ya bude,ya kammala warwareta tas kenan.
Tsam ta miqe daga saman toilet seat din tana kallon qwayoyin idanunsa data jima da sanyawa suna da LION EYES,ta fada ta sake fada,a duk sanda yake kallonka irin haka,idanun nasa basa mata kama da idon kowa sai idon zaki sanda yake kallonka cikin fusata,tun ranar da sukaje zoo tace wai ta tantance hakan. Tun su chafa'atu na mata dariya har suma sukayi amannar hakanne.
Yadda ya qureta da kallo ya zuba mata ido itama hakan tayi masa,abinda kaf rayuwarsa yafi tsana kenan,kayi laifi sannan ka tsare mutane da kallo kamar sa'anninka?. Duk wani yaro da ya girma ya taso a gidan yasan baya son wannan dabi'ar,sun kuma kiyaye,abinda ya zaunar dashi da su lafiya kenan
"Zo ki fita a gurin" ya fada mata a tsawace,tsawar da taji kamar zata tarwatse da kwanyarta,ta gigitatata har sai data kulle idanunta gaba daya hadi da qanqame jikinta guri daya. TSAWA na daya daga cikin abinda ta tsana,saboda muddin kayi mata ita ka gama birkitata kenan. Duk da kafiya taurin kai da zafin zuciyarta kuwa.
Idanunsa ya lumshe had'i da budesu,yadda tayi din ya tuna masa da naffeesa,abinda ya sassauta ranshi da zuciyarsa kenan,ya kuma sassauta muryarsa
"Fita nace tun kafin na sake kai hannuna kanki"
"Taho muje,ya isa hakanan" muryar bibi ta ratsa toilet din. Ita ta sanya hannu ta jawota ta fito da ita daga bedroom din,ya tako a hankali ya biyo bayansu yana sake karantar canjin halaye matuqa daga gareta. Musu,taurin kai,tsiwa,rashin kunya da rashin tsoro
"Saketa bibi,ta canza kayanta ta fito taci abinci,kuma wallahi kika wuce minti goma sai na zane miki jikinki,dukan da ban taba kwata yi miki shi ba" ya fada yana juyawa yana fita a dakin.
Da jiqaqqun idanunta ta bishi da harara tana jin kamar zata hadiye da zuciyarta
"Wai shi me nayi masa?,daga dawowarsa yabi ya takura mutane?,kuma ai da ba haka yake ba,salon muguntar da aikin sojin suka fara koya masa kenan?" Dafe goshinta bibi tayi,gaba daya sultana din ciwon kai takeson bata
"Ke bakiga kin canza ba,kin zama mara kunya,ana gaya miki kina musu?,idan akace ki bari ba zaki bari ba,to na godewa Allah da dawowar tasa,shi kadai ne maganinki ai" wani baqinciki ya mamayi zuciyar sultanan,kamar ita za'a ce wai wani zaiyi maganinta?.
"Ki gaya masa ya fita a hanya ta to,ai zama yaya da qanwar ba dole bane,kuma bai isa yayi maganina ba Allah,saidai muyi maganin juna" ta fadi tana soma zare kayan jikinta. Zata shirya taje din bawai don tana tsoronsa ba,saidai don kawai bata qaunar duka,bata qaunar abinda zai taba lafiyarta sam,daga lokacin daka saka hannu a jikinta to ta daura da kai kenan,ba ita babu komai,saidai kuma ka shiga uku a gurinta.
Bibi tana tsaye har ta gama shiryawa abinta,riga da wando ta sanya,skinny jeans mara nauyi,sai shirt dinsa me gajeran hannu,sako sako lallausar sumarta da tsahonta ke sanyawa saidai ta lanqwasa ta sau biyu tayi,don ribbon din dake kantan saboda bala'in da takeji bata ko tsaya gyarashi ba.
Light blue ne kayan,sun yi masifar yi mata kyau,sun haska jar fatarta qwarai,idan ka kalleta zaka dauka ta fito ne daga yankin india ko qasashen larabawa. Tun asali kyan sultana na dabanne,wanda akayi ittifaqin ita daya ce tal ta dauko ainihin kamannin LAILA babar kakanninsu. Har yanzu daidaikun tsofaffi da manyan dake cikin unguwarsu dake tushen jaharsu ta AGADEZ basu manta da LAILA ba,tarihinta bai goge ba,macen data zuba kyau daya banbanta da kyawun kowacce 'ya mace da tayi rayuwa ƙarni guda da ita.
A saman kujerun dining din suke zaune,biyu cikin masu aikin gidan na kaikawon shirya abincin daren a samansa. Ysatsunsa cikin na juna,idanunsa zube fes akan fuskar bibin. Cikin nutsuwar da tun yana mitsitsinsa ta zame masa dabi'a kuma halayyarsa yake magana
"Amma why bibi?,me yasa za'a bari halaye da dabi'unta su canza?,ya akayi sultana ta canza?,ba haka na tafi na bar muku ita ba" ya fada har tsakiyar ransa yana jin radadin rushewar tubalin ginin tarbiyyar da ya fara yi mata,wadda tasha banban data qasarsu.
"Duk wani iya bakin qoqari inayinsa mainassara,to amma kasan komai yana da alaqa da muhalli da kuma abokan mu'amala na yau da gobe" kansa ya girgiza yana furzar da iska me zafi daga bakinsa
"Bibi,goumar ya fara fadamin,mais(but) na dauka kawai surutu ne irin nashi,certainement(definitely)banji dadin abinda idanuna suka tarar ba". Ajiyar zuciya bibi ta saki,itadai ta sani,babu ta inda tayi sake ko saakcin tarbiyyar,tun daga kan uwayensu ma ballantana su,kwadayi da son samun cikakkiyar tarbiyya ya sanya ta yiwa hamidou magana,suka tattara suka bar niamey izuwa maradi,maradinbda take kallo da hangen sunfi kusa,alaqa ta qut da qut da nigeria. A nutse take masa bayanin iya abinda zai iya fahimta. Kansa a duqe yana latsa wayarsa tare da sarrafa maganganun bibi cikin kansa,yana kuma son lanqwashe bakin matsalar da kuma yadda zai bullo mata. Nunfashi ya zuqa yana daga qawatattun idanunsa wadanda suke da wani irin shape,idanun da sultana din ta sakawa suna da yeux de lion(lion eyes) ya zubesu kan tafkekiyar TV plasma din dake maqale a bango,suna haska labaran dare a channel din niger 24tv. K'aramar yarinya ce da bayanta ya mamaye fuskan tv din,tana bayanin yadda wani matashi yayi mata fyade(rape). Kasuwa hankalinsa yayi gida biyu,fiye da rabin hankalinsa yana kan labaran,yayin da wani kaso dan kadan kunnuwansa ke ga bibi.
A hankali wani abu ya soma tsaya masa a rai,bacin rai ya fara sauka a hankali saman zuciyarsa yana mamayeta. Maqurar bacin ran da hatta bibi dake zaune a wajen sai data fahimci hakan.
Wani dogon tsaki mai matuqar sauti ya fidda,dai dai sanda tani shugabar masu kula da sassan bibi ta kawo tray na qarshe ta ajjiye
"Miqo