Showing 33001 words to 36000 words out of 51618 words
Chapter 12 - Gudun Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete
batun kwata kwata,ba hurumina bane,kai kafi kowa sanin haka,ni zan taba diyar nafessa?,a wanne matsayin kenan?,hatta da ubanka ka manta kallon da yakemin a kan sultana?" Kansa ya mirgina gefe,wannan maganar ta tsahon shekaru kudan sha uku zuwa sha hudu ta gaza mutuwa
"Karki duba wannan duka ama"
"A matsayina na wa?" Ta jefa masa tambayar
"Yarki ce ama jikarki ce kema"
"Kaine kaga haka,tashi ka bani guri maina,ni bana sanya kaina a abinda bai shafeni ba ko zai taba mutuncina"
"Sultana bata tana miki rashin kunya ba,bazata miki ba ama"
"Ka bani guri nace ko?kaidai da kaga zaka iya sai kayita yi...." Dauke kanta tayi tana qwalawa saddi kira
"Dauko remote ka canza min channel" ta fada tana sake bude album din nata,saidai can qasan zuciyarta itama wani abu yana tsunkulinta amma tana qoqarin kautar da kanta da tunaninta daga kai. Haka ya qaraci zamanshi a gabanta ya miqe jiki a sanyaye ya fice a falon.
[4/18, 10:43 PM] C.E.O HUGUMA CLOSET: *_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
PAGE 19
*_THE DESTINY |_*
Su hudu ne zaune cikin falon bibi da babu kowa sai tanja dake kai kawo ita da biyu cikin masu aikin bibi.
Su biyar ne a falon,hanan maama rachida bilkissou sai kuma sultana din. Dukkaninsu su biyar din kowacce idan ka kalleta akwai alamu na samun cikakken gata a tattare da ita,cikin duba na biyu kuma zakasan kowacce ta fita ne daga gidan da sukunin rayuwa ya samu muhallin zama. A tsakanin su biyar kowacce shekararta tsakanin sha biyu ne zuwa sha uku,saidai tarin iyayinsu da rawar kai zakayi tsammanin sun tasamma shekaru sha takwas takwas ne. Sosai halinsu yazo daya,shi yasa abota a tsakaninku keda matuqar qarfi da tasiri,duk wanda yasan daya a cikinsu yasan daya,kowaccensu tana ji da gata da kuma sakewa,duk da cewa a cikinsun babu kamar sultana,wadda bayan fifikon gata data samu,ta samu wani irin fifiko na kyawun sura tun gabanin ta kammala cika mace. Ta mugun iya dressing kamar yadda yaren faransanci ya zauna daram a harshenta,hakan kuma baya rasa nasaba da zaman da tayi a waje cikin turawan faransa na tsahon wasu shekaru harta kammala primary dinta.
"Ni so samu da magariba za'a fara birthday dinnan maganar gaskiya sai yafi dadi" sultana da ta qare karanta katin birthday din hanan ta fada tana maida dubanta ga fuskar rachida. Qaramar dariya rachida ta saki
"Allah ya shiryaki kedai,duk wani harkar rawa kina gaba gaba" ido sultanan ta lumshe
"Hmmm ke bakisan yadda rawa take da dadi bane,Allah ji nake kaman na fara takawa tun yanzu,ni hanan kin gama biyana,irin wannan birthday din nakeson yi qarshen shekarar nan" sultana ta fada tana tashi ta zauna sosai saman kujera,saboda tana hasaso yadda abun zai kasance
"Idan yaa maina ya bari ba" bilkissou ta fada tana zuqe madarar hannunta.
Harara sultana ta jefa mata
"Kina daga kwance kina shanyen madara kina min fatar tsiya,wanne ya maina din da yanzu baya zaman gidan nan ma,saidai munafukai irinsu goumar su gaya masa"
"Baqin buzu?,yana burgeni wallahi" hanan ta fada tana dan murmushi. Caa sukayo mata suna tsokanarta,yayin da sultana ke binsu da ido tana tabe baki. A rayuwarta haka kurum taji ta tsani koda zancan soyayya ma,duk da su din wannan ba fagensu bane dama,ba wani abu bane da sukeyin Maganarsa ba
"Meye abun burgewa a wajen wannan?,kaf halin yaa maina daidaiku ya baro" sultana ta fada tana tabe baki
"Wai ina su najma"
"Kin kuwa tunamin,basu nasu card din" idanu hanan ta zaro
"Ko kema fa lallabawa zakiyi kije baresu?"
"Kada ki damu,sun jima suna cewa a gayyacesu idan za'a yi,barema duka date din da aka saka dodon nasu baya nan,kinga nima hankalina kwance zamuje mu dawo abinmu ba wanda zaya matsa mana,wannan babban hotel da dad ya kama mana hall a ciki ai ya gama mana komai" ta fada tana dariya.
Sun jima suna hirarrakinsu suna sake tsara yadda zasuyi abinsu
"Sauran abinda m ba zamu iya ba auntie haula tace zata tsara yadda komai zai tafi mana yadda mukeso"
"Sai auntie" sultana ta fada tana dariya, tana jin dama itace cikin gidansu hanan,babu matsi babu kuma takura.
Sallama sukayi da Bibi ta rakosu makeken parking lot dinsu inda suka zaunar da driver dinsu yana jiransu. Sai da suka fice a gidan sannan ta juya ciki tana gyara card din hannunta.
Sassan uncle umar t soma shiga,ta samu mamma na sanya turaren wuta a falo. Gaidata tayi mamma ta amsa tana dubanta yadda ta shigo a wani mugun nutse
"Najma fa?"
"Suna daki ita dasu aminata" bata ko waiwayo ba ta zarce dakin da zumudinta,sai mamma ta bita da kallo har ta shige sannan ta dauke kanta tana ci gaba da zuba turaren wutan.
Cikin sa'a dukkansu ta samesu a dakin,aminata najma yasmin da lamira
"Kuzo kuga wani abun arziqi" ta fada tana rarraba musu card din. Karban nashi kowa yayi yana dubawa,najma ce ta fara daga kai
"Birthday din hanan?,haka akeji da ita aka kama mata wannan babban hall din?" Dariya sultana tayi
"Don hall kawai?,sai kinje ma kinga yadda aka tsara gurin"
"Zuwa kuma sultana?" Aminata ta fada tana zare ido. Da wurwuri sultana ta jefeta da harara
"Eh mana,hanan ce fa,kuma idan ya maina kuke tsoro ai baya nan,hasalima shekaran jiya duka duka ya tafi,shi kuma da sake dawowa sai wani satin nan da kwana goma ma,kunga hankali kwance zamuje mu dawo" shuru suka danyi suna kallon juna
"To ta yaya zamu fita su mamma basusan birthday muka tafi ba?"
"Karku damu da wannan kun manta ina da modu?" Dariya suka saki plan din nata yana musu dadi. A nan suka sake suna maida yadda abun zai wakana.
Tun daga ranar take shirya kaya da shigar da zatayi. Duk da dimbin suturunta da suka kusa kala dari biyu amma sai taga sam basuyi mata ba. Ta tashi hankali har sai da aba yasa aka dauketa taje ta siya abinda ranta yakeso da sunan wani taro zasuyi a makaranta. Ba wanda ya qaryatata tunda makarantarta daban data sauran.
*_THE DESTINY ||_*
*****Wadatacce kuma yalwataccen daki ne wanda a qalla yake dauke da manyan katifu masu azabar tudu da taushi guda uku. Turkey carfet ne malale a qasan dakin wanda ya dace da curtains dake maqale jikin manyan windows da qofar dakin.
Ba wani tarkace a dakin,domin kuwa komai yana tsare ne bisa muhallinsa cikin tsaf da kuma wayewa. Akwai babbar cupboard ta jikin bango wadda daga samanta akwatune masu kyau a qalla sunkai shida mallakin samarin dakin.
Daga gaban murfin cupboard guda daya maina ne a tsaye yake dauko wankakkun kayansa dake shimfide a ciki suna fidda qamshin sassanyan mayataccen turarensa yana jerawa cikin wata kyakkyawar madaidaiciyar luggage milk color da torches na Navy blue a jikinta. Daga yadda yake zaro kayan yana jerasu a ciki zakayi tsammanin yana yine saboda tsabar yanga da kuma salo irin nasa. A'ah,a yau din ba haka take ba,domin kuwa tun daren jiya ya tashi baya jin dadin jikinsa sam,wani irin kasala da mugun ciwon kai harda tsarabar guntun zazzabi su suka tayashi kwana. Zuwa wayewar garin yau kuma yaji babu abinda yake da buqata irin yaje gida,duk da cewa suna tsakiyar karatunsu da ya soma daukan zafi da gaske.
Wani matashinne kamar shi yayi knocking qofar sannan ya turo ya shigo dauke da jakar leda dake dauke da tambarin wani gidan abinci dake nan kusa da ecole din nasu. A bayansa wani matashinne da dukkansu shekarunsu zasu zo guda.
Kadan ya waiwaya yana amsa sallamar tasu sannan yaci gaba da qoqarin zuge zip din luggage din
"Ami(aboki)Me nake gani?,ya da hada kaya cikin bagage(luggage)?" Ya fada yana neman daya daga cikin sofa da suka qawata dakin da ita ya zauna akai idanunsu dukka su biyun suna kan maina din. Idanunsa yadan lumshe kadan yana jin kansa yana dan sarawa kadan duk da yadan samu sassauci
"Gid nikeson zuwa,amma gobe ma zan dawo ko lundi(monday)"
"Kace dai kawai raki zaka nuna da langwai,kanaso kaje ama tayi jinyarka" murmushin gefen baki kawai yayi,da mahadi da sultan din dukkansu gwanayen tsokana ne,ana cewa sai hali yazo daya ake abota,to amma su a kansu abun ba haka yake ba,akwai banbacin halaye da dabi'u masu yawa tsakaninsu. Kusan dukkan abokansu dake shigowa dakin mahadi da sultan ke kawosu,don ta maina kam shi daya ma zai iya qare zamanshi.
Yana jinsu sunayi masa tsiya ya wuce toilet dinsu dake manne cikin dakin,ya fiddo brushes dinsa da toothpaste da sauran kayan wankanshi ya dawo ya qarasa hada kayanshi. Order yayi na mota har cikin makarantar,ta iso bakin hostel dinsu sultan da mahadi sukayi masa rakiya har ya tashi.
Lamo yayi cikin motar,bai motsa ba har sai da kira ya shigo wayarsa. Da ya duba da kyau sai yaga meena ce,yaja siririn tsaki yana maida wayar silent ya jefata cikin jakar hannunshi da ya zuba qananun tarkacensa. Yadanbi jakar da kallo,shi da yace gobe ko jibi zaya dawo,besan me ya sanyashi debo kaya haka ba.
"Alhamdulillah" ya fada a nutse sanda ya sauka tsakiyar farfajiyar gidan yana duba yadda sassan gidan yayi shuru. Sake duba wrist watch din hannunsa yayi wanda ke dauke da sunan kowacce rana yanason ya gani ko yayi kuskuren tunanin yau din weekend ce saidai kuma koda ya kalla dai dai lissafinsa ya bashi. Bai tsawaita tunaninsa ya janye luggage dinsa kansa tsaye ya wuce sashensa,don duk cikin mutanen gidan yasan ba wanda yasan da zuwansa.
Ko yaya yaje makaranta ya dawo bai iya zama a daki haka,mafi yawan lokutta ma ama na sanyawa a gyara masa ne tun kafin ya iso din saboda saninsa da tayi da shegen tsantsami da tsaftar tsiya. Yau ba wanda yasan da zuwansa bare yayi masa wannan tanadin,don haka ya zage ya gyara dakin nashi yadda yakeso sannan ya shiga wanka.
Yaji qwarin jikinsa sosai,kamar ciwon dama yana jira ya baro makarantar ne. Wannan ya bashi damar shiryawa cikin trouser silk shirt me gajeran hannu. Ainihin cikar zati da surarsa suka fito muraran,kyakkyawan ba'abzinen matashi aliyyu haidar mayak'i.
Da salon nutsuwar nan tashi ya wuce zuwa sassan bibi. Duk yadda sukayi fada ko suka samu sabani,duk yadda sukaso share juna ita dashi amma hakan bai yiwuwa,shi yasa sam ba'a shiga fadan bibi da haidar maina,idanma ka shiga din kaine da jin kunya. Sai daya dan kalli sassan amansa kadan kafin ya shige,ya san muddin taji ya shigo gidan ba ita ya fara nema ba saita nuna masa fushinta koda da kalaman baki ne,sai ya qudirta a ransa bazai jima wajen bibi din ba,zai fito yaci abinci a wajen ama din nasa. Dab da zai shiga saqo ya shigo wayarsa,sai ya rage sassarfar da yakeyi yana dubawa.
Tailor dinsa ne yake gaya masa ya kammala dinkunansa duka,zaiyi tafiya zuwa diffa,idan baya gari ya aiko daga gida a karba masa,kada ya buqacesu shi kuma baya nan. Saqon ya rufe yana rayawa a ransa zai fita idan ya gama cin abinci ya karba,ko miqe qafarsa ya danyi qila ya sake jin qwarin jikinsa.
Baki bibi ta sake da ganinsa,abinda basuyi tsammani ba tunda duka duka wancan satin ya tafi,kuma a yanzun yakanyi sati uku ma baizo gidan ba
"Hala kewar matarka ta isheka kazo ganina ko?" Bibi ta fada tana dariya. Fuska yadan yamutsa kadan yana dubanta sannan ya nuna qirjinsa da yatsanta
"Ni maina?,Allah ya kiyaye,na barwa su saddi" wasa ne da ba kasafai suke yinsa ba ita dashi,amma duk sanda kaga ta jashi da wasan to tabbas tana cikin nishadi ne da jin dadin ganinsa.
Suna gama gaisawar bai jima ba ya miqe
"Bari na qarasa ciki"
"To,saika fito".
Kyakkyawan falon da ko yaushe yake cikin tsafta da kyau,komai nashi bata taba bari ya tsufa ko kyansa ya disashe. Ba kowa cikinsa sai masu aiki guda biyu dake yayyafin turare suna gohe marbles din dake shimfide a qasan falon. Wannan din kusan al'adarta ce,kowacce rana sai anyima qasan falon irin wannan gugar sau biyu zuwa uku,wannan ya sanya qamshi sosai ya kama wajen.
Sun shaida masa tana samanta,sai yace su barta,ya sanya suka shirya masa abinci ya soma ci,sannan ya fidda wayarsa ya fara kiranta.
[4/18, 10:43 PM] C.E.O HUGUMA CLOSET: *_GUDUN ƘADDARA_*
*H U G U M A*
PAGE 20
Ba jimawa ta sauko tana fadin
"Wanne irin shashanci ne haka maina?,zaka taho ba zaka sanar ba?" Dan qaramin murmushi ya saki,har yanxu ama tana kallonsa ne kamar wani saddi
"Banajin dadi ne ama,hakanan naji inason zuwa na ganku". Fuskarta tadan nuna damuwa,taja kujerar dake fuskarsa ta zauna idanunta a kansa cikin kulawa tana tambayarsa meke damunsa?.
"Zazzabi ne sai dan ciwon kai bame yawa ba"
"Subhanallah,Allah ya sawwaqe,to ya jikin yanzu?"
"Alhamdulillah,da sauqi sosai"
"Ma sha Allah" ta fadi dai dai sanda wayarta ta dauki tsuwwa. Fuskar wayar ta kalla sannan a hankali ta furta
"Mariya?" Sai ta daga kiran ta saka a kunnenta.
Sallama ta farayi sannan sauran maganganu suka biyo baya,tun tana maganar a hankali har alamun fushi suka dan fara bayyana saman fuskarta,kuma alamu sun nuna ranta ne ya far baci. Dukka maina yana ankare da ita yana diban abincin kadan kadan yana ci yana nazarinta
"Shikenan na gode,Allah ya qara zumunci" ta qarashe fada tana katse kiran.
Iska ta furzar daga bakinta tana hade yatsunta waje guda
"Lafiya ama?" Ya tambayeta yana ture kwanon abincin daga gabansa
"Wato shi zumuncin yanzu haka ya koma?,Allah ya sani ina bakin qoqarina gurin ganin na gina zumunci me qarfi tsakanina da 'yan uwana amma kowa sai ya watsamin qasa a ido saboda Allah ya jarabceni da son 'ya'ya mata kuma bai bani ba....."
"Wani abu ya sake faruwa kenan?" Ya kuma fadi ransa yana sosuwa saboda yadda fuskar ama din ta sauya ta fara hada ja,alamun dake nuna inda zata samu sarari kuka ma zatayi
"Mun gama magana da mariya zata bani bintu,ina ganin kamar diyata take tunda dan uwana ya hanani ita din 'yaruwatace mace zatafi fuskantata,har daki nasa an gyara mata an zuba furniture da nayo order dinsu daga turkey,an mata dinkin dukka kayan da zata saka,na siya mata foam zan canza mata ecole duka a nan,na ajjiye mata driver personal,na gama komai cikin satinnnan nake shirin zuwa Nigeria na daukota,shine yanzun ta kirani take gayamin wai abbanta ya hana,kakarsu tace ba zasu bada ita ba" ta qarashe maganar da alama abun ya sosa mata rai sosai.
Kyawawan idanunsa ya lumshe yana jin ciwon abun shima,bawai kuma ciwon hanasu bintu bane,tunda ko ba komai,duk da auty mariya masu wadatane sosai suma din amma basu kama qafar ama ba,ama nada son yara da riritasu,cikin gidan kaf banda sultana baiga wanda baya cin moriyar ama din ba wajen kyauta da jan mutum a jiki,ya sani bintu din zata samu gata da kulawar da babu lallai ta samu a gidan mahaifinta. Bacin ransa na ganin damuwa me tarin yawa saman fuskar ama din,inda yana da hali da ya samar mata wannan abun da zai wanke wannan baqincikin da takeji a duk sanda ta nemi riqon diya cikin diyoyin 'yan uwanta bata samu ba.
Matsowa yayi sosai ya kama hannunta ya riqe cikin nasa,cikin tausasa murya ya soma magana
"Kiyi haquri ama,daga yau kiyi haquri kibar musu diyoyinsu daga yau,ni na miki alqawarin in sha Allah duk sanda nayi aure zanyi addu'ar Allah yayita bani diyoyi mata,zan fara addu'a tun yanxu,sannan na miki alqawarin ko diyoyi mata nawa na haifa naki ne har sai kince kin gani da riqon 'ya'ya mata". Wani qawataccen murmushi da ya bayyana kyau da sauran quruciyarta ta saki bs tare da ta sani ba
"Maina,ta yaya zan gaji da riqon diyoyinku koda taron arfa zaku haifa?,ai saidai naci gaba da addu'ar Allah yaci gaba da baku masu albarka ya kuma hore mana abinda za'a kula dasu" daya hannun nata itama ta dora saman nasa
"Na gode sosai,daga yau in sha Allah na haqura,zan kuma jirayi jikokina komai tsahon lokaci kafin zuwansu" Murmushin shima yadan saki yana jin dadin yadda maganarsa ta faranta mata.
Agogo ya duba sannan ya miqe yana cewa
"Zanje na karbo dinkunana ama"
"Allah ya tsare,kada ka jima kaga bakajin dadi"
"In sha Allah......Key din mota daya zaki bani aro"
"Ya kamata kayi zuciya kayi motar kanka mana" ama din ta fada tana dan